ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 88

102K to 105K   out of 262.2K words

suka zauna sunaci atare suna hirarsu na yaranta


ammi babba bata farka ba sai can wajajen 4.30pm agurguje taje tay wanka tay sallahn asr snn tasake rabza wani uban kwalliya ta canza kaya ubansu da niyyar zuwa warming in abinci dan tasan duk tsiya 5-5:30 haka bappa zaidu zai dawo.

koda ta shiga kitchen taga yadda aka debe naman bakaramin baci ranta yay ba duk ta dauka me aikinsu ne siddika ta kwashe mata nama ranta a dagule tay warming tashirya tray wanda zata kai dinning sai kuma ta fasa tawuce sama da niyyar zata gwada kunna wayarta tunda yamma yayi.


tana kunna wayar kuwa abun afarko datagani shine sakonsa wanda atake atake idanunta yabi yay jazurrr da fushi dan har wani hucin bacin rai takeyi tamiƙe tsaye ta wuce kitchen din danta kwashe abincin kawai ta zuba a fridge kafin ta dawo daki taci kukanta na uban asarar effort da lokacin ta datay wajen tsara masa abinci .

aganinta wann ma walakamci ne sosai da zai wuce har wata kasa bai sanar da ita ba kuma tunda taji batun kungiya tasan babu shakka da ammi qarama akaje

har wani duhu duhu take gani akan hanyarta na isowa kitchen lokcin kuma ayana tashigo gidan da sauri debo ma sultana ruwan sha kenan sabida shakewar datay awaje, tazo da sauri harta debi ruwan a cup zata juya suka ci karo da ammi babba abakin kofa

gabanta yay mummunan
fadi ta saki ruwan akasa ganin wani irin kallo da ammi babban tamata musmn ganin hannunta baja baja da maiko da wani irin hatsala tace kan uban can... dama kece kike kwashe min nama na kinaci dan bura ubanki????

hawayen tsoro ya fara zuba a idon ayaanah zirrr bakinta ya fara rawa rawa zatay mata bayani, da dukkan fushin datakeji ta daga hannunta sama zata falla mata wani hatsallalen mari mai cike da tsana tana daga hannun kuwa taji an kira "mummy" da karfi ata baya dasauri ya shigo ciki tare da riƙe mata hannu..


SHARE.......
[19/11, 17:26] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ⏯️2️⃣5️⃣💫
Tunda taji anrike mata hannun tatsaya cak tareda juyowa da uban sauri, wani irin kallon juna sukeyi har ya shigo cikin kitchen din tana ganin ibaad ne tawani fauce hannunta anashi dawani irin hucin tsana me zafin gaske, ibaad yay sama da idonsa yana kallon kwayar idanunta bayabo ba fallasa yace mummy lafiya meye faru, metayi kuma?

wani irin zazzafar huci ta saki tanamai hararsa upandan tunma be gama rufe bakinsa ba cikin hatsala tace "me kuwa zai faru banda satar nama da na kama wann walakntacciyar yarinyar tana min...

da mamaki yace sata kuma amma mummy..sai kuma yay shiru baice komi ba ya juya yana kallon ayaanahn data dan sunkuyar dakanta can kasa tana zubda hawaye sosai jikinta na mugun rawa rawa.

muryansa na fita ahnkli salon rashin son ya tsoratata yace
"..ke kuma meya kawoki nan?

lumshe idonta tay dan bata san da kuka ya kufce mata ba ahnkli muryanta na rawa tace "ruwaa..a kawai nazo debewa ni wallah ban mata sata ba

."..zai magana da mugun sauri ammi babba ta karakawo hannu zata jawota gaba danta falla mata mari yasake yin wuf ya rike hannun yace mumy pls wait mana let her answr all the questions dan Allah,"...yana sake mata hannun ransa abace yakara kallon ayaanah yanamai tuhumarta akan abunda ya kawota kitchen din,..duk ta rude sai takasa bashi kwakwarn bayani tana kuka itade cewa take bata dauka mata namanta ba"..

a mugun masife ammi babba tace "ibaad bangane kana wani tambayrta ba, nayi maka kama da wacce zata maka karya ne? okay naa pls lets look at her hands tunda baka yarda da ni ba..ahaukace takamo duka hannun ayanahn tanamai nuna masa maiko maikon naman, amugun zafafe tace kagani ko? inda ba namar tazo sacewa ba ta ina wann maikon zai fito? toh wallh walh saina miki shegen duka, dan ni gidana ba amin sata, kuma ba'a min karya, saidai kikoma can kauyenku inda kika fito da wann mummunan dabiar taki ta mayunwata barayin abinci, ai inma kwadayi kikeji saikizo kicemin wanda nabakin ne bai isheki ba, i will undrstnd you dan nasan babu a house, gidan miji babu tabbas, makwabta sai ɗaiy-ɗaiy..amma tunda kikace ke satar abinci zakiyi agidan nan toh wallah saina ci ubanki kuma bazan taba kyaleki yauba har sai anbiyani nama na da kikaci...

ayaanah tafara kuka sosai har tana jan shsheka cikin rudewa tace "Umman sultana kiyi hakuri ni wallah ban miki sata ba ruwan sha fa kawai nazo debawa zan kai ma sultana..

tace "da Allah kimin shiru, bakin samu ana bin bayanki ba?last week kinmin asarar dumbin kudina anbi bayanki, yanxu kuma wato bari ki tsiromin da halin bera to badai agidan nan ba, yau ko abiyani ko kaf masu daure miki gindin suzonan sugani snn suji cewa ke babban barauniyace kuma makwadaicya...

kuka kawai ayanah takey dan duk wyannan maganan ji take kamar sun mata nauyi..

ibaad yace" mummy dan Allah kiyi hakuri..if u cant let her explain herself properly atleast let her apologise to u"

ya kalle ayanan ransa a mugun bace yace "ke kuma mekike jira da bazaki bata hakuri ba tunda ai naman kikazo sata saiki bata haquri
...ayaana ta kara fashe masa da kuka batace komi ba ta tsuguna kasa cikin masa biyayya tace "yace ince miki kiyi hakuri. wai bazan kara ba..

ammi babba tace kan facalin bala'i wato shine ma yace kice min inyi haquri?kuma ma bazaki kara meye ba..ki fada da bakinki...kowa anan ya shaida cewa ke barauniya ce

ihun datake mata yasa sultana tafara shako muryansun daga kan stairs dan already tafara tahowa dubata, sai ta tsaya cak idonta ya ciko da hawaye ata bakin kofar kitchen din tanamai jin bakin tsoro karta shigo ciki asata ta fadi gaskiya yaa ibaad yasan ita ta saci naman ya casata...

ihu ammi babba take ma ayaana akai tana cewa ki fada masa da bakinki cewa sata kikamin..ke barauniya ce..say it ryt now!

ayaanah tana kukan sosai da wani irin taurin kai tace nifa wallah ban miki sata ba..ni ba barauniya bace...ai ban dauka miki abunki ba...

da mamaki ammi babban tace ohh dan ubanki karyan zaki ci gaba damin? toh wllh inhar baki furta cewa kinmun sata agabansa ba yau dinnan sai anbiyani nama tareda dukkan wasu abubuwana da kike min asararsu ai ba ubanki bane ya bani su...

haka kuwa ayaanah taki sam ta furta komi sai kuka takeyi daga tsugunen daf da shi
ayayinda kukantan yake daga masa hanklinsa yanasamai rauni taciki bana kadan ba..

wani irin ruwan balai take saukar musu tana cewa ''ko abiyani nama na kona miki dukan mutuwa, shegiya makira kawai barauniyar abinci, ke abubuwan ma sun miki yawa wai shege da hauka...if u want me to forgive u just open ur mouth and admit it cewa ure a big thief..ole..oloriburuku barauniya...young anini...

tanakan maganan ayanah na tsugune agabanta tanakan kuka itama sam takiyi shiru sai cewa take ni ban miki sata ba wanda hakan bakaramkn dada mugun hatsala ammi babba yakeyi ba...

can cikin lumshe tare da budewa da comanding voice dinshi me sanyi yace mummy please is enuf. fuskarsa a dore yabi yakalle ayaanah yace ke tashi kibar nan wajen ynxn nan..

da wani irin mugun gudu ayaanahn ta miƙe daga tsugunen ta fita waje tanata kuka sosai harta tawuce sultanan abkin kofa ma bata sani ba, can waje gaban pool din taje ta tsuguna tanata kuka tanajin kamr ta gudu ta koma wajen ummanta

ruwan masifar ta dawo akansa tana kallonsa kamr wacce zata falla masa mari tana huci "'and what was the meaning of that ibaad? kai waye da zaka ce min enuf agaban yarinya
...bayan kana kallo yarinya tana karya kiri kiri zaka kuma wani ce mata ta tashi ta tafi dan tsabar ka rainani ko? hmm ko da shike ba lefinka bane, uwarka ai ita take mulki agidan nan shiyasa kaima kaje har kauye ka kawomin wata sabuwar annoba fitinanniyar yarinya barauniya, wacce a kwana biyu kawai da tazo saida tabarar min da abuna dat is worth 10million naira, yau kuma gashi tahau tsince min nama acikin abinci..

toh wallah wallah tunda abun naku rainin wayo ne ko ka biyani kudi na ko in ma yarinyar nan dukan kudi na inyaso saika kira uwarka kace mata tasaka bappanka yasake ni yau ya aurota..yan bura uba kawai macuta...inka ga maganan nan tawuce toh wallh biyana akayi inba haka ba kuwa saidai kafitar min da barauniyar nan agida na yanxu, ni bazan iya ba, ga asara, ga sata da karya, ga uban raini, haba da wanne zanji, inde bazaka biya ba tou muzaba mugani saidai in bazan kara hada ido da yarinyar nan agidan nan ba wallh sai na mata dukan million goma tare dana kudin nama da sata..


sosai idanunsa yay jaa yana jin ammi babban harta gama balbalin bala'inta akansa

muryan sa adan dakile yace mummy toh kiyi hakuri.. azafafe cikin katsesa tace wallah ni ba uwarka bace dan kuwa bakasan darajata ba..

cikin lumshe ido da budewa yace okay fine nawa ne kudin naki. i will pay u back..amma dan Allah karki tabata...her medical condition is quiete...

tace "i do not care abt that stupid conditon of hers, banason ji, in taga dama ta mutu mana nina kawota duniya ne ehhhh?..aini bakasan halin da tasaka ni aciki ba dake ni ba uwarka bace duk bai dameka ba..if u want her to breath in dis house u shud just pay my money ryt now.

ahnkli kuma a dakile yace okay..shikuma naman nawa taci miki..

....cikin yatsinawa tace dubu dari cass na saya turkey dina, kuma duka za'a biyani...baice mata komi ba yaciro babban wayar samsung dinsa daga cikin aljihunsa ya bude daya daga cikin microfinance app dinsa da kwanan nan akayi legalizing masa yasa biometrics nasa for swift transfer, acct din na buduwa Allah yaso shi sai yaga cassh limit din transfer dinsa ksan 15million naira ne kacal sumwhat beyond what she is even asking him for.

idonsa nakan wayar yace"wani banki ne?

wani rau tay da idonta looking desperate nd very wicked babu dandanin kunya acikin kwayar idanunta tace masa" "zenith bank..yace ok acct number, acikin sauri tana yatsinawa tahau gaya masa digits inta yana rubutawa har snn full sunanta ya fito atake atake yasaka mata cak cak kudinta dats 10million 100k yana gama nuna mata receipts taga kudin yashiga atake tajaa masa wani dan banzan tsaki

tace..mtsw aikin banza aikin wofi,.. ka kyauta makanka, danni wallah gaba takaini gobarar titi a jos, daga nan inkunga dama kucigaba da daure mata gindi tana abunda taga dama agidan nan nide wallah bazan taba daukar wani asara ba...nd pls if u want to test my patient ibaad kaje kadau wayarka ka gaya ma kawunka ko uwarka cewa kabiya ni kudina, nikuwa zan dawo maka da kudin amma wallah wallah ibaad, duk abunda nazo nayi ma yarinyar nan kasani kaine ka jawo.

wani uban tsaki taja masa snn tabarsa awajen yana tsaye baice mata uffan ba cikin shanye bacin ran dake cinshi a kirji yafito yana tafiya calmy da duka hannunsa acikin aljihun sa,yana steping wajen kitchen din kuwa yakalle sultana agefe ta rakube da jikin bango tanata matse ruwan hawaye zuciyarta na bugawa da sauri sauri

suna hade ido ta dan firgita, fuskansa a mugun daure yace "ina ayaanah take?muryanta na rawa tace tafita waje inaga tana can wajen pool tana ku...
...tun bata karasa gaya sauran ba yadauke kansa yanufi wajen pool din shima walking very gently kamar ba abunda ke damunsa

samu tay tadukunkune kanta waje guda tana rabza uban kuka, dan babu abunda takeji arnt kamr ta gudu taje wajen ummanta ynxu.

kuka takeyi abar tausayi tabi tacusa kanta atsakankanin cinyoyinta har ya iso wajen bataji steps insa ba saida taji qamshi tare da dirar inuwarsa akanta snn ta dan dago cikin sauri, suna hade ido tay maza tamiƙe tsaye da hawayen a fuskarta, jikinta a sanyaye sosai. shide baice mata komi ba sai tabita tsuguna kasa agabansa da ladabi itama tay shiruu.

idonsa akanta yace keee kin taba cemin kinason kici wani abu agidan nan na hanaki?

cikin giragixa kai da muryan kuka tace mishi aa..adan masife yace toh uban meyesa zaki je har kitchen inta ki daukar mata nama, ke kika aje ne da zakije ki dauka? nd when has dis nonsense start..

hawaye na zuba a idonta tace wallah ni ban dauka mata komi ba..

yace "Dont u dare lie to me.

jin yadda yafada hakan da bacin rai yasa ta kara fashe masa da kuka me sanyi

cikin controlling emotions dinsa yana kallonta anitse yace "inkin san kinyi abu marar kyau, just admit it.. bawai kina yin karya ba. dan da ace baki dauka ba ta ina har hannunki zai samu maikon namanta?ni bana son karya. i hate lies in any form...

tana girgiza kai tace amma wallah ba karya nake maka ba..

batare da ya daga maya murya ba yace ohhh just shut up ina magana caraf kema kina amsawa irinke gaki me taurin kan nan ko? to ai me taurin kai baya sata..dan shiru yay.. snn yakuma cewa kee kalleni nan. hawaye na zuba a idontan ta dago ido ta kallesa "yace kinaji, araunce tace masa ehh..

da wani irin stern voice yace dont you ever..kar inji ko na sake ji ko ma sake ganin kin sake taɓa abun wani, inde abu banaki bane just take ur hands off it idan ba hakaba nidakaina zan miki shegen duka agidan nan..nd when ever ure wrong just admit it, nd shut up...ki tashi kiban waje kar kuma na sake ganinki kina kuka anan wajen....


tana zubda hawaye sosai ta mike kanta na kallonn kasa jikinta a sanyaye ta doshi kofar main mansion din tana budewa ahnkli kuwa caraf suka hade ido da maheer tare da sultana suna saukowa kusan atare..

wani cak ya tsaya da sultana abayansa dan already yazo ya sameta tana kuka anan ya tuhumeta shine ta gaya masa cewa ai mummyn su ne tay ma yaa ibaad da ayaanah masifa wai akan dan ayaana ta dauka mata namanta a kitchen ynxu..

cikin idanunta dake fidda hawayen ya kalla tay saurin sunkuyar dakai kasa, tuni jikinta ya bata hala shima yaji komi shikennn yanxu kowa zaina mata kallon barauniya.

wani sabon kuka taji yaxo mata batace mai komi ba ta wuce sama da sauri tay sashensu tanajin nauyi da kunya sosai ..

tausayinta yaji ya kamashi da can har zai fita waje ya same ibaad din dan yaji sauran bayani saikuma ya fasa kawai yabi bayanta dan ya lallasheta

shortly after sun wuce sama shikuma ibaad ya dawo gidan room dinsa direct ya wuce ya zauna abakin gadonsa jin kirjinsa na masa zafi sai ya shafa fuskansa ahankli cikin rasa gane abunda yake masa
dadi. cikin raya wani abu aransa ya dauki wani sabon atm card dinsa da ake yawan saka masa school fees dinsa aciki ya saka a wallet dinsa kafin nan yabude closet dinsa ya canza kaya zuwa wasu casuals masu kyau snn ya dau key din mota da sauri yay waje, within few minute yay driving kansa out of the mansion zuwa wani katon exclusive unisex boutique...

daga dakin kuwa sultana sam takasa zuwa kusa da ayanah sabida guilty consience najin cewa itace me asalin lefin ita sato naman sukaci tare, kuma har ga Allah tana tsoron ta fadi gaskiya agaban yaa ibaad sabida bata kaunar ya bugeta ko ta shiga red list insa na makaryata agidan. she cudnt help but to feel guilty nd sad, agefe taja ta tsaya tanata satan kallon ayanah yadda ta matse kanta acan dungun gado tanata kuka ahankli

maheer ne ya nufo inda take yana kallonta da tausayi har ya zauna agefe daf da ita bata dago fuskarta ba.

muryansa na fita ahnkli da sigar lallashi yace "pretty one, zaki iya min magana "can we talk? wani uban shiru ta masa tanakan kukanta saida yakara memeta hakan snn ta gyada masa kai yana murmushi me sanyi ya kara matsowa daf da ita ahnkli yace toh prettyna pls gayamin meyafaru mana, ko ibaad din ya miki wani abu ne?

idanunta na kallon kasa suna fidda ruwa ahnkli cikin muryan kuka tace"..aiyaqi ne yaji abunda zan fada, yace wai na mata sata yanata min masifa kuma wallah ni banmata sata ba..

jawota yay jikinsa yace shuhsh its okay, kidena kuka hakan nan kinji ko, ai sultana tagaya min iya abunda ya faru..so just chill ,ire iren wannan kananan mistakes din dama are bound to happen..shima i will talk to him zai gane cewa ba halinki bane its just a mistake ko?

tana sharewa hawayenta tace "nifa banaso ka gaya masa komi ai ya riga yamin fada kuma nace masa bazan kara ba, kawai kabarshi .nide tsakanina da Allah ai nasan ban mata sata ba..

yace hakane pretty one nd dats what matter ynxu dai kidena kuka kishare hawayenki kinga ankusa kirar sallahn magrib ni zanje nay alwala then we wll talk later ko?.

ahnkli ta gyada masa kai tanata mamakin irin kirkinsa harya fice bata dena kallon inda yabi ba..

yana ficewa a dakin wani irin shiru ne ya ratsa tsakaninsu da sultana..haka kuwa basu ce ma junansu komi ba, ayaanah tagama share hawayenta ta tashi sum sum ta shiga bayi domin yin alwala...cikin rasa nay sultana sai tafice a dakin ta koma can dakin quest dinsu tay nata sallahn awajen ta cigaba da zama dan batasan ta ina zata fara bawa ayaanah haquri ba..she neva had any close friend or sister, duk wnn abubuwan datakeji na quilt da tsoron fadin gaskiya danta wanke wata yau ne tafarajin jinsu aranta dake duk zamanta da causin sisters din nata baifi insunje weknds a family house ba kuma dama da kulthum kawai tafiye yin magana.


Dagata dayan bangaren kuwa tun biyar da rabi zainab Arifa tagama daukar wanka ta saka wata xpensive saudi arabian abaya classy handwoven frm safiya abdallah of saudi, shikadai kawai ta siya jiya da suka dawo daga 5days business trip to paris din da sukaje ita da babanta, daga wnn bakin abayan sai sabon bag pack dinta na school data dawo dashi, she feels like she needed to buy clothing gifts nd more chokolates da zata bawa kawayenta rukky da nala tsaraba dan haka yamma liss taci wani irin kwalliya da sabon abayan ajikinta,only herself and her closest two maids wato elizabeth da aqeela zasuje wata private boutique dan ta siya kayan tsarabtanta acan.. daga ita sai driver a katoton

35 / 88