Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 58

48K to 51K   out of 172.2K words

na menene?

Ya dan rage tsawo cikin girmamawa ya bata amsa

 E Hajiya dama wanda Yallabai yace a kaiwa Hajiya Karama ne, shine zan mika mata.

Ta kara shan kunu

 To ka barshi idan an gyara za a mika mata.

Ya sunkuyar da kai

 Hajiya ai ko ni din ma sai na mi& '

Ba tare da ta bashi amsa ba ta kwalawa Hansatu kira. Nan da nan ta sheko da gudu daga bayan gida ta tsuguna
 Hajiya gani.

 Kwashi wanna naman ki kirawo Sadik ya zo ya dauki wannan a kai baya zan zo nayi bayanin yanda za a gyara.

Nan da nan kuwa ta dauki cinyar rago tayi bayan gida, kafin wani lokaci Sadik ya zagayo ya dauki cinyar san ya zagaya da ita. Ta koma ta zauna ta bar Malam Sule yana tsaye da baki a bude.

Sai da aka gama gyara naman nan tsaf ta tabbatar duk wanda ba a bayar sadaka ba an zagaya da shi bayan gida sannan ta tashi daga wajen. Malam Sule da Mai gadi suka hadu suka wanke wajen.

Tana zagayawa bayan gidan tace a hade naman gaba daya a saka mata a freezer tayi miya da shi.
& & & ..

Tunda ya sanar da ita a gidan Zahra za a yanka sa a kawo mata nama ta san ba lallai ta samu ba. Da fari ta so tace ya bata rago a yanka mata a gidanta to amma bata so ta nuna rashin amincewa da matarsa don tana kula da tsananin yardar dake tsakaninsa da Zahran. Ya kawo mata itace da mai da duk wasu abubuwa da zata bukata na suyar.

Tunda gari ya waye ranar Sallah ita da Amira suka wanke kayan suyar suka ajiye yanda da an kawo sai su fara aiki. Abu kamar wasa har la asar ba a kawo komai ba. Haka abun ya dinga bata dariya; wai naman sallar shi akewa wannan rowar da mugun halin.

Ta riga tayi layya a gidan Hajiya kamar yanda ta saba duk shekara, kuma dama naman yawanci ajiye mata akeyi. Don haka waya kawai tayi tace idan an soya a ajiye mata wani a danye gobe sai a kawo mata.

Cinyar sa aka kawo daga gidan  yanuwan babansu Abdallah don haka kawai sai Umma tace a soyawa Aisha ragonta gaba daya sai kuma a ajiye mata cinyar sa din a danye tayi miya.

Haka kuwa akayi, washegarin Sallah da yamma aka kawo naman nan a gyare aka shigar mata babu wanda ya gani.
......

Ranar kwana uku ga Sallah Nafisa; wadda  yar wa da kani suke da Abban Sadik; suka kawo musu ziyara ita da yaranta. Gidanta babu nisa da nan gidan nasu shi yasa duk shekara take kawo musu irin wannan ziyara.

Kamar yanda ta saba kai tsaye a gidan Zahra ta sauka, tun basu dade da zama ba Rukayya ta kwashi yaranta su uku suka tafi gidan Aisha, a can suka ci abinci suka ci nama da cake suka dawo. Suna shiga Bashar dan wajen Nafisan ya fada jikinta yana surutu

 Ummu munci nama da yawa, Anti ta bamu abinci kuma ta bamu cake da zobo baki ji dadi ba.

 Um.

Da yayi wannan maganar Zahra ta zata irin wanda ake kawowa daga makota ne, amma dai sai ta bincika don ta san ko Abba ya munafunceta.

Can da yamma Nafisa zata tafi ta dubi Mommy tace

 Zamu tafi Mommy, idan na fita na shiga gidan Anti Aisha mu gaisa sai mu wuce.

 To kuje mana idan kun fito sai ku dawo nan kafin nan na hada muku kayan yara.

Don haka suka fice suka nufi gidan Aisha tare da Rukayya, Nana da Ummi.

Wannan ne zuwan Nafisa gidan na farko wanda kafin nan duk labaran da take samu a kan Aisha na rashin mutunci ne don haka tana dari-dari ta shiga gidan. Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da Aishan, ta sa Rukayya ta tayata suka kawo ruwa da lemo ga kuma cake da nama. Suka dan taba hira sukayi sallama zasu tafi.

Aisha ta tsayar da su ta shiga daki ta fito da sabbin kudi 'yan dari bibbiyu ta bawa Nafisan guda goma sannan ta bawa yaran  yan hamsin kowa guda biyu. Bayan ta bawa kowa harda Nana wadda ta karba a raine sai ta boye sauran a bayanta ta dubi Ummi tace

 Bazan bawa Ummi ba bata zo min yawon Sallah ba sai yau.

Ta matso da sauri ta kama zaninta tana fada cikin shagwaba

 Anti na zo fa, kin gan ni ma fa.

Sukayi dariya gaba daya ta kawo kudin ta bata. Ta sa Rukayya ta kullowa Nafisa nama a kicin, nan da nan Nana ta bita.

Suka fito da kullin naman ta bawa Nafisa sukayi godiya suka tafi.

Suna komawa gidan Zahra suka yi mata sallama suka kama hanya.

Saida ta haye sama sannan ta kwalawa Nana kira, da hanzari ta tashi ta hau saman. Ba zata tamabayi Rukayya ba domin tun tuni ta fuskanci Rukayyan ba zata gaya mata abinda take son ji ba, kuma dama tun kafin a auro Aisha ta kance Rukayya 'yar Abbanta ce domin ta fi son shi.
Sai da suka shiga kuryar daki sannan ta tambayi Nana

 Nana wai Antin nama aka kawo mata ne da yawa take ta rabo haka?

Ta gyara zama

 Ai gaskiya Mommy sai dai idan rago aka yanka mata fa, kin ga naman kuwa? Manyan robobi ne fa guda biyu duka a cike da nama kuma ga karamar roba ta kayan ciki. Ina ga ma harda danye don kwanukan da aka ci abincin rana gasu nan duk kashi a kai.

Ta dan numfasa

 Allah Mommy. Kudin ma fa da bamu tana da su da yawa don  yan dari bibbiyu ma ta bawa Anti Nafisan kuma da yawa za su kai ten ko twenty. Ita ta samu sabon kudi mu kuwa da yake Abban baya nan bamu samu ba.

 Eh watakila sai ya dawo.

Ta sallameta ta sauko da gudu wajen  yan uwanta.

Tana fita ta mike tsaye tana kaiwa da kawowa a daki; kenan Abba ya munafunceta, nan ya ce a bawa Aisha nama ashe kuma ya zagaya ya saya mata rago. Ko kuma Aishan ce ta gaya masa ba a kai nama ba shine ya sa aka kawo mata daga wani wajen? Yanzu haka kuma munafuncin Malam Sule ne, don shima ta rasa yanda zatayi da shi ne da tuni ta sa Abban ya koreshi.

Ta koma ta zauna a gefen gadon.

Ta cigaba da tunani; gashi harda sabon kudi ya bata, kenan yanzu haka kafin ya fita ya bata ko kuma daga baya ya sa aka kawo mata.

Yanzu kiri-kiri Yusuf ya koma munafiki, buya kenan yakeyi yana yiwa Aishan abubuwa wadanda ita ba zai yi mata ba. Tayi kwafa tace

 Zai dawo ya sameni don wallahi ba zan yarda ba.

Haka ta wuni ranar tana shirin yanda zata bullo masa idan ya dawo.

Bata son ta ga Aisha a cikin walwala, tunda dai ta kasa rabasu da Yusuf to ta fi so ta ganta cikin damuwa da takura. Idan dai farin ciki take so to taje ta nemi mijinta ta bar mata Yusuf.
------

Kamar duk Babbar Sallah ranar hudu ga Sallah a gidan Umma suke wuni, don haka ma wannan sallar duka suka hadu da yaransu.

Zainab da matar Abubakar Fauziyya suna daki waken Hajiya yayinda Aisha, Zahida da Zuwaira sune a zaune a falo yaran kuma suna ta kaiwa da kawowarsu.
Aisha ta dubi Zainab tace

 Ya Zainab nifa mota zan saya bayan sallar nan.

Ta gyara zama tana murmushi

 Haba! Ko ke fa? Tun tuni kike maganar nan amma sai wani jan kafa kike.

 Ba zaki gane ba Yaya Zainab. Kin san shi Yusuf da a tsarinsa yana da driver wanda ya kamata ya kaimu duk inda zamuje, amma matarsa ta hanani morar direban nan. In kika ga na hau motar nan to mai ita yana nan a gabansa ne amma yana juya baya haka zata barni da hawa motar haya.

Zahida tace

 Yauwa Yaya Aisha ai gara haka wallahi, ta karata da waccan motar.

 Hmmm! Kin san na fara yi masa maganar kwanaki yace na bari zai duba, a tunanina so yayi ya saya min to amma kinga idan ya saya min dole ya saya mata kuma inaga ko dai bashi da kudin sayen biyu ko kuma baya so ya bata motar. Su dai suka sani.

Zainab tace

 To ai ke da kudinki zaki saya ko?

 Eh, next month zan dauki adashi dubu dari uku idan na debi wasu a kudaden hayar gidana da nake tarawa na hada kamar miliyan daya da rabi na san zan sami mota mai kyau kuma kinga tunda Yaya Abubakar zan bawa ya siya min na san idan da ciko zai cika min.

Zahida ta mika mata hannu suka tafa tana fadin

 Baki da matsala Mrs Yusuf.

Haka suka gama hirarrakinsu Aisha ta gama yanke shawara zata sayi mota saboda ta huta da wulakanci da Zahra take mata akan motar gidan.
& & &

Ya rigar ya sanar da su ranar Lahadi da sassafe zai dawo don haka duka suke ta shirin tarbarsa.

Wajen karfe bakwai na safe aka bugawa Aisha gate, Rukayya ce da kayanta niki-niki. Aishan ta dubeta bayan ta bude mata ta shigo tace

 Rukayya ya na ganki da kaya?

Ta sunkuyar da kai ta bata amsa

 Mommy ce tace na taho dasu na dawo tayaki kwanan.

 To shiga muje ga Amira can tana bacci a dakin sai ta tayaki ki ajiye kayan ku fito muyi breakfast.

Ta amsa ta wuce dakin, ita kuma Aisha ta koma kicin inda take aiyukanta.
Tana aiki tana dariyar Zahra; tabbas ta tabbata mai fuska biyu. Wato yana tafiya ta turo aka kirawo mata  yarta saboda kada ta tayata kwana, yanzu kuma da yake ya ce yau zai dawo shine har ta turota. Wato duk tsagerancinta ma akwai wanda take tsoro, sai dai tsoron Allah ne kawai bata yi. Haka tayi ta aiki tana dariya ita kadai.

Karfe shida da rabi na safe jirgin su Abba ya sauka a Nigeria. Suna sauka Malam Sule yana jiransu, a nan airport din ya sami taxi ya sa Yaya Bello don a kai shi gida kai tsaye.

Tun da suka fara shirin dawowa dama ya sanar da su a gidan Zahra zai sauka. Tayi shiri sosai na dawowarsa, an gyara gida sosai sannan ga abinci ta shirya masa funkaso da farfaesun naman Sallah ga zobo kuma sai kamshi kawai ke tashi.

Karfe takwas saura kwata motar Malam Sule ta tsaya a bakin gate din gidan Zahra, Malam Sule ya danna horn suna jiran mai gadi ya zo ya bude.

Dan ga ruwan da yake kawowa Aisha ruwa ne ya zo ya tsaya a bakin gate dinta, Abban yana hangoshi. Ya dauki dutse ya kwankwasa gate din ya dawo ya fara sauke jarkokin ruwan a wajen.

Abban ya dubi Malam Sule yace

 Malam Sule me dan ga ruwa yake a kofar gidan can?

 Ah, yallabai Ina ga ai ruwa ya kawo amma ban sani ba, ko na karasa na tambayo Hajiyar?

A dai-dai lokacin mai gadi ya zuge gate din, Abban ya bude kofar motar yana fadin

 Shigar da motar, bari na je na ji.

Ya fice Malam Sule ya tura motar ciki.

Yana isa gate din Aisha tana budewa, sanye da jilbab dinta. Ta dubi me ruwa tace

 Sauke min a nan.

Ta nuna masa wajen daga ciki.

Abba ya karasa shiga da fara arta tace

 Alhajin Allah, Sannu da zuwa.

Da fara a shima ya amsa sannan yace

 Ya naga Dan ga ruwa?

 Uhm, ruwan ne Ina jin ya sami matsala shi yasa ba a kunnawa.

Ta nunawa dan ga ruwa bokitin fentin da ta ajiye tana fadin

 Juye a nan na dauka.

Abba yace

 Ke kike kaiwa ciki.

 Eh ai saboda nauyi, in na kai sai na dawo na kara kaiwa har na cika drum din.

 Gafara.

Ya dauki jarkar ya nufi cikin gidan ta bi shi a baya yana tamabaya

 A Ina kike juyewa?

 Akwai drum a kitchen.

Yana shiga falon Rukayya da Amira suna zaune suna kallon TV. Duka suka mike suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya wuce kicin ya juye ruwan. Ya dawo ya sake dauko wata jarkar ya komo ciki.

Rukayya ta dubi Amira tace

 Bari naje na gayawa Mommy Abba ya dawo.

Ta fice da gudu suka hadu da Abban a tsakar gidan yana dauke da jarka tace

 Abba bari naje na cewa Mommy ka dawo.

Ta fice da gudu.

Haka ya gama juye mata ruwan ya cika mata drum biyu sannan ya fito ya sallami Dan ga ruwa ya koma ciki.

A daki ya sameta tana goge inda ruwa ya zuzzube, ya tsaya yana kallonta yana murmushi.

Ta dubeshi itama tana dariya tana fadin

 Bari na sama maka ruwa ka dan sha.

Ta zo wucewa ta gefensa ya sha gabanta ya janyota jikinsa ya rungumeta, suka sa dariya.

Bayan sun fito falon ta ajiye masa kunun aya mai sanyi da cake, ya ci ya koshi suna dan taba hira sannan yayi mata sallama ya wuce gidan Zahra.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

18

Tunda Rukayya ta kawo labarin ya dawo yana can yana diban ruwa Mommy take faman cika tana batsewa, dama Malam Sule ya shigo da karamar jakarsa.

Sai a lokacin sannan Mommy ta tuna Sadik ya yanke wayar injin janyo ruwan, ta dubeshi tace

 Sadik baka mayar da abun nan ba ashe?

 Wallahi na manta Mommy, ba komai kafin dare zan mayar.

Suka cigaba da harkarsu yayinda ita kuma ta wuce daki.

Duk nishadin da take ciki ya gushe saboda gaya mata da akayi yana can gidan Aisha yana kai mata ruwa. Ce mata yayi a nan wajenta zai sauka amma saboda munafinci yana can wajen amaryarsa yana hutawa, tabbas zai zo ya sameta.

Da sallama ya shigo gidan, tana sama ta jiyo yara suna oyoyo. A falon saman tayi zamanta tana jiransa tunda dama a nan ta saka masa abincinsa.

A zaune ya sameta a kan kujera tana ta cika tana batsewa, bai ma kula da yanayin fuskarta ba.

Yana rike da hannun Ummi ya shiga falon da sallama, bayan ta amsa sallamarsa ta bude baki kamar wadda aka yi wa dole tace

 Sannu da zuwa.

Ya karaso ya zauna a kusa da ita bayan ya amsa yace

 Ya akayi babu ruwa a gidan Aisha ne, me ya sa ba a kunnawa ruwa yaje can na ga kuma nan da ruwa don fanfon waje ma a kunne yake?

Ta dan gatsina fuska

 Lalacewa yayi ina ga don kullum kuwa ana kunnawa, kuma bata fada baya zuwa ba ai da an duba.

Ya gyara zama ya zaro waya, ya lalubo lambar wayar plumber ya danna masa kira, tana ji yana cewa lallai ya zo kafin la asar don yau yake so a gyara ruwan nan.

Ranta ya kara matukar baci; tun da ya dawo unguwarnan yake hidimar Aisha kuma har yanzu ma ya shigo wajenta kallon kirki bata isheshi ba balle ma ya san yanayin da take ciki.

Ta daure ta tashi ta nufi dining table don ta kula sai ma tayi da gaske sannan zai dubeta. Ta dauko jug din zobon da kofi ta dora a kan tray ta kawo inda yake zaune shi da Ummi ta ajiye. Ta fara zubawa yace

 Kai ba zan sha zobon nan ba ruwa dai zaki bani.

Ta bishi da kallon mamaki, to me yake nufi?

Ta dauke zobon ta mayar kan table ta dauko masa ruwan roba ta kawo masa ta koma ta zauna.

Ya bude ya sha kamar rabin roba sannan ya dubeta yace

 Ya na sameku? Ya gidan da yaran?

Ta dan yi murmushi tace

 Lafiya muke gaba daya, ya ibada? Ya gajiyar hanya?

 Lafiya kalau, mun gode Allah. Bari na watsa ruwa na fito na ci abinci kin san ban yi breakfast ba.

 Sai ka fito.

Ya shige dakin tabi bayansa da kallo.

Sai da ya dauki lokaci ya shirya sannan ya fito, ya ce ta saka masa abincinsa a kan kafet ba zai ci a tebur ba don haka nan ya baje a kan kafet ya ci funkaso sosai ya shanye romonsa.

Naman sallan da ta sa masa a plate kuma ya ajiye a gefensa yana ci suna hira da yara. Sai a lokacin ne take jajanta masa barin da Aisha tayi, duk ba bata je ko kofar gidan ba haka kiri-kiri tace masa ta je.

Can zuwa azahar yana zaune a falo yana hutawa maigadi ya shigo ya sanar da shi isowar plumber, don haka ya tashi ya fice.

Kamar yanda al adarsa take idan dai za ayi wani gyara a gidan nan to sai dai ayi a gabansa, don haka yau din ma tare suka zagaya bayan gidan.

Mai gyara yayi 'yan dube-dubensa ya juyo ya dubi Abban yace

 Yallabai yara sun yi wasa a wajen nan dai ko?

 Ka san bana gari, ba zan iya sani ba. Me ka gani?

Ya janyo wata waya ya dan matsa yadda Abban zai hango yana fadin

 Ka ga wayar da aka yanke nan Alhaji, don gaskiya ba tsinkewa tayi ba sai dai ko idan reza aka saka aka yanketa gaskiya. Tunda kuma ka ga ita kadai aka yanke balle ace bera ne ko wani abu, kuma idan bata jiki

17 / 58