Author : NONE Category : African Stories & Novels
hotel ne tay 2 days,intay wkend a family house sai ta koma schll saidai duk da haka babu wani abunda ya sauya a tsakaninsu the more she ask him questions the more yake dada jadadda mata cewa yana da wacce yake kauna yanxu.
bayan kmr wata biyu suna abu daya sai abun taji kamr ya fara taɓa mata kwakwalwa worst enuf that she cant find the girl nd bisa ga dukkan alamu ibaad is damn serious abt his secret new rlshp.
ta saka ido kota ina bataga komi ba, saidai tunda akay waliman saukar su ayaanah taga irin special abubuwan da ibaad ya siya mata ranar sai taji bala'in kishi da haushi sai bata kara dawowa nigeria ba.
zazzabi me rai da lafya tay harna sati biyu insctint inta sosai yafara gaya mata kode ma ayaanah ce budurwan tasa dan taga kamar ibaad baiya wasu gentle nd soft loving behaviours din dayakey da kowa face ayaanah
And...God!!! she hates that girl so much,..tana jin tsanar ayaanah da zafi zafinsa har wuyarta yana mata kaikayi kullum.
ranar juma'a bataje lectures ba tanadai kwance akan couch dinta ta lullube jikinta da off white comfoter tay shiru cikin tunani, dan tsabar damuwar kishi da yunwa jikinta na rawa rawa kmr me ciwon masashhar kaji, daga ita sai masu mata aiki acikin apartment inta saiganan nala ta taho, ta danna bell ya kai sau uku zainab na ji bata miƙe ba har saida maid ta sauko kasa tazo ta bude nala ta watsa ma maid din harara ta karaso da masifa har ciki tasaka wani damammen riga da wando da wata babban jaka tanamai karewa zainab arifahn kallo "Babe ke kuma meye haka? ashe abunda rukky take gaya min ba karya bane kenan? what is wrong with you look at you so unkempt kamr ba ke ba?
wani soft tissure ppr zainab arifah tajawo tanamai tare sauran hawaye da majinan dake shirin sauka mata muryan ta adan dashe tace "nala kenan aike bazaki gane bane..i am lost..i am going insane. bana tsammanin ina da karfin cigaba da rayuwa ta, i am so confused nala ibaad is going to leave me wallah i can feel it in my hrt!!
da wani irin sauri nala ta karaso ta zauna kusa da ita cikin lallashi ta dafata da maraitacen murya tace
yanxu dan Allah akan sa kike wann abun ynxu fa almost 2 weeks kenan akace min baki da lafya..wai meyafaru ne tsakaninki da shi?? i tot u guys are cool by now ai.
cikin cizza labba da baqin ciki tace "no we are not nala, ahnkli ta dada rushewa da kuka tace "na shiga uku,na boyewa kowa damuwata ne sabida a tunani zan iya samun mafita..but nothing really works....nala hankalin ibaad yakoma kan wata yarinya, ya zanyi????
cikin matsanancin kuka take furta hakan gabaki daya saida hanklin nala yabi ya tashi ta rungumota..
tace 'its okay Zee-Arifah, its okay babe, kidena wann kukan kinsan dad dinki yaji labarin nan it will affect ur life nd studies.
cikin kukan tace "i know. nadaure nadaure amma bangane komi ba,..he keep spoiling one little brattttt, giving her all his attentions asif i dont even exist...ni ko ma yarinyar nan me yake cewa yana so? toh wallah in itane saina kasheta, she cant take him away. i will kill her..i will make sure she is deadddddd...
da karfi cikin girgiza ta nala tace "haba!! 'Enuf Arifah!!!! wai me haka ne, kiga yadda jikinki yake rawa fa.. snn kar ki manta ba a nigeria muke yanxu ba..u got to mind ur own words..why wud kill her when ure not even sure itace..
da zafi aranta tace amma ai yafi sakaltata fiye da kowa a duniyan nan nala, wallah ko kece kikaga yadda yake janta ajikinshi yake mata wani murmushi saikinji kamar zaki hadiyi ranki ki mutu...i even did everything to look as beautful as her inma wai kyaunta yake gani but he is not even looking at me.
nala tace okay maybe ure looking at the wrong girl..ni fa wallah ban yadda wnn gayen zaice yana son yarinyan nan ba, waima me take dashi, tsabar kyau kawai??Zee-Arifah babu mahalukin da zai ganki a duniyan nan yace baki hadu ba, plus kinfita gata, kin fita arziki
..girl next week fa babanki zai daura ki a akan kujerar daya daga cikin babban kamfaninsa nd u want to kill urself over a guy?downplaying ur value nd beauty over a village girl haba karki bada ni mana..i hate to say this, but gaskiyar rukky ce datace min kamar baki yarda dakanki ba. karki ga muna yawan kushe ra'ayin ruky amma sumtimes gaskiya take fada mana..zainab arifah akan
gayen nan kina bala'in zubda class dinki tun ba yau ba, ke ko dan ajn ajin nan baki masa
,..even rukky thinks ure soo classeles for him, dagske ne baki handling insa yadda ya kamata, tunda yace miki akwai wata macen ba kuka zaki zauna yi ba mafita zamu nema .
shiru zainab arifah tay dan tunda aka haifeta ba ataɓa tsaya an gaya mata maganan daya shige jikinta kao tsaye kamar wann ba, cak ta tsaya da gunjin kukan, ta zubawa nala ido can cikin jan numfashi tace "okay fine i think u might be ryt..i loved him soo soo much shiyasa banama iya gane me nake aikawa..tou ke yanzu me kika ganin zanyi? i really really want to knw that girl ko nawa ne san bata ta kyalemin mijina i knw i am meant to be his wife, in ibaad bai aureni ba zan mutu nala
nala ta riko hannunta tace zamu nemota but you wont kill her zainab..kisa fa yana da mummunan hatsari snn kituna strong international reputation na babanki da familynki gaba daya kika kashe wata wallh u have alot to looose.
Da wani irin hatsala tace "toh me kike so nayi nala?in zauna in zuba ido ya aure wata??lkcin dana bar nigeria ya riga ya gama housemship dinsa har ya fara nysc nd he will soon leave the country kuma bana cire tsammanin da aurensa zai taho UK karatu kamr yadda brother maheer yayi..u knw my family da wuri ake musu aure fa..and ibaad is very stubborn in yace zaiyi bamai hanashi
Nala tace okay calm down..i have n idea amma bansan ko kinada ra'ayinsa ba
desprerately zee arifah tace kigayamin kawai koma miyene ki gayamin zanyi.
ahnkli nala tace i know a woman in nepal, around northen india zata iya taimaka mana musan wacece yarinyar, ko kuma ta taimaka kawai a raba tsakaninsu all we need is just alot of money nd strict intentions
wani dan uban harara zainab arifah ta watsa mata da hatsala tace tuntuni kinsan da irin haka kika kyaleni inata damuwa??amma nala kema ai kinsan nafi karfin kowani irin kudi ko? ...a mugun dame tace so when are we leaving? ni wallah nafi damuwa da insan wacece yarinyar tunda kince min halama ba wancan bane
cikin kyabe baki nala tace "toh why not now tunda yau friday ne ba schl muje da wuri, dan acn acikin kathmandu take zama we need to book her early. inmunje yau muka huta gobe zuwa jibi sai tamana aiki.
cikn sauke ajiya zuciya zainab arifah tace cool toh muje ciki in shirya please help me call my maids daga nan suka mike suka haura sama kusan atare suka fara shirin tafiya india cikin gaggawa
Suna gama shiri jirgin karfe 6 na yamma ya saukesu a yankin garin kathmandu dake cikin north indian cos shi kathmandu is the capital city of nepal amma dake duk waje guda ne most ppl think is just north india.
gari ne me masifar kyau na gargajiya it doesnt shout luxury at all, manyan masana sunfi kirarsa da the Gateway city cos Kathmandu is the doorway to the beautifl Himalayas, mountain Everest, Annapurna, nd Langtang.
akwai manyn wajajen bautan gumaka da aljanu bana kadan ba. duk dama gari ne na tarihi but yanada tarihi na sihiri da tsafi, maita da duk wani naiuinkan evil jinns, devilish act, da bokan ci me bala'in karfi. addini awajen baiya wuce Hinduism da Buddhism cos they live side by side naturally ga monkey temple for (lord Boudhanath and Swayambhunath) ga ka babban lord shiva temple (Pashupatinath) na yan mabiya addinin hinduism wanda yafi kowanne mabiya a duniyar masu bautar gumaka
..wann gumaka da mai hankli yariga yasan cewa bakomi bane acikinsu face manya manya kuma bakaken tsofaffin aljanu da mutane suke kan bautawa.
garin kullum acike yake da baqi masu zuwa neman kowani irin mafitar rayuwa, da masu neman ilimin tsafi da masu neman normal ilimi, da writers, da su monks, wandarers da sauransu.
Da yamma suna isa nala ta bar zainab a local motel tafita neman lay practitioner da zai musu jagora gobe da sassafe
tunda tafice bata dawo ba sai can wajajen karfe sha biyu na dare.
baccinsu suka sha washe gari da safe mutumin yazo ya kirasu suka fito yakaisu can KOPAN Area inda taron buddist women suke nasu bokancin, kowace mace awajen ana ce mata ANI shiyasa ake ce matayen wajen ANI gompas..direct wajen wata ba indiya aka kaisu wacce itama budhism intakeyi
yauko karyawa basuyi ba aka kaisu wani dakin hutu aka basu herbal tea me masifar dadi suka sha after like 40 min of waiting aka musu iyo suka shigo ciki....
wata kiɓabbiyar mata ce a zaune akan jan dadduma kararrawa da jan candle yagewayeta
tana ganinsu tafara murmushi kamr wacce tasan me ya kawosu dake mahaifyar nala regular customer ce sunsan ta anan sosai shiyasa bata shan wahala indan tazo.
tun basu gaishe da matar ba suna zama ta fara gayawa zainab arifah damuwarta.
hanklin zainab ya kara harzuka ya tashi tafara rokon matar akan ta duba mata komi.
matsafiya Ani gompas tace mata ta kwantar da hanklinta, nan ta xana wani circle da farin chalk tace ma zainab din ta taso tazo ta zauna aciki..
tana zama aciki aka sa ta nade kafafunta a tsakiya, Ani gompass ta dau chalk din ta kara sana circle da cross a goshin zainab arifah snn ta saka ta lunshe idonta karta bude, tana yin hakan, ita kuma ta fara zana abubuwa kmr astrology stars tana yi tana wasu sibbace sibbace bayan ta gama ta umarce zainab ta bata tafin hannunta
tana mikowa ta danna sau buyu akan stars din snn ta sakata ta doka goshinta da aka mata zanen circle din akai duk tayisu babu garga dama.
bayan nan ta bata ruwa a wani bakin kwarya ta sha kadan snn tace musu suje dakij jira su jira fitowarta, suna fita ta dauko sauran ruwan tamike dashi ta shiga wani waje..
tunda suka zauna a falon jira nala sai ce mata take ai daga yanxu matsalarta da ibaad ya kare kenan har abada dan wann matar bata wasa ko kadan..
sunfi awa suna zaune da fargaban kalar sakamakon da zasuji duk dama sunriga sun saka aransu nasararsu kawai zasuji
can wata mata tazo ta kira nala wai tazo ta karbi aikan mamanta, sai aka bar zainab arifah anan azauna, nala tana shiga dakin kuwa ta samu matar a tsaye Da alaman Hankalinta yayi matukar tashi dan ko murmilushi bata iyawa
sun tsani suyi aiki a dawo musu dashi da wani evil energyn. it turns out sosai juma da taawure suka kulle jikin yaransu da kariya asalin irin tasu na fulani da buzaye.
ashe abu kam tayi duba an gano cewa tauraron ibaad dana zainab arifah ne ma kwata kwata basu hadu ba dan haka zaman aure ko yin auren ma tsakaninsu zaiyi matukar wuya
Ani gompas ta tabbatar mata cewa ibaad yana da matarsa and she cundt see even her bare ta gaya musu wacace sabida an rufe ta kirif da kariya, snn bazasu iya raba soyayr ba sabida me daurewa ce. ita kuma zainab wnm soyayar tata kamr karman ta ne.
da baqin ciki aran nala tace haba Ani amma dai kinsan hakan bazaiyu ba. dan idan naje na gaya ma zainab wann magana daga kaina zata fara kisan kai just do sumting abt it ...
babu bayanin da Ani gompas bata ma nala ba amma taki sam tace badai agaya ma zainab arifah wann batun ba tunda suna da power suyi kkri abasu wani abu da zaisa koda ace soyayyar ibaad zainab arifah ta dandana..
daga nan Gidan wani mutum aka kaisu Gidan kamar temple din bautar gumaka duk an sakaya shi da jan kyalle an kuma ajiye wasu halittun gumaka ga hayakin dake tashi daga manyan kaskon wuta wanda basusan me aciki Ba.
Wani tsohon ba indiye ne yafito kirjinsa babu riga yadaura wata farar kyalle akan kugunsa goshinsa an zana farin layi har zane biyu
Yaren su yake yi dan haka ba sujin meyake fada .
Wani daki ya nuna ma zainab arifah anan aka shiga aka fito da ita daure da jan yadi Ta fito narai narai Ko dan kwali babu akanta.
Ita dai binsu take amma badon ta gane komi ba domin kuwa idon nala akan ta yake takuma hanata yin questions akan komai..
wani shirgegen bath mai fadi da sakewa mutumin ya mata nuni yace ta shiga har sai da ruwan dake ciki ya rufe mata goshi
Aciki ta nitsu,ba abunda take yi sai yatsine, Sau uku mutumin yana sata tana nitso tana fitowa daga bisani sai yace ta fito ta zauna akasa
Tana zama ya shiga wasu irin addaoin irin nasu ma india,
yana turara ta da wani irin hayakin ganye.
nala tana zaune tana kallon su haka ma Ani gompass
Haka akayi ma zainab arifah wannan wankan sau biyu har na ranar sunday kafin nan suka biya kudi suka fara shiri zasu dawo gida.
wani kasko aka basu an rubuta sunanta dana ibaad akan jan kyalle sa bebin roba namji da mace aciki sunce daga taje dakinta daf ana kirar sallan magrib ta dau kaskon ta rike ta kalle gabar gudu da arewa ta kira sunan ibaad sau uku uku da zimman zaiji wann kiran a duk inda yake zaiji hanklinsa ya mugun tashi ya rasa nitsuwarsa bazai kuma taba samun nitsuwa ba har saiya taho inda zainab arifah take
nala duk bata gaya mata meye hakan yake nufi akan ibaad ba duk dama tay tay a fada mata menene wannan din kuma waye yarinyar amma sai shiru wani bin sai tace bazata gane ba.
Haka suka dawo UK babu wani kwakwaran bayani, nala warn her to take care of the clay pot kar ta bari a fasa ko ta zubar da abunda yake ciki.
daren ranar suna rabuwa zainab ta dau magananin ta saka a drawa inta tay banza dashi sabida batasan asalin amfanim da xai mataba, tafi maida hankli wajen son sanin wacece yarinyar.
washe gari monday a lalace ta tashi sabida tana da sakalci da lalaci dan haka wanka kawai tay ta wuce schll abunta bata kara duba kaskon na.
ata bangaren nala kuwa tsabar gulma tun jiya da dare da suna dawowa data bar gidan zainab arifah direct ta sauka agida kawarsu rukky jikinta na rawa ta fara bawa rukkyn labarin duk abunda yake faruwa
wanda haryau rukky mamaki takeji, na yadda nala take nuna tana tare da zainab arifah dari bisa dari amma a zahiron gaskiya kuma ta tsaneta, tana balain kishinta, da duk wani gatan datake dashi, infact batun cewa za'a dora zainab next week akan kujerar daya daga cikin mayan kamfanin babanta yana balain cixon nala aranta har yanzu
da murna da rawan jiki tace ma rukky kawata ingaya miki matar nan tace min she is just wasting her time on ibaad, yarinyar da yake so din ma tafi karfinsu, bansan wani karya zan mata bane yasa nayi shiru amma zuwa gobe idan nay tunani i will tell her cewa boka takasa raba soyayyar, then i wll be collecting alot of money from her cewa ni zanna zuwa nepal ina mata jigila untill i become god damn rich hahahahaah..
da mamaki rukyya tace toh yanxu intazo taga abu baiyu bafa, ke fa kinsan zainab arifah once she is angry kisa ne kawai ke zuwa mind inta..
snn banga amfanin soyayar da babu riba da kika karbo mata ba. wallah wahala zatasha koda yajuyo yana sonta. matar nan ta gaya miki they dont match, soyayya babu aure meye amfaninsa? kenan dukansu biyu kin lalata musu rayuwarsu gashi kuma zaki amshi kudi...nala i knw dis isnt my businsss but i think this it too much for zainab you went too far gaskiya
wani yatsina fuska nalan tay tace "wann fa ita taso, dan ni bai shafe ni ba. banyi kkri bane dana samu mata soyayyarshin ma ? abeg abeg i know she will be thanking me soon in ibaad ya fara kulata.
rukky sai batace komi ba ta kyabe baki suka gama hirar nala ta kwana agidanta washe gari sassafe ta koma england tabar rukky da tunani, she started to feel like in suka ma zainab arifah haka basu kyauta ba, or lets just get to the queen of pretence..
gaban madubi rukky ta je ta kura ma kanta ido cikin lumshe ido da budewa tafara tuna cewa fa itama son ibaad dinnan takey kamar zata mutu aranta, kuma yana daya daga cikin manyan dalili datake kushe lamarin zainab arifah dashi, she wanted to use logic ta cire ma zainab sonshi sai ita ta samu daman shigewa jikinshi amma inaa ga nala yau tanaso ta jawo mata babban matsala yanxu..
daukar wayarta tay ta kira zainab arifah jin datay ance tana school yasaka tay maza maza ta fada wanka zuciyarta cike da sake saken abunda zata aikata. tana fitowa ta tsantsara shiri, direct ta dauki spare key ta wuce gidan zainab arifah masu aiki ne kawai dake ma sunsan zainab bata da wasu kawaye face su daga sukaga rukkyn ta iso agaggauce sai basu damu ba.
rukky tana gama parking tun daga kofa tafara pretending kamar bata san zainab tana schl ba nan tafara kwallara kira zainab arifah...zeee baby, ..Arifah...masu aiki na kkrin gaya mata batanan tawani daka musu tsawa tace karsu sake su zo jikinta suna warin baki...
kai tsaye cikin izgili tawuce dakin kmr zainab din kawai take nema, sharply tayi dube dubenta har ta samu kaskon tsafin da sauri ta saka a katon jakarta ta fito da sauri, ta shiga wani sashe...kafin ta sauko can kasa, while still pretending tace ma masu aikin ina zainab take? nan suka mata bayani, cikin bude musu ido tace musu surprise tazo ta mata dan tagaya mata cewa tay