Author : NONE Category : African Stories & Novels
tazarar dake tsakanin su zai iya sakawa kai tsaye kace basusan junansu ba...
tafiya take kirjinta na tsananin bugawa, with each step sai taji kamar akan rolling coster ball take yawo, kanta nawani irin juyawa kmr tana sararin sama cikin gajimare, kafin kace wani abu tafara ganin mutane bibbiyu, hatta dakin ya dawo yana mata duhu duhu hanklinta gabaki daya na neman gushewa
suna isowa daf da bakin kofar asibitin batare da ta shirya ba jikinta ya sake tayanki jiki ta fadi
wani securityne yay sauri yazo kanta da tunanin "she is all alone dacan har zai dagata sai kuma ibaad ya juyo, suna hade ido yace ma securityn its okay sir, i am with her. security ya masa wani irin kallo, "yace amma shine ka kabarta haka but you are suppose to hold her
ko za'a ko koma ciki a kira muku nurse ne..ibaad yace masa "a'a Allura aka mata bai saketa ba but she will be fine
...suna cikin maganan ayaana ta fara bude idonta cikin layiii tafara fulatanci tana cewa zata kwanta, ita tagaji zata kwanta, bazata iya takawa ba.."
yarensa ne shima yanaji sarai amma yay kamar be gane me take fada ba, wani cak taji ya dagata tay firgit kmr ta tsorata suna hade ido sai kuma ta lafe akan kirjinsa tare da tantame masa riga, qamshin turarensa atake ya bugar da ita saii luuuu ta koma bacci daga nan bata sake sanin me yafaru da ita ba.
yana fitowa waje ya ajeta seat din gaban motar ya saka mata seat belt ganin tana zufa ya kunna musu A C a low snn yafara driving dinsu calmy yana tukin very calm bazaka taba iya fayyace abunda yake rayawa aransa ba.
frm time to time yakan juyo ya kalle fuskar ayanahn cos u cant ignore the fact that she is girl with a rare beauty, kyau me dauke ido da sanyi irin wanda bai taba gani ba..ita abar tausayi ne, she is calm, and peacefull. any man in his good will senses may want to love nd spoil her bcos of her calm aura nd fragility, saidai shi aransa ba wann kadai yakeji ba, da akwai wani awkward feeling da yakeji akansa kmr wasu dabiaun ta yana mugun bashi haushi, he just can't seem to forget dat agabanta aka taru ana masa sharrin zina duk dama ya tambayeta gaskiyar abainar jama'a amma tay shiru takasa budan baki ta wankesa. yasan he is not even supose to be angry bcos of that amma wnn shegen rauni, da mugun tsoron dayake kallo acikin ayanayinta abune wanda bazai taba iya tolerating ba, inhar dagaske ne zaicika alkawarin daya daukarma taawure kusan dolene mishi ya kasance atskaninsu akwai kakkarfan ginin tarbiya, gyaran hali, da kuma ladabtarwa.
wajajen karfe sha daya saura na dare suka iso GRA cikin gidan bappa zaidu, tsabar gajiya har ji yake kamar bazai isa dakinsa ya kwanta ba, yana kammala parking kuwa ya juyo ya kalleta yaga har yanzu tana kan baccin ta peacefully.
kallon scnds biyu yay mata kafin ya dauki jakarsa da kominsa ya rataya snn ya zago ta inda take ya buɗe motar ahlkli yadda ya jawota jikinsa da karfi ya ratayata akafadansa nan da nan kuntacen dan kwalinta ya sulale kasa abunsa. haka wnn doguwar curly nd wavy hair dinta dat is so soft and shiny ya barbazu masa a fuska da kafada, ahnkli ya dinga takawa da ita har suka kai bed room dinsa snn yay saurin ajiyeta akan gadonsa tare da sauke ajiyan zuciya mai nauyi
yana tsaye amma idonsa gabaki daya nakanta dan bai taɓa ganin natural buzu hair irin nata ba duk dama dukan kannen sa suna da kyau da dogon suma.
na ayanah nada wani irin cika ga yawa ga uban yauqi da tsayi , tagaban is so wavy nd damp, kasan lenght din kuma is curly nd very dark. yadda ya ajeta a ringine haka suman ya zubo yarrr ya rufe mata fuskarta kirif
it was hard for him to stop staring sai da yay minti uku atsaye cikin tunanin me zaiyi kafin ya dauke idonsa ya saukar da jakansa daga kafadarsa ya zauna akan chair ya ciro duka kayan ciki da suke da datti, snn yacire takalminsa da komi na jakan yay empting ya aje komi awajen zamnsa neatly
dan coridor dake tsakanin bathrom ya shiga da kayan ya jefasu cikin engine wanki, ya wanke 2 blood stained shirt din har da kayan dake jikinsan duka machiine din ya matse su, yay masa drying sama sama snn yay pressing dinsu so neatly kafin ya kaisu hanger ya rataye su.
blue shower trobe mai kauri ya nannade ajikinsa bayan ya kimtsa dakin kadan ya shiga wanka, he spends like 20 minutes just washing his hair and face kadai with this luxurious swiss brand na la praire, brand inda is excellent for lifting, firming nd anti aging saikaga kullum fatarka rass da karfinsa baiya yamushewa kamar dai bazaka tsufa ba.
BHA made face scrub da enzyme exfoliant dinsu yay using kafin nan ya shiga shower, wato idan kaga tulin kayan gyaran jikinsa ryt frm hydrants, retinols, SpF, sheet mask, da cleansers, shaves set ,dss. zakasan kowata ƴa macen ma bata isa tanuna ma gayen nan son gyaran jikinsa ba. he is a very neat guy dat priotise his looks nd skin health.
bayan kamar minti talatin ya fito a warm shower sulbabben fatar jikinshi yana qamshin sabulai da shampoos din la praire din cos all his men luxury items are of the same brand baya hada tarukuce, brush yay agaban sink yay rinsing bakinsa da ruwan kanunfari snn yay kamilallen alwala ya fito da wani sabon bathrobe din ajikinsa.
kallo daya yay ma kan gadonsan yaga kmr yadda ya aje ayaanahn haka ya dawo yasameta batako motsa ba banda sautin numfashinta dake fita ahankli ahankl. cikin kyabe baki ya dauke kansa walking gently kamr wanda baison ya tasheta yaje gaban mirrorn ya tsaya, after dabbing his skin with a clean white towel yafara jawo set na skin care items insa musmn na amfanin dare, kusan yadda komi na wanka, wanke kai da gyaran jikinsa ya kasance brand daya hakama komi na shafawa a jikinsa ya zama brand daya, he use only "la mer" for his body, hair nd face. a very luxurious american brand na mutanen da suke son zallan jikinsu yana glowing bana haske ko bleaching ba. with good skin barrier repair, rich hydration and luxury feel. anan ganinka ansan jiki duk madara duk A.C..
abu uku kawai ya shafa dake yasan dare ne is merely time for his serum, vitamin nd retinol kafin nan ya mulke jikinsa da soft soothing moisturizers, ya shafa turare ya gyara kansa tsaf ya jawo doguwar wando dark blue colour marar nauyi na CK da rigarsa me kamr t shirt yasa. yay lisafin duniyan nan a brain insa amma yarasa ta ina zai aje ayaana ta kwanta, gashi baison takuri shiyasa bai iya kwana akan kujera ba.
tsaftaccen cotton comfortersa ya jawo ya shimfida akan soft couch dinsa ya dawo zai dauketa wani cakk ta firgita acikin baccin ta kara cakuikuye masa riga kmr wacce za'a saceta, gently yariko hannun nata anashi, sann ajeta akan couch din tukun ya samu ya kwace rigarsa ahannunta ya dauko katon rigar sanyinsa da yake sawa in sunje holiday a united state me dauke da fur ya lallubeta da shi kirif.
kara gudun Ac yay jin kmr duka gabobin jikinsa na masa ciwo yasha kwayar magnessium glycinate for deep relaxation nd quality sleep, after like 5 minutes ya iddar da adduar bacci saiya kashe wutansa gabaki daya ya kwanta hankli akwance baijima ba wani bacci me nauyi ya daukesa...
wajajen 2pm nayi cikin nisan bacci ayaanah tay firo da rigar sanyin daya rufeta dashi da alama allurar sedatives da aka mata ya fara raguwa, wani dan uban zafi da zufa tasoma ji ajikinta. tunda tay firo da bargon ta cigaba da sheƙa bacci me nisa ba ita da farkawa ba sai can ana daf za'a kira sallan farko da sanyin asuba ya hadu dana ac ya bugota, kallon dakin ta dingayi acikin duhu tana jin kanta wani iri kamar ba ta cikin duniyar, tsoro me matsanancin yawa sai ya riƙe mata kirji dan bata san yaushe sukazo nan ba, itade tasan sunbar asibiti gabaki daya sai taji ta rude sosai, fitsarin daya tasheta a baccin takejinsa kamar zai fasa mata mararta ya tsulalo waje duk sai ta rasa me zatayi.
lkcin is just few mins ya rage ma ibaad ya farka daga bacci amma dake yariga yasha wnn magani yasaka yau ko motsi bataga yanayi ba.
dake yaran taawure akwai jarumta inuwar sa kawai tagani acikin duhun tagane cewa shine yake kwance akan gadon, da kyar da karfin hali irin na mutumin kauye ta tashi ta dada lekensa kafin nan hanklinta yay sanyi ta miƙe tsaye jikin ta na rawa rawa dan kwata kwata batasan ina zata dosa acikin duhun ba ga fitsari ya mugun cika mata mara sosai
lalume ta dingay har saida ta isa gaban inuwarsan ta durkusa, hannunta dake rawa rawa ta miƙa kansa amma ta kasa taɓashi, tay hakan yakai sau biyar mugun tsoron sa datakeji ya hanata iya taba masa jiki.
nishi take fitarwa ahnkli tana dan mammatse kafafunta
jin fitsarin yafara jika mata pants,cikin dauriya ta dan taɓa jikin gadon da karamin muryan ta mai tsananin sanyi tace" umm umm dan Allah me mee..mme...mai..mota zan
..zanyi fitsari..ina jin fitsari sosai...maganan nata sai ya fara fitowa tare da maqudan hawaye masu zafi itakanta batasan mesa take yawan jin matsanancin kuka intaga ibaad ba.
a mugun shagwabe cikin fashewa da kukan tace ..mai mota..nifa zanyi ajikina dan Allah ka tashi ka nuna min wajen fitsari ...mai motaaaaa....
can cikin duniyar baccinsa yaji kmr ana jajjan masa bedsheet
yay tsam sai yafara ji harda sautin sheshhekar kuka da sauri ya bude idonsa ganin ayaanah agabansa ta durkusa tanata mammatse kafa tabi tazuba masa ido tana rabza uban kuka sosai..
gam ta rike bedsheet dinsa tana jajjansa tana cewa wayyo Allah na zanyi ajikina faaa
a firgit ya kunna bedside lamp haske yadan karede dakin fusknsa mugun daure yace "ke kuma meye haka..meye zakiy ajikin ki..uban wa ya bugeki kike kuka da tsakar daren nan..are u a child?
maƙe kafadunta tay a shagwabe tana hawaye tace
"nifa fitsari nakeji..
cikin galla mata harara yace "bakisan hanyar bayi bane...sai kuma ya tuna batasanin ba cikin dafe kansa yace shittt.. "tashi..
dakyar ta miƙe tsayen tana rawa rawa tana mammatse kafarta..
kai tsaye ya kunna asalin switch na wutan dakin wajen yay haske sosai kamr rana ya kalleta snn ya kalle kofar bathrum dinsa yace kizo kishiga kiyi fitsarin anan
da wani iri sauri ta gyada mai kai zata daga kafarta kenan sai zurrrrr fitsarin ya sace ya fara zuba mata ajiki..
ahnkli ta runtse ido tay tsamm jin fitsarin na bibiyar kafarta taki sam ta kara bude ido ga kalle ibaad daya zaro manyan idonsa waje yanamai shirin daka mata wani irin hatsalallen tsawa.
#SURAYYAHMS/08060712446
ENJOY THE WEEKDNS
SAI MONDAY...IN SHA ALLAH!!
[10/11, 18:48] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: 1️⃣8️⃣⏯️AKB💫
zararren idonshin take kallo jin matsanancin tsoro ya tiƙeta tunma kafin yay magana tabi tarushe masa da wata iriyar uncontrllable kuka mai kara, ƙwafa yay bai fasa bakuwa, a mugun tsawacen yace"..what d hell did u think ure doing? fitsari fa kikeyi ajikinki kuma atsakar dakina dan baki da hankali ke wata irin kazama ce ?
runtse idonta tay tam cikin datsar numfashinsa da muryan tsoraccen kukan tace "toh kayi hakuri mana mai motaaa fitsarin ne ya dan matseni ai bansan zai zubo ynxu ba.."
wani dan uban harara ya watsa mata yace fitsari ya matse ki ko tsabar iskanci, da girmanki ne zakimin fitsari kuma tsaye toh badani zakiyi wann kazantar ba, karaso nan ko nazo na wajen na wanka miki mari..
dake bada tsawa ya fadi hakan ba, kukan ta tsagaita jikinta na rawa rawa tafara tahowa tana takawa ahankli ahankli tkmr bazata taho ba kukan nata na fita ahankli...
wani irin fixgota yay ta firgita zata fadi ya rikota jin tana jan wani irin numfashi me karfi, kasar wuyarsa yace.."ke da Allah kimin shiru kinbi kincika min kunne da kukan banza dama uban waya aike ki kiyi fitsarin toh..mtss.
shiru tay tana hawaye ganin ya mugun hade ransa sai batace mai komi ba har saida ya dora hannunsa akan kyakkwar fuskarta ya tattaba wuyarta zuwa goshinta just to make sure she is fine, snn yakuma tabbata cewa ba zazzabin bane yasakata fitsarin dan ya mugun tsanar kazanta..
yana kan observing dinta yana mita akan fitsarin sai hawaye take zubarwa kmr ruwa batare da ta kallesa ba ahankli cikin runtse ido tace kayi hakuri aifa ya matseni ne. shiru yay kmr badashi take ba har ya gama snn yakamo hannunta tareda tura keyanta cikin bathrum dinsan ya rufe kofar ahnkli daga wajen yace "ki karasa fitsarin awajen ina zuwa" tun bata amsa shi ba da sauri ya wuce corridor ya dauko clean self absorbed mopper da ruwa me tsafta ya zuba awajen ya goge tasss kafin ya koma ya dauko dettol yasaka awajen yakara gogewa snn ya fitar da mopper waje..
..dakin maheer ya wuce yasamu ko farkawa a bacci baiy ba, kai tsaye ya wuce bathrum dinsa yay sarki yay kamilallen alwala snn yazo ya tashesa, maheer yana bude ido ya dinga shan mamakn ganin sa yana tambayarsa yaushe ya dawo ganin ba kulashi zaiyi ba kawai shima ya miƙe dakyar yay alwalan suka nufi masallaci atare.
sosai masallacin ya cika sabida yau monday kusan kowa ya farka da wuri dan shirin zuwa aiki, ibaad ya ja su sallah within few mins duk maza aka watse shida maheer ne kadai suka tsaya sukayi karatun qur'ani atare can around 6:20am suka kamo hanyar gida suna tafiya ibaad ya sanar dashi kalar rikicin da yake faruwa da hajiy mairo acan tudu batare da ya gaya masa komi akan rayuwar taawure bare zuwan sa gidan da ayaanah ba....
suna shigowa cikin gidan kai tsaye suka wuce part din bappa zaidu,Zaune yake a babban falon sashensa dayagaji da haduwa jikinsa sanye da wata original dubai jallabiya black colour mai ratsin fararen duwatsu...
wani irin qamshin hadin lime basil nd lemon grass tea with pinch of cinnamon mai dadi ke tashi a falon,hannun sa dake rike da white tea cup maikyau yakara mikawa gefe ya hau tuntuda wnn hadadden herbal tea dinsa dan yana matukar son shan wann herbal tea da safe musamman dayagane amfaninsu wajen digestion nd detox, kara lapyar garkuwar jiki da rage kumburi nd the best part yadda tea din yake mugun calming anxiety da boosting na clear mind. kusan rabi ya zuba tea din a cup sannan yakai bakinsa idanunsa a lumshe ya dan shaqa qamshin ta ramin hancinsa sann ya bude idon tare da furta bismilla ,a nitse yakai kan labbansa sann yadan kurba harya masa kyakywaan kurbi biyu, bayan nan ya mayar da cup din ya ajeshi agefe acikin tray dinsa tare da wasu hadaddun royal tea set da babban flask na zallan ruwan zafi
Tsohon jarida yagani agaban sa zai dauka Sautin takunsu daya jiyo tun daga bakin kofar ya dakatar dashi, kansa ya dago yanamai gyara zamansa mai cike da kamiya ido ya kafawa kofar yana jiran ganin mai shigowa aranshi ya bari kawai ibaad ne dan tunda yadawo jiyan basu wani samu kyakkwan zama dashi ba, sometime he wonders if he will eva had a break time in his life dan tunda yafara karatunsa na medicine ya zama he is always busy and ocupied da wasu abubuwan.
Haka kawai kuma sai yaji hanklinsa na yawan tashi kwananan, musmmn akan lamarin strange obsession din zainab arifah akansa, barin ma inyatuno da abubuwan da prof zayyanu yake yawan cewa da yadda yake bude musu ido da tada jijiyar wuya wajen nuna musu shima yana da cikakken iko dashi, shide yasan koma menene bukatarsu akan ibaad da yarsu zainab arifa bazai wuce na kaskanci da son zuciya ba kuma abun dai bazai taɓa ma ibaad sauki aynxu ba musmn ma da aka hado sa da sabuwar responsibityn ayaanah.
Duba da yanayin ibaad din wani bin har sai an mance dashi agidan sabida baida fitina sam sam yamafi saka karatunsa agabansa fiye da komi, No one in his right senses zaice yaron yanada lokacin kulawa da kansa bare wasu..
shida maheer da mujaheed kusan sune musu manyan ƴaya maza agidan, in tun ayanzu ba su samuwa cikakken nitsuwa sun zamo wani jigo da jagora wa yan uwansu da familynsun ba gani yake kmr nan gaba insuka barsu a duniyar da wuyane rayuwa tay musu sauki da armashi. har ransa Yana mugun alfahari da jajircewa da kuma gwazon ibaad, amma harga Allah cikin zuciyarshi zaiso ace rayuwarsa ba hakan take ba, he thinks there is more to life than taking too much responsbilty musmn daya zamo shine kawai silar farinciki da gatar mahaifyarsa ynxu.
Kwafa yay jikin tunanin maganan da yay da hajy mairo jiya akan zuwan ayaanah yadda ta jadadda masa cewa dolene saida saka hannun ibaad arayuwar yarinyar nan sabida uwarta taawure tafi nuna amincewarta da shi, cikin ransa yace Shknan rayuwar yaron nan babu hutu? dada leka bakin kofarsan ya dadayi yana Allah Allah ace shidin ne yake shigowa saboda akwai tarin maganganun da zaiso yaji amsar su daga bakinsa direct..
"Assalamu Alaikum"
kusan atare suka furta hakan shida maheer cikin nitsuwa suka bude slide door da akayi da glass suka karaso..
bappa zaidu yay gyaran murya snn yace wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarkatuh.
Kai tsaye dukansu suka bayyana acikin main falon takalmansu suka cireta tundaga bakin kofa fuskn ibaad yay makutar kyau da haske duk dama a hargitse ya tashi yau wani dan uban gamshin oud ne yake binshi kamar ba sallan fajr suka fito ba.
straight suka nufo inda bappa zaidun yake, ibaad yana tafiya kansa na kallon kasa, maheer ya zauna bisa lallausar turkish carpet ata gefen dama, shikuma ibaad a kasa kusa da kafafun bappan yanemawa kansa wajen zama cikin yanayin nade kafafunshi dayake bayyana tsananin ladabinshi da boyayyiyar sanyin halinsa..
bappa zaidu ya kasa daga ruwan idanunsa akansa dan Allah ne kadai yasan yadda yakeji aransa game da ibaad
haka kawai yakan ji tausayi da kuma farinciki inya tuna cewa shine ya riƙesa har yakai wann lokci, ata wanni fannin kuma yakanji kamar yatakurashi