ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 88

15K to 18K   out of 262.2K words

fayyace kalar tashin hanklin data ballo ranar ba, dan ranar gidan prof ko xama basuyi ba, hjy hamida tana gama aje waya jikinta yafara ɓari da tsananin bacin rai, nan da nan takira mijinta tacemai duk inda yake kawai yazo gida yanxun nan za'a kashe musu yarsu da duka, yana can airpot kano amma jin anfurta batun yarsa hakanan ya mance komi ya dawo, yazo gidansa ga samu matarsa cirko cirko duk ta birkice tana huci kamar zakanya tanakuma safa da marwa a wargagejen falonsu da hadadden wayarta a hannu dan tagama qudirawa aranta kawai sojoji zata tura aje har family house a zane kowa dake wajen ciki da bai snn akama shi ibaad din akaisa military gurd room amasa lilis sabida dukan yarsu dayayi

sosai abun yayi ma prof ciwo aransa bana wasa ba, danko shi bai taɓa yin tsawa wa yarsa ba bare duka, saidai harga Allah yasan bazai taɓa iya kama ibaad yakaisa gurdroom akan haka ba yasan za'aje ne akashe shi, kuma haryau yana dan girmama babban wansun aransa wato marigayi dr almustafa mahaifin ibaad, dake shine kawai adangi bai taɓa guje masa ba duk mugun halinsan nan yana tolerating dinsa har ya rasu.

hakanan dai yay masifa yay bori yay bambami snn yabi ya danne xuciyar matarsa aka bar maganan sojoji agefe, nan sukaje har dakin zainab Arifah suka tasota agaba da maganan ibaad, dacan taki sam ta gaya musu amma suma nace mata da nuna bacin rai da lallashi dai har saida ta hakura ta gaya musu dukkan abunda takeji na matsanancin soyayya akan ibaad.

lamarin ya matukar daure musu kai, ya saka musu tsananin baqin ciki tare da dumbin mamakin yadda at this young age soyayya me tsananin zafi ya kama zuciyar yarsu, tunda suke da ita bata taɓa musu kuka irin nayau ba, sai rokonsu take akan kar su masa komi har cewa take zata mutu in sukasa ibaad yakara tsanarta itade tana sonshi. it was pretty serious nd obsessive, amma dake suna matsanancin so ta kawai sai suka bar maganan, suka mata fake promises suka lallasheta sosai cikin nuna mata dumbin soyayya da kuma matsanancin gata, a tunaninsu duk yarinta ne sunaji aransu maybe tsabar kyau da kuma kwarjinin ibaad din ne kawai yake dan rudinta inta girma ma zata manceshi sabida matsayin rayuwarsa ma aiba daya bane.

suka mata wayo suka nuna sun fahimceta, hardai ta amince tay shiru, likitansu na musmmn aka kirawo yazo ya dudduba jikinta musmn wajen shatin bulalan aka bata wasu special pain relievers da kuma underage antidepresant drugs tasha sabida yadda ta bi ta galabaice sosai.

dan kawai hankalinta ya kwanta haka iyayen suka nuna mata cewa zasu mata dukkan abunda take so din, bazasu taɓa ibaad ba tunda ma bata so ataɓashi. amma fa sosai abun yayi ma mahaifyarta ciwo aranta bana wasa ba dan tabalain so ace taci mutuncin kowa agidan akan wann abun da akama yarta. shikuma prof zayyanu
ji yake ko a mafarki bazai taɓa aura wa yarsa talaka ba bare kuma har ajega batun auren dangi. dukkn su iyaye ransu bai musu dadi da lamarin nan ba. they just try to numbed it a fuskarsu, acting all fine nd supportive while they are not dan kawai kar zainab arifah ta gane basaso ta shiga wani mummunan hali gashi
dakyar Allah ya basu ita.

arana ranar da daddare bayan likita ya gama dubata nan danan prof yasaka hajy hamida ta shirya tawuce da zainab Arifah din izuwa kasar sydney on a 5 days daddys girl petting break waidan kawai hanklinta ya kwanta

ahakama prof bai daddara ba, suna wucewa sydneyn maza maza ya kira uncle moh a waya, ko sallamarsa bai amsa bare gaisuwa yahau sauke masa buhun masifa ta inda yake shiga batanan yake fita ba, kai tsaye babu sakayawa ya masa ihu ihu ya zazzagesa sosai yace musu da shi da bappa zaidu sune suke daure ma ibaad gindi dan ya kashe masa yarsa kwalli daya, yace dama can yasani bason suga ya haihu sukeyi ba kawai so suke ya mutu a dau dumbin dukiyarsa abasu,.

babu irin zage zagen da zarge zargen da baiyi ba. tun uncle moh yana shiru har kirjinsa ya fara zafi tsabar fushi kawai sai ya kashe wayarsa..

yana katse wayar yazo gida yahau sauke fushin akan ibaad tareda sakamai dokan cewa karya sake dukan kowacce yarinya agidan inba hakaba kuma shi gskiya zai kai kararsa wajen bappa zaidu.

har yagama masa fadar Ibaad dai baice masa komi ba san already ya riga yay ma mum dinsa ma alkwari.


daga fannin ammi babba kuma duk ta kasa zanne ta kasa tsaye tana Allah Allah washe gari yay taga anzo har gidan an ci mummunan mutuncin ammi karama tareda danta ibaad amma sai shiru kakeji, ita bata karajin bayani daga wajen hajy hamida ba hakazalika nan ma bataga anzo anyi hatsayina ba, kai hanklinta bai kwanta saida ta kira anty safeerah toh abakinta taji cewa ai prof ne kawai ya kira ya zazzage su uncle moh. ranta baiso ba duk dai ba haka taso aranta ba.

bayan kusan sati biyu da faruwar haka da kyar iyayen zainab Arifah suka barta ta dawo tana zuwa gidan duk weeknds, saidai wnn karon ta dan shiga hanklinta bata fiye wulgawa ta inda ibaad yake ba dake ma yanxu baya zama yana kan kkrin shiga jami'a ne abunsa. da mujaheed kawai suke dan magana sama sama intazo gidan dake shine sa'arta, shikansa Mjn wani irin mamakinta yake dada sha musmn yadda yaga duk ta sauya salo tanata kkri taga lallai tasaka hanklin ibaad ya dawo kanta, dan kamar ma kara hura mata wutan son ibaad din aka ɗadayi aranta kwana biyun nan..

_ANGUWAR TUDU_ ...

Da yamma ne lis gari yay sanyi yara suncike kan tituna da hayaniya da alamun lokacine na sakosu daga babban makarantar higher islam na yara dake anguwar dake mashi kadaine a anguwar duk wani yaro ko yarinya dake zuwa schl a wann yankin nan duk ake zuwa karatu.

daga cikin rububin yara yan mata inayah da ayanah suka fito suna tafe manne da junansu, yanayinsu na nuna dumbin soyayya na yan uwantaka da dumbin shakuwa a fili take nunawa, duk dama wuni sukeyi makarantar amma tsaf tsaf zakagan uniform dinsu, rigarsu fari kal ne sai hijab da wandon kuma dark green colour kowacce da yar jakar littafanta
ta saƙa akafadarta.

Fasalin jikinsu da kuma kamaninsu dake saurin fallasa mixed tsatsonsu na asalin jinin buzaye haɗe dana fulanin daji ya saka sukayi masifar kyau atare, yanayinsu gwanin ban sha'awa suke tahowa duk jikin su akillace yake acikin green hijab dinsu..

kalar bakaramin yi musu balain kyau tayi ba saboda yadda ta amshe kyakkwan tsarin fuskarsu da yanayin su na yan mata masu fallin tasowa, gaban su gadi suke takawarsu cikin nitsuwa da sanyin jiki dan inda sabo yanzu sun saba da yanayin yadda idanun kowa ke satan kallonsu msmn ma ayaanah datake da wani irin rare calming beauty ita ba fara sol ba ita ba baƙa ba ita ba cokolate ba, tana dai tsaka tsakiyar hasken fulani dana buzaye duk ta hada kamannin biyu, ita kuma inayahr akwai kyan ta dake nuna na fullo haƙƙ babu mix da kuma tsayin ƙafa na mahaifyarsu taawure data gada, duk da kankantansu kallo daya zaka musu kasan cewa tabbas wayann yaran zasu zuba dirin jiki me daukar hankali, kai daga nan ma zaka san sudin nadaban ne acikin mata.

Kamar yadda suka saba kullum adaidai hanyar da yabi kwanan gidan sarkin kasuwa sukeyin sallama da sauran yaran schl dinsu nan bayan sun rabu sai kowacce tanufi cikin gidar iyayen ta.

lokacin yamma ne liss masu zuwa kai haraji da reports gidan sarkin kasuwa anata kkrin kai da komawa yawanci zaka ga kofar gidansun da matasa sosai da yamma

tunda suka doso inayah ta sauke kanta kasa cikin sauri sauri sanin bamai yin lokacin kula gaisuwar su saidai ayita comparing kyanta dana yar uwarta, ayanah kuma mugun tsoron maza takeji dan haka tun kan su iso ta wajen ta fara ɓari ɓari ta kuma kara tantame hannun addanta inaya.

tafiya sukeyi cikin sauri sunajin yadda kananan zunde da gulma kala kala yake tashi ako wani tsirkon taro dake kofar gidan
nasu ,tabbas mafi yawan matunen dake zuba musu ido kullum ba dan Allah bane sai dan gulma munafurci da nuna hassadar su a fili dan kaf anguwa an ririta zancen cewa yayan tàawure me saida nono da suke ɓakunta a anguwar sune masu dumbin kwaxo a makarntar tudu gabaki daya gasu kuma da balain kyau har ana kafa caftersu agidajen mutane.

kamar kullum ido ne ratata akansu, inayah ce me karfin xuciyar kanta akasa sai jan hannun kanwarta take da sauri, suna kaiwa
kofa tsabar ɓari kawai sai jakar ayanahn ya subuce a kafadarta ya faɗi. da sauri inayah ta saketa ta tsuguna kasa zata dauka jaƙar tana tsugunawa kuwa a mugun gigice kuma abazata ta riƙe gefen cikinta da sauri tanamai furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....da karfi

tun kan ayaanah ta dago kai gabaki daya sai sukaga idanun matasa da dumbin mata dake kofar gidan sarkin kasuwa sun dawo da idanunsu kan inayahn atake da wani irin mummunan kallon zargi....

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 👇🏻

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*


*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*


#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[24/10, 19:47] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️6️⃣
Da wani irin ƙarfi zuciyar ayaanah ya buga bisaga kallon reaction na zargi dake cikin kwayar idon mutanen da suke zubo musu ido sai taji ta mugun razana da yanayin inayan jikin ya dau rawa itakanta batasan sadda ta zube kasa tariko kafadun addan nata cikin ruɗewa ba...

"Subhanallah… lafiyá de kuwa adda? Méyé sàmèki haka..Mei yé sàmèki a cikin?”

muryanta maicike da tsoro da dumbin rauni yafito da rawa rawa ayayinda harshen buzancin nasu ya dada bayyana cikin kwababben hausarta ta abazata...


wani irin zafi inayah taji agefen acikinta dake tahowa tun daga wajen cibiyatta kamar ana zungurosa da icce irindai kamar ciwon ulcer ko irin ciwon cikin nan da ba asan asalinsa ba.

ganin idon mutane akansu yafara yawa yasaka inayahn tay ta maza tabi ta shanye dumbin zafin datakeji acikinta ta dagokai tana dan ƙoƙarin yin murmushi saidai ji take kamar bazata iya miƙewa tsaye ba..

kallonta ayanaah ta dingayi ganin wani irin sudaɗɗen hucin zufa yadan fansama asaman fuskar addanta me bayyana halin da take ciki na ciwo da tsananin zafi, tsamm inayah tay ganin irin kallon razana da anayahn take mata cikin dauriya tay saurin dauke idonta kasa ahnkli ta danne komi tadauki jakar tadan miƙe tsaye ahankli ahnkli dakyar tana cewa "hai kekam, à handi mboni baki da dauriya sham anyi babban matsoraciya ganin ayaanahn tanata kallonta har yanxu batace komi ba yasa ta kara mikewa
"karki damu Lafiyata lau… wataƙila yunwa ce ko saboda nagaji...

Abunka da yaranta wani irin nannauyar ajiyan zuciya ayanahn ta saki feeling a bit relieved ahnkli cikin sanyin murya tace tohm shikena,sannu da jin yunwa adda am. toh muje ciki ni zanje madafi na kawo mana abinci yau bake ba..ke aizaki huta yau ko??

a daddafe kuma a ɓoye inayah tay still a tsaye da hannunta ɗaya data zamarshi ta cikin hijabi tadan riƙe gefen cikin nata dake mata ciwon sosai sai murmushi kawai takey ma yar uwarta ayanah badon ciwon cikin ya tsaya mata ba sai danta dada kwantar mata da hankli.

not minding ydda ake satar kallonsu da yanayin gulma ahaka har suka saka kai suka karasa cikin gidan nasu atare. saidai dake yamma ne basu tarar da kowa agidan ba, lkcin duk dai ana kasuwa da alama dai izuwa nan bada wani jimawa kowa zaidawo dan ankusa kirar sallan magriba ynxu..

duk da rashin girma da wayon ayanaah yau sosai take saka ido akan yanayin addarta inayah da taga kamar ya dan canza, suna shiga harabar gidan tanema mata wajen zama akan dakalin kofar daki snn ta amshe jakunansu dukka ta kai daki ta ajeshi, aguje tadawo ta same ta tadan jingina da bango tana dan nishi har yanzu da hijabi ajikinta ta damke cikin nata taciki, da gudu gudu sauri sauri ayanah ta je wajen da ake aje musu kwanon abinci ta dauko musu tuwon dawa da jar miyan kubewa har da ruwan sha tazo ta ajeshi agaban addanta duk hanklinta ya tashi ta dauka kawai tsabar yunwace ke neman ya naƙasa mata addanta inayah..

ita kuwa inayah gashi dai ciwon cikin na mata kamar na yunwa yunwa amma koda ayaananh ta zubo musu abincin sai taji abincin kamar yana daga mata zuciya tana jin ɓacin rai sai tanaji kamar ta washe abincin aranta, saidai dake batason ta dagawa yar uwarta hankli yasaka ta daure
taci abincin kadan baifi loma biyu ba snn ta sha ruwa sai tace mata zataje ciki ta cire uniform ta dawo tunda ta taɓa abincin kadan. tafiya ahnkli ahnkli tayi har ta shiga dakin ta cire kayanta ta saka riga da zani jin ciwon cikin gabaki daya yane neman ya hanata tsayuwa da kyau, kawai sai ta nemi waje ta kwanta atake kuwa wani bacci me nauyi ya kwasheta abazata

wanda kusan abun al'ajabi ne kaga inayah tana bacci gabanin magriba sabida bata kaunar abunda zai saka tay lattin sallah a rayuwarta dan in batay sallahnta akan lokaci ba har kuka takeyi.. jim kadan koda su taawure suka dawo gidan gabanin magrin suka tarar da Ayaanah ita daya a haraba ta saka tuwon agabanta ta tsaya cak bata cigaba da ci ba, ta kuma rabza uban tagumi hawaye sun ciko acikin kwayar idanunta sosai abun yadaga musu hankli.

hajya mairo ce ta fara rufeta da tambaya toh ita bata gane komi ba, sai tahau gaya musu iya abunda ya faru, cewa takewa addanta tana jin yunwa amma taqi cin abinci dayawa kuma gashi nan bata baccin yamma sai yau taga tanayi, yadda ayanah ta daga musu hankli babu shiri taawure ta shiga dakin tahau tattaɓa jikin inayah ta na duddubata sai kuma taganta kalau, kaidai dakyar suka wanye maganan aka bari akan cewa ko yunwa ne ya haɗu mata da gajiya. hajy mai tuwo har da cewa kar asaka inayan aikin gida gobe da sassafe abarta tana dan samun isasshen bacci...

Bayan awanni biyu ana daf da ishai snn inayah ta farka lkcin zafin ciwon cikin nata yaƙara matsawa izuwa gefen dama kusa da kasan cikinta. but the pain is bit bearable, duk sai ta farka a ruɗe, ga kuma anxietyn rashin yin sallah akan lokaci kawai saita daure ta waske ta miƙe garau ta yi sallolinta har ta dan saki jiki ta zage ta koyawa ma anayah karatun sukayi basic _phytogoras theorem_ dan kawai hanklinsu taawure ya kwanta sosai.


washe gari basu barta tay aiki mai yawa ba duk dama ta nace saida tay yar shara da wanke wanke snn suka ci abinci nan ma sama sama taci snn suka wuce makaranta

yau suke cike wata daya da sati biyu a tudu, ana saura sati guda kenan ayi ma inayan saukar qur'ani, ga kuma tests na boko shima sun farashi dan anata tsammanin exams dinsu na zuwa ajin gaba yazoshi akan lokaci

sosai yaran suka kara zage damtse wajen karatu, saidai ata fannin inayah kmr kusan kominta ne takejin yana canzawa acikin jikinta, tun data fara ciwon ciki sai taji takasa gane ma jikinta gabaki daya amma dake tanada taurin zuciya sai ta matse komiii tana kaucewa duk wani abunda zai jawota baya a karatu dan batason tay wasting wann dumbin Risks da effort da kuma ubam kudaden da mahaifiyasu take zubawa akan batun ilimin datake basu.

kasancewarta ƴar fari, al'adar kunya da dumbin kawaici dake tsakanin uwa da ƴar fari bai ɓari sun shaƙu sosai da taawure ba, saidai fiye da kowa a duniya inayah ce take mugun mugun tausayawa ma mahaifyarta aranta, duba da tsauraran dokoki na al'ada da sukebi a kauyensu, da kuma irin jahilci, taurin kai da tsaurin ra'ayin irinna mahaifin su malam juma.

tasan bakaramin jarumta da soyayya me yawa taawure take musu aranta ba musmn data iya daukar wann babban Risk na rintse ido akan batun al'ada tare da saɓawa ra'ayin mijinta nazama acikin jahilci har tay burus tasakasu a makaranta a ɓoye donta ilimantar dasu addininsu da zamani duk dama abune wanda tasan zai iya ƙarar mata danata rayuwar, zai jawo mata mutuwar aurenta da juma, da kuma tsangwamar mutane duk sanda aka kamasu suna aikatawa.

shiyasa koda wann ciwon ciki ya fara mata taki sam tana nunawa a fili, babban burinta shine taga ta karfafawa taawure gwiwa, sun zamo silar farincikinta ita da yar uwarta ayanah, duniya da lahira. dan taawure jajirtacciyar uwace data musu dumbin sadaukarwan da bakowacce uwa bace zata iyashi.

bayan kwana biyu rayuwarsu ya cigaba ahaka, alamomin ciwo sunata zuwa ma inayah suna tafiya, wani lokaci ta ji sauƙi, wani lokaci zafin cikin nata sai ya dawo, musamman bayan cin abinci ko wani aikin wahala. wata rana koda ayaanah tayi kmr ta ganota sai ta ce mata gajiya ko ulcer ne.

satin sauƙar qur'ani na zagowa aka qaddamar, wanda kusan babban hidima hjy mairo me tuwo tay domin jikarta inayah

nan akayi mata gagarumin murna na zamowa gwarzuwan karatun qur'ani na gabaki daya yankin tudu, anyi abinci hilimi guda akay sadaka aka ciyar da almajirai sosai, kai dai tamkar bikin auren inayah haka hajy mairo ta daukaka abun har anko na kaya saida tay musu shadda me kyau. ayaanah duk tafi murna da cigaban da addanta ta samu na zamowa gwarzuwa kuma mahaddaciyar littafi me tsarki, ranar Taawure bakaramin dadi tare da alfahari da yarta inaya tay ba.
basu taɓa magana cikin nuna soyayya ta uwa da ƴa me tsayi ba ma sai aranar. bayan hidiman ne ciwon cikin ya fara taɓa inayah acikin dare sosai, wani bin da dadderen zata ji ciwon ciki da ba ta taɓa jin irinsa ba.

Cikin nata kamar ana murɗa shi da icce mai kaifi, haka zata kasa bacci tayita juyi tana huci, Ayanah takan ji tsoron duk abunda ke faruwa da yar uwarta inayah da kuma mugun tausayinta amma hakanan inayan take hanata gayawa kowa halin da suke ciki dake kuma suna farkawa da safe sai taganta garau har suje makaranta.

tunda aka ma inayah sauƙa sai ta dan bude karamin islamiyatta na dare, bayan isha

6 / 88