Author : NONE Category : African Stories & Novels
ba, inma ana tunanin anyi kulle kulle ne akan yarsa dan aga karshensa toh shiyasan yadda zaiy da mutum
yafi minti ashirin yana ma hajiya mairo magana da izza da zafin rai, yanamai dada gaya mata cewa akan dukiyar sa aka kulla komi, they cant stand the fact that shima Allah ya bashi yarinya me ilimi da tarbiya, hassada da kiyayyar da ake masa agidan ne yasaka ba acigaba, kuma wallah akan maganan zai saka ido, koda kuwa ya bada yarsa aure su sani ba a son ransa bane dan shi yasan cutarsa kawai za'ayi
maganganu dayawa dayake fadan sosai yah ma bappa zaidu zafi dan yaga alamar borin hauka kawai yakey, technically, shine yazo musu yana neman alfarman a aure yarsa amma sai yazo yana wani burga yana zage zage yana habaice habaice yana zargin kowa akan dukiya yana nuna musu kamar shine kawai zai rufa musu asiri yay musu alfarma...
hajiya mairo sai kuka take tana karkada kai batace komi ba gani take kamar eh dagaske ne anaso acuce zayyanu ne kawai akan yarsa zainab
ransa a bace ya cigaba da cewa "Dole ne asan yadda za'ayi hajiya, inaso yata ta dawo hayyacinta, snn duk wani maison ganin bayana shi zai fara faduwa ni xanyi ma yata duk wani gata har karshen rayuwarta dan haka aja kunnen yaro dan wallah next time wani abu makamancin haka ya sake faruwa hajiya kece kika haifi ni amma koke wallah baki isa ki hanani daukar tsatsaurar mataki akan yaron nan ba dan bazai kashe min yata a banza ba haukar banza haukar wofi.
cikin kukan tace kai zayyanu ya isheka haka, maganan nan ya kare, ni wallah ma tausayin yarinyar nakeji yanxu duk wata masifa da kukeji dashi ku aje kuhada kai kawai ayi auren nan, zaidu kaine uban yaro a hannunka yataso kuma yanxu kaine me wuƙa da nama ga zayyanu ya kawo batun yuyuwar auren zainab da rayyanu banji kace komi ba...dan Allah ayi ayi asaka musu rana dan yarinyar nan karta zauce ta haukace tafara shiga bololi tana tsince tsince
dago kai bappa zaidu yay cikin haɗiye bacin ran dake cinsa aransa yace "hajiya na gode da kika tabbatar ma kowa da hakan, haihuwar ibaad ne kawai banyi ba amma nina raineshi tun bai mallake hankalin kansa ba, tnk god da bakinki kince nine me wuƙa da nama..hajiya kiyi hakuri magana ta nasan bazai miki dadi ba amma hukuncin dana yanke shine ibaad bazai aure zainab arifah ba. tunda ubanta yace ita mai ilimi da tarbiyace suje ta sako ilimi da tarbiyan acikin rayuwata i assure u with time xata samu sauki, snn kuma shi uban nata dayake cewa shime dukiya ne kenan yana da halin da zai kai yarsa har bangon duniya dan ta samu lafiya kenan suna da wata hanyar mafita ba lallai sai an kulla aure ba..ni bana son auren da za'a dora ma yaro na dole akansa, snn azo ana zarginsa da kwadayin dukiyan wani ko azo ace hassada ne yasa muka badashi..to avoid all this gara ma kar afara..dama ynxu yagama cemiki baida niyyar hada jininsa damu toh banga amfanin basu auren ibaad ba tunda awajensa ibaad baida amfani, baida daraja, toh meye kuma na neman taimakon aure awajensa... ai a kyalesa kawai ya zauna da halinsa ita kuma zainab Allah ya bata lafiya tareda mijin aure nagari.
miƙewa tsaye hajiya tay in shock tace kan uban can zaidu wai abuge kake ne? waime kake cewa ne ana neman sulhu mai dorewa kai kana warwarewa ba duka rifin asirin mu bane in ayi auren nasu?
yana daga zaune yace aa hajy, wallah auren nan ba rufin asirin ibaad ne dan yafi karfin wani dan adam ya rufa masa asiri..danki ne dai yake ganin kamar zai rufa mana asiri zai mana alfarma hamshakiyar yarsa zata aure ibaad ta rufa masa asiri to wallah bazaiyu ba bama bukatar rufin asirinsu sukai kasuwa.
idonta arufe ta hargitso kansa zata shalla masa mari, uncle moh yau sauri ya riketa hajiya tafara ihu zaidu zaidu ka janye wannan maganan nan bana wasa dakai zaidu kay gaggawar janye maganan nan kafin inci maka mutunci
miƙewa tsaye bappa zaidu yay yana kallonta da taurin kai yace "Babu wanda ya isa yasaka ayi auren nan, inde wai zayyanu shine zai rufa ma ibaad asiri toh abari ibaad har ya mutu asirinsa bai rufu a duniya ba..what nonsense!!
yana gama fadin hakan yawuce ransa a bace yafita daga gidan.
gabaki daya gidan ya karade da ihunta "zaidu,..zaidu mani kake gaya ma wann magana kai zaidu ka dawo nan nace maka zaiduuuuu...
uncle moh na riirrike ta fashe da kukan mai tafe da bori prof daya sha mamakin maganan bappa zaidu ya mike da fushi muryansa harna rawa yace "hajiya ba kinga irin abunda nake gaya mikin ba..babban burin zaidu shine yaga na rasa ƴata, hassada da baqin ciki da kyashinsa yasa har ya mutu baxai taɓa zamowa kamr ni ba. kinga irin rainon da kika masa ko? dama baba saida ya fada baki iya raino ba, aida baba yana raye da ba'a isa amin wann abun ba dama kuma kece kike daure ma kowa gindi ni kin wareni sabida dama can kin tsaneni dan kawai na zabi in kare dukiyata daga wanda basa kaunata
tana kukan tace kar ka sake kagayamin bakar magana xayyanu, ubankan bashi ya lalata ka ba? kaima da kashi a tsuliyarka.. aure kuma dukanku baku isa ku hana yuwarsa ba innhar nace za'ayi ni na haifeku ba ku kuka haifeni ba.
zai magana da tsawa ta daka masa tace maza kasamu guri ka zauna ka gayamin me kake ciki shikuma zaidu zan gamu dashi bai isa ya raina ni haka ba wallah kryansa.
dakyar kura ya lafa ya zauna yana ciccin magani yafara gaya mata dokokinsa da zai shimfida, na farko ya jadadda mata cewa auren nan bada son ransa bane alfarma zaiyi, snn babu wani hidimar family da za'ayi, taron daurin aure kawai za'ayi snn zai gayyato manyan mutanen sa a bainar jama'a a masallaci, snn shi xai dauki nauyin komi har gidan da zasu zauna aciki sabida yarsa ta zama comfortable, zatayi aiki, xatay karatu snn zai hada su da likita da zain yawan zuwa duba lfyarta kwakwalta akai akai. snn duk wani kudin kashewa da sutura da komi shi zai nayi wa yarsa baya son komi awajensu face a tabbata yarsa ta kasance cikin koshin lafya kuma tana raye,..yace ma hajiya mairo ta dauke wann maganan a matsayin kwaji, inshi danta ne dagske zai gani dan ta hanyar wann auren ne kawai zai tabbatar da cewa ba son kashe masa yarsa sukeso suyi ba, snn hassada da tsana da bambamci ake nuna masa ba gaskiya bane.
duk taji abunda ya fadan amma bata yanke wani hukuci ba tace masa yaje zatay tunani daga ta gama kawai saka rana za'ayi ya gayyato mutanensa ranar daurin aure a daura.
su ukunsu suka dinƙe maganar kafin nan prof ya fita ya dawo gida..
yanayin tashin hankali da rudanin ganin kalar zafin kai da zaidu ya nuna mata datake ciki yasaka uncle moh bai bijiro da nashi batun auren ba
can after like 2hrs bayan komi ya lafa ta kira ammi karama ta sakota agaba tace lallai lallai ta kira mata zaidu awaya yazo tana son magana dashi, tunda ita inta kirashi baya daukawa. duk sanda ammi ta kirashi zai dauka sai tagaya mai sakon yace toh zaixo amma haka suka sha jiransa baizo ba kuma still ya hana ibaad karasowa.
har saida akaci kusan kwana uku bappa zaidu yaki amsa wayar hjiya kuma yaqi yazo gidan gashi ya hana ibaad motsawa, ko maheer da yaxo shima bai barsa yaxo ba kwana biyu shikam ma yay ya koma. akwana na ukun ne abun ya isheta, tana tashuwa daga shago ta naɗe garinta da yamma taxo gidansa ko amsa gaisuwar ammi babba batay ba ta inada take shiga bata nan take fita ba harsaida bappa zaidu ya dawo daga aiki yazo ya sameta a falo
Duk masifar duniya ta masa baice mata uffan ba, dan koda yay kkrin nuna mata rainin wayon dayake cikin proposal din prof kai tsaye cemasa tay yanawa dan uwansa zayyanu mugunta da hassada. yana so ya jawo lamarin da zai saka zayyanu ya rasa haihuwa a duniya, she called him selfish nd heartless. ko ajikinsa bayan ishai ya saka aka kira masa ibaad ya shigo falon yaxo ya samesu suna xaune
fushi takey ko amsa gaisuwar ibaad din batayi ba shikuma dayafita danyen kai sai ya shareta bai kara ce mata uffan a falon ba
agabanta bappa zaidu ya maimaita duka ababen da prof yagaya nabatun cewa bada son ransa ma zai hada jini dasu ba, saidan sabida zargin zasu kashe masa yarsa ne akan dukiya, snn auren nan ma fa alfarma zai bayar dan yarsa ta samu lafiya amma badan yaso ba.
witout any bias ya tambaye ibaad ko ya amince da wannan batun aure snn yasani inhar ya amince shi bazai hanasa ba, dama shi auren dolene baya son yay masa.
tun kafin ibaad ya amsa tafara tsigeshi tana cewa bai isa yaki auren zainab ba tunda shi ya lalata mata rayuwa ya jawo mata ciwon hauka dolene ya aureta su rufawa juna asiri.
ibaad baiko kalleta ba yace ma bappa zaidu shi bai amince ba kawai Abata hakuri Allah ya bata miji nagari
bappa zaidu yace" hjy toh kinji da bakinki yace bazai aureta ba saiki isar musu ds sako.
hajya tay wani irin kukan kura zata cakumo ibaad din yay saurin miƙewa tsaye yanamai kare mata wani irin dakakken kallo wanda batasan sanda ta rusa ihu ba...ni kake min irin wann tsinannren kallon? au dukana zakayi?dukana zakayi rayyanu..tafara tutture shi, toh dakeni. nace ka dakeni..
..darajar bappa zaidu yasa ibaad yay shiru baice mata uffan ba ya tsaya yana kallonta tana hargagi.
she is doing all this to make them know she is very serious and hurt, musmm ma shi rayyanun dataga kmr bai dauki abun da muhimnci bama .
tashuwa bappa zaidun yay ya rikota tana masifa tana ihu tana cewa rayyanu wallah yadda ka lalata ma yarinyar nan rayuwarta ta haukace dolenka ne sai ka aureta
...inkun ga dama kaida zaidu kuyitayi amma maganan aure kam yana nan daram..
tanakaiwa nan ta bankade bappa zaidun ta fita agidan tana matse ido da bakin hijabinta tana zage zage..
haka lamarin ya kasance kullum cikin tashin hankali, hajiya tana gida kullum tana bori tana rantsuwar sai anyi auren nan, amma bappa zaidu yayi burus yace ai tunda ibaad yace baiyaso baiga uban daya isa yasa a daura masa aure da zainab ba.
week din su ayaana suka gama practicals na neco zasu fara wrting amma gaba daya hanklinta baya jikinta sabida inba a awaya ba bata samun jin muryan ibaad shima kuma ba kullum sabida bappa zaidu har wkend in ma ya datse yahana ibaad lekowa family house sabida baison suyi wani hayaniyar da zata yi amfani da ammi karama ta tursashi
duk wani hanyar wayon hajiya mairo akan auren bappa zaidu ya toshe wanda yasaka duk su uncle moh suka farajin mugun haushinsa, gashi anty safeera tana yawan fita kusan koyaushe taje gidan prof zata dawo musu da labari marar dadi game da jikin zainab arifah.
satin gabaki daya zainab ta lalace dake pretending take she had takes more hard drugs dan tay acting din da kyau wanda kwayar ya fara ramar da ita, sai taki cin abinci tayi ta amai tana birgima da fake ciwon kai da suman karya.
prof zayyanu yajira yaga kiran hajiya batun saka ranar aure amma sai shiru, gashi bai gaya ma zainab din yaje har yay maganan aurenta ba, so yake har sai abun ya kankama snn ya gaya mata dan itama yana da tsauraran dokokin dayake so yasaka mata wanda dolene ta bishi inhar auren ta zaba.
kwana sha biyu da faruwar komi lkcin su ayaana sunfara writing exams dinsu anata shirye shiryen final graduation duk hanklinta bai jikinta sosai ibaad kuma yana can yayi nisa a rubibin kammala nysc tareda tests da su exams dat will get him qualified for his intnl admission da zai yi major course dinsa a kasar waje.
kamar da wasa Hajiya mairo tay ta jiran tsammanin ko zaidu zai shiga hanklinsa ya sauko ya kyale ayi maganan auren nan amma sai shiru..
bata taɓa sanin cewa zaidu yana da wann kalar taurin kan ba ko kadan.
cikin kwanakin nan gabaki daya yabi ya sauya mata, ya canza daga mutum mai kawaici da tsananin biyayya agareta data san dashi ya dawo me taurin kai da kafiya, dan haryau tunda yay magana daya tak bai sauya ba, duk fitina duk bala'i duk tashin hankli datake tayarwa agidan kullum abanza yake karewa..
nd worst part ma da ibaad yay banza da abun dan ko lkcin amsa baqar magnrta bai fiye samu ba bare ma yazo har gidan.
kusan satikai biyu ana wann case din, wanda ya bala'in jawo jiji da kai da ikon da prof yake ji dashi yay sanyi, atunaninsa yana da wani izza da ikon da zai saka hajiya mairo kai tsaye ta amshi batunsa ya zama maganansa kawai akaji, ya dauka dayaje gidan aka zauna akayi magana duk zasu rusuna ne abishi asaka rana.
yana tsammanin cewa kowane acikinsu yakejin matsanncin shakkarsa, he expect them to be worshiping his words as per thr richest son of the entire family, tunda yasan iyayensa sai yasan iya abunda yaga dama yake zanta musu, a tunaninsa aiyafi sauran yan uwansa daraja ne kuma ya isa ne shiyasa tun dacan iyayensu suke yawan bin bayansa akowani case inya taso.
saidai ayan kwanakin nan sosai dan uwansa zaidu ya bashi mamaki, despite all the threats, nd tantrums na hajiya amma wai zaidu bai rusuna ya musu biyayya akan maganan ba..
hankalin prof ya tashi matuka, musmn daya ga kamar he wont be able to have full control of the marriage ayi komi cikin tafin hannunsa kmr yadda yay tsammani, dan yanaso ne ace kowa na karkashin ikonsa ne sai abunda ya gindiya musu gameda yarsa kawai zasuyi.
arana na sha hudu da faruwar Abun tunda anty safeera tazo gidan zainab arifah tay lumi tafara musu eaves droping har saida taji kishin kishin lkcin anty safeeran take kan gaya ma hajiya hamida cewa ga abubuwan dake faruwa acan agida bappa zaidu yace kaza kaza ibaad ma yace bazai aure zainab din ba haryau kuma babu wata cigaban magana akan haka. tunda zainab taji haka tsoron yuwar rugujewar shirin ta sai ya bala'in rufeta
tarasa meyake mata dadi, tay kukan, ta shiga tsananin mamakin jin wai harma kenan tay yunkurin kashe kanta amma ibaad baisauko ya rusuna ba, to kenan batasan kuma me zatay yanxu ba.
her eyes were shut nd soaked in tears cikin rasa nayi tafara jin gara kawai tabar duniyan indai zata rayuwa taga ibaad da wata macen da ba ita ba, gara ta bar duniyan kawai. it was very hard for her to decide to end her life for real tunani tay wanda yakaita har safiya, as early as 5 am ta jawo wani allura da drugs da ake ma sport horses, lkcin tasan an kusa zuwa a dubata dan 6am ake zuwa duba jikinta tana miƙewa zaune kuwa ta danna ruwan alluran a hannunta witout regret for 5 min tana zaune can kafin yafara reacting tafara birgima kasa kafin kace wani abu ta dauke gabaki daya jikinta ya dawo kamar kankara da alama her body is shutting down dakansa dan wann karon dagske takey ba wasa ba.
haka aka sake farkawa da wata sabuwar tashin hankali agidan da sassafen aka rushing inta I.C.U under strick medical attention aka fara kkrin dawowa da circulation inta da oxygen da allurai likito ci sunkai shida akanta
untill it begin to feel like she is really dying hajya hamida tana kuka daga kofa tana faduwa akasa ana riketa, ana fara saka ma zainab shock...jiri ya debi prof ya fito waje jikinsa na rawa idonsa cike da hawaye da kuma fushi
ya dauko wayarsa dacan bappa zaidu ya fara kira da niyyar zaici masa mutunci snn ya jadadda masa cewa inhar zainab ta mutu toh wallah sai ibaad ya mutu..
yakira kira for some reasons bappa zaidu yana ganin kiran amma ya share sai bai daga ba har ya gaji ya dena.
gashi dama baida layin hajiya mairo ma saida ya kira uncle moh kai tsaye, yace ya kawo mata wayar, a hujajn sassafe lokacin ta idar da sallah lenan sai gashi ya shigo..yace hajiya yaa zayyanu ne ke son yin magana dake.
tunda taji ance shi ne gabanta ya fadi da sauri kuma acikin fargaba ta amshi wayar tace zayyanu lafiya kuwa kira da sassafen nan?
tunda taji muryansa ya fashe ya zama abun tsoro yana rawa rawa tamike tsaye tana cewa meye haka zayyanu meye kar kace min zainab ta mutu?
fadin hakan datay yasaka ya fara mata ihu yana gaya mata wasu irin tsauraran kalamai dat contains alot of threath na kisan kai kamar ba acikin hayyacinsa yake surutun ba.
suna gama wayar hajiya mairo ta yanke jiki ta fadi a sume jikinta na convulsing dakansa uncle moh yay maza maza ya daukota a hannu ahannu ya fito da ita awaje gidan ya kara rikicewa da hayya hayya ammi karama ta bishi ruwa ruwa aka kaita asibiti aka samu jinin ta ne yay mummunan hawa atake ashiga ciki da ita ana bata taimakon gaggawa
rudani yasaka kowa yay tsammanin ko mutuwa zainab din tayi, uncle moh yakira bappa zaidu da guntun rashin kunyarsa zai fara masa maganar banza kenan yaja tsaki baima tsaya jinsa ba ya katse wayar ya kira ammi karama
lkcin tuni anty safeera ta wuce asibitin da zainab din take wanda da kyar da wahala da tashin hankli kafin ECG na zainab ya dawo 30% kuma har yanxu bata farfado ba. sai a sann su prof suka dawo cikin hanklinsu saidai sosai suka dau zafi yanxu...
kafin isowar su bappa zaidu asibitin da hajiy mairo take already anty safeera ta kirasu uncle moh da ammi karama ta sanar dasu cewa zainab tana raye but she is not out of danger yet, anadai kan monitoring dinta...
hanklinsu ya dan kwanta amma kowa cikinsu na mata addua isowar su bappa zaidu ke dawuya Ammi babba ta tada sabon gulma tanata tambyr uncle moh abubuwa wanda ko gaisawa da yayan nasa baiyi ba ya hau dokin xuciya wai shi