ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 88

18K to 21K   out of 262.2K words

sai ta jawo ayaanah zuwa zauren gidan ko gindin bishiya inda take koyawa sauran yaran anguwar wanda iyayensu basuda halin sakasu a makarnta karatun qur'ani dana bokon sama sama ayaanah tana tayata.

hajy mairo mai tuwo ce ta dada daure mata gindi, dan ita macece me kaunar taga yaro karami mai dumbin kwazo tare da son kawo babban cigaba musmn ma ga dumbin al'umma, riƙe ƴayan taawure kusan abun alfahari ne agareta duk dama riketa kawai tay basu haɗa jini ba, duk safiyar Allah sai sun sakama inayah Albarka a rayuwrta.


kwanaki basu karya suna cika wata biyu sharp a tudu aka fara batun exams dinsu ayayinda shaƙuwar ayaanah da inayah yake cigaba da burge kowa dan babu wanda yasan halin ciwo da inayah take ciki kamar ayaanah, duk hanklin taawure yafi ta allaka ne ga shirin komawar su gida can kauye majiya sabida nan da sati uku taji labari cewa mijinta juma zwi dawo, at same time tanata kkri wajen kare sirrin ƴayanta, ko kadan bataso ace ankai gulman yaranta garin majiya musmmn ma da inayah tay kaurin suna kwana biyun nan, duk inda taje zakaji ana kiranta gwarzuwan tudu, sabida aikin koyarwa datakey wa ƴaƴan marasa karfi wanda ya jawo kusan babu wanda baisan sunan inayah a tudu ba.

babu irin addua da fatan alheri da bata samu daga bakin mutane. matsalarta daya ne wann ciwon ciki me tsanani dayake cinyeta ahankli ahankli, an shiga satin jarabawa ne amma bata samun isashen bacci sabida zazzabi, gefen cikinta yafara kumburi yana tauri tauri taciki, wanda ko tsugunawa tay ko mistakely ta taɓa tawajen kumburin cikin bakaramin zafi takeji ba. ahaka kuma ta dinga dauriya har suka fara rubuta jarabawa, hanklin ayaanah bai fara tashi ba saida taga kasala, rauni da rashin ƙarfi ya fara nunawa sosai ajikin addanta. ranar tana kuka tace addah bazan iya ba kawai zan gayawa ummah inyaso akaiki asibiti, amma inaaa, haka inayahn taki barinta tace tabari sugama jarabawa, tay mata alkwari ita dakanta zata faɗa musu komi.

soyayya da kulawa na musmmn ayaanah take nunawa addanta dan duk tafi kowa sanin halin ciwo datake ciki, ayan kwanakin nan daga sun zauna zakaji inayah tana mata nasihohi masu shiga jiki......


kano..9.30pm


wajajen ƙarfe tara na dare Rahma exclusive private Hospital Kano.
karamin asibiti me zaman kansa da akayishi domin ƙrban emergency na masu hannu da shuni dan yawanci turawa ne da indiyawa suke aiki anan asibitin wanda acikin masu kudin ma bakowa ne yake da arzikin kawo jinyarsa anan ba.

security ne kusan guda hudu sunsha uniform agaban wata kofa nan cikin special ward na private consultation dake nan ne kusan ƙebetaccen waje ne na manya.

babu wani hayaniya bare wulgawar wani mutum, koina tass yake da kayan alatu da naurorin kiwon lafiya na zamani kamar ba a nigeria kake ba.

Daga cikin Room 7 iyaka Sautin ƙarar “oxygen machine” da ƙamshin magani shine ya cika ɗakin ayayinda Zainab Arifah take kwance shame shame akan gado an lankaya mata na'urar taya nunfashi da kuma drip a hannunta na hagu.

idanuwanta a lumshe suke tamkar wacce take cikin nisan bacci saidai ahakikanin gaskiya babu abunda yake yawo acikin zcyrta da kwakwalrta face tunanin yadda dan uwanta ibaad zai zamo nata har abada

wanda tun bayan zaneta dayai basu kara samun wani ganawa dashi ba intaje gidan ta gaishe sa zai amsata normal saidai tunda yafara karatun jamia rashin yawan ganinsa da kuma samun sakin fuskansa sosai agareta shine yafi komi daga mata hanki yanzu. tsakaninta da ibaad a shekaru baifi ace 4-5yrs ba, tunda mujaheed dake sa'an ta agidan dai 4yrs 11 month yabata baima cika full year ba kuma tasan akalla dai shekara hudu ne cass tsakanin ibaad da mujaheed. ita bata ga wani dalilin mugun jan aji da miskilincin da ibaad yake mata ba shiyasa ma haryau take ji kamar bazata taba iya kiransa da inkiyar yaya ba.

gani take tana da komi na duniya kama daga kyau, ilimi, gata, da kudi to menene kuma zai saka wani ɗa namiji ja mata aji?

takaici take jin ita tuna kamar ibaad bai wani girmeta cancan ba nd she want noting frm him face for him to be free with her, tanaso taga tana iya masa magana a duk sanda taga dama, intace mai yayi mata abu shima marmaza yay, kamar yadda kowa yake haba haba da ita saidai amma duk ta tuna cewa yataɓa dukanta last time data gwada jan hanklinsa da maganan soyayya sai taji duk takara shiga damuwa sosai

gashi har ilayau tana mutuwar sonsa aranta wani bin inta zauna tana tunanin rasashi sai dai kawai aga numfashinta yana sarkafewa...

yauma kusan abunda ya afku kenan wanda har yajawo akayi rushing inta izuwa emergency, iyayenta duka biyu suna tsaye agefenta idonsu cike da damuwa gashi sam taki tabude idanunta barema har susamu dama su tuhumeta abunda yake damunta dake yanxun tadany wayo tamugun kwarencewa wajen boye feelings inta acikin zuciya..

jim kadan wani babban Likita sanye da farin labcoat da green file a hannunsa yashigo dakin, jikin rank tag dinsa an rubuta Dr. Yusef suleim ajiki, wanda daga ganin yanayin dattakonsa kasan tabbas kwararren likita ne, yana musu sallama kai tsaye ya ƙarasa kusa da gadon zainab din yay yan dube dubensa snn ya bude file din ya fito da dawata takardar sakamakon gwajin numfashi ya dudduba kadan yana rufewa ya juyo kan prof zayyanu da matarsa da suka kafesa da wata iriyar idanu

cikin gyaran murya yace ranka shi dade Alhaji, Hajiya. ina so mu je ofis ɗina mu dan tattauna daku kadan game da lafiyar Zainab Arifah if you dont mind please.

kafin su amsashi saida Suka kalli juna sannan hjy hamidar tacemai "sure" daga nan suka bi shi har izuwa ofishinsa. ofis ne mai girman gaske ga tsafta yasha set na pure white L shape cushions dan tamkr wani palorn haka zaka gansa.

Dr yusef ya zauna yana dan kallonsu har saida suka samu nitsuwa snn ya bude file din da calm voice dinsa yace Alhamdullhi ga sakamakon gwajin da muka mata ya samu fitowa saidai kamar yadda kuka tsara mana ne babu inda bamu duba ajikinta ba
cikin gyaran murya yace toh agaskiya dai alhji, bazan boye muku ba Zainab Arifah tana fama ne da provocked asthma wato tasowar ciwon numfashi da bai riga ya haɓaka ba, saidai da akwai wani abu nadaban da nalura cewa shinei ya jawo mata wnn ciwon wanda gwaje gwajen mu ya tabbatar mana da cewa ciwon Damuwa ce.

cikin katsetsa prof yace ciwon damuwa kuma kai kasan me kake cewa kuwa?

da calm voice Likita yace " yes sir, ayi hqri. ciwon Damuwa mai tsanani ne wanda yaketa kokarin ya jawo mata matsalar wahalar fitar da numfashi.”

dede nan Ya dan ja numfashi kafin na ya ci gaba cikin nutsuwa “shawarar da zan bayar shine a samu a kula da bangaren damuwartata cikin gaggawa tun yanxu inba haka ba zai iya rikidewa nan bada jimawa ba za zamo mata matsalar raunin zuciya ko kuma jikin nata ya gaji gaba ɗaya. in har ana son zainab arifah tay tsawon rai sai anjuri kwantar mata da hankali snn aguji komai da zai rinka shigewa cikin tunaninta.

kafin ya dora kalma na gaba gabaki daya idon hajy hamida ya cika da hawaye. prof dai ya yi shiru yanata kallon likita kamar baisan ma meyake cewa ba.
fuskarsa ba awani sake ba yace "toh shikenan likita munji bayananka amma ynxu meyene mafita?

doc yace eh to alhaj mafitar kenan she has to use a terminal inhaler for now, snn Zan rubuta mata wani magani, to be taken once daily ko wani rana sabida ya rage mata tunani. amma fa lallaine ta sha, snn ta zauna a gida na wasu kwanaki tadan huta a kuma tabbatar during dis time bata shiga wata damuwa ba..

hajy hamida dai batace komi ba dan sosai zuciyarta yake tafarfasa taciki dan haka kawai jikinta yake bata kamr duk akan lamarin yaron nan ibaad ne yasa har yarta kwalli daya take kan azabtuwa..

Likita yace inba wata tambaya inaga we can call it a day, i will make an arngemt so dat you can take her home with you within few minutes. prof ya gyada mai kai baice komi ba, dake manyan mutane ne shi likitan ne ya miƙe ya basu waje, yana ficewa kuwa prof ya miƙe tsaye yana kallon sama cikin tashin hankali tareda lumshe ido da budewa yace "ya salam, what is all this? mutanen nan ashe bazasu barni in cigaba arayuwata ba, ƴata kenan mini tall a duniya amma sukeso sai sun kashemin ita hmm hamida did u have any idea why my only doter is behving like this? damuwan uban waye tasaka aranta? kece nake barin miki amanar zainab arifah agida, babu abunda kuka taba cemin kuna buƙatarsa wanda ba baku ba, but why dint even the god damn family doc say anything to me..wallh inhar ƴata ta mutu toh duk duniya sai ansan antaɓoni.

daga jajayen idanunta da sukaji kwalliya tay ta kallesa muryanta a raunace abunka da farin fata har fuskanta yayi jaaa, hawaye na zuba mata tace alhaj ni ina zan san maka meke kumshe acikin ran yarka? bayan kaima kasan zainab tagama raina uban kowa, batajin maganan kowa sai naka, nima i just found out abt her health frm elizabeth daya daga cikin maids dinta dake shirya mata daki, wai each time home doc yazo dubata ashe wai ita takece mishi karya sake yana gaya mana halin datake ciki...our doter is clearly trying to kill herself bcos of one stupid local boy
..wallah ba haka ƴata take ba, Arifa tana da wayo da ilimi, saidan in sihiri aka mata tabi ta dora walakntaccen yaron nan aranta, kaima dai kasan zainab arifa ba matar karamin mutum bace, nide wallah wallahi bazan bada ƴata ma wann yaron ba, tafi karfinshi har abada, saidai in zasu kasheta su kasheta..

tana fadin haka dede nan ta rushe mishi da wani irin kuka..

yay sauri ya dafa kafadarta yana cewa ohh nooo hamida kinjiki ke kuma,toh meye haka?

a mugun harzuke tace alhaji kaima fa kanajin abunda likta yake cewa yarmu zqta iya mutuwa da ciwon damuwa ko zuciyarta ya buga anan gaba, shikenan sai ninasha wahala na haifi zainab dakyar bata taɓa saba maka ba amma sai gashi wai yau zainab tana boye mana halin datake ciki akan yaron nan? this is insane.. toh bagashi ance ma ciwon zuciya zai iya kamata ta mutu ba shikenan yan uwanka sunji dadi sun hadakai zasu kashe mana yarmu kwalli daya wanda da kyar muka sameta wayyo Allah na

shima sosai abun yake kuntata masa aransa amma yayita maza yace 'shushhh hamida calm down kefa ba yarinya bace kuma ban mutu ba tukuna..kidena kukan nan mana ehh. cmon darling its okay ninasan me zanyi i know what to do zainab arifa bazata taɓa mutuwa ba, i know she hides it sabida bata sone inhanata bare ta saɓamin, i knw my doter, abun kawai yafi karfinta ne shiyasa take boyewa..so, dole ne mubi abun ahankli cos is getting pretty serious with her health, ynxu haka rayuwar yarmu ne on the line. get urself together idan munje gida we will make some key decisions to save her life bazata iyayi iya kadai ba.


cikin gyada mai kai ta share hawayenta da wani hadadden farin hanky data fiddashi daga cikin jakarta mai matsanancin tsada ta maida hankun jaka kenan securitynsu yazo ya kirawo su akan angama komi..


dauƙar jakarta tay ta dada gyara zaman mayafinta dayaji original silver stones babbane sosai rare design daga mum ramlat collections, ya bi yarufe mata duma duman jikinta na manyan mata isasshu koinanta acike yake tamm bata da ko ƙashin wuya bare alaman rama, wani shegen abun wuyar gwal ne kwance a wuyartata, gata da farin fata koinanta yayi soll tana sheqi gata doguwa, tsabar iya daukar wanka zakace ko balarabiya ce dan bakaramin cika babban mace tayi ba.

tana gama yafe gyalen tabi bayan mijinta suka samu har na gama shirya musu komi, nan suma sako yarsu zainab arifahn atsakiya suna mata sannu sannu tun anan ta sharesu batace musu uffan ba har suka kama hanyar gida, tun a mota tay bacci dukunkune ajikin mahaifinta dake likita yagaya masa cewa ya mata allurar bacci dan ta samu isasshen hutu sai bai damu ba, suna isowa gida kai tsaye prof ya wuce da ita purple colour princess theme bedroom inta na yar gata ahnkli cikin kulawa ya shimfidata akan makaken italian gadonta me tuff board double spring saida ya fita kafin nan masu aikinta kusan su biyar suka karasa sauran gyara mata jiki da kwanciyar me gabaki daya..

fitowarsa falo tun daga saman stairs ya fara jiyo muryan matarsa tana kan amsa waya dagaji kasan kanwarta ne hajy hajara shettima
duk sanda kaji ta nemi wann matar to da akwai babban matsala itadai sam taki ta amince aranta cewa har yarta zainab arifah zata saka wani soko matsiyacin yaro aranta da sunan soyayya tunma bataje koina a shekaru ba gani take kamar kawai asiri ne akama yarta

jin motsin saukowar mijinta cikin falon yasaka ta karkare wayar tare da cewa hajiya hajjara dan Allah ace ma malamin nan its very urgent, inde sihiri aka ma ƴata kawai agaya min insan nayi kafin su kashe min ita..pls i will wait for ur call
..daga haka ga katse wayar tana sauke ajiyan zuciya me nauyi....

cikin tafiyar takama tareda nitsuwa prof ya karaso cikin palon wanda komi cikinsa golden colour ne, anitse ya nemi waje zauna yanamia dafe kai Hajiya hamida tay sauri ta ƙaraso kusa da shi a hankali ta dora hannunta dayaji jan kumshi akan gadon bayansa tana cewa Alhaji Idan muka ci gaba da barin zainab Arifah ahaka wannan ciwon numfashi nata ba zai taɓa warkewa ba honey pls we have to do sumtin fast. kasan bata saɓa ma umarninka why not ka rabata dashi ko kawai gobe gobe taɓar kasar nan taje tay karatunta gabaki daya akasar waje..

laushin hannunta dake yawo gadon bayansa yasa ya lunshe idonsa tare da kara relaxing yanamai cewa "Na san da hakan hamida amma fa duk wnn matakan naki bazasu saka ta daina tunaninsa ba inhar kuma bawai tunaninsa zamu cire a ranta tabbas abunda muke gudun shine zai faru damu duk inda zamu kaita a duniya hakanan zata cigaba da lalacewa.

Shiru ne ya dan ratsa falon kafin can hjy hamida ta kallesa tace toh me kake ganin zamu iyayi mu ciresa a tunaninta.

hannunta ya kamo yana kallom kwayar idanunta yace leave that part to me..
zainab Arifa yarinyace yanxu tabbas idan muka matsa mata ta rabu da yaron nan toh tabbas zamu rasa ta. so, i am going to have to use a reverse psychology here, mu jawo yaron jikinmu mu bata abunda take so ynxu, nan gaba zamu zo matsayinda inhar nasaka mata doka akan yaron ma bazata iya tsallakewa ba, but for now dolene mu saka rayuwarta da lafiyarta as our main priority.

shafa fuskarsa takey ahankli cikin sauke ajiyan zuciya tace honey, are you suggesting we just let her be with him for now?

amugun kasale yace yes my love..inason zainab ta samu nitsuwa ne kawai tay karatunta me zurfi ta cimma burikanta dana tsara mata tukuna
..just trust me..i will handle her personally inta girma ta mallake hanklin kanta Inhar kinga wani a dangi na ya aure min yata sai inbayan na mutu...

kiss kawai ta dora mai agefen kunci ahnkli da alaman taji dadin furucin nasa ahnkli tace "your wish is my comand my love. amma kuma nasaka hajiya hajara ta duba min lamarin awajen malamai

yace hakan ma yayi..

daga haka ya miƙe, ya ɗauki wayarsa "kije ciki ki shiryamin kanki da kyau zanzo gadon naki na sameki.

wani murmushi tay irin wanda tun dazu baigani tay ba face sai yanzu daya furta mata hakan, cike da kasaita mai haɗe da rangwadi irinna manyan mata ta miƙe tsaye tanamai cewa "okay love..Dont keep ur queen waiting.
gyada kai yay yace sure. tana wucewa ciki ya ciro wata sim a wallet dinsa ya saka awata yar karamar waya snn yay dialing lambar dan uwansa bappa zaidu tun wayar baiy ringing ba ya wani hade rai yafara jan tsaki.

wayar yana fara ringing ya fice waje dashi a kunne after like 30 min ya dawo ya same matarsa har ta gama shiri jikinta sanye da wata arniyar nite gown ta bude tuma tuman fararen cinyoyinta akan gado tana jiransa, yan kwabe garensa wani dira yay kan gadon ya dora mata kiss me zafi snn ya kalli cikin kwayar idonta yace "
"jibi yaron nan ibaad zaizo gidan nan zanyi magana dashi nd i need you to be cool with him too..

wani chak annurin dake fuskarta ya dauke a mugun hargitse tace alhaj bangane ba, akan me zaizo mana gida kuma?

atake ya dan haɗe rai yace "kin manta ne, is All part of my plan hamida. kedai kawai kiyi abunda nace miki..

tun bata kai ga budan baki ba yawani irin wawushota jikinsa yanamai susuta da kisses daga haka har suka fada kan gado...

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[27/10, 19:03] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️7️⃣


G.R.A..
5;30~AM
kirar sallahn farko ya dira cikin kunnen ibaad dake kwance lumui akan lallausar madaidaicin italian bed dinsa dayaji off white cotton bedsheet me taushi yarufe daga jikin shi har izuwa kan kyaywan fuskansa da bargo me laushi, da adduar farkawa daga bacci abakinsa yadan bude ido cikin kasala bai motsa ba sai after like 5 scnds bayan ya idda adduar snn ya dire kafarsa akasa da bisimillah ya mika hannu ya kunna wuta, tsaftacciyar farar riga ce ta bacci kuma marar nauyi ajikinsa da dogon wando shima marar nauyi, goran ruwan dake gefen gadonsa ya dauka ya sha kurbi kamar biyu sann ya mayar ya ajiye, adan gaggauce ya mike ya shiga bathrum yay alwala ya dawo ya cire rigarsa snn ya dora goggyar bakin jallabiya me tashin kamilallen qamshin kylian love ajikinsa, snn ya saka karamin farin hula, nan take ya saka bedroom sleepers dinsa yabude kofa ya fito just few steps daga inda room dinsa yake ya tsaya jikin wata hadadden

7 / 88