Author : NONE Category : African Stories & Novels
ahaka adaddafe sama sama, full of hidden malices, and classism na ciki duk na ciki.
maheer da Ibaad sun shaku da junansu sosai, duk dama uwayensu mata basa jituwa amma sosai ake zumunci, maheer din ya bada ibaad like 2yrs gap dake ammi babban aka fara aurowa, snn ya kuma bawa mujaheed 4yrs dake shi mujaheed sa'ar zainab arifah ne,
wacce ko tazo gidan kwainanenta na sangarta kawai takeyi bata fiye son harka da su ba, kulthum da sultana kuma are all almost same age da safiya duk dama sun bata 2yrs dan a gidan safiya itace karama as of now batafi 10yrs ba.
duk da hadewar kan yaran, ammi babba haryau tulin kishi na dawainiya da ita haka kawai ta tsani ibaad har cikin kokon ranta, zama dashi kawai take agidanta na dole sabida batason ta saɓawa mijinta bappa zaidu, amma bata kaunarsa ko kadan, dan wani bin ko amsa gaisuwarsa baso takey ba gani take kawai kamar duk shirin aure mata miji ammi karamar take kanyi shiyasa ake kan cusa ibaad a zuciyar bappa zaidu haryake daukar nauyin komi na karatunsa tun daga primary gashi nan har scndry.
haka rayuwa yake tafiya a familyn alhj almansur na tsawon lkaci, prof zayyanu adan dole kawai ya hakura yabar yarsa zainaba arifah take shigowa dangi, kamar yadda ammi babba take zaman dole da ibaad anata gidan na GRA.
gabaki daya yaran gidan sun kasance mabanbanta hali, but one thing they all have in common is deir natural striking pure fulani beauty da albarkan ilmi me amsa sunansa ilmi.
babban cikinsu yaa maheer is faintly chokolate skinned, calm, and reserved kamardai babansa bappa zaidu, inkaga yana surutu to musun ball suke da ibaad, yana da kama kai,da sanin yakamata hakan yasa sukafi jituwa da ibaad din sosai dan baifiye son mutum me kananan magana ba, shikuma ibaad din mutum ne murdadde, a walking puzzle in human form,yana da piercing hazel eyes da dark pink lips, farinsa kuma is more like a ethiopean beauty, soo calm, yellowish skin tone ba irin dau innan ba, babu karya yafi uban kowa kyaun jiki da tsarin fuska tareda farinjinin yan mata sabida mum dinsa farar shuwa arab ce yake da suma baqi qirin, saidai kmr yadda hajy mairo take yawan faɗa ne, ba asan gaban ibaad ba bare bayansa, yana da mugun son tsafta, in yay dressing damnnn kamar italian model, saidai birkitaccen mood swings da wnn emotionless face din nasa yasa ake ganin kamar ma shine babba agidan sabida baiya wasa ko kadan da kannensa msmn ma mata, komin rikici da surutun da akey agidan yana shigowa zakaga an watse waje yay shiru, he is deeply introverted with a touch of hot temper, highly emotional intelligent, sosai ya iya karantar halin da mutane ke ciki shiyasa ba masa karya, akan ra'ayin kansa ya fiye zama. baida tsoro sam, amma kwata kwata baison hayaniya, duk duniya babu abinda yake mutuwarso aransa kamar murmushin mamansa, itace kawai intacemai yayi abu ko da baiyason abun to zakaga yayi atake,
mujaheed kuma shi fari ne sosai kamr yellown inyamuri, MJ sarkin tausayi ne yana da saurin kuka ga rauni, baida raayin kansa his dad alwys tell him wat to do, he is hopeless romantic at heart, snn yanason soyayya mai zurfi da ma'ana. sai dai daga zarar ya gane mace batayinsa toyakan hakura hargara yabar abun dayakejin ya kashe shi acikinsa.
duk wani hali da MJ yake dashi ajikinsa kusan shi zainab arifah shitake ji dashi, a kyau babu ta inda takasa, itama fara sol ce sol kamar mjn din tanada kuma manyan idanu da pink lips me kyau da yar doguwa fuskarta, kawai dai tana da dan girman jiki ne tun tana yar karama, da tun lokacin datake at arnd age 10 shatin fitowar nono already yafara bayyana mata sabida irin kulawar datake samu na wuce kima, tana da rauni, she is so soo vulnerable nd hopeless romantic at age 7 tafara wani irin silent crushing akan yanayin dressing in ibaad, abun yafara mata kamar wasa, saidai tsoronsa da ake mugunyi yasa bata iya nunawa ba then the more she sees him the more obsess she bcm with him, hardai takai 12 yrs shikadai ne namiji aranta duk dama ko kusa dashi basa iya zuwa tsabar tsoronsa da sukeji.
inda kawai suka dan bambanta da mj shine inhar tana son abu koda abun bayasonta bata iya haqura dashi saidai a mutu. yar a mutu a love ce, bata san meye babu ba, bata san meye kalmar hakuri ba, she believe duk abun da zuciyarta yakeso kawai xata sameshi. sultana da kulthum kowacce tana kama ne zak zak da mahaifyarta, safiya ce kawai take kama da mahaifinta sosai, nd each of them are so beautiful in their own ways. saida zainab takai har 13 kafin ta fara nuna alamomi a fili cewa ibaad yana ranta sosai. kullum akazo wekdns inbata gansa ba bata sake fuska da kowa, ya zama kamar ganinsa shine kawai abunda yake kawota gidan.
wa Ammi babba hakan ya farayiwa zafi dan ta tsanesa sosai, toh amma sunsan zainab arifah yar gata ce na bugawa a jarida basu isa su fara juya brain inta ixuwa hana yuwar komi ba duk dama sunga aboye take zuba crushing inta akn ibaad sabida yadda taga ake mugun tsoron masa shirme. tun da zainab takai jss 1 ta dada fallewa da jiji dakai snn tagamu da kawaye irinta sangartattu yayan masu kudi"Nala, da rukky, haka zasu zugata tayi wann tay wancan domin ibaad, amma bai taba kulata ba dan ya tsane yadda ake nuna mata fifiko tare da sangartata agidan, nd worst part ma yadda take xuba ma uban kowa fi'ili da manyance ana kyaleta dan ba ason ran ubanta ya ɓaci, tun tana wannan kananan shekarun tafara koyan kwalliya da saka matsatsun kaya wai dan kawai ibaad yayi noticing inta amma inaa shi mugun haushi ma take bashi aransa.
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[23/10, 18:55] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE 'BOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*
⏯️5️⃣lamarin boyayyr soyayya me zafi da zainab Arifah take kumsawa aranta akan ibaad yakan daure ma kowa kai musmn dake ita da kanta ɓoyewa takey sai ya zamana kowa yana dan dauke idonsa akan wasu abubuwan datakeyi, kafin takacika 14yrs duk matayen familyn al-mansur saida suka san da wannan ciwon obsession datakema ibaad wanda ynxu yafi karfin ace masa tsaftacyar soyayya dan wani bin inbata gansa ba iskar datake busan numfashi dashi kamar dauke mata yake a makwogoro, haka ma duk ran da akace tazo gidan ta gaishesa yahade rai ya wuceta be amsata ba haka zatayta kuka da tsananin fushi kamar me fama da aljanu a dakin anty safeera, wani bin har kaga tana zazzabi me tsananin zafi, haka ma inta koma gidansu xata kulle kanta a dakinta tay ta rabza kuka kmr an bugeta tanajan zuciya wai dan ibaad bai amsa gaisuwarta ranan ba,
gabadaya sai ta Ɗaga ma kowa hankalinsa agidansun, saidai duk rintsi duk wuya bazata taɓa iya furta ma kowa cewa ibaad ne matsalarta ba, kuma shine take mutuwar so aranta a fili ba, yanxu haka iya kawayenta na schl ne kawai suka san asalin meyake damunta aranta..
wasa wasa abun har ya fara zame mata kamar wani strange ciwon ODD wato (oppressive defiant disoder), kowadai ya damu, ganin iyayenta sun fara fita hayyacin su wajen bincike akan sabon sabbin bhvrs dinta yasaka tadan fara kamewa,musmn dataji prof dakansa ya farayin tunanin hanata zuwa can family house dinsun kwata kwata, anashi tunanin hala cutar da yarsa akeyi aɓoye dan baya yawan bada kudadensa ma dangi ana bushasha dashi, hjy hamida kuma gani take kamar maita ne kawai ake so alashe mata yarta kwalli daya dashi acan family house hala shiyasa yartan take behaving strangely dan har malamai takira anyi ma zainab din ruqiya da su hayaki basu san damuwar soyayyar ibaad ne kawai aranta ba.
Ganin iyayentan sun fara daukar zafi akan maganan har sun fara batun yanke hukunci akan zasu hanata zuwa family house din ma kwata kwata yasaka marmaza ta hau neman mafita dan bata kaunar wani abunda zai jawo ace bazataje can gidan taga kyakkwayr fuskar ibaad a wknds ba.
Sangartattun Kawayenta na schl Nala bala da rukky hamza sune suka soma bata shawara, sukace since her 14th birthday is coming up soon ai ynxu tawuce ajin ace mata yar karamar yarinya yanzu kawai taje ta samesa kai tsaye ita tafara masa magana akan abunda takeji akansa. abunka da yara kanana kuma sangartattu yan gata cikin iko da rashin tarbiya da nuna tsagwaron manyance
suka zugata sosai kuma ta zugu,ata fannin ibaad din kuwa lokacin anata rububin ganin sakamakon jarabawane na school of medicine nd surgery pre test zai shiga jamiar Bayero na kano, jarabawar ya fito kenan yacinye sosai yanata kkrin tunkarar karatun medicine dinsa daya ke buri, satin saiga zainab arifah tasha wanka tazota weknds as usual taci uban gaye sosai tasaka wasu purple and white english wears masu aji ,hakanan tazo ta hakimce a karamin falo tasaka anty safeera agaba da shagwaba da manyance akan dole dole taje kawai takira matashi tacemai yazo nan shashen ya samete inyaso snn sai tamasa maganan datake tafe dashi, ita sam bata san hakan ma rainin wayo bane. wai in tana da magana da mutum da mutum toh ita bazata daga kafarta taje ba saidan in mutumin yazo har inda take ya sameta koda kuwa ya girmeta sosai.
dake tariga tasaba komi tace musu tana so ana mata haba haba, kawai yau sai taji mugun mamaki dataga anty safeera takekeshe ido tace mata bazata iya zuwa sashen ammi karama dan ta kira mata ibaad nan ba saidai in ita taje ta samesa dakan ta, a wasa ta dauki maganan dake ba'a saba ce mata "no" ba can kuma sai taji haushin hakan sosai, saidai duk a tunaninta na yaranta ta dauka hala kawai tsoronsa suma manyan matan gidan sukeji, mugun yarda dakanta datayi yasaka tamike tana mao gyara zaman kayan jikinta cikin jan tsaki kai tsaye tajeta har sashen ammi karama tana takunta ahnkli kuma ayangace kamar bazata taka kasa ba.
cikin cin sa'a kuwa sai ta samesa tun a babban falon gidan da laptop agabansa yana kan kkrin registering kansa for clearance dan shi babban likitan zuciya (cardiologist) yake da burin yaga ya xamo dan haka karatu ne meyawa agabansa, lkcin kansa yadau zafi yanata cike cike sqi ganan zainab arifah ta doso, tsayuwar cak tay daga samar stairs tana kallonsa dan duk dama tana mutuwar sonsa babu karya dakakken kwarjininsa yana mugun girgizata, tafiya take kirjinta na tsananin bugawa amma data doso kasa ta falon tadan kare mai kallo duk sai taji takara mucewa da sonsa a tsaye, he was wearing this very clean plain cream shirt da yaji karin guga haɗe da plain coffe brown trousers, tsaftarsa da kwarjinin sa sosai yakara cike mata ido gashi bao saka turare me karfi saidai me sanyi wanda daga ka doso sa zakaji kamar a fatar jikinsa qamshin yake tashi.
jin kirjinta na bugawa fat fat kamar zai ballo waje taji tsoro yadan kara rufeta, dacan har zata hakura takoma dakin anty safeera ta kara shiri sai kuma ta tuna cewa iyayenta zasu iya hanata zuwa gidan kwata kwata in har batay wani abu akan abunda takeji akan ibaad ba, nan da nan kuwa sai ta cije ta danne tsoron, gashi dama bayan gaisuwa sama sama basu taɓa yin wani maganan 2 scnds dashi ba all this years is like baisan ma tana existing ba dan ya jima da tsanar behviours inta na raini da sangarta.
kwas kwas ta karaso cikin rangwadi da yadda da kai batay mai sallama ba iyaka qamshinta ne ya bule wajen tabi ta kuresa da manyan idanunta tanaji aranta kamar zata haɗiyeshi, idanun sa stiff suke akan system dinsa ko daga kansa baiyi ba haka zalika baice komi ba har tanemi waje daf da chair dinsa ta dan zauna ta kuresa da ido., shiru ne ya dauke wajen ganin bazai kulata ba aftr like 10 min cikin rollng idanu tace amm hi, can i have ur attention here. yay shiru kamr badashi takeyi ba
tweeking fingers dinta tay ayagance gaban screen din laptop din suna hade ido tace "hey, bakaji abunda nace bane ?? fusknsa a mugun harde yace "what? tace "you" i just talke to u .cikin katseta yace ohhhh "sallamar ki kenan?
"my bad"..assalamu alaikum.
dauke kansa yay saida yaja kamar 3 min snn ya amsata ciki ciki.. tace "can i talk now.. irin kallon ohonkin dataga ya mata yasata dan kyabe baki cikin sauke ajiyan zuciya tace "anyways.You should probably calm down before I actually admit I’ve been crushing on you. maybe your ego won’t survive it. ina so in gaya maka cewa ive been thinking about u, i think i am in love with you ibaad.. ina so..wani irin dakakken kallo yamata tunkan ta karasa ba cikin datsar numfashinta yace "i have heard enuf kitashi kibarnan.
karamin murmushin ko inkula tay snn tazuba masa manyn idanunta masu cike da tsagwaron rashin kunya atakaice tace
"excuse me?? iya abunda zaka ce kenan? Ugh i cant belive this, I don’t even know why I’m saying this, but I’ve kinda had a thing for you, wai ko baka gane me nake nufi bane...
wayar chagersa kawai ya cire a wuta ya miƙe tsaye har zatai mai magana cikin daka mata tsawa yace kee bance miki kibar nan wajen ba? sai zuttt zutt taji saukar bulalan ajikinta..
within mins akaji ihunta yana tashi agidan..
ahhh, wayyooo,wayyo daddy, daddy, daddy naaa, mummy wayyo Allah ibaad kayi hakuri..daddy kazo ka cece ni wayyo ihu kawai take zubawa me kara tana daka tsalle a mugun rude tana kuka me kara
kusan babu wanda bai razana da ihunta ba, kaf matayen gidan suka firfito duk akayo falon ammi karama arude dan basu taɓa jin zainab arifah na wann ihun ba, nan aka samu Ibaad ne ya rike hannayenta biyu yana cauda mata wayar chargensa ajikinta yana kuma tmbayarta "ko shi sa'arta ne? kiris ya rage ta sume masa dan tunda aka haifeta ko tsawa ba ataɓa mata na bare duka.
yaa maheer ne yay sauri ya karɓeta a hannunsa dan wani irin razannen kukan takey a mugun mugun tsorace jikinta na rawa rawa kamr ba ita ba, wanda hakan yasaka tuni idanun mujaheed ya tara ruwa dan yana da tausayi sosai, atake kowa yafara daga hanklinsa ana ta tuhumar ibaad ko me zainab arifah tayi masa, ammi babba da anty safeera duk sun dau zafi suna kiran sunan sa ana tuhumarsa falon ya kacame da hayaniya sosai.
baice musu komi ba yahaɗe ransa ya koma yazauna snn ya dauke kansa ya cigaba da latsa computersa anata surutu ko ajikin sa face saida uncle moh dakansa ya shigo wajen yafara tambayarsa, agaban kowa ya mike tsaye snn ya maida musu abunda zainab arifah tace mai nawai tana sonshi bla bla bla, ibaad ya nuna bacin ransa sosai, ya hada harda sauran cousins dinsa matan duka wato (kulthum da sultana) yace karda wata yarinya ta kara masa wann wasan shi baison hauka yaushe ma sukakai da su furta ma namiji batun soyayya tun suna early teenagers???
daga uncle moh sai maheer ne kawai suka nuna sun fahimce shi, mj kam baice komi ba saboda kukan balai da zainab arifahn tayi sosai ya jefasa cikin tausayi da rauni gashi dama suna dan shiri sabida shi yaron anty safeera ne kuma age mate dinta kenan dama agidan they are both going to tru the same age.
sauran yaran gidan ma sosai suka dada firgita da tsorota da fushin ibaad, sanin cewa babu mahalukin dayake da ikon taɓa zainab arifah ko ɓata mata rai agidan yadda ake mugun daukarta yar gwal saigashi ibaad ya zane yar banza ciki da bai kamr baisan waye ubanta ba.
duk dama dattijan matayen sun san cewa dagaske ne Zainab arifah tanason ibaad amma haka suka haƙikance suka bi suka dora masa lefin komi duk sukace ai kawai gigin yaranta ne yake damun zainab ibaad bai kyauta ba yayi over reacting yaci zalin yarinya baida haquri,..
kai wasa wasa wasu bakaken maganganun da ammi babba ta hau furtawa ma zaka dauka wani babban zunubi ya aikata, har cewa take zainab arifa din ma aitafi karfinsa a batun soyayya sabida ita tanada bright future ahead na gadon dumbin arziki daga kawu babba shikuma ibaad din yananan ba'asan ma yazai kare anashi rayuwar ba. tanayi kuma tana soka zagi ma uwarsa asakaye itadai ammi karama hakuri kawai ta bayar ma kowa sai bata kara cewa uffan ba ta koma daki.
haka matayen sukayi ta kananan magana a gidan ranan babu kalar rarrashi da kwalemar kwainane wanda ba ama zainab arifah ranar agidan ba,
ammi babba anty safeera Da mj duk suka taru akanta suna ta lallashinta a daki.
shikuwa ibaad ko ajikinsa har yanxu ma mamakin tsaurin idon zainab arifah din yakeji aransa yadda tazo masa gatsau ta samesa babu wani dandanin tarbiya ko kunya ajikinta tamasa maganar soyayya da dumbin tsaurin ido da shegen manyance kamar wata yar shekaru talatin, mugun hade ransa yay da kowa agidan shima, bai kuma bawa uban kowa haquri ba face saida mahaifyrsa takirasa daki snn ta masa faɗa tacemai da baidake zainab din ba da faɗa kawai yayi mata, nn ne ma ya sassauto ya ba da mum dinsa hakuri har yace mata bazai kara dukan musu ƴa ba tunda bataso. da kyar da wahala dai wann maganar tay sanyi ranar ma da dumbin zazzabi zainab arifah tawuce gida, taki sam iyayenta suga shatin zanan dukan ajikinta.
shiru shiru har ana zaton komi ya lafa washe gari da yamma ammi babba dataga alamar maganar zai mutu abanza aikuwa nan tadau waya takira gidan prof zayyanu wanda da kyarma aka samu aka haɗata da hajy hamidar suka dan gaisa babu ɓata lokaci tahau zuba zance cikin sigar makirci harta sanar da ita komi da ke faruwa bata rage ko aya aciki ba saima gishiri da maggi data zuzzuba dan labari yayi zaƙi ita kuma ta samu karbuwa.
bazan iya