Author : NONE Category : African Stories & Novels
a dole xaa kashe musu uwa
wasu maganan ma da gatse yake gaya ma ammi babba game da halinda zainab din take ciki.. bappa xaidu ko ajikinsa baice musu uhum ba, ko Allah ya sawwaka baice ba, iyaka fatima yay wa few questions game da jikin hajiya tace masa likita yace hawan jini ne.
sun zauna a waiting room for a while kafin nan akaxo akace musu hajya mairo ta farfado ta xama stable, kusan atare suka shiga suka sameta ta kifa kanta tana hawaye kowa ya mata sannu ta amsa bata amsa bappa zaidu ba. sai can da likitta yazo yay musu bayani yace kar asake barin jininta ya hau haka of not zata iya samun temporary paralysis ga jikin tsufa, ana gama bayani ta kalle bappa xaidu tareda nunasa da yatsa cikin tsananin fushi tana cewa zaidu sai ka zuba ruwa akasa ka sha tunda kay amanna saika hada kai da rayyanu kun kashe yar dan uwanka har lahira,..tace itama kawai ya kasheta yaga bayan ranta ta amince zata mutu ta bar masa duniyan ya jika ya sha shida rayyanu.
shide baice komi ba tafara kuka duk su ammi karama suka taru akanta suna bata hakuri kawai tafara bori tana cewa "zaidu inhar nina haifeka toh ka bari ayi auren nan kodan yarinyar nan ta samu lafya idan kuma kakiji wallah baxaka ki gani ba, kafin ka kasheni saina tsine maka albarka inde nono na kasha ka girma ba tsintar ka nay a bola ba tsinuwata wallahi saiya bika marar hankali kawai taɓabbe.
tana gama koke kokenta ya bata hakuri, shide baice eh ko aa ba. ya kama hanyarsa ya fita kowa nashan mamakin irin taurin kai da kafiyarsa.
wajen aikinsa ya wuce direct ya shanshantr da maganan duk dama kalaman hajya ya balain sosa masa ransa sosai, sosai jikinsa yake bashi wann auren da sukeso su kullan kawai lalata rayuwar ibaad zasuyi dashi. he wil not have freedom, or will in it, infact he wont have a say in it so suke su maidashi bawa ga rayuwar xainab arifah da mahaifinta sai abunda sukaga dama zasuyi da rayuwarsa ta nan gaba. he knws what he is doing sosai shiyasa yaki sam ya sauko dan inyayi sake tamkar yaci amanan maraicin ibaad ne dan yasan kasancewa surki awajen prof yana tafe ne da kalubale babba.
tunda yaxo office bai kara kula wani kira daga gida ba, har aka sallame hajiya mairo ammi karama ce take wahala da ita kusan komi ita take mata asashenta. banda raki da baqaqen maganganu babu abunda hajy take xubawa daga ta kwanta sai tafara kuka tana cewa wallah wallah akan wann magana dai ta tsine ma zaidu albarka zata daga masa nono wann furucin nata sosai ya dinga daga ma ammi karama hankli.
da yamma bayan komi ya lafa prof dagacan yayi xuciya already ya fara hada case zazzafa yana neman yay sueing din ibaad a kotu da case me karfi wanda xai gigita musu hankali, kmar kuwa ammi karama tay nazarin hakan babban kawar hajy mairo tana zuwa ammi ta samu sarari ta musu sallama ta koma sashenta ta shirya sharply ta saka doguwar jilbab dinta dark green colour dayay mata kyau sosai, babu dandanin kwalliya a fuskarta ta shafa turare ta sabi jakarta ta dau motarta cikim gaggawa ta nufi ofishin bappa zaidu da yamma
ana daf da zai tashi ta iso wanda tun a mota ta riga tay duk wani nazarin da zatay akan maganan nan ba, tasan in akaci gaba haka za'ay asarar xumunci da zaman lafya atsakanin su dayawa. aganinta tunda dokokin prof bai shafe kar ibaad ya kara aure anan gaba ba, ai zai iya auren xainab din kodan darajar kwacinyr hanklinsu duka inyaso daga baya ya auro duk wacce yakeso ya aura.
da wann tunanin aranta ta shigo ta samu bappa zaidu duk dama baisha mamakin ganinta ba amma dakyar ya nitsu ya kulata, dan kwata kwata baison ta saka baki acikin case din nan, yasha mamaki ma da hajiya bata umarce ta akan ta tursasashi ko ibaad su karbi auren nan ba. duk dama yana mutuwar sonta amma it was hard for her to convince him cewa a radin kanta tazo ba hajiya bane ta aikota ta lallabeshi..she try to convinced him to her best of ability amma inaa, bai sauko ba saida yaga ta xuba masa gwiwa akasa tana hawaye tana kuma jaddada masa cewa ita kadai baxata iya langwasa ibaad ba shine kawai zai iya gayama ibaad abu snn ya amince masa kai tsaye, idan shi bai sauko sun gyara abun acikin nitsuwa da hankali ba mutunci zai zuba, kima da darajar gidansu kwanan nan zai xube a gaban kotu, snn shikansa bazaiso yay rayuwa da tsinuwa da bacin ran mahaifyarsa akansa ba
da kyar da lallami da karya masa murya ta rarrashe shi, tace zata rakasa yanxu suje gida kawai ya bawa hajiya hakuri inyaso ayi magana ta kare daga yau...
har cikin ransa baiso haka ba, amma duba da manya manyan hikima dake cikkn zantukan fatima da inda ta durkusa agabansa tana masa kuka yasa kawai ya hakura yabita sukaxo gidan atare.
wanda tun a mota yake ta fayyace mata illar da wannan auren zaiyi arayuwar ibaad, da yadda baiya kaunar ace shida hannunsa ya jefa ibaad acikin wani yanayn rayuwa dazai cutar dashi...
yana maganan muryansa harna rawa cos at some point zaka rantse shiya haife ibaad
bcos the way he loved him nd cared for him ko mahaifinsa na asali baimasa son dayake nuna masa ba, inda kuwa an barsa da bazai taɓa saukowa ba saidai ayi duk abunda za'ayi bai damu ba dan inda gidansu ne ansha nuna irin wann son zuciyar bayau aka fara ba...
ubansu al-mansur ma halinsa kenan yafi hajya mairo son kai da nuna bangarenci da nuna bambamci, saidai baiyo tsammanin hajiy mairo son ƴayanta zai rufe mata ido harda zata zaɓi ta cutar da maraya kamr ibaad ba. wani bin sai yaga kmr ana wasu abubuwan ne dan anga asalin uban ibaad din baya raye, ammi karama kuma karamar mace ce har yanxu duk sun girmeta nesa ba kusa kai ko muhammadu ya girmeta ko tacema zata karba ma danta yanci bazasu taɓa saurararta ba dukan kawunanta na can maiduguri duk suna bin bayan hajiya ne, saidai ma agaya mata maganan da xaizo ya dameta a zuciyarta.
dada fahimtar irin son dayake ma ibaad din yasa ammi taji sanyi aranta hawayenta na sauka tanajin tausayin shi tare da kaunarsa aranta har suka iso cikin gida
idanunta sosai yay jaa, kafin su sauko sai ta dau lokaci acikin mota tana bashi hakuri da tattausar lafazi ta dinga lallabashi har suka karaso cikin gida...
yamma ne lisss ammi babba tana sama sashen anty safeerah taje jin gulma game da jikin zainab,wani dan uban dadi taji dataji cewa prof ya harxuka ya fara kiran lawyers zasu kafa babban case akan ibaad dan axo a kulleshi a walakanta sa.
lkcin gidan yay shiru ammi karama suka karaso inda tun akofar ashen hajia sukejiyo muryanta tana kan koke koke ma kawarta hajya hajara akan abunda ke faruwa da ita duk ta rasa yadda zatayi da ranta dan bata taɓa sanin zaidu yana da wann taurin kai da kafiyar kafurcin ba
ita babban damuwarta shine kawai a amshi auren kodan kar araba danta xayyanu da yarsa a duniyan nan, cewarta mutuwar matashi ya fi girgiza iyaye gashi itace musu kwalli daya inta mutu bazasu sake samun haihuwa ba har abada.
ammi karama tana gaba bappa zaidu yana biye da ita abaya anitse sunayin sallama a falon hajiya mairo ta kara hade rai tana kan jan majina jin muryan xaidu yasa bata amsa ba ta kauda kanta gefe cikin tsananin fushi..
da sanyin jiki ammi karama ta masa jagora bata barsa ya zauna akan kujera ba suka zauna akasa atare...
tun basu furta komi ba hajy hajara ta kallesa da muryan kuka itama tafara cewa zaidu wallh kabani kunya ko kadan banyi tsammanin zaka mana haka ba. kai da nace kaine zakka shine zaka watsa min kasa a ido, ace kaine dakanka ka rufe idonka akan maganar da bai taka kara ya karya ba?? kana cutar da rayuwar dan uwanka da kuka zauna aciki daya kuka fito atare, haba zaidu haba zaidu habaaa
...yanxu kaji dadi kenan da kasa hawan jinin mahaifiyarka ya tashi?? gaskiya bansan ka da wann mugun halin ba..
cikin katseta da sasanyar muryarsa me cike da dattako yace Hajiya mama hajara ayi min afuwa. daga sai bai kara cewa komi ba, har saida ammi karama ta kalleshi da fuskar magiya snn ya mike ya karaso kusa da hajiya mairon yace "Hajiya kiyi hakuri da dukkan abubuwan dake faruwa, ina sane da cewa ke mahaifyata ce wanda darajarki bai taba gushewa araina ba duk wani hukuncin da kikaga na yanke akan ibaad bawai nayi bane dan na kuntata muku saidan na kare amana da martaban maraya da yaa mustafa ya tafi ya barmana, gadai fatima tana kallo kuma tana zaune akusa dake kusan kowani lokaci tana kulawa dake but at same time kina zagin dan cikinta, kina ambatarsa da mugayen halaya duk da kinsan ba gaskiya bane, kin bijiro masa da auren dole me cike da tsauraran dokoki bakiyi la'akari da yadda abun zai gurbata rayuwarsa ba, shin kin nuna masa kenan farincikin wasu acikin yayanki yafi na wasu?inda yaa mustafa yana raye shima xaiso ne ayi ma dan cikinsa irin wannan kaskantcen auren? agabanki zayyanu yace bayason ya hada jini da mu..kuma alfarma xai ma yaron nan, snn ga zargi, ibaad fa jikanki ne hajiya, kenan farin ciki da rayuwar jikokin ki masu abun duniya da dukiya sunfi miki na shi dayake maraya ko? ke baki tunanin duk wnn abun da kikeyin zai dame zucyar ibaad? kuma zai ce inama da ubana yana raye ya karba min yanci?...shin idan muka taru muka nuna masa shi marayane baida daraja a gidan nan waye ya kamata ya tsaya masa a duniya? ina zaije yaji sanyi, bayan ga fatima anan tare dake bata taɓa saba miki ba...duk da zagin dakike ma danta koyaushe, shin hakan yana mata dadi ne? ke uwace fa hajya bazaiyu kice komi laifi bane, musmn inde har bai sauka an favorites dinki ba.
yana maganan wani irin shiru falon ya dauka cikin sauke ajiyan zuciya hajy hajara tace
hakane zaidu kay magana ta hankali amma kuduba Allah aceto rayuwar yarinyr nan, duk wani uzuri da zaka bayar baikai nauyin rai ba, duk wani qaddarar da ibaad zai dauka bazai kai wanda zayyanu zai ji aransa indan ya rasa yarsa kwalli daya daya haifa a duniya ba..memakon kuyita hayaniya maslaha zaku samo acikin wann matsalar dolene fa sai wani ya dauki mummunn qaddara acikinsu tunda shi soyayya Allah ne ya dora mata bayin kanta bane...yarinya kyakwya haka data taso acikin dukiya da gata wallah bazata so ta kashe kanta ba inba akan abunda yafi karfin tunaninta ba, zaidu ka duba Allah arufe maganar nan
yace "bakomi hajiya ni dama fatima ce ta dauko ni akan inzo abama hajy hakuri kuma in sha Allah zan tuntube shi ibaad din da maganan..saidai muy addua Allah ya bashi ikon cin wann jarabawar..
yana rufe bakinsa hajiya mairo ta fashe da kuka harda shsheka taki tace komi dan bakaramin taɓa mata zuciya kalamansa yay ba, musmn na maraici da kuma yanda yajawo hanklinta akan abunda take yawan furtawa agaban fatima.
tashi yay ya koma wajen da ammi karamar take zauna sukay magana kasa kasa
hajy hajara kuma tana famar lallashin hajy mairo tana bata baki kasa kasa cikin kuka take cewa 'hajara kicewa fatima ta yafeni, wallah na rude ne
haka kawai bazan kuntata mata ba..sosai hjy hajaran ta tausaya mata
sai can ta dago ta kallesu tace toh zaidu yanxu sai munji kenan daga gareka...
a nitse yace in sha Allah..zuwa gobe!..yana gama furta hakan ya miƙe batare da ya kalle hjiya mairon ba da sanyin murya yace fatima muje ko?
mikewa tay da sanyin jiki tay gaba yana biyi da ita abaya har suka fice a asashen gabaki daya tarakasa har jikin motarsa suka cigaba da maganan awajen har ixuwa sallan magrib snn suka rabu ta dawo cikin gida.
kitchen ta shiga dan ta dora masu hajiya wani snacks da shayin da zasu kwana dashi ita da hajya hajara.
dagata bangaren su kuwa ficewarsu bada wuya ba kunya yabi ya lullube hajya mairo tana kuka tana fadin halacci, kawaici da alherin da fatima take mata..
hajiya hajya kuwa batay kasa agiwa ba,sosai ta cire son zuciya tay mata nasiha akan abubuwan datakeyi ta bala'in nutsar da ita musmn akan batun bambamce bambmce datake nunawa.
sunjima suna magana kafin nan ta shigo mata da maganan zaidu da fatima
..tace bata gane me ake jira dasu har yanxu ba? da sanyin murya hajiya mairo tace "toh Allah ne dai baiyi lokci ba naje wajen malamai sunfi dubu a tudu amma duk ana cewa sihiri akay aka hanasu aure
..kullum sai ace muje mu cigaba da addua gashi lokci yana ta ja sunata tsufa...ai da tuni yanzu ta haifa masa yaya sunkai hudu ko biyar.
hajya hajara ta saki baki tace wann ma maganan banza ce, ke kuwa mai tuwo yarinyar nan fatima har nawa take? inbanda ma karya da kika dinga shera ma mutane fatima fa a yar shekara 16 tazo cikin gidan nan ko kin manta ne? har yanzu fa yarinya ce atata ace anbata shekaru arbain da hudu zuwa da biyar ba toh wallah in zaki mike tsaye ki mike bawai kawai anzauna ana ta cutar yarinya ba duk anbarta da juyi a gado me sanyi kullum ruwan sha'awa na taruwa mata amara, tunda dai addua bai yi ba ai munjira, ynxu kawai mu hada kai munemar masu mafita.. yau kiga dai inda taje ta lallabo miki shi yaxo har gabanki ya durkusa ya baki hakuri, shin ita wancan balamar matar tasa tay miki hakan ne?shegiya mummuna banda gulma bata iya komi ba tunda nazo gidan nan ko ruwa banga tazo ta aje agabanki ba taje can tana yawo da sakakken duwaiwaka tana jin gulma awajen safeera toh wallah baxaiyu ba, inke yar kungiyar izala ce ni nariga na wuce nan sabida haka xanje
duk inda xanje wallah sai an cire yarinyar nan a azaba an aura mata mijinta ke kuwa maituwo wann uban mugunta har inaaaa kema fa da lefinki akanbyaran nan dan fatima ba yar cikinki bace shiyasa baki damu da halin da zatana shiga ciki ba shekararta nawa babu namiji aikekuwa kya tausayawa rayuwarta
jan ajiyan zuciya mai nauyi hajiya mairo tay tace "kune fa kawai kuke ganin kamar bana tausayawa fatima amma har raina bana tsammanin inada wata a duniyar nan danake jinta kamar yar cikina kamar ita, fatima fa tasha wahala dani. kedai tunda kince zakiyi wani abu akai toh ki gwada mugani nide inhar sihirin nan ya kunce ko yau yaune zan iya sawa a daura musu aure kowa ma ya huta..malamin nan cewa yay fatima zata mutu in akay auren ba a karya asirin nan ba, yanxu so kuke na mata auren da zai kasheta inta mutu ai ni aka cuta
hajy hajara tace yanxu naji magana toh yanxu dai kibani nan da wani lokaci in sha Allah wann aure sai anyishi nan bada jimawa ba, koma waye tay asirin zanje can kauyen mijina na, kinsansu ai kabilar jukunawa ne, dole ne muma mu tashi tsaye mu gwada musu muna da yadda zamuyi haba cutarwan yayi yawa....
#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[13/12, 19:36] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.
⏯️4️⃣6️⃣
tunda hajiya hajara ta gama tsige aminiyarta hajiya mairo akan batun maganan auren zaidu da fatima sai bata sake cewa komi ba, suna zaune anan suna yan hira har ammi karama ta kawo musu abin taɓawa albarka suka saka mata da har zata wuce dakinta taje tay wanka hajya hajara ta zaunar da ita ta dinga mata nasihohi masu ratsa zuciya da shiga jiki, nauyi da kunya duk yabi ya hana hajy mairo cewa kowa ba har hajiya hajara ta sallameta ta fita.
ata fannin bappa zaidu kuwa gabaki daya daren ranar juyi yakeyi akan fankacecen gadonsa da tunanin yadda zai iya bullowa al'amarin aransa saida yasamu cikakken nitsuwa yay tunani me zurfi snn ya iya sake ransa yayi hakuri.
washe gari da safe as usual suka fita sallahn fajr ibaad ya jasu bayan an idar suna shigowa cikin gidan ya kirawo shi sukaje private palonsa acikin sashen sa. ibaad yana daga kasa shi yana sama.
kai tsaye yafara sanar dashi abubuwan da ya farun jiya, dan yasan da wuya ne inyana da masaniya dake tun asubah jiyan ya fita kuma bai dawo ba saida yamma lisss.
har saida ya gama fayyace masa halin da ake ciki snn yay masa nasiha, ya kuma sanar dashi bada son ransa bane daya zo yana dawo masa da wnn maganan. su dauka kawai duk wannn abun qaddara ce dan haka umarni yake bashi da yay hakuri ya amince ayi auren, inyaso daga baya in komi ya lafa sai ya aure duk wacce yakeso ya hadasu su biyu.
tunda bappa zaidu ya furta masa wnn maganan saiyaji kamar iska ya dauke masa baya shaqar numfashi ganin yakasa amsawa yasa bappa zaidun yace masa yaje yay tunani zuwa yamma ya bashi amsa yay masa nasiha ya kuma bashi hakuri sosai..
jikin ibaad a sanyaye ya tashi ya bar wajen bai masan sanda yakai kansa dakinsa ba he laid on his bed for a while yanajin kamar baya duniyar ne gabaki daya, sai can ya jawo wayarsa yafara kkrin danna lambar mum dinsa ganin bata dauka ba kawai ya miƙe ya shirya kansa duk sonsa da tsafta yau ko kula wanka baiyi ba, karfe 7 dede saigashi ya shigo cikin gidan idonsa a rufe kai tsaye dakin amminshi ya nufa hanklinsa a tashe sosai...
tana gama gyara koina kenan zata fito ta shiga kitchen yay sallama ta amsa masa yashigo gani tay kawai ya zauna kasa jikinshi a mugun sanyaye yayi shiru baice komi
throw pillown dake hannunta ta aje ta karaso wajensa tace "rayyan ya naganka da sassafe haka lafiya kuwa? ko bakajin dadin jikinka ne...
jin kamar idan ya budi bakinsa zaiy kuka yasa ya sunkuyar dakansa can kasa gwanin ban tausayi baice komi ba saida