Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 58

117K to 120K   out of 172.2K words

Gashi zuwa yanzu matan unguwar da take harka da su sun fara tambayarta labarin Aisha a kan sunji a unguwa cewa auren Aishan ya mutu; duk da dai ta gaya musu itama bata san me ake ciki ba domin da ta tambaya ma Abban yace kada ta sake yi masa maganar.

Tabbas dole ta koma Doguwa; tunda dama akwai maganar Yaya Bello da take so a rabashi da Abban. Dama azumi ne ya hanata zuwa da aka sallace kuma bata da aiki sai bacci saboda cikin da take dauke da shi; ko da yake lokaci zata saka taje gidan Amina su tsara yanda za ayi don watakila ma Aminan zata iya zuwa mata Doguwan.

Haka ta karasa wunin ranar tana tunanin mafita.
--------

Ita kuwa Aisha tunda ta dawo gidanta sai ta sake mayar da hankali wajen addu a, ranakun aiki taje aiki ta dawo ranakun Asabar da Lahadi kuma sai taje islamiyya. Rashin kulata da Abban yakeyi yana damunta sai dai da yake dinkin mayafai da takeyi yana rage mata zama haka nan sai abun yayi mata sauki;kuma ta samu ana sayen mayafan sosai don haka kusan kullam cikin aiki take Amira tana tayata.
---------

Ranar Alhamis ce don haka yara babu islamiyya da yamma, tun safe ta gayawa Saddiku kada ya fitar mata da mota don zata fita da yamma amma ga mamakinta sai da ya fita; koda yake yanzu ta kula ko sauraron maganarta baya yi, yanda yayi niyya haka yake aikatawa. Malam Ali yana kawo yara daga makaranta tace ya tsaya zai kaita unguwa don haka nan ya zauna ya jirata.

Saida ta gama abinda takeyi tayi sallar la asar sannan ta fito suka kama hanyar gidan Amina.

Duk da gidan Amina bai kai girman na Zahra ba amma shima ya tsaru, domin maigidanta ma ya fi Abba Saddiku dukiya. Cikin walwala ta sauketa ta ajiye mata lemo da cake sannan suka gaisa.


Bayan sun gaisa Aminan ta dubi Zahra wadda damuwa ta bayyana a fuskarta tace

 Ya na ganki duk kinyi yaushi ne kawata, meye labari?

Ta tabe baki ta kawar da kai

 Mtseww, wallahi kin san na ce miki Aisha ta tafi gidansu ko?

 Eh kwarai kuwa.'

 To wallahi yarinyar nan ta tattaro kayanta ta dawo.

Ta rike haba tana mamaki

 Ikon Allah, to amma dai Abban bai ce komai ba ko?

 Bai ma san da ita ba komai normal, kawai dai bana son zamanta a gidan ne. Nifa na fi so ace babu igiyar aurenta a wuyansa shine kawai zan huta.

Ta dafa cinyarta

 Ki daina damuwa, ki bawa banza ajiyarta kawai tunda dai maigidan yana hannunki. Kuma na gaya miki aikin bokan nan ba zata iya karyashi ba ko waye malaminta a garin nan.

 Hmm! Kin san kuma da maganar Yayansa da nace miki yana mun shisshigi, duk da dai na sa Yaron Malam yayi min aiki amma dai naga alama aikinsa bai yi ba. Ni wallahi Doguwan ma nake son zuwa don dai kawai cikin da yake jikina ne ya sa bana son zuwa.

Ta dan zaro ido

 Ciki uwar Saddiku? Lallai matar nan himmarki tana da yawa.

 To na sani ko shine namijin da nake ta nema, ai kin ga dole na tattala.

Ta mika mata hannu suka tafa

 Da kyau kawata. Nima wallahi ina son zuwa Doguwa saboda mijin Asiya, ya fara kawo mata wargi gara na nema mata taimako. To amma gaskiya sai an dan kara kwana biyu, in kina so idan na shirya sai muje ko kuma na tafi da sakonki mu gani ko zai karba. Sai dai shi kinsan fa baya aiki da sako sai dai kai da kake da bukata kaje da kanka, kuma gaskiya ba zan baki shawarar zuwa wajen nan da ciki ba.

Ta dan yi tsaki

 Wallahi nima abinda nake ji kenan, to amma bari mu gani a kwana biyu tunda ma yanzu babu wata major matsala.

 Gaskiya dai. Idan kuma wani abun ya taso ai sai kiyi maleji da Yaron Malam tunda shi ko ta waya zaku gama komai.

Suka karasa hirarrakinsu sai gefin magriba sukayi sallama Zahra ta shiga mota Malam Ali wanda yake jiranta ya mayar da ita gida.
Haka ta hakura ta cigaba da rainon cikinta tana fatan ya zama namiji; tunda ko babu komai yanda bokan nan yayi mata alkawarin babu wanda yake maganar Aisha. Domin har dangin Abba ma babu wanda yake maganarta kamar ma babu ita, kuma tana da yakinin kwanan nan kudin hayar gidan zai kare ta san dole Aisha ta tashi tunda babu mai biya mata.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

35

Duk yanda Aisha ta kai ga son boye damuwarta game da rashin ganin mijinta abun yana mata wahala; lokuta da dama ta kan kwana tana kuka. Wasu lokutan kuma idan ta yi sujuda da nufin ta roki Allah sai kuka yaci karfinta, haka zatayi mai isarta sannan ta dago daga sujudar. Tana zuwa aiki da islamiyya ga kuma cinikin mayafanta amma duk wannan bai isa ya debe mata kewar mijinta ba.

Yau din ma haka ta tashi cikin yanayi na damuwa, gashi ranar hutu ce don haka babu aiki kuma gashi da wuri Amira ta fita saboda ana bikin babbar kawarta; don haka ita kadai ce a gidan.

Duk yanda ta so ta kawar da damuwar daga ranta abun ya faskara, haka tayi ta faman aikace-aikace, har aikin ma da batayi niyyar yi ba. Sai wajen karfe biyu ta gama goge gidan, ta dauko tsumman ta fito ta wanke a faffon tsakar gida ta shanya. Har ta kama hanyar shiga gidan sai kuma ta zauna a kan dankalin da fulawoyi suke ciki; ta karewa tsakar gidan kallo kamar mai neman wani abu.

Haka kawai kuma sai ta ji kamar ita kadai ce a duniyar; ya za ayi ace tana zaune a gidan mijinta amman saboda Zahra babu mai kulata? Makota gaba daya basa harka da ita gashi mijin ma yanzu ya daina kulata. Ta manta rabon da a buga mata gate don daga ita sai Amira suke rayuwarsa, sai dai da yake duk sati sai Anti Uwani ta kawo su Abdallah. Ta share zazzafar kwallar da ta zubo a kan fuskarta.
Tabbas ba zata taba yafewa Zahra ba da ma duk wani wanda yake da hannu wajen sakata a wannan halin.

A da ta yiwa kanta alkawarin zata zauna tayi jiran har mijinta ya dawo hayyacinsa amma kawo yanzu bata sani ba ko zata iya cika wannan alkawarin. Domin zaman ya fara isarta, ta fara rasa walwala gaba daya tunda komai ya daina bata farin ciki. Tabbas bata san zuwa yaushe zata iya jira ba amma dai ta fara tunanin yiwuwar ta koma gidan Hajiya kawai ko jiran ne tayi a can.

Ta share hawayenta lokacin da ta tuna la asar ta kusa kuma bata ma yi azahar ba, ta mike cikin sanyin jiki ta shige cikin gidan domin yin sallar azahar.
___
Da yake tazarar dake tsakanin karamar Sallah da babbar Sallah babu yawa har har an fara lissafin babbar Sallah.

Kamar yanda ya saba haka yayi wa kowa kayan Sallah; baiyi maganar Aisha ba wanda wannan ya kara kwantarwa da Zahra hankali ta kara sakankancewa lallai aikin boka na Doguwa ya kama.

Sa ya siyo da rago daya wanda aka yanka Uwara Saddiku tayi yanda take so da shi cikin walwala. Cikinta ya fara girma domin ya shiga wata na hudu don haka ba da ita akayi aikin suya naman ba, masu aiki ne su uku sukayi. Sai dai kawai tana zaune daga gefe a kan tabarma tana nuna yanda take so ayi.
Haka suka gama aikin suka tattare mata naman aka saka a cikin gida.

Ita kuwa Aisha tun ana i gobe Sallah suka tafi gidan Hajiya, a can aka yanka mata ragonta aka gyara aka soya. Saida suka gama yawon Sallah lokacin bayan Sallah da kwana biyar sannan suka koma.
Haka rayuwa ta cigaba.
__

Ranar Talata ce tana zaune a staffroom, bata da aiki a daidai lokacin don haka take ta faman duba wayarta tana kallon status; daga kan wannan ta koma kan wannan. Suna ta wucewa har tazo kan status din Anti Karima, matar Yaya Bello.

Hotuna ne na yaronta na uku wato Yusuf wanda suke kira Adil, daga kallon hotunan zaka gane bikin sauka ake yiwa Adil din wanda tabbas ta tuna kamar wancan satin ta ga hoton katin gayyatar bikin saukar a status din Yaya Saratu. Daga rubutun da Anti Karima tayi a status din ne kuma ta gane saukar hadda yayi; tayi murmushi tana kallon hoton zayyanar dake hannunsa.

Idan taga yaro ya haddace alkur ani tabbas yana bata sha awa kuma tana alfahari da su domin Abdallah da farha ma tana fatan su haddace izu sittin.

Ana cikin bikin Sallah ta gani a status din Anti Karima an kawo kayan auren Asma u yayar Adil din, ta manta dalilin da ya hanata koda waya ne ta yiwa Anti Karima tayi mata barka. Lallai yanzu ya kamata taje gidan nan don ba zata ma iya tuna rabonta da su ba, ko babu komai dai ya kamata taje mata murnar auren Asma u da ake shirin yi kuma da saukar Adil din.
Nan take ta yanke shawarar ranar asabar idan ta tashi daga islamiyya zata je gidan tunda dama karfe sha daya suke tashi kuma ranar Amira tana da lecture har karfe daya; don haka daga islamiyya sai ta wuce gidan Yaya Bello daga can ta tsaya ta gaida Hajiya sai ta wuce ta dauko Amira.

Ta dan gatsina fuska a lokacin da tayi tunanin zuwa gidan Hajiya; bata son zuwa gidan Hajiya saboda yanda Hajiyan takeyi mata wanda ya sa Anisa ma da take gidan bata ganin girmanta don ko gaisheta bata yi. Ta tuno zuwanta na karshe gidan wanda bayan ta gaisa da Hajiyan haka Hajiyan ta tashi ta shige daki ta barta, itama Anisa da mai aikin Hajiya suka shige kicin suka barta ita kadai a falon Hajiya. Saida ta gaji da zama sannan ta taso ta fito kuma babu yanda bata yi ba Anisan ta kirawo mata Hajiyan tayi mata sallama taki; sai ce mata kawai tayi tayi bacci kuma idan tana bacci ba a tashinta. Haka ta hakura ta tafi tana mamakin dalilin da yasa suke mata wannan kiyayyar. Kusan zata iya cewa kaf  yan gidan su Abba Yaya Bello ne kawai da iyalansa suke zama da ita yanda ya kamata.

Ta kawar da tunanin ta cigaba da latsa wayar tana hakurkurtar da zuciyarta a kan haka zata hakura taje gidan Hajiyan, in ya so ta dauki dan rakiya daga gidan Yaya Bello watakila abun yayi mata sauki.
& & & .

Tun ranar Juma a ta tanadin alkur ani izu sittin da turaren mai kamshi da agogon hannu wanda ta saka a leda a kan zata kaiwa Adil. Da tayi tunanin zata dafawa Hajiya funkason alkama da farfaesun kifi to amma gaskiya bata son ta sha wahala taje su lalatar da abincin basu ci ba don haka ta yanke shawara gara ta sayawa Hajiyan tuffa da kayan shayi irin wanda ya dace da masu ciwon suga ta kai mata.

Ranar asabar suna tashi daga islamiyya ta wuce gidan Yaya Bello.

Tana tsayar da motarta a bakin gate din gidan yaran gidan suna dawowa daga tahafiz; tun daga nan yaran suka fara gaisheta, bayan ta amsa suka nufi cikin gidan a tare. Suna tafe tana yiwa Adil murnar haddar da yayi.

Cikin girmamawa Anti Karima ta karbeta, Muhammad da Asma u wadanda basu je tahfiz ba suka gaisheta sannan Asma u ta kawo ruwa da lemo. Suka zauna ita da Anti Karima a falo sunata hirar yaushe gamo, daga baya kuma aka janyo akwatunan kayan auren Asma u aka bude mata ta gani tana ta sa albarka.

Anti Karima ta dubeta tana daga mata kayan tace

 Kinga yanzu saura wata uku da kwana goma bikin.

Da murmushinta tace

 Allah ya nuna mana, kice abun ma ya matso.

Jimawa kadan Aishan ta dubi Anti Karima tace

 Anti to me ake shiri? Akwai wani anko da za ayi don gara na karbi nawa kafin na tafi.

Ta kama haba ta bude baki

 Tab, ai Abbansu baya son anko babu ma wanda ya isa yayi wannan zance. Kina ji event center ma yace ba za aje ba wai a nan gidan zamuyi gaba dayan bikin. Har yanzu faman lallabarsa nake yana burtsewa; tunda kinga gidan ai ina muka ga filin yin biki idan banda rigimarsa.

 Gaskiya dai Baban su Muhammad da ya bari munje event center din. Amma fa kin san duk abun suna ne ko a nan din aka yi kalau za a gama shike nan, ai albarkar abun ake nema.

 Hakane.

Suka cigaba da hirarrakinsu.

Sai wajen sha biyu da kwata sannan Aisha ta mike zata tafi. Ta nemi wanda zai rakata gidan Hajiya aka ce Asma u ta shirya suje, don haka ta dan zauna tana jiran Asma u ta kintsa.

--------

Kamar yanda ya saba duk ranar da babu aiki da safe yake tafiya gidan Hajiya, idan rana tayi sai ya wuce gidan Yaya Bello inda a can zai ci abincin rana. Ba zai koma gidansa ba har sai anyi sallar Magriba. Duk yanda Zahra taso ya daina zuwa gidan Yaya Bello ko kuma a kalla idan ya je ya daina dadewa abun yaci tura. Tunda yace mata a can yake cin abincin rana ta fara zargin wani abun suke barbada masa a abincin shi yasa ya kasa rabuwa da su.

Sau biyu tana turawa Yaron Malam kudi yayi mata aikin da zai raba Abban da Yaya Bello amma ko sauyi bata gani ba. Daga karshe Yaron Malam din ya sanar da ita aikin ba zai yiwu ba domin mutumin da ta bayar da bayaninsa idan sun tashi zasuyi aiki ko ganinsa basa iya yi.
Sosai abun ya bata mata rai amma babu yanda zatayi tunda tana tsoron zuwa Doguwa da cikin jikinta; musamman da yake sau biyu tana yin scanning a gurare daban-daban kuma duka biyun sun tabbatar mata namiji take dauke da shi; bata son wani abu ya sameshi.

Haka ta hakura ta daga musu kafa, amma tayi alkawarin idan ta haihu da zarar tayi arba in zata je Doguwa duk sai tayi maganinsu ko waye malamin Yaya Bello bai isa ya mallake mata miji ba.

Yau din ma bayan ya gama cin abincin safe tana kallonsa ya shiryo ya fito, tun safe take masa korafin bata jin dadi da nufin ya fasa fitar amma bai ma kulata ba. Kawai sai ya sanar da ita idan da matsala tayi masa waya sai ya dawo. Da kyar ta bude baki tayi masa a dawo lafiya shi kuwa ya amsa ya fice ya kama hanya lokacin wajen karfe goma.

Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce don ya san a yanzu Yaya Bello yana can, domin tunda diabetes dinta ya tashi da azumi da kanshi yake zuwa yana bata abincin safe da na dare. Sosai suke lallabata saboda bayan diabetes din kuma to tana yi musu rikici irin na tsufa domin ko abincin ma idan ta ga dama sai tace sai taci abinda likita ya hanata ci. Haka dai suke ta fama.

Lokacin da Abban ya shiga gidan Hajiya ta gama cin abincinta, suna zaune dai a falo suna hira ita da Yaya Bello. Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu gaba daya.

Can zuwa shabiyu lokacin har Hajiya ta fara gyangyadi a falon, sukayi mata sallama domin ta samu tayi baccinta. Suna fita suka nufi gidan Yaya Bello a motar Abba tunda shi Yaya Bello bai zo da mota ba.
__

Lokacin da Yaya Bello da Abban Saddiku suke shiga gidan Yaya Bellon yayi daidai da lokacin da Aisha suke fitowa tare da Asma u yayinda Anti Zalihan take biye dasu tana yiwa Aisha sallama da godiya.

Kana shiga gate din gidan dan karamin farfajiya ne inda daga nan zaka shiga wata kofar mai irin siririn soron nan sannan ka fada tsakar gidan. Kasancewar kofar falon baki wanda take a farfajiyar farko a rufe take sai Yaya Bello ya wuce gaba suka nufi cikin gidan ta wannan soron.

Suna daf da kaiwa karshen soron Aisha ta sako kai Asma u na biye da ita. Ganin Yaya Bello ta tsaya ta fara kokarin kaucewa ta bashi hanya ya shige, tana shirin rage tsawo ta gaisheshi ta hango Abban Sadik a bayansa.

Take ta manta da gaisuwar da take niyyar yi ta bi shi da kallo baki a bude. Ta kusan shekara biyu rabon da ta ganshi kamar haka, ya dan yi kiba amma kuma ya kara tsufa. Yanda take binsa da kallo shima haka yake binta da kallon.

Yaya Bello ne ya katse musu kallon yace

 A a! Aisha. Sannu da zuwa.

Ta kauda kanta ta rage tsawo ta gaishe da Yaya Bello. Bayan ya amsa ya juya bayansa ya dubi Abba yace

 To kai kaga amarya ta biyoka fa.

Kamar bai ji abinda yace ba ya bude baki a hankali har yanzu idonsa a kan Aishan cike da tsananin mamaki yace

 Aisha! Daman nan kika dawo?

Ta kawar da kai ta dan share kwallar da ta fito daga idonta, a dai-dai lokacin Asma u ta koma cikin tsakar gidan ta zauna a kan kujera domin jiransu.

Cike da mamaki Yaya Bello ya fara binsu da kallo daya bayan daya yana kokarin ya fahimci abinda yake faruwa. Ya gyara tsayuwa yace

 A a! Me yake faruwa ne? Me yake faruwa ne? Ya zaka ce nan ta dawo bayan da na fita ma bata zo ba.

Kafin ya bashi amsa ya kama hannunsa ya dubi Aishan yana nuna mata cikin gidan yana fadin

 Mu koma naji abinda yake faruwa, kunata kallon

40 / 58