ABUNDA KE BOYE

Author :  NONE Category :  African Stories & Novels

Chapter   73 / 88

216K to 219K   out of 262.2K words

ce ba, amma ina fatan a karo na farko zaku saurare ni da kunnen basira ba tare da kun kalle ni kamar wata yarinya marar hankali ba. najima ina kokarin yin murmushi saboda ku amma wallahi na gaji... Na gaji..da jin kamar babu wanda yake ganin zafin da nake boyewa kullum game da rayuwr soyayyata.

tana gama rubuta wann ta aje papern akasa snn ta sake dauko wani fresh ta rubuta

Dearest Ibaad, masoyi na..Kai ka fi kowa sanin cewa ban taɓa roƙonka komai na duniya ba abu ɗaya kawai nakeso kabani wato zuciyrka da kulawarka da lokcinka amma Sai ka guje ni kamar ni wata mummn abace, Na san baka sona, na sani tun tuni. Amma da zafi sosai dayau ka fito ka nuna min kamar ban cancanci komai daga gareka ba.

tana kaiwa nan ta sake yagewa pagin ta jefar akasa
..ta dauko final paper ta rubuta..

the three of you shud knw dat i respected ur decisions, kuma shiyasa zan yanke ma kaina wann hukuncin bawai dan na saɓa muku ba sai dan bazan iya saba maka ba daddyna.ina rokonka kayafemin amma bazan iya rayuwa babu ibaad ba, na yi iya ƙoƙarina, na yi kuka, na yi haƙuri amma babu wanda ya kula da damuwa ta. Idan wannan rubutun nawa ya dameku ko ya taɓa ku, to hakan kaɗai ya nuna cewa akwai ɗan ƙaramin wuri na fahimta a zuciyarku da ya rage min. kada ku damu dani. inna mutu komi zai wuce mana, kowa zaiyi rayuwarsa cikin sauki..ni kuma kabari na zai zamo wuri ne da babu wanda zai iya tambayana me nake ji aciki, nide dan Allah ku yafemin!

yours zainab arifah..

tana gama rubuta last part din tay wani irin darriyar mugunta sann shima ta yarda dashi kasa ta dauki wayarta taduba internat tay dan browsing sai tay maza ta maida hoton ibaad a screen inta tay setting maid alarm 10min sai dau scizzors ta yanka wani karamin jijiya a hannunta atake jininta ya fara zuba along with the effect of drug alarm dinta na bugawa ta wuce uncounsious.

dede nan private maid inta elizabeth ta karaso jin alarm din tay tsammanin hala wanka zaynab arifah take son tay dan baifi minti 30 ya rage babanta ya dawo ba tana isowa tay knocking sai shiru, tun abu na wasa wasa har ta sauka taje ta karbo spare key tazo tabude kofar tana ganin zainab arifah da scizzor a hannu akwance ga jini ga yankakken gashi ga
takardu akasa a mugun razane ta fasa ihu tayo waje

hajya hamida duk ta dauka shirmensu da zainab din ne jim kadan kawai taga elizbeth ta shigo a ruguje tana ihun sunan zainab Arifah kusan arikice hajy hamida ta miƙe ta bita taje ta tarar da halin da ake ciki

da sauri suka applyng pressure a inda jinin yake zuba sosai

kafin kace wani abu gidan ya balain rikicewa marmaza hajy hamida ta kira mijinta kafin ya iso harta riga ta isa emergency da zainab wanda atake aka shige da ita cikin Resuscitation Room batare da tunanin ko zatay rai ko ma ta mutu ba..


acikin tsananin kaduwa da tashin hankli hajiya hamida take jeka ka dawo a ward din sai nanata ta shiga uku takeyi cikin kuka da dukan wasiqun a hannunta tana karantawa tanajin wani irin tsoro da fargaban rasa yarta mai tsanani yana lullumeta

jim kadan ƙofar wajen ta buɗe da wani irin karfin tashin hankali prof ne ya shigo ciki da sauri tareda gaggawa da wani irin yanayi da ko shi baisan wani hali yake ciki ba, yana tahowa kamar iska da sauri sauri gudu gudu jikinsa yana rawa rawa kamr an zuba masa ruwan kankara kusan a rufe ya damke hajy hamida yana cewa “Ina take? Ina Zainab Arifa? Ina Arifah? kusan a muryar da ba tasaba jinsa ba yake maganan duk hnklinsa yakai kolowar wajen tashuwa, wani irin kuka hajy hamida ta miƙe tsaye dashi babu hankali ajikinta ta bashi wasiqun jikinta na kyarma tace alhaj yanxu nan suka shige da ita ciki ta zubar da jini yayi yawa na shiga uku alhaji yata kenan kwalli daya na shiga uku

tana maganan idonsa nakan rubutun hannunsa na rawa rawa, har saida ya gama karantawa snn ya ja numfashi, tsayuwar cak yay jin Kalmomin nata namai sare masa zuciya kakkarfan jiri ne yaso ya kwashesa yay saurin mannuwa da bango ya dafe kansa sosai, snn ya rufe idonsa da ƙarfi kamar yana ƙoƙarin hana kansa amincewa da abubuwan da ya karanta yanxu


kusan a rikice yace “hamiida Me muka yi wa yarinyar nan? Me ta rasa a duniya?”yanxu akan wann tsinannen yaron har zainab zata kashe kanta??ya furta muryarsa ta karye da karfi.

hawayen hajiya hamida na gangarowa tace alhaj ni damuwata da zainab arifah bata nuna min komi ba, bata yi magana ba, she even told me yanxu zata sauko a ci abinci only for her lock her self up and try to take her own life wallah wallah idan yata ta mutu sai dai ayi biyu babu yaron nam bai isa ya shaki numfashi a duniya ba dan da hannuna zan kasheshi


prof ya yi wani dogon jan numfashi ya share fuska da tafin hannunsa ya kara kallon letters din suicide note ɗin nata ya kara memeta karanta kalmomin dake cikinsu cikin natsuwa duk dama zuciyarsa tana farfashewa.


zuciyarsa sai tambayrsa yake wai shin yarsa zainab ce ga rubuta hak ta rubuta haka kuma a gidansa kuma wai ba lura ba.” ji yay atake hannunsa ta yi sanyi ya kasa numfashi na dan lokaci.

yace lahawla wala kuwwa sam ni na kasa gane kan yarinyan nan i tot zainab is way more evolved than this, batay tunanin halin da zan shiga ciki ba?? lallai yaron nan ya cuceni


cikin jin zafi hajiya ta ce tana kuka alhaj ai duk shawararka ce, saida nace maka tun tana karama a rabata da wann gurbataccn soyayya ta yaron nan dan Bana son a ce ita ce da matsala kace min sam sai tagirma toh gashnan ta girman babu abunda ya canza saima wanda yay qaru .


baice mata komi ba ya jingina da bango idonsa arufe numfashinsa ya yi nauyi inda dede lokcin ne wata Nurse ta fito dukansu suka miƙe da sauri sukayo kanta


tace sirr maaam kuy hakuri the Doctor is stabilizing her…amma kusata a addua

atake hajiya hamida ta narke da wani irin kuka prof ya rike kujera saboda tsananin raunin zuciya.

“Zan iya ganinta?” ya tambaye nurse din cikin murya mai taushin da ba a saba ji daga gare shi ba.

Nurse ta girgiza kai tace
“Ba yanzu ba sir… but she’s
fighting…

cikin rutse idonsa ya dafe kirjinsa for hours suna zaune cikin jimami daga su sai masu gadinsu.


daga can gidan kuma babu wanda yasan meke faruwa,
dan tunda uncle moh yay asarar kudadensa da time dinsa ya gama jiran ayaana ransa ya turmusa yay baqi ya dawo gidan yazo zai sauke haushinsa da masifarsa a gida hajiya mairo har tace masa ai ayaanah tun safe ta fice bata dawo gidan ba taje wajen ruthy sai sann yaji dama dama saidai bakaramin disspointed ya zama ba....

dake sosai anty safeera tana lura dashi ynxu sai jikinta tuni ya fara bata, haka tay ta tambayarsa meyasa mood dinsa ya canza, yace mata ai matsalar business ne kawai sai tay shiru ta kyalesa batace mai komi ba.

har saida ayaana ta dawo gidan kafi talura taga duk ya kasa zama yana ta neman hanyar da zai saka akira masa ita amma dake idon da anty safeera tazuba masa yau yawa yasa bai samu wann daman ba


washe gari kuwa da sassafen Allah labarin abunda ya faru da zainab arifah yazo kunnen hajya mairo anty safeera ce tazo tasanar dasu dan itama a bakin wata kawar hajy hamidan taji da safe cewa zainab has tried to commit suicide last night...

wann labari yasaka kaf gidan aka rude hajiya mairo ta fara ihu tana koke koke gida ya zamo kamar na mutuwa.

tun safen ta dinga kirar bappa zaidu dake monday ne wyarsa na falo shikuma yana daki bai gani da wuri ba, ammi babba ne tazo da gurmi ta hau gaya masa..

wayar dan uwansa uncle moh ya kira yaji yana busy yay sauri ya kira hajiyan kawai cewa take masa yazo ataro duka suje asibitin tare yar zayyanu kenan kwalli daya a duniya da kyar Allah ya bashi maza maza aje masa dan batasan wani hali zayyanu zai shiga ciki ba.

the story came as a shock to ibaad ya sha mamaki amma bai nuna a fuskarsa sosai ba kowa ya fara shiri zasuzo family house asan me za'ayi

within 20 min bappa zaidu da ammi babba da ibaad da sultana duka suka sauko kasa jin wani sabuwar tashin hayaniya awaje na tashi tundaga gate kakejin karar shgwan motocin polisawa

mota guda aka turosu maza sunkai sha biyar suka tunkare su bappa zaidu

"bappa zaidu yace officers lafya naganku haka dayawa a gidana?

cike da girmamwa babbansu yace "lafiya kalau sir. nan ya ciro papern arrest warant ya mika ma bappa, yana maicewa sirr we are directed frm above to come nd arrest ur son person of Dr ibaad almansur with immidiete effect...

cikin katsesu da tashin hakali bappa zaidu yace and on what charges...arrest kuma? dis is abslutely ridicoulos!! me yayi?

nan babban cikinsu yahau ma bappa zaidu bayanin wai charges ne akan Intentional Infliction of Emotional Distress (IIED), he is also going to be held in detention for infliction of emotional trauma to zainab arifah leading to self harm..

its just a protective custody detention, some interrogations nd detntion for some hours.

wani officer yana kkrin sakama ibaad handcuf bappa zaidu ya daka mai tsawa yace heys dont u dare... barawo ne, ko kuma kisan kai yay da zaku taru masa


ibaad ya kalle bappa zaidu yace bappa karka damu i will go with them ku kuje gidan

bappa zaidu yace Dats not ur decision to make young man...

driver ya kira aka saka su ammi babba da sultana zuwa family house hanklin sultana yay bala'in tashi tun a mota take kuka ammi babba kuwa Allah Allah take su isa ta bada kanun labarai


daga nan kuma bappa zaidu bai sake an saka ibaad a motar polisawa ya daukesa dakansa suka bisu police station din, ya zauna a waje suka shiga da ibaad ciki


fadin irin tashin hanklin da family house ya shiga da ammi babba taxo ta gaya musu antafi da ibaad an kulleshi tareda bappa xaidu bazai kiyastu ba hankalin kowa saida yay mummunan tashi

abubuwan suka taru suka ma ayaana nauyi a kirji musmn ma tunda ammi babba tafara zuba wani irin karya da makirci agaban hajiya mairo..

nan ta kwashe labari a juye ta gaggaya musu cewa ai fada sukayi da zainab din jiya da yamma,kuma zainab din ta bar gidansu tanata kuka basu san me ibaad ya gaya mata dahar taje tay tunanin kashe kanta tace musu kuma bappa xaidu yaxo yagani yana daure masa gindi duk da ma sunga halin da xainab din ta shiga ciki

labarin take bayarwa tana kuka agaban hajya xaka rantse da Allah agabanta akayi komi dan babu irin karyan da batay akan ibaad ba, kuma ta kwashe komi tace lefin bappa zaidu ne dama tajima tana gaya masa ya sakalta ibaad, baya ganin leifinsa ko yay laifi baya masa fada snn yana nuna fifiko da bambamci, cikin habaici tarinka cewa ai yanayi ne dan ya burge ammi karama bata dai fito fili ta kama suna ba amma babu kalar gori da habaicin da batay ma ammi karama ba.

tun jin wann batu hajy mairo ta birkice ta fara tsine tsine tana zagin ibaad, ayaana tabar wajen ta koma daki tanata kuka dan tasan bazai taba yuwa yama xainab wani abu me muni da zaikai har haka ba, sultana ne take rarrashinta sai safiya data fice wajen jin gulma..

ammi karama batace komi ba tay shiru musm dataga kowa ne yahaura sama, uncle moh, ammi babba da su anty safeera duk magana daya suka taru suna gayawa hajiya mairo cewa laifin duka na ibaad ne kuma ya samu daurin gindi ne daga bappa zaidu .

cikinsu babu wanda yaso yay bincike ko yasan asalin meke faruwa kusan kowa ya hau dokin xuciya sai tay shiru abunta batace komi ba.

uncle moh ya kira prof yafi sau talatin amma bai daga ba maza maza yace ayi shiri kawai aje asibitin tunda bappa zaidu yana tare da ibaad a police station...


daga asibiti kuwa kusan sabida content na hard drugs ajinin zainab arifah yasaka bata farka akan lokaci ba it took her 6 good hours snn aka samu ta dawo hayyacinta she wake up very weak duk an lakaba mata IV fluids da pressure dressing a hannu

tunda asubah data farkan iyayenta kowa yaxo jikinta kowa da salonsa na nuna mata soyayya amma kuma hawaye take sam sam taki tace musu komi tun suna mata lallashi har suka aje so agefe suka fara mata fada kowa ya harzuƙa yana fadin mata asalin manufarsa akan tarayyarta da ibaad tuntunin nan saiyau suka iya cire so da gata sukahau bayyana mata asalin yadda basu kaunar ibaaad kuma suka tsane tarayyarta dashi kwata kwata..
saidai basu sanar da ita cewa har sunsan an kama ibaad din ba

their words of hatred akan tarayyarta da ibaad din'nt hurt her much sabida ta riga ta jima da lura da hakan musmn ma awajen mummynta hajiya hamida da tasan ko kadan bata kaunar dangin ubanta bare kuma ta haɗa jini da wanda take ganin kamar bai kaisu arziki ba.

duk hargaginsu da lallashinsu shiru kawai tay tana hawaye batace musu uffan ba wanda hakan ya kara daga musu hanklinsu sosai.

strickt security akasa a inda suke, wajajen 10am manyan gidan gabaki daya suka taho asibitin a motocinsu amma haka kememe aka hanasu shiga ciki..

hajiy hamida sosai ta haukace ta haura can sama da fushi da tsana tace Burin yan uwansa kenan dama su kashe masa yarsa kwalli daya, dan shima a cusa masa baqin cikin da zai kashe shi, snn idan ya mutu a dauki dukiyarsa abasu

tana masa kuka ta maimata masa wann maganan cikin bori da fushi yafi sau hamsin..

daga wajen kuwa bakaramin rikici akayi da hajiya mairo ba in kaganta ma daukawa xakay an mata mutuwa, can daga baya saida akazo aka mata wayo akace ai zainab din tana cikin wani hali ne ana kkrin dagata ba asok hayaniya kuma hukuma na ciki ana bincike shiyasa ba ason kowa ya shiga kawai suje gida.

bada son ransu ba ammi babba ta dawo da hajiya mairo uncle moh ne da anty safeera kawai suka tsaya a reception na asibitin.

ammi karama kuma daga wajen ta wuce police station duba halin da su ibaad suke ciki...

tana zuwa station dake ana matukar daraja familynsu sharply aka kaita wani waiting room ta samu bappa zaidu a zaune yana kan waya suka hade ido dan hawayen datake dannewa atake suka fara sauka katse wayar yayi har tagama karasowa gareshi tun basu gaisa ba yace haba Fatima meyasa kema kika zo nan kuma baga ni nan anan ba?

da matsanacin damuwa a kwayar idonta tace "yaa zaid Kay hakuri kawai so nake naga halin da rayyan yake ciki

bappa zaidu yace 'interrogations ne kawai babu komi ba tunda bawani laifi ya aikata musu ba neman fitina ne kawai. the highest they can do is to detain him here kuma insha Allah i wont let that happen.

cikin lumshe ido da budewa da karyayyen zuciya tace Amma meyasa rayyan zai saka kansa acikin wnn matsalar..cikin fashewa da kukan da yazo mata bazata tace kaikuma kamar baka ganin lefinsa. yanxu duk cikin gidan kowa yana fushi dashi, hajiya ta dau abun da zafi dan Allah inde rayyan ya aikata wani abu na cutarwa akan zainab kawai ana gaya masa gaskiya ni wallah banason hakan yaje ya jawo masa karin baqin jini acikin gidan nan dan baida kowa a duniya inbasu ba.

cikin sassauto da muryansa kasa yace haba fatima yau kece da kanki kike furta min wann maganan? i tot kinfi kowa sanin cewa ibaad kamar dan cikina na daukesa meyasa kike tunanin inhar yay wani abi ba daidai ba zan zuba masa ido in kyaleshi...in dis case he is just a victim of circumstances tsaya masa yakamata muyi bamu hau dora masa laifi ba...ita hajiyar tasan asalin meyafaru ne??

ammi tana share hawayenta tace ni bansani ba amma ai maman sultana ce tazo ta gaya mana wai fada sukayi da zainab din jiya shine ya mata wani abu hartaje tay tunanin kashe kanta..kuma tace tun jiya kay shiru baka masa fada ba duk dama agabanka akayi komi

ahnkli yace fatima
ive personally talked with zainab jiya, nazo kam na sameta tana kuka nd she told me they had a fight..da naje na tambaye ibaad kuma yace min tazo tace masa ne akan suyi aure next week, snn ta dau dollar cheque ta bashi claiming wai zatay sponsoring auren...

i scolded him sabida tace min yagaya mata magana dabai mata dadi ba, but dan yaqi karban wnn qudurintan kuma sai nahau masa fada akan me?an taba siyan soyayya da kudi ne ko ana dole ne?..kuma kekanki kinsan da wuyane in iyayentan ma suna sane da wann abun, wallah inda ya biye mata wani matsala na daban zata jefashi aciki...karshe suce yay manipulating yarsu ya sace musu kudi, ko su masa sharri cewa shi yy influencing maganan aure akan yarsu..na lura kamar kaf kuna yin abune kamar bakusan waye ubanta ba. he will protct his child bazai taba karban laifin yarsa, so why i cant protect mine, badan ganin darajar su hajiya ba da nima fa ina da dama in shigar dakara akansu ai ba a relshp na dole, sun takura ma yaron nan tunda jimawa ohh wato mune bamu iya kaiwa kara ba ko? is not fair mana haba fatima...nayi ma yara na alkawari bazan musu auren dole ba saidai a bisa qaddara kuma kema kinsani, i cant force ibaad ya aure wacce bayaso gaskiya...so wnn kananan maganan raihanatu da hajia kawai kibarsa dukn su basu san asalin meke faruwa ba...kema kiy hkuri ki kwantar da hanklinki babu abinda zai same ibaad in sha Allah..

shiru tay kanta na kallon kasa har ya gama maganan kafin can ta share hawayenta ta dago kai cikin sauke ajiyan zuciya tace "toh shikenan..inde

73 / 88