Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 58

18K to 21K   out of 172.2K words

ba; ita kuwa a wannan juma ar take so ayi ta ta kare. Ta danyi gyaran murya tare da bata rai

 Uhm! Ashe fa naku tsarin da ban ne. Naga dai abun karramawa ce da girmama uwargida tunda iyayenta ne da iyayenka zasu kawota, idan basu kawota sun nuna mata mu zauna lafiya ba ai dole tazo ta kalleni banza banza& '

Ya ajiye cokalin hannunsa ya hadiye abincin bakinsa da sauri ya tari numfashinta

 A a ai ba zata yi haka ba, nima ba zan barta ba ai kuma fa& '

Ta tabe baki itama ta katseshi a daidai lokacin da kwalla take fadowa daga idonta

 Um um ai ba sai kace komai ba wanne bari kuma? Tun yanzu ka fara raba kan gidanka! Ka ce ba zata shigo cikinmu ba ni da  yayanka, yanzu kuma kace ba za ma a kawota a nuna mata girmana ba, ai shikenan ku yi zamanki ku biyu nima na koma cikin  yan kallo.

Ta juya da hanzari ta nufi hawa sama, ya mike tsaye yana kallonta da mamaki da damuwa

 Haba Zarah& '

Kafin ya karasa ta haye sama tana share hawaye, ya koma ya zauna a kan kujerar kamar wanda aka tunkuda, ya bi hanyar da ta bi da kallo yana mamaki.

Tabbas Aisha ce ta nuna ta fi son gidanta ita kadai kuma da ya gayawa Zahra bata nuna damuwa ba, amma yanzu shi da kansa yace ba sai an kawota ba saboda gudun ayi wani abu da zai tada rigima. Ya ma riga ya gayawa Aishan da Yaya Zuwaira cewa idan an daukota a kaita gidanta kai tasye.
Ya dafe kai yana mamakin Zahra, wai shi da kansa ya tarwatsa gidansa kuma anki a girmamata. Ya ma za ayi tace haka bayan duk wannan kaffa-kaffan da yake yi dominta ne?
Ya ture kwanon abincin ya mike ya bi bayanta.

Kamar yanda ya zata a dakinta ya sameta, tana zaune a gefen gado tana tunani tare da fitar da hawaye; ta riga ta karbo layar da Malam ya bata ta sa a wajen da amarya zata tsallaka kuma a ranar Malam yace tayi don da gari ya waye amarya ta bar mata gidanta, idan ba a kawo mata amaryar ba ya za ayi ta samu wannan damar?
Da yake bata hade kofar dakin ba har ya shiga bata sani ba saboda nisan da tunaninta yayi, sai da yayi gyaran murya sannan ta dawo hayyacinta.

Ta yi sauri ta share hawayenta ta mike tsaye tana kokarin shigewa bandakinta, yayi sauri ya kara taku biyu ya riketa.

Ta juyo ta gefe tana kallonsa tana kokarin saita fuskarta.

 Mm! Bandaki zan shiga.

Bai bata amsa ba ya riketa ya zaunar da ita a gefen gadon ya zauna a kusa da ita sannan yace

 Kiyi hakuri ki fahimceni, da kai a nace kada a kawota saboda kin san halin mata ban sa da su wa za a taho ba daga can gidan nasu. Amma idan dai wannan ne ya bata miki rai to ki daina damuwa za a kawo miki ita nan, tunda dama su Goggo Habiba ne zasu daukota. Shikenan? .

Ta kawar da kai tare da gyara zama

 Ni bani da wata damuwa kuje kuyi yanda kuka tsara kawai.

Ya tsattsareta da ido, har sai da ta sunkuyar da kai sannan yace

 Ku cigaba da shirin tarbar amarya, za a kawo miki ita idan kuka gama sai su kaita nata gidan. Shine tsarina.

Ta amsa murya kasa-kasa

 Uhhm!

 In akwai wani abu da kike bukata sai kiyi min magana.

Tayi shiru na dan lokaci, har zai tashi tayi gyaran murya tace

 Dama akwai kudi da zan bawa amaryar kyauta kuma sababbi ake bayarwa, to na bada naira dubu goma a samo min sabbinsu har yanzu ba a kawo ba, ban sani ba ko zan samu a wajenka.

 To babu damuwa, idan kika shigo sai na baki akwai wasu da na canza.

 To na gode, Allah ya sanya alkhairi.

Ya mike ya fice ya ja mata kofa. Ta bi kofar da harara da murguda baki kamar yana wajen tace

 Asabar i yanzu ka dawo hayyacinka.

Ta mike ta shige bandaki don ta wanko fuska.
____
Tun da aka ce an tafi kafi Aisha ta sake shiga damuwa, kana kallonta zaka ga ta wani firgice. Hajiya tana kula da ita sosai don haka ta cewa Zahida kada ta bari su rabu, ta dinga bata hakuri tana tauson zuciyarta. Ko da su Yaya Zainab suka dawo daga kafin ma kin zama tayi a inda suke, da yake sun ganeta sai kawai kowa ya fita harkarta.

Duk a gidan suka kwana ana ta hira da kuma shirin biki. Gari yana wayewa Aisha ta kara firgicewa, hawayen da take makalewa ma yau kyaleshu tayi. Tana hawaye tana yake duk a lokaci guda saboda yanda zuciyarta ta jagule.

A falo suke zaune kusan duk dangi ne a kewaye da ita anata raha da kokarin kwantar mata da hankali.

Ta sha kwalliya cikin wani shudin leshi mai ado da fulawowi ruwan gwal ta yafa karamin mayafin nan da ake kira Chantilly a kanta. Hannuwanta da kafufunta sun dauki kunshi ga fatarta sai sheki takeyi. Kunshin yayi matukar kyau a kan fatar tata duk da ita din ba fara bace, fuskarta babu yabo babu fallasa domin ta ki bari ayi mata kwalliya; sai dai hakan bai hanata yin kyau ba.

Tana zaune a tsakiyar danginta amma kamar ace kyat! ta ruga da gudu.

Farha ce ta shigo da gudu itama ta sha kwalliya, da murnarta ta tsallake mutane ta fada jikin Aishan tana fadin

 Mama Baba Abba ya zo, da Anti Bushra da Anti Rakiya harda ma Sultan da Hajiya karama. Bari ma naje na shigo da su na manta.

Kafin a bata amsa ta mike ta sake fita da gudu cikin murna da farin ciki tana ta tsalle-tsalle.

Take jikin Aisha ya kara sanyi, ta dubi Zahida wadda take gefenta suka hada ido Zahidan tana kokarin kara mata kwarin gwiwa da idonta; nan da nan hawaye ya kwace mata ta mike da gudu tayi dakinta. Kafin ayi magana Zahida ta mike ta bi bayanta Anti Uwani tana fadin

 Ke ki dinga tashi a hankali saboda cikin jikinki.

Ko saurarenta bata yi ba ta rufa mata baya suka turo kofar. Ta kusa kaiwa bandaki Zahida tace

 Ya Aisha.

Ta juyo ta tsaya, yayinda Zahidan ta kara matsowa. Ta fada jikin Zahida suka rungume juna; duka su biyun kowacce tana fitar da hawaye, sai da suka dauki lokaci a haka sannan Zahida tayi kokari ta banbare Zainab daga jikinta saboda yanda take ji yaron dake cikinta ya fara takura yana zullo. Suka rike hannun juna suna kallon juna suna hawaye, Zahida ta jasu suka karasa suka zauna a bakin gado. Aisha ta matse hannun Zahida ta bude baki cikin raw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ar murya tace
 Hida zan iya kuwa? Hida Mustafa ya tafi da rabin zauciyata, ya za ayi na iya sallamawa wani mutumin ruhi na?

Ta kifa kai a cinyar Zahida ta cigaba da kuka Zahida tana shafa kanta tana share nata hawayen. Da kyar ta lalubo bakinta tace

 Ki yi hakuri Yaya Aisha, ki cigaba da yi masa addu a. You will be fine in sha Allah kuma wannan auren da zakuyi shine zai tabbatar da cewa kin karbi hukuncin Allah a kanki, ki cigaba da addu a.

Motsin bude kofa ya sa Zahidan ta waigo yayinda Aishan ta dago kanta fuskarta duk hawaye. Bushra ce ta turo kofar a hankali ta shigo da sallama ta mayar ta rufe kofar.

Aisha ta kalleta tayi mata murmushi da fuskarta me hawaye a hankali ta kirawo sunanta

 Anti Bushra.

Ta karasa ta tsuguna a gaban gwiwoyin Aisha ta dafata tana dariya

 Bari na tari hawayen amarya.

Sukayi dariya gaba daya, su Aisha suna share hawayensu.

Zahida tace

 Kiyi hakuri Anti Aisha kin ji, wannan shine hukuncin Allah. Allah ya sa miki albarka a rayuwarki. Hajiya tana gaisheki, kuma don karta sakaki kuka ne taki zuwa amma duk da haka sai da kikayi kukan.

Tayi murmushi ta share sabon hawayen da ya zubo mata.

Bushra ta kalli Zahida tace

 Anti Hida kin barta zata latse mana hancin yaro saboda kukan amarci.

Sukayi dariya gaba daya, Aishan ta mike tana dariya ta shige bandaki tana fadin

 Bari na wankon fuska.

Sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar da hawayenta ta fito ta gyara fuska, suka fito aka cigaba da bikin wanda dama amaryar da kanta tace bata son kida.

Ana saukowa daga sallar Juma a aka daura auren Yusuf da Aisha.

Kafin ayi sallar magriba matar Yaya Abubakar ta tattara yaranta ta hada da Abdallah da Farha da kuma yaran Zahida suka wuce gidanta; haka Hajiya ta sakata saboda yanda take ganin idan an zo daukar amarya zasu sata kuka.

Ana idar da sallar magriba Anti Uwani ta leka dakin Aisha tacewa Zahida su shirya  yan daukar amarya sun taho. Nan take hawaye ya sake ballewa a idon Aisha, haka Zahida da Zainab suka sakanta a gaba suka tayata shiryawa.
Atamfa ta saka dinkin riga da siket, rigar fitted ce shi kuma siket din dogo ne mai tattara a baya. Ta nade jikinta da farar laffaya wadda Sajida  yar kanwar Hajiya ta aiko mata ita daga Switzerland; inda take zaune da mijinta. Kana ganin laffayar nan ka san an kashe kudi, fara ce kal da zanen shudayen fulawowi a kasanta ga duwatsu sai kyalli take. Tunda aka ware laffayar kamshi ya cika dakin saboda yanda Zahida ta dauki lokaci tana yiwa laffayar nan turaren wuta.

Tayi matukar kyau musamman da yake an samu ta daina kukan, sai kwalla kawai wadda da zarar ta fito take gogewa da tissue din da yake hannunta.

Wajen karfe takwas na dare masu daukan amarya sukayi sallama a gidan, ba tare da wani bata lokaci ba aka basu amarya. Anti Uwani da kuma Inna wato kanwar mahaifinsu tare da su Zahida sune suka tafi rakiya.

Sai bayan sun kama hanya sannan Yaya Bello ya kirawo Yaya Saratu ya sanar da ita idan sun dauko amaryar su fara kaita gidan Zahra sannan su kaita dakinta. Shi kuma Yusuf Zahida ya kirawo ya sanar da ita domin da sun gama maganar gidanta za a kaita.

Ba tare da wata damuwa ba suka kama hanyar unguwar Sokoto road inda nan ne za a kai amarya.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


9
An riga an bawa ango hutun aiki na  yan kwanaki don haka ranar Juma a ma sai wajen sha daya ya tashi daga bacci. Bayan ya gama karin kumallo ya shirya abokinsa Alhaji Safiyanu yazo suka fice, sai da suka karbi kayan da ango zai sa daga wajen guga sannan suka wuce guest house din Alhaji Safiyanu inda daga nan zasu shirya su wuce daurin auren.

Yana fita itama Zahra ta hau shiri, nan da nan aka gyare gida aka sa turare ya dauki kamshi. Zuwa azahar aminiyarta wato Hajiya Amina ta karaso da abincin da baki zasu ci domin ita aka bawa kwangilar, bayan sun kule a daki suna zaune a gefen gadon Zahra Amina ta dubeta tace

 Baki da matsala kawata, sai wani sheki kikeyi kamar ba wadda za ayiwa kishiya ba.

Tayi dariya suka tafa

 To me yafi raina kawata, auren dare daya ai ba zai daga min hankali ba.

 Hakane.

Suka gama shirya yanda za ayi sannan suka sauko falon aka cigaba da hidima inda  yan uwan Zahra suka zo aka hadu.

Daga baya wajen la asar kuma Hajiya Karima matar Yaya Bello ta iso tare da Maimuna matar Musa kanin Yusuf din da yaransu.
& & ..

Ana cikin kiran sallar magriba Hajiya Amina ta mike ta yiwo alwala a dakin baki da yake kasa, ta tsaya a falon ta dubi Karima tace

 Yaya Karima kuyi alwala sai ayi Sallah a dakin don a samu a share falon a gyara tunda ance da anyi sallar magriba za a kawo amaryar.'

Nan da nan kuwa aka mike, aka fara alwala ana Sallah.

Jummaice ta share wajen tsaf ta gyara kafin a gama Sallah.

Kana shigowa falon kujerar zaman mutum uku ce ta bawa kofar baya, don haka idan mutum ya shigo akwai waje tsakanin kujerar zaman mutum uku da Kuma ta mutum daya inda ta nan ne mutum zai karasa tsakiyar falon ga zauna. Duk wanda ya shigo ta nan wajen yake wucewa don haka Zahra da Amina suka yanke shawarar a nan za a ajiye  yar layar da Malam ya ce a saka inda amarya zata tsallaka.

Da fari Amina ta so a saka a kasan dan carpet din da yake bakin kofa amma Zahra ta sanar da ita shi ana yawan dagashi saboda yawan wucewa, idan aka saka a nan akwai yiwuwar wani ya gani. Wannan babban center carpet din kuwa tunda kafar doguwar kujera a kansa suke ba a dagashi, gara su saka a nan tunda dole ta nan za a wuce da ita.

Ana gama shara Hajiya Amina ta faki ido ta daga carpet din ta ajiye layar ba tare da kowa ya kula ba, daga baya suka idar da sallah suka fito aka zauna aka cigaba da hirarraki. Daga baya makota suma suka shisshigo aka hadu ga yara sunata guje-guje don haka aka cika falon.

Tunda  yan kawo amarya suka daukota suka kamo hanya Yaya Saratu ta kirawo Zahra ta sanar da ita sun taho kamar yanda ta nema; a cewarta don su kintsa. Karfe takwas da kwata motocin amarya suka tsaya a kofar gidan Zahra.

Sai da kowa ya fita daga mota sannan aka bude motar amarya, Inna ce ta fara fita sannan amaryar ta fito yayinda Goggon Yusuf din ta fita ta daya gefen suka saka amarya a tsakiya Goggo na rike da hannunta. Duk matan da suka fito daga motocin su suka wuce gaba don haka amarya ce a karshe da su Goggo, sai Anti Karima matar Yaya Bello wadda itace a karshe ta dafe musu baya.

Suna shiga falon aka fara zabga guda, nan da nan wasu daga cikin matan dake falon suka mike.

An shigo da amarya sai kuma aka dan sami tsaiko mutane sun dan yi yawa ana ta magana su gafara a karasa a zaunar da amarya. Kafin su gama budawa Anti Karima ta tabo Goggo ta nuna musu daya gefen tace

 Goggo ku zaga ta nan mana, yara sun cushe nan din yanzu sai na fitar da su.

Don haka Goggo ta ja amarya suka kewaye kujerar mutum biyu suka shigo ta daya gefen tsakanin kujera da TV, nan amarya ta kwabe takalminta fuskarta lullube da mayafi aka karasa da ita aka zaunar da ita kusa da Zahra bayan an tashi matar da take zaune a wajen.

Nan take zuciyar Zahra ta cushe, suka kalli juna ita da Amina dake gefenta Amina tayi mata alama ta nutsu don haka ta hadiye takaicin da ya taso mata ta waske.
Nan su Goggo suka saka su a gaba da nasiha a kan su zauna lafiya, bayan sun gama akayi addu a. Duk yanda Amina taso ta canzawa layar nan waje bai yiwu ba domin yarane ma a daidai wajen a tsattsaye suna kallon amarya suna surutunsu.

Bayan an Shafa addu a Amina ta mikawa Zahra canjinta naira dubu goma ta dorawa amarya a cinyarta tana fadin

 Ga wannan amarya babu yawa.

Zahida ta sa hannu ta dauke suka yi godiya amarya ta mike, daidai lokacin Amina ta mike ta wuce musu gaba tana kokarin su bi ta daya gefen inda ta saka layar dai-dai lokacin Inna tabi ta daya gefen tana fadin

 Ga takalman mu nan, ku biyo ta nan.

Don haka suka bi ta inda suka shigo ana ta zabga guda, suka fice amarya ta bar falon yana kamshinta.

Makotan Zahra duka sukayi mata sallama suka wuce don suna son su ga gidan amarya, nan da nan zugar yara suka bisu harda  yan uwan Zahra ma don babu wanda yaga gidan sai yanzu kowa yake so yaje ya gani.

Aka barsu daga ita sai Amina da Yaya Murja sai Yusra wadda itama take taya uwarta kishi.

Suna ficewa Yusra ta shige dakinsu ta turo kofa, Yaya Murja ta dubi Zahra da Amina tace

 Kowa ya tafi ganin gidan amarya, to Allah ya baku zaman lafiya. Bari na dauko wayata a dakinki Zahra can na sa chaji.

Tana hayewa sama Zahra ta dubi Amina rai a bace harda kwalla a idonta

 Kin gani ko Aminoni, kin gani ko! Na gaya miki Karima bata kaunata tun tuni, tunda aka fara maganar auren nan ita da mijinta suke rawar kai da shisshigi. Ita ta hana ayi mata kishiya amma don iskanci duk wadda za ayiwa itace a gaba wai ita nan matar Babba a dangi. Wallahi sai na gyarawa matar man zama ko da wa take yawo.

Amina ta dafa cinyarta

 Ki bar wannan maganar, yanzu zan dauke miki layar tunda na san gobe da safe zai kawo miki ita in ya so sai kiyi amfani da wannan damar kinga daga ku sai ku.

Tayi kwafa ta share kwalla

 Aminoni ban so matar nan ta wuce gobe a gidan nan ba, amma bari Allah ya kai mu goben zan yi maganinta.

 Kada ki damu kawata ai sai mun& '

Motsin saukowar Yaya Murja ne ya dakatar da ita, take kuma ta sauya zancen

 Ai hakuri ne naki, kece babba idan baki bada wata kafa ba babu abinda zai faru.

Yaya Murja tace

 Gara dai ki gaya mata, ki rike girmanki babu matar da zata fiki a wajen miji. Kuma gashi ma ke danginsa duk suna sonki

7 / 58