Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   52 / 58

153K to 156K   out of 172.2K words

jin a cikin yaran zata rike wasu wasu kuma ba zata zauna da su ba? Tabbas ya san da sa hannun Zahra a lokacin da ya manta da Aisha na wani lokaci to amma menene laifin Yusra a ciki?

Ya daga fuskarsa ya gyara zamansa; in dai Aisha tana son zama dashi dole ta zauna da yaransa gaba dayansu, kuma zai yi iya yinsa wajen ganin hakan ya faru. Ko babu komai yana son ta sosai kuma a iya tunaninsa ita kadai ce macen da zata zauna masa da yaran tsakanin da Allah babu cutarwar. Ya tabbatar bata da mugunta kuma bata da sharri, hasali ma zai iya cewa idan dai magana ake ta tarbiyyar yara ta fi Zahra iyawa saboda yanda yaga mu'amalarta da yaranta da kuma yanda take kula da Rukayya. Ba zai taba rabuwa da Aisha ba kuma ba zai kara aure ba, itace dai zata hakura ta zauna masa da yaran.

Yana nan zaune ya jiyo motsin su Sumayya suna shigowa sun dawo daga islamiyya. Yana matukar tausayin yaran kuma tabbas ya san suna bukatar uwa kamar Aisha, yana fatan kafin gari ya waye ta farka daga mafarkin da takeyi ta tattaro kayanta ta dawo gidan.

& & ..

A guje su Sumayya suka shiga gidan suna murna saboda sun zata zasu sami Aisha a gidan. Yusra ce kawai a falon, ba tare da ko sallama ba Sumayya ta dubeta tace

'Yaya Yusra Anti Aisha tana nan?

A gajarce ta amsa

'Bata nan.

A dai-dai nan Rukayya ta shigo falon bayan ta yiwa Yusra sallama ta sanar da ita sun dawo kai tsaye ta wuce dakin da aka gyarawa Aisha ta tura kofar. Babu komai a dakin don haka ta mayar da kofar ta rufe sannan ta wuce dakinsu na kasa. Yusra da take zaune a kan dining table ta bi bayanta da harara sannan tayi tsaki; wanda Rukayyan ta ji amma sai ta kawar da kanta.

Tana shiga dakin ta ajiye jakarta ta canza hijabinta, Ummi da take zaune a gefen gado bayan ta ajiye tata jakar tace

'Yaya Rukayya Antin bata dawo nan ba, gidanta zaki je?

'Eh, zan je na gani idan ma ta shirya sai na tayata debo kaya.

Ta mike ta nufi kwandon kayansu tana fadin

'Bari na sa hijabi muje, mu sulale mu bar Sumy naji ta haye wajen Abba.'

Sukayi dariya a tare.

A dai-dai nan Yusra ta shigo dakin, ta dubi Rukayyan tace

'Ku kuma Ina zaku je kuke wani gyara hijabai?

A gajarce Rukayya ta bata amsa

'Gidan Anti Aisha.'

Dogon tsakin da Yusran ta ja shi ya sa Rukayyan ta dubeta, ita kuwa Ummi a take ta fara kokarin cire hijabinta don tana shakkar Yusran. Cikin izgilanci Yusran ta matsa gaba Rukayyan tace

'Babu inda zaku je wallahi. Ke wai wace irin marar tunani ce Rukayya, uwarki ta mutu amma ko sati biyu ba ayi ba kin fara karya dokokin da ta shinfida miki lokacin tana raye. Iya biyayyarki da Mommy kenan? dama jira kike ta mutu ki koma wajen makiyiyarta? To wallahi baki isa kije wajen wannan ma-sharranciyar matar ba yau. Ke kenan saboda tsabar ba kya kishin Mommy kullum ki kwashe mata yara ki kai su inda ta hanaki zuwa sai kace mai kwakwalwar kifi. To yau babu inda zaku tunda uwar taku nan zata dawo sai&  

Cikin takaici idonta yana fitar da kwalla ta matsa kadan zata shige ta gefen Yusran amma Yusran ta tareta, ta sake matsawa Yusran ta sake tareta tana fadin

'Malama ki cire wannan hijabin ki zauna babu inda zaki je. Lallai yau da Mommy zata dawo duniya da tayi mamakin yanda kika manta da ita kike kokarin sake uwa& .

Kafin ta gama fadin abinda tayi niyya Rukayya ta dage iya karfinta ta tunkudata. Ta tafi taga-taga, saura kadan ta kai kasa ta dafe kofar dakin ta tsaya tana kallon Rukayyan da mamaki. Cikin kunan rai tace

 Kan bala'i, wato saboda matar nan ta gama dake ni kike turewa saboda baki da kunya kuma kinga babu idon Mommy ko?

A fusace ta nufo ta yayinda ita kuma Rukayya take tsaye ta nade hannuwanta a kirjinta tana fadin

'Babu ruwanki da ni Yusra, fita a harkata! Zan je na tambayi Abban idan yace kada naje sai na fasa amma ke baki is& 

Kafin ta rufe bakinta Yusran ta dauke ta da mari. A take ta dafe kumatunta tana huci, kafin tayi wani tunani ta zare hannu itama ta gaurawa Yusran mari.

Da gudu Ummi ta fice tana kuka ta haye sama don ta kirawo Abba.
Yusran ta cakumo wuyan hijabin Rukayya, cikin zafin nama Rukayyan ta fisge ta tunkede Yusran wadda ta fadi kasa, ba tare da bata lokaci ba Rukayyan ta bita kasa ta haye kan ruwan cikinta tana ta kai mata duka ko ta ina; duk wani bacin rai da Yusran ta dade tana cuzguna mata da shi tun kafin rasuwar Mommy ya dinga dawo mata don haka ta rufe ido tana ta faman kai mata duka. Ganin abun yayi yawa yasa Yusran ta fara ihu tana kokarin ture Rukayyan daga kan cikinta wanda ya gagara, kamar ma karawa Rukayyan karfi takeyi. A dai-dai nan Abba ya banko kofar ya shigo Ummi da Sumayya suna biye da shi. Da karfi ya fincike Rukayya daga kan Yusra wadda idonta ya rufe, ta fizge daga rikon da Abban yayi mata tana huci. Ba tare da bata lokaci ba ya gaura mata mari wanda ya dawo da ita hayyacinta ta dafe kumatun tana kallonsu shi da Yusran tana fitar da hawaye masu zafi.

Da gudu Sumayya ta fice ta nufi bayan gida inda Jummai da Nana suke wanki don ta kirawosu.

Abban ya tsuguna a kan Yusran ya kamata ta mike tsaye yana nuna Rukayya yana fadin

 Wannan wane irin rashin hankali ne Rukayya, yayarki kikewa wannan dukan kamar kin sami wata jaka?

Ta sunkuyar da kai hawayenta yana diga yayinda Abban ya tallafi kafadar Yusran yana kokarin zaunar da ita a kan gado yana duba fuskarta inda bakinta ya fashe yake fitar da jini.

'Baki da hankali Rukayya? Kalli yanda kika ji mata ciwo. Fice kije dakina ki jirani kuma ki daina wannan kukan don sai jikinki ya gaya miki.

Ya zaunar da Yusran a gefen gado yana share mata hawaye yayinda Rukayya ta ja kafa ta fito daga dakin. Tana fitowa taci karo da Saddiku yana shirin shiga dakin wanda shigowarsa gidan kenan yana dauke da jakar computer dinsa. Ya sha gabanta ya dafa kafadarta da mamaki a fuskarsa yana tambaya

'Rukayya me ya sameki?

A nan Jummai ta shigo da gudu Nana da Sumayya suna biye da da ita, suka tsaya a inda suka ga Saddikun yana tambaya. Sumayya ce ta bashi amsa tace

'Fada sukeyi ita da Yaya Yusra shine Yaya Rukayyan ta zane Yaya Yusran.

A nan Rukayya ta fada jikin Saddikun ta fashe da kuka, ya dafa bayanta yana bata hakuri.

Jummai ta wuce shi ta shige dakin, ta tsuguna a gaban Abban tana fadin

'Subhanallahi. Muna can ni da Nana muna wankin uniform ashe fada suke yi haka. Yaya me kika gayawa kanwarki ya fusata ta haka? bari na samo ruwa a wanke bakin.

Abban yace

'Yauwa wanke mata, ina zuwa.

Yana fitowa yaci karo da Saddiku yana bawa Rukayya hakuri, ya dubesu yace

'Ba ce miki nayi kije dakina ki jirani ba, mara kunya fitsararriya?!

Ya maida dubansa ga Saddikun yace

'Ka kyaleni da ita ka shiga kaga yanda ta kama  yar uwarta da duka sai kace mara hankali.

Cikin damuwa Saddikun yace

'Abba Yusra ce fa bata da gaskiya.

Abban ya harareshi yace

'Gafara ka bani waje Malam, ka ga abinda ya faru ne zaka ce Yusra ce bata da gaskiya. Ka shiga ka ga yanda ta yiwa Yusran duka. Wuce kije ki jirani a saman.

Ta ja kafa ta wuce saman tana shesshekar kuka, shi kuma Saddiku ya wuce dakinsa.

A hankali Abban ya ja kafa ya karasa kan dining a table din kasan ya zauna ya dafe kai, wannan wacce irin musiba ce? Yaran da basu taba yin wani fada irin wannan ba? Me yasa Aisha tayi masa haka? Da tana gidan nan ai da hakan ba zata faru ba. Jummai ta fito daga dakin ta sameshi a zaune, ta rage tsawo tace

'An wanke fuskar Alhaji, ciwon ma ai baiyi tsananin ba. Yarinta ce take damunsu, gashi Yaya ta iya tsokana. A yi hakuri a yiwa Rukayyan a hankali.

Kai kawai ya daga mata ta tashi ta wuce kicin tana rike da hannun Sumayya. Jimawa kadan shima ya tashi ya haye saman zuciyarsa a jagule.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

43

Ba a jima da idar da sallar Magriba ba ta tsaya a bakin gate din gidan, ta matsa horn don ta san Abdallah yana nan. Kafin ta danna na biyun ya leko, yana ganinta ya koma da murna ya bude gate din. Ba tare da bata lokaci ba ta tura motar cikin farfajiyar gida, ta sami guri a cikin garejin gidan ta ajiye motar ta yanda duk wanda ya kalla ya san motar a nan zata kwana.

Tana fitowa daga motar ta mikawa Abdallah mukullin motar ta nuna masa akwati a bayan motar tace shi kadai zai dauko ya bar sauran kayan sai daga baya.

Kamar mara gaskiya ta shiga gidan da sallama, Hajiya, Anti Uwani da Farha suna zaune a falon. Da gudu Farha ta mike daga kusa da Anti Uwani ta rungume Mamanta tana mata sannu da zuwa. Kafin ta gama amsawa Abdallah ya shigo da akwatin ya nufi dakin Anti Uwani da shi. Itama Farha ta dubi Aishan tana murmushi tace

'Mama kwana zakiyi na kai miki jakar dakinmu ko?

Ta daga mata kai a take ta bi bayan Abdallah.

Ta karasa cikin falon ta zauna a kan kafet daga gefen Hajiya wadda take zaune kafafunta a mike. Ta gaida Hajiya sannan ta juya ta gaida Anti Uwani. Hajiya ta dubeta fuskarta da alamar tambaya tace

'Lafiya dai da magribar nan kuma naga ana kwana zaki yi kina daga kai?

Ta danyi murmushin yake ta kawar da kai saboda yanda kallon da su biyun suke binta da shi yake saka ta jin kamar wata mai laifi. Tace

'Kwana zan yi Hajiya, sai gobe zan tafi.

Cike da mamaki Anti Uwani tace

'Ikon Allah! To wa kika barowa gidan da yaran?

'Suna can Anti, ai akwai mutane a gidan.

Ta mike da hanzari tana fadin

'Bari naje nayi sallah, ko magriba ban yi ba ga shi nan har an fara kiran isha'i.

Ba tare da ta saurari abinda zasu fada ba ta bar wajen da sauri ta shige dakin da yaran suka shiga da kayanta.

Hajiya ta dubi Anti Uwani tace

'Kin ga yarinya don Allah, guduwa fa ta yi. Tabbas wannan zuwan nata akwai dalili.

Anti Uwani tace

'Barni da ita, bari ta idar da sallar na ji abinda ya kawota.

Har aka ci abinci akayi sallar isha'i tana daki, babu wanda ya nemeta. Sai dai Anti Uwani ta zuba abinci ta bawa Farha ta kai mata daki. Da yake tana tattare da yunwa ta dan taba tuwo, ta mayar ta rufe kwanukan ta wanke hannunta a bandakin da yake cikin dakin sannan ta dawo ta kashingide a gafen gadon Anti Uwani.

Bata dade da zama ba Anti Uwani ta turo kofa ta shigo dakin, bayan Aishan ta amsa sallamarta ta wuce ta zauna a gefen gadon yayinda Aishan ta gyara zama ta janye kafafunta. Bayan Anti Uwanin ta zauna ta dubi Aishan, suna hada ido ta sunkuyar da kanta yayinda Anti Uwani tayi murmushi. Tace

 Kya ji kunya mana Shatu! To ya aka yi? Don dai wannan zuwan na san ba na lafiya bane.

Sukayi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tana sauraronta ita kuma tana kallon hannunta tana tunanin ta inda zata fara. Jimawa kadan ta gaji da yanda Anti Uwanin ke kallo da sauraronta ta bude baki da kyar tace

'Cewa yayi idan na zauna a gidan zaman kaina nakeyi, shine na taho.

Mamakin Anti Uwani ya karu, ta gyara zama tace

'Ban fahimceki ba fa, Yusufan ne yace zaman kan ki kikeyi ko kuwa? Kiyi min bayani yanda zan gane.

Ta dan muskuta ta fara yiw????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a Anti bayanin abinda ya faru a kan umarnin da ya bata ta koma gidan yaransa har zuwa inda yace idan bata koma ba zaman kanta takeyi ba zamansa ba. Ta kara da

'Shine na taho.

Mamakin Anti Uwani ya sake karuwa, domin duk wannan bayanin da Aishan ta dauki lokaci tana yi kara kulle mata kai kawai tayi; ta kasa gane dalilin da ya sa ita Aishan ba zata koma wajen yaran nasa ba. Tace

 A a! To ai dole yace zaman kanki kikeyi Aisha, matar nan ta mutu fa me ya sa ba zaki bi umarninsa ki koma gidan ki kular masa da yaran ba? Wannan ai kowa ma ya san haka ce zata kasance.

Nan ta fayyacewa Anti Uwani dalilan da suka saka ba zata rike masa Yusra da Nana ba, ta bata misalan wasu daga cikin abubuwan da Yusran ta yi mata.

Suka yi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tace
'Kina da gaskiya Aisha, to amma fa gaskiya bana jin akwai wanda zai saurareki. Kowa cewa zai yi yarinya ce in an tsawatar mata zata daina; amma ni na fahimceki sosai. Rayuwa ce mutum zai yi ta yi rigima daga wannan sai wannan, kuma tsakaninki da miji kullum sai fitna.

'To ai shine. Kuma ni Allah bai dora min zama da yaransa ba, ya kai su dangi uwarsu ko kuma ya auro wata ta rike masa su amma ba ni ba. Kinga ni uwarsu musamman take koya musu tsanata don haka zai yi wahala a sami wanda zai saukesu daga kan koyarwar uwarsu, amma kinga idan wata ya aura watakila su bata dama ta zauna da su.

 Hakane Shatu. Amma fa gaskiya duk bayanin nan naki babu wanda zai fahimceki fa don ina jin ko Hajiya ba zata saurareki ba. Ina ga gara kiyi hakuri ki koma in ya so a zauna da Yusufan ya tsawatarwa yarinyar watakila ki ga abun ya zo da sauki.

Ta share kwalla sannan tace

'Wallahi Anti Uwani ba zai tsawatar mata ba, kuma ko ya tsawatar mata babu abinda zata fasa tunda yaran sun saba ba sa jin magabarsa. Ba zan iya rayuwa da wannan yarinyar ba wallahi don idan ta kasheni nawa marayun yaran ta cuta shi ubanta wata zai auro su cigaba da rayuwarsu. Idan kuma bata kasheni ba to in ta kureni nace zan dauki mataki a kanta wallahi kowa ba zai ji dadi ba tunda ai duk muguntarsu nima na iya Allah ne yake katangeni.

Sukayi shiru na dan lokaci. Abun ya sha kan Anti Uwani sai dai ta san babu wanda zai fahimcesu. Ita ta san irin wadannan yaran don ta zauna da su, don daya har bayan an yi mata aure ma haka ta dinga zuwa cikin gidan tana haddasa fitna a karshe sai da ubanta ya saki Anti Uwani a kan laifin da ba nata ba. Ta muskuta tace

'Hmm! To yanzu ya za ayi Aisha?

'Su Baffa suyi masa magana, idan ya dauke Yusra da Nana bani da matsala da sauran yaransa, ko dan shege ya bani kuma zan rike masa da amana. Amma idan dai aka ce sai na zauna da Yusra to gaskiya na hakura da aurensa.

'A'a abun ma ba zai kai haka ba in sha Allah. Amma dai ina kokonton yiwuwar abinda kike so domin su fa maza gani suke kamar tunda suka aureki to ko me suka rakito dole ki zauna da shi. Iyayenku ma kuma goya masa baya zasuyi. Kuma daga baya idan ta kashe miki auren a cigaba da zaginki.

'Duk ma abinda zasuyi sai dai suyi don wallahi Anti Uwani idan aka ce sai na zauna da yarinyar nan zaku nemeni ku rasa ba zaku sake gani na ba.

Ta bata rai tana harara Aishan tace

'Bana son rashin hankali, kada na sake jin wannan zancen kin ji na gaya miki. Ki ci gaba da addu'a in sha Allah za a sami maslaha.'

Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Anti Uwani ta tashi ta fice ta koma dakin Hajiya; inda ta tarar Farha har tayi bacci yayinda Hajiyan take zaune a kan dadduma inda ta idar da shafa'i da witri.

Nan ta zauna ta bawa Hajiya labarin abinda Aishan ta gaya mata. Cike ta mamaki da takaici Hajiya tace

'Kin ji ko Uwani, na gaya miki yarinyar nan fa bata da hankali har yanzu. Ya za ayi kina matsayin matar mutum kuma kice yaransa marayu sai kin zabi wadanda zaki rike masa?

'To Yaya ai tayi mutunci ma tunda ita nata marayun ko daya bai zaba ba balle ya taya ta rikonsu.

Ta harareta

'Kinga Uwani ki daina tunzura yarinyar nan fa. Ke da baki taba haihuwar nan ba ba kin zauna da  yayan kishiyoyin ba kala-kala, me ya kasheki? Duk sharrinsu ba haka suka hakura suka barki ba?

Ta kawar da kai

'Na hakura na barsu dai Yaya bayan sun sa ubansu ya kore ni. Kuma zama da su din ai rayuwa ce wadda na cikin gidan yari ya fi ka  yanci kuma ko makiyi na bana yiwa fatan irin wannan rayuwar Yaya.'

Suka yi shiru na dan lokaci. Hajiya bata so ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar ba don ta san tabbasa ta sha wahala a hannun yaran kishiyoyi domin ita din Allah bai taba bata haihuwa ba. Kuma haka Allah ya hada ta da mijin da ya dinga auren mata suna haifa masa yara yana sakinsu, kusan duka yaran ita ta rikesu. Duk wata fitnarsu haka zai muttsike ido yace itace bata san ciwon yara ba don bata haifa ba, haka tayi wannan rayuwar kuma daga karshe ya saketa a kan laifin da ba nata ba.
Sai daga baya kafin rasuwarsa ya dinga kokarin mayar da aurenta ita kuma a lokacin ko sauraronsa bata yi ba.

Anti Uwani tace

'Idan gari ya waye zan gayawa Abubakar ya sanar da Baffansu; ai tayi mutunci ma tunda ba duka yaran tace ba zata rike ba. Tunda na bude ido nake zuwa islamiyya har yau ban daina zuwa ba kuma ban taba ji a cikin karatu an

52 / 58