Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   45 / 58

132K to 135K   out of 172.2K words

gara mu lekashi sai mu nemi masallaci muyi Sallah ko.

Suka mike gaba daya.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

38

A nan asibitin suka zauna, sai waya Yaya Bello yayi gida ya sanar da su Asma u taje ta bawa Hajiya abinci.

Tun shigowarsu abokin Sadik din ya bawa Abban mukullin motar Sadik din ya sanar da shi hotel din da sukayi party din inda a nan motar take. Don haka suna nan zaune ya kirawo wani yaronsa Shamsu yace ya zo ya sameshi a asibitin. Da yake lokacin da suke wayar Shamsun yana court road ba tare da bata lokaci ba ya hawo Babur ya karaso ya samesu. Mukullin motar Mommy din ya bashi ya sanar da shi inda motar take, yace yaje ya dauki motar ya ajiye masa ita a wajensa zai nemeshi. Sukayi sallama ya hau babur dinsa ya kama hanya.

Bayan an idar da sallar la asar su Abba suka koma inda Saddiku yake kwance. Zuwa lokacin daya yaron wanda ya rigasu farfadowa har an canza masa daki yana tare da iyayensa. Shi kuma daya yaron kanin saurayin da su Abban suka tarar mahaifiyarsu ta riga ta zo inda ta yiwa likitan bayanin tana so su sallameshi zuwa gobe don ita da yaran zasu bi jirgi zuwa Lagos daga can zasu wuce Dubai hutu; tana so likitan ya rubuta mata medical report idan sun je can likitocin zasu sake duba yaronta.

Bayan ta gama bayanin suka gaisa da Abba suka jajantawa juna, likitan yayiwa su Abban bayanin cewa su Saddikun ma yanzu sun farka don haka ana bukatar a samo madara su sha sannan za a canza musu daki inda za a cigaba da kula da lafiyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba Abba ya fita ya siyo madarar ya kawo, da taimakon ma aikaciyar jinya Yaya Bello ya daga Saddikun wanda har zuwa lokacin idonsa yake a rufe ya dura masa madarar aka samu ya sha kadan.

Zuwa karfe biyar da rabi sun dan kara farfadowa domin shi Saddiku har yana kiran Mommy yana wasu zantuka da ba a gane me yake fada. Nan aka turashi a gadon jinya aka mayar dashi wani dakin a sashen kula da kwakwalwa. Aka saka mishi drip kuma aka sake yi masa allurai.

Bayan likitan ya fita Abba ya zauna a kujerar dake ajiye a dakin yayinda Yaya Bello ya tsaya a daidai kan Saddikun yana tofa masa addu oi.

A hankali yayi shiru ya daina surutun, Yaya Bello ya dawo ya zauna a kujerar dake kusa da wadda Abban yake kai. Ya dubi Abban yace

 Ko Zahran za a sanarwa saboda a sami wanda zai zo ya kwana da shi mu samu muje gida zuwa safiya ko?

Cikin sanyin murya yace

 Eh ba zan ma kirawota ba don bana jin zan iya saurarenta yanzu. Namiji dai ya kamata a samu ko kuma ni din in an jima sai na dawo zuwa safiyar mu gani.

Yaya Bello yace

 Ba za ayi haka ba, gamu da samari a dangi. Ko wajen su Jamilun Inna ai za a sami mai kwana da shi ko kwana nawa za ayi. Kuma ma yanzu ina ga Muhammadu zan kirawo ya taho musu da kayan bukata ya zo su kwana da shi tunda ba abu ne da ake so ya baza dangi ba ayi ta faman cewa yana shaye-shaye.

Kafin Abban ya bashi amsa ya kirawo Karima ya sanar da ita halin da ake ciki, yace ta bawa Muhammadu kudin mota kuma ta zubo musu abincin dare ta bashi abun shimfida suna jiransa idan ya zo sai su tafi.

Muhammadu shine yaron Yaya Bello na farko wanda zai bawa Saddiku kamar shekaru hudu, don a halin yanzu shi yana ajin karshe a Jami a inda yake karantar aikin jarida.

Nan suka zauna har zuwa lokacin da Muhammadu ya iso sannan sukayi masa sallama suka tafi.
-----------

Tunda Abban Saddiku ya fita ya sanar da ita gasu a asibiti kuma shima bai san me ya sami Saddikun ba don baya cikin hayyacinsa take cikin matsananciyar damuwa. Gashi Abban ya ce kada ta sake ta zo asibitin sannan kuma ya ce ta daina damunsa da waya idan ana bukatar wani abu a wajenta zai nemeta. Haka ta kasa sukuni kuma ta rasa me zata cewa yaran da suke ta faman tamabayarta ko bata da lafiya; don haka kawai sai ta biye musu a kan bata da lafiya sannan kuma Yaya Sadik ma bashi da lafiya yana asibiti Abba ya kai shi.

Har la asar tana rike da waya tana jiran shigowar kiran Abba ko kuma ta ji shigowarsa gidan amma shiru. Hankalinta ya kara tashi don haka ta sake kiran Yaya Murja ta rushe da kuka. Cikin firgici Yaya Murja tace
 Subhanallahi! Zahra Saddikun mutuwa yayi ne kike kuka haka? Ki gaya min me ya faru.

Cikin shesshekar kuka tace

 Yaya nima ban sani ba Abbanshi yana can tare da shi kuma yaki yayi min bayani har yanzu shiru, cewa ma yayi kada na sake yi masa waya sai ya dawo.

 Ikon Allah! To kiyi hakuri mana, na san tabbas da mutuwa Saddiku yayi da yanzu kin ji labari ai lafiya ce take buya akasinta baya buya. Kiyi hakuri zuwa lokacin da zai dawo gidan sai mu ji.

Suka ajiye waya.

Jimawa kadan kuma Yaya Murja itama ta kasa nutsuwa saboda yanda Zahran take kuka, don haka nan da nan ta barwa abokiyar zamanta girkin da yake nata ta kama haryar gidan Zahra.

A dakin ta sami Zahran suka zauna tana ta bata baki; sai dai har zuwa lokacin Zahran bata gaya mata gaskiyar abinda ya samu Saddikun ba. Ta dai sanar da ita cewa lafiya kalau ya fita abokinsa ya kirawota yace bashi da lafiya har sun kai shi emergency. Don haka suka zauna suna jiran Abban ya dawo ko ya bugo waya.
Har Magriba ta kawo jiki bai dawo ba don haka Yaya Murja tayi mata sallama ta tafi nata gidan a kan duk abinda taji ta sanar da ita, sannan kuma idan dare ya kara yi Abban bai dawo ma ta sanar da ita sai ta gayawa Yaya Muhammad ya nemeshi.

Ta tafi ta barta zuciyarta fal damuwa.
---------

Suna fita daga asibitin suka sami masallaci sukayi Sallar Magriba sannan suka wuce ya sauke Yaya Bello a gidansa.

Ya ji dadi matuka da Allah ya sa ba a gidan Zahra zai kwana ba don yanda zuciyarsa take tafasa baya jin zai iya saurara mata; domin duk halin da Saddiku ya shiga laifinta ne.

Ba zai kirawo wannan abun da jarrabawa ba domin sakaci ne kuma ya san da laifinsa a ciki; to amma me yasa Zahra take katangeshi daga yiwa dansa tarbiyya? Shi din me ya rufe masa ido yaki ya jajirce? Tabbas Zahra itace ta san kulle-kullen da ta dade tana yi a kansa kuma baya jin zai iya yafe mata idan ta lalata masa yara.

Kai tsaye gidan Aisha ya wuce; ta gama abincin dare ta jera a table gidan yana ta kamshin turare.

Kallo daya tayi masa ta san cewa akwai damuwa a tare da shi. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubi dining table yace

 Kin gama abinci ko? Yunwa nake ji.

 Na gama, zaka sake kayan ko sai ka ci abincin?

 Hakane, bari ma na fara yin wanka.

Yana fitowa daga wankan ta zuba masa abincin wanda tuwo ta dafa da miyar agushi, ya ci ya koshi ba tare da yace mata komai ba. Bayan ya gama ya taso daga table ya dawo gaban TV, ta kwashe kwanukan sanna ta hado shayi ta ajiye masa. Ya dauki remote ya kunna TV a daidai lokacin da ta zauna a kusa da shi tana kallonsa.

Ya kalleta yayi gajeren murmushi yace

 Ya ake ta kallon fuskata kamar ana karanta littafi?

Ta mayar masa da murmushin tana wasa da gashin kansa tace

 Na ga kamar ka shigo da damuwa ne shine tunda ba a gaya min ba nake kokarin karantawa, tunda ka san an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

Yayi murmushi.

Nan ya bata labarin abinda ake ciki, sosai ta jajanta masa sannan tace

 Kuma ka ga maganar Yaya gaskiya ne, idan aka samu ya farfado gaba daya akwai rehabilitation centers inda idan ka biya zasu ajiye shi tsawon wani lokaci a dorashi a kan magunguna da therapy har a samu ya rabu da shan kwayar. Sai dai fa su yawanci gaskiya a can ake kwana kamar boarding school.

Ya kalleta cike da damuwa

 To ya za ayi, ai dole a kaishi tunda idan na barshi a gida uwarsa ba zata bari a yi masa abun da zai bata masa rai ba.

 Amma fa babu uwar da zata so ace danta yana shaye-shaye, ita din ma na san idan kayi mata bayani zata gane kuma zata so a rabashi da mugun abu. Ka dai yi mata bayanin tunda ko babu komai yana bukatar addu arta.

 Hmmm!

Ya mayar da hankalinsa ga kallon TV din yana shan shayinsa.

Bayan ya kurbe shayin ya ajiye kofin, ya dauki kafafunsa ya dora a kan cinyar Aishan tare da gyara zama. Ta muskuta ta fara matsa masa kafafunsa tana yi masa tausa domin ta san idan yayi mata haka abinda yake bukata kenan.
Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya tashi yayi sallar isha i wadda bai samu yayi a masallaci ba saboda gajiya. Bayan ya idar ya dauki mukullansa yayi mata sallama a kan zai je gidan Zahra ya dawo.

Yana fita itama ta tayar da Sallah.
---------

Tana kwance a dakinta ta jiyo shigowarsa gidan, nan da nan ta taso ta fito falon sama don ta tareshi.

Yaran duka sun yi bacci sai Rukayya da Yusra wadanda suke zaune a falon kasa suna jiran suji halin da Yayansu yake ciki kafin su kwanta. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya nufi saman.

Suka biyoshi a baya Rukayya tana fadin

 Abba kwantar da Yayan aka yi?

Yace

 Eh, sai zuwa gobe zasu sallameshi watakila.

Yusra tace

 Abba wai me ya sameshi?

Baya son ya amsa wanna tambayar don yana ganin bai dace ya ce musu dan uwansa shaye-shaye yayi ba. Ya kada kai yace

 Zuwa yayi gidansu abokinsa suka sha lemo wanda yayi expiring ba tare da sun sani ba shine suka sami food poisoning shi da abokansa biyu.

Yana cikin bayanin suka shiga falon saman don haka Mommy taji lokacin da yake maganar food poisoning, sai da tayi ajiyar zuciya saboda yanda ta dan sami nutsuwa; to da me yasa bai yi mata bayani ba ya barta cikin damuwa?

Suna karasa shiga cikin falon ya cewa su Rukayyan

 To tunda an ji inda Yaya yake sai aje a kwanta ko?

Suka yi masa sai da safe itama Mommy din suka yi mata sai da safe suka shige dakinsu na na saman domin kwanciya bacci.

Suna shigewa ta mike ta bi bayan Abban wanda ya nufi dakinsa tana yi masa sannu da zuwa. Bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, ta dai san bata ji yayi magana ba sai dai da yake bata ganin fuskarsa bata san yanayin da yake ciki ba.

A tare suka shiga dakin, ya wuce ya ajiye mukullan hannunsa a kan mudubi sannan ya janyo  yar kujerar da take gaban mudubi ya zauna yayinda ita kuma ta zauna a gefen gado suna fuskantar juna. Tace

 Ya jikin Saddikun? Naji kanacewa yara food poisoning ne, wanne irin abinci suka ci?

Kallonta kawai yake a fusace wanda ita kuma take mamakin dalilin da yasa yake kallonta kamar itace tayi poisoning Saddikun. Ta dan bata rai ta kawar da kai , yace

 Ai nima nan zuwa nayi na tambayeki abinda Saddiku yaci ya sami poisoning din?

Mamakinta ya karu yayinda ta kara shan kunu saboda yanda ta kula yana so ne kawai ya raina mata hankali. Tace

 Ya zaka tambayeni bayan kaine kaje wajensa?

Yayi kwafa yace

 Ko da yake ba ma wannan ya kamata na tambayeki ba, dazu da safe da na tambayeki Saddiku me kika ce min?

 Ce maka nayi ya fita, kuma ai a lokacin ya fita din ko ka ganshi ne a gidan bayan nan?

Ya jijjiga kai saboda yanda take bashi mamaki, ya rasa yaushe Zahra ta kware a karya haka. Yace

 Ban gashi ba, amma bari na sake tambayar watakila zaki fi ganewa. Jiya a ina Saddiku ya kwana?

Gabanta ya fadi yayinda tayi sauri ta waske; sai a lokacin ta gane inda ya dosa. To ana maganar yau ya za ayi ya dinga tamabayarta jiya. Tana jin motsin kwayar idonsa a kan fuskarta domin ya ki ya daina kallonta wanda hakan ya saka ta kasa sukuni. Bata da wata mafita domin ta tsani yanda yake warware duk wata karya da ta yi masa ba tare da bata lokaci ba. Ta saci kallon fuskarsa suka hada ido, ta sake shan kunu sannan tace

 Yace min zasu yi party na end of session, kuma na ga tun a secondary suke irin wannan party din shi yasa ban zata da wani abu ba. Shine yayi dare ni kuma bacci ya kwashe ni ban sanar da kai ba.

 Shine kika nuna min ya dawo kuma a gidan ya kwana? Ba ma wannan ba; kin zama kece uwarsa kece ubansa shi yasa kika bashi kudi kuma kika bashi izinin ya tafi party kika bashi mota yaje yayi abinda ya ga dama ba tare da ke da shi kun nemi izini na ba tunda dama kin nuna masa ni din bana son shi?

Bata da bakin magana don haka ta sunkuyar da kai tayi shiru, so take kawai ya gama wannan hayaniyar tasa ya gaya mata abinda ya samu Saddikun da kuma halin da yake ciki.
Ya fuskanci ba zata yi magana ba. Yayi murmushin takaici yace

 To ina yi miki murna Zahra, saura kadan ki hallaka Saddiku domin jiya da kika boyemin kika bashi kudi da mota ya tafi party zuwa sukayi suka sha miyagun kwayoyi wadanda jikinsu ba zai iya daukan wannan yawan ba. Wannan shine ya janyo su ukun suka sume aka samu aka kaisu asibiti. Tun jiya basu farfado ba har zuwa lokacin da na barosu a asibitin, sai dai mu cigaba da addu ar Allah ya tasheshi lafiya tunda likitocin sun tabbatar ya dade yana shaye-shayen kwayoyi.

A firgice take kallonsa da baki bude, kafin ta sami kalaman da zata gaya masa ya mike ya dauki mukullin da ya ajiye ya nufi kofar. Sai da ya kama hannun kofar ya juya ya dubeta yace

 Kuma ban baki izinin zuwa asibitin ba, idan kuma kin ki ji to zaki sha mamaki.

Ya murza hannun kofar zai bude tayi sauri tace

 To shi da waye a asibitin?

Tana nufin ya gaya mata domin ta samu tayi waya taji halin da yake ciki tunda ta kula shi din ba zai yi mata bayani ba.
Cikin halin ko in kula yace

 Shi da mutane ne. Sai da safe.

Ya fice kafin tace wani abu ya bar mata gidan.

Take hawaye suka wanke mata fuska.

Wannan wacce irin musiba ce ? Yanzu dama da gaske ne ake gaya mata Saddiku yana shaye-shaye amma yaron nan yana musa mata? Yanzu ya zata yi? Gashi Abban ta kula wulakanci kawai yake yi mata domin yaki yayi mata cikakken bayani. Gashi bata ji ya shigo da mota ba, to ina motar tata da Saddikun ya fita da ita?

 Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.

Ta fada a fili lokacin da tambayoyin suka fara yi mata yawa a ka. Anya kuwa wannan abubuwan da suke faruwa babu sa hannu a ciki? A ce Saddiku yana shaye-shaye sannan kuma gashi Abbansa ya juya mata baya yanata faman yi mata wulakanci?

Ta share hawayenta yayinda ta mike ta fice daga dakin, wayarta zata dauko ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita. A falo ta zauna a kan kujera ta dauki wayar tata, har ta budo lambar Yaya Murja sai kuma ta tuna cewa bata shirya sanar da Yaya Murja cewa Saddiku shaye-shaye yakeyi ba. Musamman da yake taba yiwa Yaya Murja korafin yanda mutane suke faman gaya mata cewa Saddiku yana shaye-shaye. Tun a lokacin Yaya Murja tace mata ta bincika sosai kuma ta sanar da Abbansa, har ma ta ce ta tura mata shi domin idan ta gan shi ko zata iya fuskantar wani abu a tattare dashi. Ko maganar bata yi masa ba balle ta bincikeshi don a lokacin gani take kawai kiyayya ce da hassada tasa ake mata haka. Sai daga baya ta samu ta tsara Yaya Murja.

To yanzu idan ta kirawota me zata ce mata? Nan ta ajiye wayar ta kifa kanta a kan kujerar ta sake fashewa da sabon kuka.

Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa; tunaninta daya hannu aka saka mata a al amuranta take ta shiga matsala kuma ko wanene sai ta rama.

Mutum biyu take zargi; Aisha wadda dama duk itace silar rikita mata gidan aurenta wanda a baya yake cike da kwanciyar hankali da kauna, sai kuma Yaya Bello wanda sosai take zarginsa a kan al amarin Saddiku tunda ta kula yana bakin cikin yanda yaransa basu da gata kamar yanda Abban yake kulawa da yaranta, tunda shi baya iya bawa nasa yaran gata kamar yanda Abban yake bawa nasa.

Tabbas sai ta rama; tunda daman yanzu account dinta ya fara nauyi. Sarkar Rukayya ta gwal kawai zata bayar aje a sayar shikenan da zarar Amina ta sami dama sai suje wajen malamin da ta samo musu tunda itama a halin yanzun tana da tata matsalar.
&

45 / 58