Author : NONE Category : African Stories & Novels
aka barsu su biyunsu a zaune
..daukar fresh clean tea cup yay ya zuba shayin ya miƙa mata, dan dago kai datay zata karba da suka hade ido yaji wani abu ya tsarga masa yay loosing balance wanda tuni tea din ya dan zuba masa ahannu, dan gani da yay gabaki daya ta canza masa da make up dinnan, yay saurin kyabe baki tana karba ya ciro hankynsa daga aljihu yana goge inda tea din ya zuba masa itama nan take kallo batakai tea din baki ba harsaida ya gama sharewa suka kara hade ido girarsa na sama a dage ahnkli "what are u waiting for, ko sai nace miki kisha? ko kuma nabaki abaki? its almost nine bakici komi ba kinsaya kinata fenta fuskarki ko??toh ko kyau bai miki ba
dan shagwabe masa fuska tay daya kara narkan dashi batace masa komi ba, kurba daya tay ma tea din taga ya zuba mata ido yanakan kallonta, ahnki tare da kara shawgabe masa fuska tace bani nayi ba fa ai umman kulthum ne tamin"
yace "uhmm ni nace miki wani abu ne?..shanye kawao, kema kibisu ciki. shiru tay ta cigaba da shan tea din ahnkli tana satar kallonsa while yanakan latsa wayarsa, basu kara cewa komi ba awajen ba har saida ta gama snn ya sallemta yace taje kitchen din ta kira masa maheer tace ya samesa a daki dan su shirya ynxu..tana shiga kitchen din kuwa ta kalli maheer tacemai ibaad yana kiransa a can dakinsa ..
dambun kaza da ammi karama tay ya deba ahannunsa snn ya fita ya kyalesu anan sukadai
...ammi duk ta yabe kwalliyrsu tace sunyi kyau sosai sunata jin dadi.
Karfe 9am na cikawa duk aka fara hallara cikin main falo domin karyawa, da wuri ammi karama tace duka yaran nata sufita suyi gaisuwa kafin itama ta fito. dukansu hudu suka wuce main palon safiya ce ta fara sallama dake bata fiye son magana da su sultana ba, lkcin anty safeerah ce kawai mace a falon tana tsaye tana bada masu aiki su biyu oder ana jera breakfast din akan dinning ita kuma anmi babha tashiga dakin anty safeera canza kaya, daga bappa zaidu sai uncle moh da already kafin su ayaanan su shigowa falon anriga an kirasa a waya yafice cikin gaggawa dake shikam ma bai wani damu da yasan waye yarinyar ba existance dinta agidan baidamesa ba dan kwata kwata baison wani abunda zai takura ma rayuwarsa ko kadan
Dukansu yaran haka suka tsuguna suka gaishe da bappa zaidu cikin girmamawa, 10min past nine kowa ya fito aka zauna ammi babba ta wani cakare da jan atampa ta baza dauren ture kaga tsiya tana shan qamshi duk a tsammnta yadda suka ci kwaras hakama ammi karaman zata fito ta dau wankaz sai kuwa tabasu mamaki ta saka normal moroccan jallabiya dayaji dinkin zaren hannu golden colour all thru da mayafinsa
bata kuma yi kwalliya ba tabar natural beautynta a fili.
cikin girmamawa aka gama gaggaisawa kowa nakan table din face uncle moh da damsa mujaheed da already yake plane frm S.A.to nigeria bai iso ba tukuna.
lafya lafiya aka ci abinci karyawan, banda ammi babba dataki su ko irin gaisawa na fatar bakin nan da ammi karama, dan tana ganin irin kallon da bappa zaidu yake mata asace abunda yafarun jiyan ne kawai ya dinga fado mata arai tana jin tsananin kishi da kokontonsu akan ambatarta ta da mijinta yay da sunan fatima akan gadonsa jiya datake shafashi.
ana gama break fast bappa zaidu bai kula kallon kishi kishin da ake jefawa akansa ba ya fice, maheer da ibaad kuma suna cikin gida basuje koina ba suka zauna a dakin ibaad din suna kan wasu abubuwan dake gabansu time to time suke zagowa suzo su duba ammi karama a kitchen dan ita daya take abubuwanta ko yaran ma tahanasu su tayata
daga waje kuwa wani jiji dakai da iko ammi babba ta dingayi ma workers din, idan suka saka maggi tace sam su rage yay yawa, hakama zata bulbula ma abincin wuta fall fall yama ci tayita masofa tace wai sauri sukeyi ba sime sime ba...ta matsu sugama takoma daki ta sake canza kaya kafin hajy mairo su iso.
gidan yay shiru kowa na indah take, kafin 10:30am ammi karama tagama komi datake shiryawa nan tay packaging
dinsu drinks da chops din so lovely a wasu shegun bottles, classy glass, dispensers da wasu expensive luxury cheffing dish data sayasu duka ahannun uwargida collection tun daga garin kaduna...
tana gamawa ta bar komi anan kitchen din snn taje room inta batay wata wata ba ta fada wanka after a while ta fito ta ciro wata peach colour applique lace doguwar rigace me celeopatra neck ta saka
tay daurin daya rufe mata duka gashinta kanta sosai tay kyau bana kadan ba...
dacan har kamar zata fita ta duba ya su anty safeera suke ciki da girke girke sai kuma tafasa tay zamanta a daki dan tasani sarai ba wani abu me wuyane bane ammi babba ta gasa mata baqar magana acikin mutane.
har saida 11 yay kafin su ammi babba suka bar wajen girkin lokcin rabi ran masu aikin ya baci sabida yadda ta dinga kwaba musu aikin su da yawan bada oder. kai tsaye aka fara packaging abincin dana baki, dana hajya da nasu duk aka kai ciki, anyi coloured rice kala kala har guda uku, difrent kind of sauce da egg stews, ppr chicken da manyan manyan turkey da alalle daya ji cray fish, masa da miya, da kunun gyada dana tamba. ayayinda su ammo baban sukaje dakin anty safeera sake shiryawa nan wokers suka karasa kawo abincin babban sashen hajya mairo aka fara jeresu a kan dinning in falon within minutes harr angama komi gidan saiya dauka da wani irin shiruuu.
Da misalin 11:40am Wasu manyan manyan SUV jeeps guda biyu bakake kiriin masu fidda wata uban sheki suka shigo harabar gidan sukayi parking ayayin da driver yay saurin saukowa kasa ya bubbude musu kofofinsu Yana mai rusuna kansa akasa cikin yanayina tsantsar girmama wa, Wata dattijiwar mata ce wacce bazata wuce 60+yrs ba tafara sauka kasa cikin shigarta na mutunci tasha brown hijabi daba atula mai tarukucen design ajiki ba babban aminiyar hajya mairo kenan hajiya hajara wanda itama da safen tay sammako taje har tudu domin tadauko babban aminiyarta tadawo da ita gida dan tasan bazaimata sauki barin tudu ba yadda aka saba da taimkon bayin Allah datakey acan kowa baison hajy mairo tabar wajen..
tana sauka sauran baki guda uku mata da yarinya yar 12yr suka sauko suma amma su mataye ukun duk matasa ne basuda wani shekaru
driver su ne ya Taho da gudu ya amshi jakar hjy hajara ya rike mata har suka karaso Gaban dayan motan wanda har yanzu hajy mairo ce aciki amma bata sauka ba, tana karasowa gaban murfin motar taja ta tsaya tana kallonta kafafunta da hannunta Duk sunyi nauyi idanunta sunyi ciki ciki saboda tsabar gajiya, Wani dankareren medicated glass ne ta toshe kwayar idanun nata dashi Itakuma leshi ne ajikinta nata purple colour an mata dinkin buba da zani kafarta cikin wata flat shoe mai kama da Dunlop da kyar ta motsa jikinta sabida tana da Dan kauri.
hajiya hajaran ne ta riko hannunta domin ta taimaka mata zuwa kasa, kan kace Wani abu kusan duka rabin ma'akatan gidan sun kewaye su da gaisuwa hajya da bakinta duka duka mata hudu ne da maza matasa su biyu da yar yarinya
"Barkan ku da zuwa Hajiya mairo oyoyo hajiya Allah yasa anzo a lpya...kusan kowani ma'aikaci yana Miko musu gaisuwarsa cikin yanayin girmamawa da nuna farincikin sa da ganinsu
hajy mairo kmr wacce ta rude tafara washe baki kamr cele tana cewa "Sannunku dai"
Sannunku...Tana fada da kyar sabida kukan rabuwa da mutanen na tudu dataci harya shake mata murya tana yi tana dann waving dinsu dahannu tana baza murmushi...
hajy hajara data rikota tace An sameku lpya?duka Sukace lpya lau..Nan ta juya tana kallon driversu ta ciro kudi mai yawa ta basu tace sai ka babbasu na shan ruwa mungode Allah ya muku albarka
Da sauri Ya rusuna kai yace toh hajiya Allah kare ki angode, Duka sauran ma'aikatan dake washe baki suma suka bibbita da addua tuni wajen ya kaure da godiya da yabo kowa na washe baki
Itakam Bata kara ma kallonsu ba ta riko hannun kawarta suka nufi ciki A hankli suke tafiya sabida yanayin jiki sai an bita a hankli musamman ma da bata fiye son zaman waje daya ba.
Suna daf da bude kofar gidan sukaci Karo da bappa zaidu yafito fuskarsa dauke da kyakwan murmushi kallo daya zakamai kasan yana tsananin murna da isowarsun,da sauri sauri ya karaso da alamn an riga an sanar dashi labarin isowarsun ne, Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin shaddace a jikinsam wanda a ƙalla zaikai Darrikan kudi,ya ɗaura hula akansa ga wata gare datasha aiki sosai.
fuskarshin nan ta fito ras baqin sajenshi da gemunsa mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi
..Wajen hajiya mairo ya nufa da farinciki ya rikota ajikinshi ya rungumeta tsam wacce already tana Hade idanunta da nashi tafara sauke wasu maqudan hawaye, cikin muryanta da bai fitowa sosai
"tace'..zaidu? ashe zan ganka da idona..
Wani shafa kansa tayi a lalume tace Alhmdullahi,
saita juya ta kalli uncle mohammad daketa famar Murmushi cokin fashewa dakuka tace Alhamdull hajya hajara yau gani ga autana muhammadu kai masha Allah ashe haka kadawo gingimeme muhammadu?
..duka aka fara dariya itakam sai kuka takeyi jin yaranta duka sun rungumeta sosai
uncle moh yace "Ina matukar farincikin samun isowar ku hajya mama na yahanya.
Ta juyo cikin muryan kuka tace "Ohh nikam kalau nake ,toh Ina yayan naku, ya baka fitomin da suba?nima inga jikokin. Ohh Allah yajikan mahaifinku, Allah yasaka yana cikin inuwar Rahmanu ubangiji Allah yay muku albarka..
cikin tsantsar tausayinta da kaunarta dake mamaya aransu sukace "Allah ya kara miki tsawon rai hajya,in muna ganinki ai tamkar muna ganinsa ne Allah ya masa rahma..
matsanancin kukan ta kara fashewa da shi uncle moh ya rikota ajikinsa yanata lallashinta.
kafin nan suka fara sannu da zuwa suna gaisawa da sauran mutanen datazo dasu tareda su sun zama su takwas da yar yarinya karama,me suma ruthy itama age dinta kamar irinsu kulthum datazo da ita.
Cikin gidan bappa zaidu ya musu jagora tareda ma'aikatan gidan da suka shigo da kayan su da sauran abubuwan tsaraba da sukaxo dashi hilimi guda a buhuhuna
Daga cikin gidan kuwa kusan kowa shiri yake Dan yaga ya hallaro cikin babban katafaren falon sun on time,yau babu wanda bai haska yay kyau a shigarsa ba musamman ma ant safeera data sha Wani atampar again wann karon tasaka dark red in colour wanda ya amsheta shima kwarai dagske ,cikin wata golden atampa wax ammi babba ta fito suka sha dinkin su kowa da kalar nasa style din, shikuma maheer ya saka light brown shadda da dark coffee cap, ibaad ya saka sky blue colour voile marar nauyi wanda tsabr kyan data masa kamar ka cinyeshi.
har saida aka shigo da hajy mairo da bakinta kafin nan anty safeera tazo ita da ammi babba dasu ibaad , safiya da maheer cikinsu kowa ya rusuna cikin ladabi da girmamawa aka fara gaishe gaishe, ana cikin gaisuwar ne ammi babba ta fita domin duba su sultana, tasha baqar mamaki dataga ammi karama bata fito ba har yanxu...
gani tayi wnn ne perfect timr mata da zata baza gadara da ikonta a matsayinta na babban surkuwan gidan tunda ammi karaman taki fitowa akan lkci.
tana fitowa kuwa ta samu wata mai aiki da mopper tana share dattin kafar takalmn mutanen kauyr da suka shigo ciki musmn maza yan kauyen wokers din restaurant wanda basu da iyaye su biyu da hajya mairo ta rarumo su tazo da su birni
mai aikin tagama goge wajen kenan sukaji wani irin kwas kwas sautin takalmi mai shege tsini, zainab arifa ce sanye da wata iriyar english wears me fallen neck amma gown me dogon hannu red color ta daura vintage scarf taci wani uban kwalliya kamar zataje biki, ga wayarta ma dakyar take rikesa tsabar rigima, dede kan inda ynxn nan aka gama moppewa ko bushewa baiyi ba ta taka snn tabi ta zubar da bawon sweet din datake lasa akasa batama lura ba.
baki bude mai aikin tadinga kallonta, ita kuwa ko kallonta batay ba bare tace mata sannu kai tsaye ta nufi wajen ammi babba data daskare tana kallonta
tana isowa gabanta da wani irin rawan kai tare da over confidence tace "hi anty,. tay kmr zata fashe da dariya cikin gintsewa tace u look cool today da bakisa hijab ba.
..ammi babba dake washe baki tace thanks sannunki da zuwa zainab Arifah yasu mumnynki
zainab arifah na taunar cingam tace fine..umm anty kice ma wnn maid din taje car dina ta daukomin bag dina da wani gift bag i left the car open
..da rawan jiki tace okay my dear ki shiga ciki za'a'dauko.
yake kawai ta mata batako gode ba cikin wata mayyar catwalk ta wuce sashen datake jiyo surutun kai tsaye
babu sallama ta fado cikin falon tana wani irin murmushi me cike da shan qamshi like kana ganinta kasan kwata kwata ba'a bata dandanin tarbiya agidansu ba.
suna hade ido da anty safeera tace zainab karaso mana kizo ki gaishe da iyayenki
dakyar kai tsaye ta karaso ciki ta fara gaida su bappa zaidu dake uncle tace musu, sama sama ta gaida su maheer, sauran bakin kam batako kallesu ba taje jikin hajiya mairo ta mannu da ita tafara cikata da surutu tana cewa wai saida taje kauye tay baka kirin snn ne zata ta dawo musu??
..wasu nata mamakin rashin kunyatta wasu suka maida abun yaranta dake hajiya mairon ma cakka mata magana takey acikin wasan kaka da jika tana ce mata duk gidan ita ne bata gado kunya da hanklin kowa ba sai rashin hanklin ubanta zayyanu...
suna cikin haka saiga su kulthum da sultana da ayanan ce acan baya duk sun riko kayan small chops da ammi karama tay, suna ajewa duka sukaje suka rungume hajy mairo ta shafa kansu tana ta mamakin yadda taga ayaanah ta fesss saidai tun basu fara magana ba masu aiki suka karaso da sauran chops ammi karamar ce abayansu da katon tray na drinks da small chops da sanyin sallama ta shigo ciki kai tsaye taje har gaban hajy mairo ta durkusa snn ta aje tray din kayan tabawan tafara gaisheta cikin tsananin kewa da girmawa, hajy tuni ta mance da wata zainab arifah data makalkale mata ajiki ta riko hannum fatima
ayayinfa zainan tabi ta kafesu kulthum da sultana din da ido tanata kallonsu jin kmr yaran sun fara bata haushi ganin kwata kwata basa dokinta bare su gaisheta gabaki daya bata gama gane waye ayaanah ba dake akasa tabar kanta bata dago ba tukuna.
uncle moh ma sam bau gane waye ayaanah ba tukuna dan harga Allah ba haka yay tsammanin ganinta ba
da har zainab arifah zata tambaye safiya wacce wanncan din sai ga nan ammi babba takara shigowa fuskarta adan dore idonta stiff akan su.
hajya ta dan dafa kafadun fatima tana hawaye tana murnan ganinta, ammi karama duk ta juya gaban bakin hajya mairo tay musu gaisuwar mutunci ta saka masu aikin suka jejjera musu ruwan sha masu sanyi da kala kalan abubuwan sha agabansu wanda hakan barakamin batawa ammi babba rai yayi ba
tayama za'a ce sune suka fara tarban hajya amma daga zuwan fatima harta kawo musu ruwa da abun tabawa duk ganin hakan takey a matsayin makirici da neman gindin zama
hjy kuwa sai bayani take ma baqinta tana cewa ai wnan ita ce yata fatimar danake yawan gaya muku, daga nan tafara introducing kowa
hartazo kan ayaanah ta dan miƙa mata hannu ayaanah ta karaso kusa da ita, sai sann zainab arifah ta fara kare mata wani irin hamshakin kallon kwakkwafi dana maita bata taba ganin kyaun irin nata ba sai ji tay kirjinta na mata zafi
uncle mohd kuwa sai masha Allah masha Allah yake ta maimaitawa shima ya zuba idanunsa akan yarinya baya ko kiftawa
hajya ta jawo ayaanah jikinta tana hawaye sosai tace musu wannan ma jikata ce sunanta ayaanah, yar gidan yatace tacan tudu wato taawure...
anan duk bakin sukace Allahu akbar, Allah sarki itace wance addantta ta rasu ko?? atake idon ayaana ya ciko da ruwa, hjy mairo na hawaye tace eh wallh etace, Allah dai ya jikan inayah..hmm,.mutuwa bai bar kowa ba da babba da yaro intazo sai ka tafi...
da mamaki tafara tattaba jikin ayaanah tana share hawaye tana cewa masha Allah, kamr ba itace ke kula ba ta kalle ibaad daga can nesa fa karfi tace...Allahu akbr rayyanu ashe dai bazaka taɓa iya cin amanata ba..jibe yadda yarinya tay fess fesss..ohh ayaanah lallai toh mijinkin nan ya iya kiwo..
zainab arifa ta juyo tama ayanan wani irin kallo jin zuciyarta ya wani irin buga da karfin gaske duk dama taganta yarinyace...kuma taji kowa ya fara dariya.
...adan miskilance ibaad yace 'what, waime kike cewa ne? kin dawo kenan ko? tana harararsa tace yo bazan fadi gaskiya ba,..daga baka ajiyar yarinya harka mallaketa ka canza mata kamanni?
nan aka fara musu dariya yabi ya mugun hade ransa yana harararta yana cewa baya so itakuwa ..sai zuba takey abunta tana cewa sam batay tsammnin zata dawo taga ibaad yay kiwom ayaanah haka ba
ayaanah tay shiru kanta na kallon kasa jin duk falon anata dariyar jokes din hajy mairo kafin kace wani abu ibaad ya zame ya fita da wayarsa ahannunsa da alaman zai amsa waya awaje.
ana hirar maganan aure auren dangi duk dama wasa akeyi amma uncle moh ya fara dagewa da kawo batun lallai ayaanah acikin familyn nan kawai za'a bata mijinta dama bazata auri bare daga waje.
some feel it as joke amma hardaga zuciyarsa dagaske yakey dan aganinsa aima
ganganci ne a aurar da kyakkawar yarinya haka wa bare bayan gidansu bai koshi ba. he started to think for himself dan dama yana da burin kara auren amma bada wuri ba yasan kafin ayaana ta girma shim halaa yashirya
zainab arifah tafara kamar zata tashi ta bii ibaad waje sai caraf ayaanah ta miƙe ajikin hajy mairo zata koma wajensu sultana ta zauna wani dan uban kallon kurilla da zainab arifah takey ma fuskrtan Ayaanah tryn to look for one