Author : NONE Category : African Stories & Novels
sashen hajiya da cooler data zuba nata abinci itama, wanda tun zuwanta sashen mgna akan lamarin ayaanah kawai ammin take ma hjya mairo amma hajia taqi jinta sam sai cewa take ai tsoron rayyanu ne yake lalata tunanin ayaanah shiyasa har take raina manya..
ayaanah tarasa abunda ke mata dadi, tafi minti 30 bata motsa akan gadonta ba wayarta na ajiye agabanta dacan harzata dauka takashe shi gabaki daya kenan saiga wani sabon saƙo yashigo pingggg da can kamar bazata duba ba da tunanin ko uncle moh ne tana kuwa daukawa taga lambar ibaad ne rubutu ne ke yawo akan screen din ya nuna "can i see u outside?? wani irin dadi taji tuni ta ture wayar gefe ta sauko kasa ta jawo chantilly veil dinta ta kara fesa turare snn ta fito tana takowa a sannu-sannu, gidan ya dau wani irin shiru veil ɗinta yana motsawa a iska tana kuma jin bugun zuciyarta na tahowa da karfi karfi
banda securitynsu a harabar gidan bataga alamar kowa ba ,gashi ta bar wayarnta aciki dan bataso tazo gabansa da wayar yaga shegen kiran da uncle moh ya isheta dashi bata san wani kalar bayani zatamasa akai ba.
Bata ganshi nan kusa ba har sai da ta karasa bakin gate. hadadden Motarsa na kunne, headlights dinsa kawai yabari ata ƙasa, yana zaune a ciki da kananan kaya fari kal din T shirt yasaka da blue jean, yay jimm kamar wanda ya dade yana jiranta awajen
tun tana bude gate din ya zuba mata ido yanata kallonta ta cikin gilashin mota har ta karaso cikin sanyin takunta me daukar hankali...bai janye ruwan idanunsa akanta ba har saida ta bude murfin motar ta shiga a hankali daddadar kamshin motar dana jikinshi atake ya wani gauraya da kamshinta. sallama tamasa tana zama ta dan lumshe idonta kadan tana jin nauyin dake karsashi a zuciyar na kkrin lafawa.
...kallonta yake har ta dago suna hade ido ta marairaice murya da sanyi tace "yaa good evening"..idonshi still fixed on her face yace "evening madam nd why did u ignored my calls?
...karamin ajiyan zuciya ta sauke tace "wayar ne nabari a falo lkcin hjiya ta kirani kuma i called u back baka dauka ba
cikin kyabe baki yace "olryt., na kira ammi ai tace min kinata fada da hajiya wai kinki cin abinci ko?, batace mai komi ba ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun ta..shiru ne ya dan ratsa wajen ya dada kallonta yace "Are u okay? daga idonta tay da wani irin shagwaba tabi ta marairace kmr yar 4yrs har zata kalle cikin kwayar idanunsa sai taji wani irin raunataccen hawaye yaciko mata ido kuma, da sauri yace aa aah malama dakata, kafin kifara min kuka anan kisani kaina na min ciwo ynxu haka daga asibiti na fito ko gida banje ba... yana maganan ya miƙa hannunsa baya ya jawo wani brown eatry bag a seat din bayan snn ya miƙa mata fuska ba yabo ba fallasa with his calm cute voice yace...will you eat this for me tonight? it contains ur favourite starters, fruit salad, nd tasty chicken..
hawayenta me sanyi datake dannewan ya zubo tare da murmushi ahnkli tace "i will
..thank you yaa..ba yabo ba fallasa ya gyada mata kai tare da jawota jikinshi ahankli tareda narkewa cikin qamshin turarensa ta lafar dakanta akan kirjinshi batasan sanda yaciro hankynsa ba ji tay yana share mata hawayen ahnkli kuma cikin tsananin kulawa muryansa kasa kasa yace
"once i get home we will have 5 min to chat, saiki gaya min menene matsalarki da kike son min kuka, nd dont forget to send me the pictures of you after uve eating everything here... kinji ko?
Dada jingina tay ajikinshi kadan cikin sauke ajiyan zuciya ta gyada masa kai, they remain like this for a while suna jin bugun zuciyar junansu dake yi da karfi kafin can ya bude lumsashun idanunsa tare da janyeta ajikinshi ahankli ya sauka ya bude mata kofa ta fito ya raka ta har bakin gate suna kallon juna muryanta kamar na wacce zatay mai kuka tace "thank you"
..murmushi me sanyi kawai ya mata tare da shafa gefen fuskarta da cool hands dinsa baice mata komi ba ya juya ya koma cikin car dinsa within minutes ya bar wajen,.ta doso cikin gidan kenan, uncle moh dake rike da wayarsa acan corridor ya hangota daga can sama ta waje.
he was shocked daya ganta ta fito daga ta bakin gate da kuma babban ledan eatry a hannunta, jikinshi har na rawa rawa yafara saukowa da sauri, idonshi a rufe ya bi matakala yayo waje ita kuwa a dede main door taci karo da mujaheed shima ya tsareta yana kkrin tambayarta da mmki ina ta fito dan yasan 6pm ne deal breaker agidan mace bata fita koina inba da kwakkwarn dalili ba..
bata kuwa boyewa mujaheed ba tagaya masa yaa ibaad ne ya kirata waje harma ya tafi, dake zuciyarsa a wanke yake bai dau abun da wani issure ba har yasa ta bude bag din yagani sai ta bashi pack na chokolate guda daya
..immidietly ya bude yakai bakinsa ya gutsira yana kkrin bata da wasa kenan sai ga uncle moh ya iso wajen, wani irin mugun kallo ya masa da kakkausar murya yace "kaii mujaheed me kake yi anan
wani irin firgita mujaheed yay
ayaana tay saurin dauke kanta suna hade ido da babansa ya dan sosa keya yace bbu komi baba i am just coming in ne fa yanxun nan na dawo, atake atake wata wutar zargi ya cakka kahon zuciyar uncle moh, "coming in frm where? sai yay asuming cewa fita yawon shagalinsu awani waje sukayi da ayaanan shiyasa ma hala taki daukar wayarsa gashi har ya siya mata abu sundawo suna ci atare
...da bacin rai yace "ure very stupid mujaheed get inside..ya kalle ayanah da tulin kishi a idanunsa yace" ke kuma ba anhanaku fita da dare ba..
where is ur phone? muryanta na rawa rawa tace "yana cikin daki..tsabar kishi muryansa harna rawa yace ohh barin wayar kikay aciki kika bishi kuka fita. hmm bakomi, get inside ryt now...yanayin yadda yay maganan da authourity da kuma zargi yasaka tay sauri ta shiga cikin itama da mugun sauri..
bayan ya koresu haka ya dinga safa da marwa a harabar gidan yanajin kirjinsa na tafasa, wai shin duk wahalar rainon zcyr ayaanah dayayin nn tun tana karama sai dansa mujaheed ne zaizo yasa ya tashi abanza kenan...
wato harma ayaana zata iya sneaking da dare ta fice yawon banzanta da dare da mujaheed amma shi babu yadda baiyi da ita suje ko ice cream sunasha awaje ba amma sai taki wato ma yarinyan na ta mugun raina masa hankali kenan kome?
da matsanancin fushi tare da zazaafar zargi ya hana kansa sakat a tsakar compound har sai da yaji kansa da zcyarsa yana neman fashewa da fushi snn ya daga wayarsa maza maza ya tura ma Alhaj ameer text an suyi chatting akwai wata magana very urgent
within few minutes alhaj ameer din kuwa yay reponding, tun suna chat yana ranting har ya koma ciki ya dauko key din mota ya shiga motarsa ya kulle kansa dan suyi waya kawai anema masa mafita
ayayinda yake jin matsanancin kishi, zargi da kuma haushin ayaanah alhaji ameer kuma is busy telling him cewa ai dama yarinyace dolene hanklinta yafi karkata gun samari dede da ita, kawai mafita daya ne yay gaggagwa cikin satin nan ya daga mujaheed agidan tun kafin komi ya lalace.
fannin ayaana kuwa tunda ta wuce ciki bata wani samu sararin nazari akan reaction din nasa bama dan tana shiga dakinsu kirar ibaad ya shigo kuma yabi ya umarceta akan taje room dinsa taci abincin awajen suyi video call he want yo watch her eat aikuwa atake ta tattara ta koma room dinsa ta zauna da abincin agabanta tun ana wayar 5 min basu da gamawa har saida karfe 10.30 na dare yay
baima tsaya jin tarkacen labarin abunda ya farun tsakaninta da hajya ma he just focuse on making sure she has eaten nd her mood was uplifted, sha daya saura bayan sun gama video call in ta koma dakinsu yau ba karamin farinciki tay bacci dashi a daren ba, she slept smilling with alll the sudden care nd flirtious gesture da ibaad ya dinga nuna mata kmr wanda yasan abunda ke faruwa da ita..
bayan kwana biyu haka kawai taga uncle moh ya wani irin dauke mata wuta, baya kiranta awaya, in sun hadu ma saida ta gaishesa a ladabce ta wuce,
shikuwa satin gabaki daya wai fushi yakey da tsananin kishi ga zargi, yabi ya saka ma mujaheed kahon zuƙa duk motsinsa sai ya saka ido akai, babu dama yaji mujaheed baya na ydinga kiransa kenan just to make sure baya tare da ayaana
yana ayyana hakan at same time shida abokinsa alhaj ameer suna ta famar gathering all transcripts, course descriptions, credit hours daga makarntar da mujaheed yake ynxu infact they have already writen a formal letter of intent/explanation to ta Chinese university on why he want to transfer his son and to esure they meet all their requirements.
ma agent dinsu ya barma aiki kiraye kirayen International Admissions Office of the Chinese ya zuba kudinsa bana wasa ba dan a samar masa Zhejiang University of Technology agaggauce
dan tsabar zafin kishi da zargi har can can china yake kkrin tura mujaheed, gashi yana sane da cewa in yaje za'a maida karatunsa baya but he dont care
agarin cuccusa kai da tsabar neman alfarma agaggauta abun yasa har anty safeera ta fara dagoshi, afarko ta kasa gane meye ne yake faruwa tsakaninsa da mujaheed da kwana biyu ya zama so hyper reactive, ya dena sake ma mujaheed fuska ga takuri ga yawan kiransa awaya akai akai muddin baya gida
his real intentions nd reason basu fito mata asarari ba, amma wani abu yana bata cewa dolene akwai wani babban matsala daya shiga tsakanin uncle moh da mujaheed.
a sati na biyun while ayaana na kkrin fara test a schll anfara maganan biya mata su waec da neco da jamb, cos in aprox 6-7 month ake tsammanin zata gama secndry schl, unknown tension da sudden canjin fuska tsakanin mujahd da babansaa yabi ya hana anty safeera kwanciyar hankli daga can kuma shirin gaggauta daga mujaheed a nigeria yay nisa sosai, harma sun samu admission din duk bai sanar da kowa ba ya fara batun kama ma mujaheed permnt haya acan inda sai yay watanni fiye da goma ba bai dawo gida ba.
da balain zafi ya dauki abun aransa, gani yake babu mahaluki da ya isa yay masa asarar qudirinsa na samun auren ayaanah musmn yadda yaga kayan marmari ajikinta na bala'in habbaka, nonon ta ya fara cike kirji gasu round gasu a tsaye, gata da tumin shape komin ta dai dai kuma me masifar daukar hankali kuma tana da tsayi kusan halittar jikin mahaifiyarta tawure ta dauko zak zak..the more she grow the more sexy nd fresh she look. gabaki daya ya kwadaita da samun wann yarinyar a turakar sa gani yake randa ya same ayaana akan gado toh kakarsa ta yanke saka, gabaki daya tsufarsa sai ya zabgeshi adanyen jikinta kasa da kusan shekaru ashirin nd he want to have cute cute kids with her...
wann satin anty safeera kusan kullum sai ta tambaye mujaheed ko wani abu ya shiga tsakaninsa da babansa shikuma haryau bai san mezaice ba,dan baima kawo tunanin zai iya taɓa kasancewa akan ayaana ba.
ranar juma'a da sassafe anty safeerah tafarka da laulayi sosai tanata amai yau kowani baccin kirki basuyi ba amma memakon ya tsaya ya bata cikakken hanklinsa sai kuma ya kasance yana murna na ganin fitowar ticket din mujaheed ranar sunday da sassafe wajen karfe 7.30am ranar sunday jirgi zai daukesa double way trip ne, jirgi biyu, daya zai saukesa sai daya yakaisa china he will first of all go to Abuja then Istanbul kafin ya samu direct plane to Beijing
inteconecting flight is almost 18hrs journey on plane.
anty safeerah ta koma dakinta kenan zata dan watsa ruwan dumi da sassafen mujaheed na fitowa a masjid uncle moh ya kirasa a sashen hajy mairo, bayan sun gaggaisa kawai ya fara musu bayani wai zai tura mujaheed china ranar sunday, kamr almara mujaheed ya dinga jin maganan a kunnensa..worst part yadda atake ya jujjuya zancen ya dawo dashi kamr zai turasa ne kawai dan yaje yay ilimi me inganci kuma harma ya gama komi, wanda hakan yasaka hajiya mairo ta hau kai da murna da tunanin babban gata akayi wa mujaheed..
duk dama kan mujaheed ya balain rikicewa agaban hjy baiy nuna komi ba har saida suka dawo sashensu snn ya samu baban nasa a daki ya gaya masa cewa gaskiya shi bazai iya komawa china kwasam karatu ba...duk dama gentle parenting ake musu, ana barinsu suna fadin raayinsu amma wnan karon uncle moh haura masa yayi da buhun masifa har da gaura masa mari yace masa umarni ne yake bashi ba neman shawara ba...
abu tun yana wasa wasa mujaheed ya dga hanklinsa duk gidan sai da aka shiga tashin hankali sosai it turns out babu wanda yabi bayan uncle moh sai hajy mairo tace sam ba ayi ma muhammadu adalci yana kawo cigaba agidan ana kushe shi...kan anty safeera kamr zai fashe
,mujaheed yana magana yana kuka shima uncle moh yana magana yana daga jijiyar wuya wai an rainashi har ta rasa na waye guda daya zata ji
karshe dakyar saida bappa zaidu da yazo weknds ya tarasu duka aka warware magann shidakansa ya lallaba mujaheed ya bashi haquri sosai snn ya amince zai tafi amma ba har ransa yaso ba saidan out of immense respect dayake ma bappa zaidun kawai ya amince dake ma yaga bappa zaidun ya nuna ya fahimce shi sosai..
inkaga mujaheed tsakanin friday da sartuday dolenka ne ka tausaya masa gabaki daya ya fita a ahayyncin sa, fushi, rudani da baqin cikin rushe masa karatunsa anan tare da maidashi baya yasa ranar sunday ne daya tashi yin tafiyarsa ma mahaifyarsa da sauran kawai yay wa sallama baice uffan ba babansa da hajya mairo ba ya wuce abuja, ever since ya kama hanyar abujan ya kashe wayarsa for hours ranar sunday babu wanda ya samesa
ranar kusan wuni anty safeera tay tanata kuka ta rasa abunda yake mata dadi, babu yanda bata danta langwasa mijinta ya gaya mata meyasa yay ma mujaheed haka ba amma inaa yaqi sam ya kula kowa duk da abun yamasa zafi sosai da mujaheed ya tafi bai masa sallama ba.
kin kunna waya da mujaheed yay all thru his jouneuy bakaramin cusa gidan yay acikin tsananin fargaba da baqin ciki ba, hajy mairo kullum tana jigila asashen anty safeera tana bata haquri..
for almost 15hrs babu labarin mujaheed lissafin duniya anty safeera tay harta fara tunanin koma duniya zai shiga bazai jeshi wani karatu a chinan ba
hanklin uncle moh yabi ya tashi, he is feeling the urge to keep calling his agents, ko kuma koda ya rarrashe matar sa ta dena yawan kukan nan datakeyi tun jiya amma ina, abokinsa yace mai kar ya sake emotional draman mace ya rushe masa qudurinsa ai ita macece zatayi ta bari.
tashin hankli bai kare agidan ba face har saida bappa zaidu yazo gidan da yamma ranar monday da news din cewa yayi yawa da mujaheed yana lafya kuma ya isa china kalau.. dagajin haka hanklin uncle moh ya kwanta. anty safeera kuma ta kasa nitsuwa harsaida mujaheed ya huce can cikin dare ya kirata sukayi magana yay assuring inta ya isa snn ta kwantar da hanklinta, altho tay tay mujaheed ya sake ransa yaqi, daga ta masa da maganan ya kira babansa da bacin rai ko kuka zasu rabu...kawai gani yake kamar da akwai wani boyayyen lefi daya masa babansa da har yamasa wnn mugunta, cos he cant just send him far away from home gatsau, kuma ya maida masa karatu baya batare da wani kwakkwan dalili ba. kwana biyu anty safera tafara sawa aranta wai koda zata lallaba mijinta taji dalili abakinsa, she have been tryn her best amma yaki sam ya bata fuska, sai kawo mata wasu dalili yake har yasa ta fara zarginsa da wani abu duk dama bata kawo ayaana bane
aikuwa a satin data dage agarin bincike kwasam ta samo information cewa da alhaj ameer aka hada komi kuma acikin gaggawa...
tundata bincika ta gane kmr abokaine suka zugashi
ranar data dage zata je asbitin a dubatan she became all hormonal sassafe ta tashi da bori sosai, uncle moh ya shirya zai fita tay confronting dinsa akan batun sako abokai cikin harkan rayuwr su da na yaransu, tun suna magana na fahimta abunka da me sabon ciki aka fara haurawa juna, ya dinga mata ihu yace ta dena ce masa bai isa ya yanke hukci a akan rayuwar mujaheed
cikin gushewar hankli da subucewar baki ta fara shigo masa da gori da kuma barazanar cewa zata kai kara wajen mahaifinta kawai adawo mata da danta tunda bayaso, ita ba zaa saka danta karatun dole a inda baiso ba.
ran uncle moh ya baci ganin ta hatsala ta dauki mayafi shikuwa yace mata taje gidan amma tasani kafin ta dawo wallah aure zaiyi kuma zai aure wacce zatazo ne ta masa biyayya agidan nan ba wacce zata nuna masa gadara da iko da dukiyar ubanta ba.
tunda ya furta mata wann maganan kara auren ya fita taji cikin ta da duniyan na ma gabaki daya na juyawa
ficewarsa agidan da fushi bada jimawa ba aka kirashi awaya ahujajan cewa anty safeerah tana asibiti ruwa ruwa har ta samu miscarriage...tundaga inda aka gaya masa jikinshi ya fara rawa rawa dan bawai baya kaunar matarsa bane, kawai dai zuciya ce irin tasa, wanda bata da linzami ko kadan. a hujajan ya wuce asbiti
ya samu an shiga da ita ciki za'a wanke mata ciki hajy mairo ne da ammi babba kowa yana neman jin meyafaru da doc yake batun ma safeerah ciwon hawan jini...
tunda ya iso asbirin yake safa da marwa akan likitoci dan sosai ya shiga hanklinsa ido ya raina fata, ganin ana batun complication na hawan jini, tsoro ya kamashi marmaza ya jawo hajy mairo gefe ya zaunar da ita ya fara