Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 58

21K to 24K   out of 172.2K words

ai ke idan tace zata ja dake ma sune zasuyi miki fadan.

Ta jijjiga kai tana murmushin yake.

A hankali mutane suka fara dawowa gidan kuma suna yi mata sallama domin wucewa gidajensu. Daga baya Aminan ma tayi mata sallama bayan ta bata  yar karamar layar wadda ta saka a aljihun doguwar rigar da take jikinta, ta rakata kofar falon sukayi sallama ta fice.
& & ..

Sai wajen sha daya na dare saura sannan Alhaji Safiyanu ya kawo ango gida da ledojinsa guda biyu; daya na Zahra, daya kuma na Aisha.

Gidan Zahra ya fara shiga, lokacin duk yara sunyi barci don haka babu kowa a falo. Kai tsaye ya wuce sama.
Dakinsa ya wuce kai tsaye, kamar yanda yayi tsammani Zahra bata ciki. Don haka ya ajiye kayansa ya dauki ledar da ya shigo da ita ya wuce dakinta.

Tana kwance a kan gado sanye da kayan bacci an kashe fitila da alama bacci takeyi, ya kunna fitlar tare da yin gyaran murya ya karasa ciki da sallama. Ta juyo ta dubeshi sannan ta tashi zaune a tsakiyar gadon, yayinda shi kuma ya zauna a gefen gadon.

 Sannu da zuwa.

Ta fada murya kasa-kasa.

Da murmushi ya amsa

 Sannu. Ya gajiya? Ya taro?

 Alhamdulillah, kowa ya tafi makwancinsa.

Yanayinta da kuma yanda take bashi amsa ya fahimci bata da walwala kuma idan yaja hirar zasuyi rigima, don haka ya ajiye ledar a kan durowar gefen gadonta yana fadin

 Ga wannan ke da yara, sai dai naga duk kunyi bacci sai ki saka a fridge kwayi breakfast da shi.

 Mungode.

Suka dan taba hira tana ta faman cijewa saboda kada tayi kuka a gabansa, shi din ma da yake yana sauri ya tafi wajen amarya kafin Zahran ta fara wata fitnar sai kawai yayi mata sallama yace ta rufe musu gidan.
Ta biyoshi a baya har suka zo bakin kofa sannan ta rufe musu kofar shi kuma ya wuce, ya dauki ledarsa a mota ya nufi gidan amarya.
& & & .

Kamshin da ya cika gidan shi ya fara yi masa maraba, ya riga ya san ita kadai ce a gidan don haka yana shiga ya mayar da kofar ya kulle. Ya karasa ya ajiye ledar hannusa a kan dining table, ya juyo ya karewa falon kallo yana murmushi.

Ya shige dakin yana rike da Babbar rigarsa, tun kafin ya karasa ciki ya hangota a kan gadon nade da laffayarta ta kashingide daga zaune a gefen gadon. Ya karasa ciki da sallama wadda ta farko da ita daga gyangyadin da takeyi, ta gyara zama tana amsa sallamar.

Ya karasa ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta yana murmushi yayinda ta mayar masa da murmushinsa tana kokarin boye kwallar da take makale a idonta. Ya kama hannunta na hagu yana kallon lallenta, ta bi hannunsa da kallo yanda ya rike hannunta. A take hawayen da take boyewa ya kwace; Mustafa; ta kasa cire shi daga kwakwalwarta tunda aka ce an daura mata aure.

Ya matsa kusa da ita ya janyota jikinsa ya kwantar da kanta a kirjinsa; ya fahimci abinda yake saka ta kuka, ko bata gaya masa ya san tunanin tsohon mijinta takeyi. Yayiwa kansa alkawarin tabbas sai ya jiyar da ita dadi a rayuwarsu, sai ya so ta ya nuna mata soyayya fiye da yanda tsohon mijinta ya nuna mata. Sai ya jiyar da ita dadin da zata manta da duk wani namiji idan ba shi ba; domin shima yana sonta kuma ya tabbatar yana sonta fiye da yanda Mustafa ya sota.

Sai da ya dauki lokaci yana lallashinta sannan ta iya samu ta tsayar da hawayenta. Ya tayata ta warware laffayarta suka ci abinci sannan sukayi alwala sukayi Sallah.

Sai da yayi da gaske da ita sannan ta iya canza kayanta ta saka kayan bacci, yana ta yi mata dariya kamar wata budurwa saboda kunyar da take ji. Bayan sun gama ya kashe musu fitila suka kwanta, rungumeta kawai yayi saboda ya kula da yanda take cikin damuwa kuma ga bacci da take ji. Ya danne duk wata bukata tasa ya kyaleta zuwa gobe, kafin nan ta kara sakewa ta sami nutsuwa.
& &

Kusan lokaci guda suka tashi da asuba, nan da nan sukayi wanka suka yi Sallah. Yayi zaton zata koma bacci don haka ya fice daga dakin ya komo falo ya fara kokarin hada TV. Bai jima da fitowa ba itama ta fito, suka zauna yana hada TV din suna hira, har ya gama suka zauna suna kallo.

Karfe takwas ta dan gota ta dubeshi tace

 Nifa yunwa nake ji, bari na duba ko ruwan shayi na sama mana.

Ta mike ta nufi kicin, yayinda shima ya nufi dining table inda ya ajiye ledar da ya shigo da ita jiya. Ya zazzage kayan shayin da burodin da ya siyo ya kwasa ya kai mata kicin din.

Yayi tunanin Zahra zata basu breakfast amma baya so yayi maganar don bai san yanda za su dauki abun ba. Nan da nan Aisha ta hada musu shayi da burodi ta dumama ragowar naman jiya suka zauna suna kallon TV suna cci
____

Tana zaune a falonsa ita kadai tana shan shayi, shayin kawai zata iya sha a halin yanzu domin kanta ciwo yake yi saboda yanda bata samu tayi bacci ba ko daya. Kwana tayi tana tunanin yanda za ayi Yusuf, nata ita kadai, yaje ya kwana da wata mace. Kuma haka ta tashi tana ta wannan tunanin tana tsaki.

Tun sassafe Jummai ta zo don haka ta barta da yaran a kasa ta dawo sama ta zauna. Koda Jumman ta shigo saida ta tambayeta ko za a yiwa amarya abinci amma tace a a. Ta san ya kamata tayi amma bazata yi ba, domin da ana so ta bata abincin ai da a nan cikin gidan za a saka amaryar su zauna tare.

Karar wayarta ce ta katse tunaninta, ta daga wayar ta duba, Abban Sadik ne.

Saida taja tsaki sannan ta amsa wayar ta kara a kunnenta

 Uwargida ran gida, kin tashi lafiya?

Ta wurkila kwayar idonta cike da takaici sannan tayi yake ta amsa

 Lafiya kalau, ya amarya?

 Alhamdulillah. Gamu nan shigowa yanzu zan kawo miki kanwar taki.

 To Allah ya kawo ku lafiya.
Ta jiye wayar ta dubi agogon bangon dake falon, karfe goma da kwata. Ta ja tsaki ta kawar da kai, bata ma san lokacin ya tafi haka ba don ko wanka bata yi ba.

A take ta tuno abinda ya kamata ta fara yi, inda ta tashi da hanzari ta koma dakinta. Ta san dai inda suka boye layar nan jiya tabbas Abban Sadiku ta nan zai shigo falon don haka gara ta nemo layar taje ta mayar ayi ta ta kare kawai.

Tana shiga dakin ta nufi wardrobe inda ta rataye rigar da ta saka jiya a saman wardrobe din, ta zura hannunta a hankali cikin aljihun rigar ta laluba taji babu komai. Ta koma ta daya gefen ta zura hannunta a dayan aljihun ta laluba a hankali bata ji komai. Mamaki ya bayyana a fuskarta, ta fizge rigar daga saman wardrobe din ta karasa ta bajeta a kan gado ta sake lalube aljihun duka biyun bata ji komai ba. Ta daga rigar ta zazzage babu a binda ya fado, ta zauna a kan gado tana kallon rigar tana mamakin inda layar ta shiga.

Tabbas ba mantuwa tayi ba, a hannunta Amina ta bata layar kuma tabbas a aljihun rigar ta saka. Bata cire ba ta barta a kan da safe ta dauke; to a ina layar zata fadi?. Gashi tsaf aka share gidan jiya kuma yau ma Jummai har tayi shara.

Ta mike ta koma gaban wardrobe din ta sake dubawa ko a kasa layar ta fado, bata sami komai ba. Ta dawo ta zauna a gefen gadon tana tunani; to ina layar zata shiga?

 Ikon Allah!

Ta fada a fili.

Motsin taba kofar ne ya dawo da ita hayyacinta, Yusra ce ta shigo da sallama tace

 Mommy Abba ya zo da matarsa.

Taja tsaki

 Mtsewwww! Kice masa ina wanka.

 Ai ba aiko ni yayi ba na san yanzu zai hawo nemanki.

Ta mike tana fadin

 To bari ki gani.

Ta fada bandaki ita kuma Yusra ta juyo ta fito.Tana jin lokacin da Abban ya shigo dakin ya fita. Har ta gama wankan nan bata gano inda layar nan tayi ba don haka ta hakura tunda Aishan ta riga ta shigo ta zauna a falon. Haka ta fito ta zabo leshi mai kyau ta shirya tsaf ta fesa turarukanta masu kamshi sannan ta sauko.

Tun kan ta karasa saukowa ta hangosu; Aishan tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya shi kuma Abban yana kan kujerar zaman mutum uku. Sadik da Yusra tunda suka gaisheta suka bar wajen, don Yusra ma tunda ta gaisheta ta haye sama bata sauko ba. Rukayya ce a zaune a kusa da Aishan sai Ummi da take ta faman yi mata surutu.

Ta karaso da sallama, ta wuce kai tsaye ta zauna a kusa da Abban Sadik. Tana murmushi ta dubeshi

 Yallabi Ina kwana?

Yaji dadin yanda ya ganta da fara arta don haka shima tashi fara ar ta karu

 Lafiya kalau, ya kuka kwana?

Bayan ta amsashi ta juya wajen Aisha tace

 Amarya bakya laifi, barka da zuwa.

Tana murmushi ta mayar mata da amsa

 Yauwa, ina kwana.

Suka gaisa cikin walwala, Zahra ta umarci Jummai ta kawo muta ruwa da lemo, ta dubi Abban Sadika tace

 Ka san kasa tashi nayi saboda gajiya shi ya sa ban samu na dafa muku abincin safe ba, ko a kawo muku yanzu ku karya.

 A a, mun karya ma sai dai ko kanwar taki zata kara.

Tace

 A a na koshi.

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban Sadik yace

 To Zahra ga kanwarki nan, naga ma kun riga kun saba kuma ban ga alamar matsala ba. Allah ya hada min kanku. Na gaya mata duk abinda take bukata ta nemeki, yara kuma yanzu sun zama masu gida biyu, duk inda suka shiga daya ne.

Zahra tace

 Hakane, Allah ya bada zaman lafiya. Ai ga uwata sarkin kaudi har ta makale mata.

Suka yi dariya gaba daya. Abban ya mike yana fadin

 Bari na hau sama, idan na sauko sai mu wuce.

Ya Haye sama ya barsu a nan falon.

Yana wucewa Zahra ta sha kunu ta bata rai, suna hada ido da Aisha ta dauke nata kana saboda yanda taga sauyin yanayin.

Ta harari Rukayya wadda take zaune a kujerar kusa da ta Aisha tace

 Ku kuma kowa ya bace kuna zaune kuna biya bakin mutane, tashi ki bani waje.

Nan da nan suka fice daga falon ya zama daga Zahra sai Aishan, tana ta faman bata rai ita kuwa Aishan ta ma kasa hada ido da ita tunda ta kula da yanda yanayinta ya canza.
Jimawa kadan ta tashi ta kashe talabijin din dake kunne a falon ta haye sama ya zama Aishace ita kadai a falon.

Ta cika da mamakin yanda kiri-kiri Zahra tayi mata fuska biyu a cikin abinda bai fi minti ahsirin ba .

Sai da aka yi wajen minti talatin sannan taji motsin saukowarsu, yana tafe Zahra tana biye da shi rike da jakarsa ta computer da litattafansa. Sai wani faman murmushi take suka jero suka shigo falon, ta dubi Aisha da fara a tace

 A a, ina  yayan naki sukayi Anti Aisha shine suka barki ke kadai?

Murmushi tayi tace

 Yanzun nan suka fice ai.

 Kuma sai ki kashe TV, da kin canza channel din kawai.

 Uhm.

Abban Sadik yace

 To mu tafi ko?

Ta mike ta dubi Zahra tace

 To sai an jima, na gode.

Ta mika mata 'yar karamar leda dauke da turaren wuta da wata karamar burner tace

 To ga wannan amarya, sai mun shigo ni da yara.

Sukayi mata sallama suka fice.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


10

Saida amarya ta kwana biyu sannan su Yaya Zuwaira suka kawo mata ziyara tare da Abdallah da Farha. Nan suka wuni ana ta hira, sai bayan la asar sannan suka tafi, suka barta da kewarsu.

Haka Yusuf ya cigaba da kwantar mata da hankali har ta samu ta dan kara sakewa.

Ranar Talata ne ya kama kwana uku, don haka ranar ne zai koma kwanan Zahra. Ya riga yayi musu bayani da daddare zai dinga canza waje kwana don haka wadda zai kwana a wajenta ita zatayi masa abincin dare.

Bayan ya dawo daga sallar magriba ya sameta a falo tana kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya zauna a kusa da ita suna fuskantar juna, yace

 Yanzu zan wuce wajen yayarki, amma gaskiya bana son barinki ke kadai. Kinga da a can kike da bani da wata damuwa.

Tayi dariya ta dan kwanta a jikinsa

 To ai ni ban ce maka ina jin tsoro ba, tunda idan ma wani abun ya taso zan iya kiranka ko na kirawo Mommy ko?

 Hakane, amma dai bari naje gidan sai na kawo miki Yusra ta zo ta taya ki kwana.

 To duk yanda kace.

Sai da yayi da gaske sannan ya Kanye jikinsa ya tashi yayi mata sallama ya fice a kan yanzu zai dawo ya kawo mata Yusra.
&

A falo ya samesu gaba daya banda Sadik, bayan Mommy ta amsa sallamarsa duka sukayi masa sannu da zuwa. Ya karasa ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Mommy, ya dubeta yace

 Wa zaki bawa kanwarki aro ne a tayata kwana?

Ta dan tsuke fuska

 To ai kaga dalilin da yasa nace a hademu kace tace bata so, ai na zata zata iya kwana ita kadai.

Ya kalleta alamar tuhuma, ta kau da kai sannan tace

 To ai gasu nan duk wanda ka daukar mata, sai dai Yusra itace take tayani kula da kannenta idan suna bacci.

Nana da take zaune tana yin homework tace

 Ni dai don Allah ba ni ba Abba nafi so na kwana a nan.

Kafin ya amsa Rukayya tace

 Abba bari na shirya muje, amma fa ban yi homework dina ba, ga hadda ma ina so Yaya Yusra ta biya min.

Cikin fara a yace

 Kada ki damu itama Antin zata biya miki, kwaso kayanki kafin na sauko daga sama sai na raka ki.

Ya wuce saman ya barsu a zaune.

Yana kulewa Mommy ta harareta

 Ke wai wacce irin yarinya ce Rukayya, kin ji kowa ya ce ba zai je ba sai ke uwar sakarci ko? Idan ya kuma zuwa yace wa zai je kika amsa sai na ci mutuncinki wallahi, kin ji na gaya miki.

Tayi tsuru-tsuru tana mamakin yanda kawai don tace zata kwana gidan amarya abun ya bata ran Mommy haka. Yusra ta harareta tace

 Sai ki tashi kije ki hado komatsanki kafin ya sauko kuma.

Ta tashi jikinta babu kwari ta nufi sama inda dakinsu yake.

Tare suka sauko ita da Abban tayiwa Mommy sai da safe suka wuce, yana kula da yanda yanayinta ya canza don haka ya tabbatar fada Mommy tayi mata.

Bayan ya rakata ya tabbatar Aisha ta kulle kofa sannan yayi musu sallama ya dawo.

Dakin baki Aisha ta nuna mata ta ajiye kayanta, sai a hankali Rukayya ta sake sukayi homework din kuma ta biya mata haddarta, suka dan taba hira suna kallo sannan wajen karfe goma na dare aka dauke wuta.
Aisha ta shiryo suka kwanta tare da Rukayya a dakin baki.
& &

Saida ya gama duk abinda yakeyi, ya zauna a falon sama yana kallon TV. Bayan yara sun kwanta itama ta zo ta zauna a kusa da shi, jimawa kadan ya dubeta yace

 Zahra.

Da murmushi ta dubeshi ta amsa

 Yallabai.

Ya gyara zama ya fuskanceta sosai

 Ban ji dadin abinda kikayi ba, don Allah ki bar yaran nan su yiwa Aisha duk abinda take so wanda bai sabawa addini ba. Ina laifi idan yara sun tayata kwana, amma nayi magana kince ai ita ta zabi haka. Kuma Rukayyan ma saida kikayi mata fada saboda kawai na sakata aiki tayi.

Ta bata rai tace

 To ni me nace, shikenan ba zan fadi ra ayi na ba saboda matarka. Yara kuma ai naka ne, ni babu wanda na hana idan ma Rukayya ce ta gaya maka nayi mata fada to karya takeyi.
 Ni dai don Allah kiyi min alfarma ki bari a zauna lafiya, don Allah.

 Uhm.

Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya kuma ta tashi ta wuce dakinsa ta kwanta tana matse kwalla. Wato daga ya dana dadin amarya kwana uku kacal har ya fara nema yayi mata fada a kan matarsa, lallai zata gyara musu zama. Haka ta kwana zuciyarta babu dadi.

Daga wannan lokacin ya zama kullum idan zai kwana gidan Zahra to Rukayya ce take taya Aisha kwana, tun tana dagewa har ta hakura. Kuma sai ya zama jininsu ya hadu da na Aishan suka zama kamar wasu kawaye duk da dai Rukayyan tana shan gori a wajen Mommy da Yusra.
-----

Ranar Alhamis da magriba bayan ya gama shirinsa zai koma wajen Aisha Mommy take gaya masa ita da yara zasu je wajen Hajiya gobe Juma a don sun kwana biyu basu je ba. Har ya fita ya dawo yace mata zai gayawa Aisha don haka idan sun shirya suyi mata magana sai su tafi gaba daya tunda driver ne zai kaisu. Yayi mata sallama ya wuce.
----

8 / 58