Chapter 50 Reading ABUNDA KE BOYE HN Novels

ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   50 / 88

147K to 150K   out of 262.2K words

karta damu zata duba mata awayarta....

tsabar fargaba ji tay kmar tace musu a'a ammi ta shiga schl portal din tace nafa taje ta dauko reg numberta da paswd atake taje ta kawo tanaji zuciyarta kmr zai fashe dan fargaba... mannuwa tay da jikin ammi tunda aka login suna budewa suka fara ganin As da Bs..A inta biyar bs inta hudu nd she came 4th

...kulthum tay wani irin tsallen murna ta rungumeta, tace oh my god congratulations ayana atsakiyar term fa kikaje??? da mamaki ammi tace masha Allah, wwoow my doter i dint expect this ayaana gaskiya kinyi kokari sosai
..zare ido kawai ayaana take tana musu yake duk tarasa dadi zataji ko fargaba she can clearly rmber how he said is 1st or nothing...suna cikin haka taji muryansa a kofa da wani irin sauri ta kankame jikin ammi karama tareda boye fuskata abayanta harya shigo ciki......sai taga bashi kadai bane, mujaheed yana zuwa ya kalleta yace "ayaana baban mu yana kiranki..come fast..


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[28/11, 20:20] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
Arewabook@surayyahms.

⏯️3️⃣2️⃣

Ayaanah ta ji zuciyarta ta tsaya cak lokacin da Mujahīd ya furta come fast din..sai Kafin ta ce komai, Kulthum ta kama hannunta cikin murna, Ammi karama kuma na murmushi, hanklin Ayaanah da zuciyarta gabaki daya baya jikinta duk murna da jin dadin sakamakon nan da akayi kalmar da ta tsaya mata a kunne guda ce “First… or nothing wanda ta san batakai ba,Sharadi ne, kuma ka’idarsa ce.

satar kallonsa takey har ya karaso ciki Kamar kullum, shigowarsa na ɗauke da nutsuwa da kamiya babu hayaniya, qamshin turarensa me tsada atake take ya mamaye wajen da sanyin dadinsa.

idonta na kallon kasa ayayinda kulthum ke rike da hannunta A hankali sukace mai "sannu da shigowa yaa."kallo daya yay musu ya amsa da kai snn ya wuce dakinsa, asulale suka bi bayan mujaheed kai tsaye suka wuce sashen anty safeera wanda bata saka komi aranta face harsaida suka isa..

mujaheed dake shirin wucewa dakin anty safeera yace "kuje falonsa a sama ki sameshi, kulthum zata raka ki..cikin sanyn nitsuwa ayaanah tace "toh" kulthum ta rakatan kuwa har sama cikin karamin falonsa da sallama me sanyi suka bude wata shirgegen green labulen ayaanah tay maza ta ɓoye fuskarta ata bayan kulthum jin yadda uncl moh ya kira sunanta da "ayaanah Dear" da wani irin fara'a tun kan su karaso..

suna gabatowa ta lura da akwai wani baƙon abu a tare da shi wanda box ne madaidaici an nannade shi da ribbon mai launin ruwan toka.
Baiwani tsaya ba bai kuma kalli kowa sosai ba sai Ayaanah.

tana dan dago kai Idanuwansu suka haɗu dajuna na ɗan daƙiƙa kaɗan, ganin tana jin nauyinsa da kunyarsa yasa ya ɗan kauda kai yana murmushi tamkar nawanda yake jin mugun tausayinta tareda jin daɗi alokaci ɗaya.

Har zata zauna kasa tafara gaishesa yace "aa karki zauna kasa zauna anan mana dear .ya mata nuni da soft chair da ke kurkusa danashi, respcfully ta zauna kanta na kasa ahnkli tace uncle ga ni nan naji kace na zo,kulthum ta matsa gefe, yana mai dan murmushi ya turo box din gaban ayaana" Ki buɗe,” kawai ya faɗa. ta kalle shi da mamki sai taga kulthum tana dan noding mata kai, hannunta na rawa ta bude gift box din ahnkli taga wani hadadden fancy set ne na Art supplies kmr colours, sketchbook, glitter pens da wani irin tsadadden Cute hair accessories da small girlish puzzle game aciki da wata nice hoodie dark red colour shima acikinn fancy kwalinsa.

..abunka da zucyar yaro tuni taji abun ya bala'in burgeta ta dago kai da sauri ta kalleshi taga yana murmushi ahnkli yace congratulations my dear result dinku ya fito ko? ahnkli tace eh amma...cikin katseta yace ai ni ban damu da nasara ajikin takarda ba, dake kawai na damu dan haka Ki kula da kanki snn ki ƙara dagewa kifi haka..ahnkli yace "kina da daraja fiye da wannan my dear.

shiru tay cikin rasa sanin me xatace mai dan ji tay kamar maganan nasa sun mata nauyi sosai, can ta dago da ladabi da jin nauyinsa a muryanta tace uncle nagode sosai Allah ya saka da alheri,in sha Allah zany kkri sosai nan gaba

yana murmushi...yace"nine da godiya..ya kalle yarsa dake tsaye yace nd you too baby kin yi kkri ko, i neva daubted you ure the best amma wnn karon gift na ayaanah ne ita kadai. da murmushin jin dadin kalamansa kulthum tace thank you soo much baba ai tay kkri mid term taje fa. ,yace yes she tried baby, dan shiru ne ya ratsa wajen after a while kafin nan ya sallamesu..

duka suka fito suna murna dakin kulthum suka nufa suka zauna akan gado suka hau bubbude gifts din for a while harta mance fargaban ibaad dake damun kwakwalrta suka kira sultana a waya sunata surutu kowa yay ma ayaana murna sukasa taji cewa ai bakaramin kkri tay ba haka ta rarraba musu wasu abubuwa daga ciki amma tace sai ta nuna ma ammi kafin ta kawo musu kowa tabashi, kulthum tana ta murna dan dama jan rigar sanyin ne yafi tsole mata ido kuma shi ayaana ta bata kyauta,.

harsaida suka gama kallon duka gifts din duka snn ta tarkatasu duka ta dawo dashi sashen ammi karama. xuwa tay ta samu ammi na zaune a falo ita daya da tulin murnan ta tazo da box din tace "Ammi..Ammi kigani uncle ne ya bani yace wai nay kkri...da fara'a ammi tace masha Allah ahh uncle dinkun nan ya kyauta mugani, da murna ta mika mata, ammi ta bude ta gaggani tace masha Allah, ayaana u tried, in sha Allah anjima zan miki abu me dadi kici ina fata kuma next time Allah yasa ki fi haka kkri, dan kwanciya tay ajikin ammin da murmushi me yawa tace Ameen ammi nagode in sha Allah zanzo first" daga nan ammi tajata suka je wajen hajya mairo dake kan shiri gobe jumaa zata kwana agidan bappa zaidu ana nuna mata result itama tay murna harsaida tasa ayaana kuka tana ce mata ai da tudu kike da ba haka ba..kinyi kkri sosai ayaana am, waye ma zaiyi tunanin zaki rayu batare da yar uwarki da mahaifyarki ba
..haka tasaka ayana tafara hawaye dakyr ammi karama ta rarrasheta, ana daf za'a kira magrib suka rakata kofa drivern bappa zaidu yazo ya dauketa ta wuce can gidan su ammi babba.

dawowarsu ciki bada jimawa ba tazo ta dauki rigar sanyin takai ma kulthum har dakinta acan tay sallahn magrib da isha suka sha nutella da cookie suna ta hira can kafin tafara tunanin gamuwarta da ibaad sai taji atake komi ya tsaya mata cak

mikewa tay tace ma kulthum zata tafi kawai sai gobe, agurguje ta sauka cikin sauri ta dawo sashensu dan karya kasance bayan isha zai tafi gida...

gabanta na wani irin faduwa ta shigo jin babu motsin kowa a sashen yasa fargaban ta ya karu tana kuwa lekowa ta kofarsa ta tsaya cak jin kamar an danna mata remote, ganin safiya tay a kasa a kofarsa ta waje tanakan kneeling tsabar tagaji hannun sai reto yakey a sama tanata matse hawaye

da saurin fargaba ta juya zata gudu taje wajen ammi karama
tana juyawa kuwa taji sautin muryansa frm no where...a adake yace"kee, ina zaki je.., a kangare ta juyo jikinta na rawa ganin fuskrsa ne kawai ya leko

suna hade ido yace" what are u doing here"..bakin ta na rawa rawa tace dama..dama..nazo
ince...ince..."cikin katseta da tsaki yace "just come in"..Da sauri ta gyada kai ta karaso da tsananin fargaba ta bude kofarsa a karo na farko dataga saman table dinsa a wargaje
ya aje katon white A4 ppers yana drawing wasu abubuwa ajiki

jikinta na rawa rawa ta taho dan tasan na biyu safiya tazo, ahnkli tabi ta tsare sa da ido baiko kalleta ba sai har da ya aje pencil din snn suka hade ido yace "what? cikin hadiyar yawu ta rusuna kadan da sanyin murya tace "Dama kulthum ne taxo dazu tace min wai result dinmu ya fito..yace "and so? kmr zatayi kuka tace "shine nazo na gaya maka" yace okay...did u come first?.
maqudan hawayen datake dannewa ya sauka a raunace tace "a'a..i came fourth"yace "hmm 4th, shine akace kizo kimin kuka? xatay mgnan cikin katseta yace.. naji.. naji.."uve tried. but not enuf to receive a congratulation from me

..adan shagwabe tace but i will try hard next time i promise.

girarsa na sama adage yace karma kiymin alkwarin da bazaki iya dauka ba i told u, u were not dat smart saidai a can kauyenku , u came mid term nikuma i came 2 weeks to exams in my schll but i came first, kije ammi zata nuna miki ai zaki gani..kinzo kin same wanda suka fiki ilimi ko? hmmm uve a long way to go yarinya...hawaye na kan zuba a idonta cikin turomai baki tace"i will try next time... yace okay, then dont come to my room nd cry again untill u come first i dnt walk with not sooo smart ppl.

duk da serious face din dayasa har ranta she knw he is just teasing her...saidai sosai mgn nasa yasaka takarajin dolene ma ta dage ta zo na daya kodan ta kureshi...

shirun datay tana kan raya hakan aranta yasa ya juyo suna hade ido yace "inkuka kikazo yi anan ki tashi ki tafi kiban waje...dama uban waye yaje miki kije kizo na hudun

mikewa tay jiki a sanyaye taxo daf dashi da wani irin sihirtacn narkakken murya tace toh kay hqri mana yaaya..ainace zan gyara.

yace 'naji"..ya dauki hankynsa ya bata yace "share hawayenki sai ki tayani tattara wannn papers din saiki tafi .

hakan dayafada yasa taji zuciyarta yay sanyi sosai, dan tagama tsammnin tsawa da hukunci me tsauri zai dauka akanta sai taga ba haka ba, duk gidan ma shine kawai yasaka taji kmr she is deeply challenged to do better next time sosai tasa aranta zatay kkri nan gaba. tana gama share hawaye da hankyn taji gabaki daya ta dawo tana qamshi irin nasa.

cikin sanyin nutsuwa tafara tayashi tattara drawing dinsan kallonta yakeyi amma bazaka taba sanin kallonta yake ba, her cute eye balls were fixed on his bold italic fine hand writing dinsa wanda da alama ya dauke mata hankalinta sosai...

har saida suka gama snn ta daga ido suka kalle juna sai kuma taji bakinta yay mata nauyi tana son tagaya masa abunda uncle moh ya bata amma tsoron me zaice mata yasa ta kasa iya bude baki. har ya dauke idonsa akanta ya tattara jakarsa yazauna ya saka takalminsa ya gyara room din sharply ya kamo hannunta suka fice atare..

suna bude kofa safiya dake kneeling ta dinga satar kallonsu baki bude dan tagama daukawa yau zaiy ma ayaana dukan tsiya,sai taga har wani kama hannunta yay suka fito atare, wani gulluton baqin ciki taji ya rike mata wuya, ita fa na biyu taci akasata kneeling din nan bayan uban masifa da zungurin data sha. ko kallonta baiy ba kuwa suka wuce ta da ayaanan, suna kaiwa falon ammi ya sake mata hannu ahnkli yace "go to bed" ni zanje gida, hawaye taji na nemn cika mata ido sai ta shanye tace "okay..gud nite.. cikin kwayar idonta ya kalla yace "thanks" kafin ta dauke idonta anashi sukaji motsin ammi da sauri ta juya ta wuce daki har ammi ta karaso sukay bankwana da shi ya wuce ya tafi.....

tun bayan tafiyarsa harta koma dakinsun ta kwanta tunanin kalamnsa da fuskansa kawai takeyi jin wani birkitaccen shauqin yadda zuciyarta ya riƙeshi da muhimmaci wanda ita kanta bata san ya zata fassarashi ba batamasan meye takeji ba
...har tay bacci safiya bata shigo ba sai wajen around 11;30 na dare da ammi tazo ta sameta a tsugune dan tsabar tsoron ibaad datake ji har yanxu tanakan gyangydi wajen datake kneeling din bata tashi ba fitowar ammin ne yasa ta fatattaketa ta wuce daki taje ta kwanta

da tsaki ta shigo dakin dan tsabar haushin ayaanah datakeji haryau bata taɓa bari sun kwana kurkusa da juna ba kowa baccin sa yakeyi acan can edge din gado da safe ma suka tashi basuce ma junansu komi ba inba wani rikici ne ya hadasu ba. yau sosai tsanan datake mata yakara zafafa dan haryau batagama jin haushin yadda sultana take makalkale ma uwarta ba yet ayaana is just another pain in her ass, sai takeji kmar ma gara sultana, soyayyr uwarta kawai ta karbe mata, lamarin ayaana yafi ci mata rai cos it pains her alot to deeply feel in her heart that yaa ibaad yana bala'in fifita ayaana fiye da kowa, inba haka ba ranarfa ta musu laɓe taji duk sharudan daya saka mata akan karatu, amma yama za'ay ta karya sharadinsa na zuwa first snn ace bai dake ta ba harma ya wani kamo hnnunta su fito waje tare...wann abun sosai yayi ma safiya zafi har saida tay kukan baqin cikin ayaana kafin tay bcci.

bayan faruwar haka gidan bai kara zama lively ba sai ranar asabar tunda ayaana da kulthum da sultana suka hadu duniya yay dadi. gashi ranar ne aka kawo sabbin dinkuna na atamfofi da laces 20 pieces masu shegen kyau da tsada da ammi karama tay odersu wajen mum ramlat collection duka aka dinka ma ayaana

ranar asabar din tamkar ranar sallah haka taji aranta ganin yadda kawayenta suka mamayeta suna ta gwada sabbin kayanta a dakin ammi karama kowa yana mata murna suna dariya kmr sun mugun jimawa da sanin juna. she bacome so overwhelmed with joy da dan uban gatan da ammi karama ta nuna mata. wknd din yay ma su ayaana dadi, kowa yazo anci abinci anyi raha zainab arifah ne kadai haryau bata zago ba wanda hakan sosai ya fara sosa ma hjy mairo zuciya duk ta dauka ko akan ayaana ne zainab din tay fushi.

haka ta tursasa anty safeera ta kira mata ita awaya wanda dakyar ma ta dauka suka dan yi magana ta dinga ja mata aji amma ko ajikin ta tsohuwar nan tay ta bata haquri akan karta yanke zumuncin su sabida abunda ya faru tsakaninta da ayaana, bata kuwa wani bata kwakkwran amsa ba har suka gama wayar

monday nayi kowa ya shirya aka wuce schll wanda ya kasance sabuwar yanayi ga ayana dan da wani irin karfin gwiwa tafara wnn term din duba da har anyi aproaving admission inta within next four month zata samu sabuwar uniform na jss class itama. suna farawa ta dukufa tare da bada hanklinta kawayenta na schl din ma tafara baya baya dasu sai in ayi break su hadu da sultana kawai suci abinci.

satin gabaki daya was fun face saida sultana tabata labari cewa ai uncle moh yakama kulthum da hoodie data bata kuma ya mata fada sosai yace kar ya sake bawa ayaanan kyauta snn yagani ajikinsu..

bakaramin sanyin jiki hakan ya bawa ayanah anar suna komawa da driver ko sashen ammi karama bata wuce ba ta nufi bangaren anty safeera

samu tay dukansu biyu suna zaune kulthum tanacin abinci da alama itama shigowartan kenan, tunda ayaana tay sallama ta gaishe da anty safeera duk sai ta rasa me zata gayawa kulthum, face saida kulthum din ta haura sama taje ta dauko mata red hoodie in da sakin fuska tace "dama innay wanka ne zanxo
nakawo miki rigarki kiy haqri baba na yace min kar ya sake baki abu na karba..muryan ayana kmr na wanda zatay kuka tace "kai kulthum amma ai kyauta na baki meyasa bakigaya masa haka ba dazu
hakama fa sultana ta dawo min da ribbons dina wai baku so, tana fadin haka hawayenta ya fara xuba a idonta.....cikin sakin murmushi anty safeera ta jawo hannunta tace "haba ayaana, karki dauki abun haka mana meye na kuka, ai bawai sunki abunki bane nima fa ina bayan babansun this gift is specially for you...su ai anjima ana siya musu, bekamata su karbi naki ba shiyasa ma yace musu su dawo miki dashi...

jiki a sanyaye kulthum ta dafata, ganin ayaanan na hawaye sosai tace haba ayana na ai zan dinga sawa aro kinji! fadin hakan da kulthum tay yasa ayaana taji dama dama tace toh shikenan zan aje miki

shafa kanta anty safeera tay cikin lallashi tace "ure very kind my dear...yanxu kije ki cire uniform kici abincinki karki damu babu komi kinji? hawayenta ta share ahnkli tace toh anty sai anjima..ta gyada kai,suka bata red hoodie in ta karba..da kallo suka bita tana wucewa saiga mujaheed ya sauko ganin yadda sukay zugum da tausayin ayaana ya saka ya tambayesu what is going on, anty safeera ta hau gaya masa, kyabe baki yay baice komi ba cos if feels odd for him da babansu yafara behving haka, dan gaskyr shine ko su yayansa baiya saya musu kyauta..saidai dake suna zuwa first din kowani lkc yakan bada anty safeera kudi ta saya musu duk abunda suke so amma bai taba shida kansa yaje kasuwa ya siyo musu kyauta ba. da tausayi anty safeera tace musu ai ayana tamkr marainiya ce tunda babu uwa babu uba ynxu atare da ita, tace hala shiyasa babansu yake son yamata abubuwa da zaisaka taji kamr ba a wareta agidan ba,..da wann furucintan yaranta duka suka kara fhimtar haka aka bari acewa tausayi ne da kuma taimako yasaka yncle moh yake ma ayaana abubuwa nadaban.


after few days komi ya dawo normal ata ko wani bangare, karatun ibaad yanamai kara zafafawa, har ya kaiga an fara rage musu hours da sukeyi a private club dinsun dan ya dinga samun cikakken nutsuwa. basu kara jin duriyar zainab arifah agidan ba har saida tacika wata daya har da sati snn ta shirya ta sako wata abaya me kyau na mutunci taxo gidan wkends daga ita sai driver, tun ahanya ta dinga kkrin kawo duka tunanin irin magnganun da suke yi da ruqayya insunje makaranta wanda badan ruqayya tayta bata shawara yadda zatay ta dawo da mutuncinta agidan ba da kwata kwata bata san ya zatay ba.

mahaifyar ruqayyar yar siyasa ce babba,gata dai yar 14 going to 15yr amma tunanin manya ne da ita sosai tafi nala nesa bakusa ba dan nala banbamcinsu da zainab Arifah kawai dan gata ne da kuma

50 / 88