Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   47 / 58

138K to 141K   out of 172.2K words

take yi masa iya karfinta amma ko jinta bayayi, kuka yake mai ban tausayi harda shessheka.

Haka ta farka a firgice.

Irin wadannan mafarkan da takeyi su suke daga mata hankali; ta san dai kuka ba alkhairi bane to me yasa take ganin Saddiku yana kuka?

A hankali ta sauko daga kan gadon, har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna. Ta mika hannu ta dauko wayarta a kan durowar gefen gado ta lalubo lambar Abban Saddiku ta buga masa; bayan ya dauka ta sanar da shi tana so taje gidan Yaya Murja. Ba tare da bata lokaci ba ya bata dama tunda Malam Ali yana nan.

Hijab kawai ta saka saboda bata ma da kuzarin canza kaya, ba tare da bata lokaci ba Malam Ali ya dauketa suka fice.

Ba karamin dadi taji ba lokacin da ta shiga gidan Yaya Murja ta tarar babu kowa a falon kasa; wanda falon amaryar Yaya Murja din ne. Kai tsaye ta haye sama, inda ta tarar da Yaya Murja zaune da yaranta suna hirarrakinsu. Cike da farin ciki yaran suka yi mata oyoyo, ta karasa ta zauna a kusa da yayarta. Gaba daya yaran suka matso suna gaisheta yayinda Yaya Murja ta umarci Hibba; yarinyarta ta uku wadda Yusra ta girmeta da shekara daya; ta debo ruwa ta kawowa antinta.

Bayan yaran sun gama gaisheta sannan ta fara gaisawa da Yaya Murja, a nan ta fahimci kanwar tata tana cikin damuwa don haka ta jata suka shige daki.

Suna zama a gefen gadon ta kifa kanta a kan cinyar Yaya Murja ta fashe da kuka. Bata hanata ba sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, ta janyo tissue a kan durowar gefen gadon ta goge hawayen sannan Yaya Murja wadda take kallonta da mamaki tace

'Allah ya sa dai lafiya.

Ta karasa face majinar da ta taru a hancinta ta ajiye tissue din a kasa sannan tace

'Yaya na rasa yanda zan yi da Abban Sadik, wallahi ji nake kamar an canza min shi.

'To me kuma yayi?

'Hmn! Yaya kin san har yanzu bai gaya min inda ya kai Saddiku ba? Gaba daya ma ko kula ni baya yi a cikin gidan harkar gabansa yake yi. Idan a kan abinda ya faru da Saddikun ne ai na bashi hakuri amma sai ya dinga faman share ni kuma ba zai gaya min inda ya kai min yaro ba, kashe ni yake so yayi tunda idan na mutu bashi da asara ya auri wata matar?
Yaya Murja tayi murmushi ta kamo hannun Zahra ta rike a nata hannun tana kallon fuskarta a nutse, sai da suka dauki kusan minti daya a haka sannan tace

'Abinda nake so dake shine, kwata-kwata ki cire tunanin kishiyarki a ranki idan kikayi haka shine zaki iya fuskantar rayuwarki kiyi gyara a inda kike bukatar hakan. Kin ji ko?

Ta gyada kai alamar ta fahimta, sannan Yaya Murja ta cigaba

'Abban Sadik mijinki ne kuma a halin yanzu laifi kika yi masa, ki sake kwantar da kai ki bashi hakuri. Ki sake janyo shi a jiki kamar yanda kuke da. Kuma ina son ki kwantar da hankalinki, Saddiku dansa ba zai taba cutar da shi ba don haka ki barshi ya nemawa yaronsa lafiya. Kada ki sake yi masa maganar Saddiku. Ki nuna masa duk yanda yayi da yaransa dai-dai ne, ke dai so kawai kike ku koma kamar yanda kuke a da. Ki kuma nuna masa duk wani laifi da kika yi masa da wanda kika sani da wanda baki sani ba ba zaki sake ba; domin kin san wani lokacin maza saboda mulki ba zasu gaya mana laifin ba sai dai muga sauyi a halayyarsu. Kuma kullum dare ki dinga tashi musamman ranakun da ba kwananki ba kina yin sallar dare kina addu'a, wallahi a hankali zaki ga komai ya dawo dai-dai.

Ta gyada kai; ta sami natsuwa da wadannan kalaman duk da dai babu yanda za ayi ta cire kishiya daga lissafinta tunda ta san duk abubuwan da suke faruwa da ita sa hannu ne na kishiya. Amma dai tayi alkawarin zata gwada shawarwarin Yaya Murja.

'Shi Kuma Saddiku ki cigaba da yi masa addu'a amma don Allah ki bari a gina rayuwarsa. Kinga yaranki kamar mu suke, dukkansu mata sai shi kadai namiji. Idan ya bi hanyar lalacewa zasu taso basu da wani uba bayan ranmu. Kina kallo mu iyayenmu duka sun rasu yanzu Yaya Muhammad muke takama da shi; to da ya zama dan shaye-shaye ai da kinga bamu da sauran gata a duniya.

Cikin sanyin murya tace

'Hakane.'

'Yauwa.'

Saida suka dauki lokaci Yaya Murja tana kwantar mata da hankali sannan da magriba ta fara kawo jiki tayi mata sallama ta kama hanya.

Duk yanda lokaci ya kure sai da ta tsaya a gidan Amina domin tana so ta samu tabbacin maganarsu tana nan ta zuwa wajen malamai.

Bayan a sun gaisa da Aminan ta rakata daki ta duba Ummansu wadda take kwance sannan suka dawo falon Aminan suka zauna.

A nan suka cigaba da kulla yanda da zarar Umma ta dan ji sauki zasu kai ziyara wajen malamansu don samarwa kansu mafita a aurarrakinsu wanda a halin yanzu suke cikin wani hali.

Sai bayan sun yi sallar Magriba sannan Zahra ta fito suka kama hanyar gida da Malam Ali.

 ----

A  yan kwanakin nan jikin Hajiya kara rikicewa kawai yakeyi, duka da cewa Yaya Bello a tsaye yake a kanta. Kusan shekaru biyar kenan tana fama da hawan jini wanda daga baya ya hade mata da diabetes. Shi yasa ma kullum Yaya Bello yake zuwa yana bata abincin da kansa don ya tabbatar ta ci abinda ya dace. Sai dai duk da haka  yan kwanakin nan da an samu jininta ya sauka sai kuma diabetes din ya tashi, idan kuma ya yi sauki sai jinin ya sake hawa. Haka dai suke lallabawa.

Ranar Juma'a ce don haka da wuri Abban Sadik ya tashi daga aiki. Ya je ya gaida Hajiya da safe amma duk da haka yaji yana so ya sake komawa, don haka ba tare da bata lokaci ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Hajiyan.

A kwance ya sameta a dakinta tana hutawa, ya shimfida dadduma a gaban gadon ya zauna. Ta rage yawan hira sosai don haka a mafi yawancin lokuta sai dai kawai su sakata a gaba su zauna. Bai dade da zama ba akayi kiran sallar Magriba, don haka ya tasheta ya rakata har kofar bandaki ta shiga ta yiwo alwala. Sai da ta zauna a kan daddumar ta inda zata yi Sallah sannan ya fito ya barta da Anisa ya nufi masallaci.

A masallacin suka hadu da Yaya Bello wanda shi kuma ya zo ne don ya duba Hajiyan ya bata abincin dare.

Tuwon alkama da miyar zogale Yaya Bello ya kawo mata; wanda shine abincin da ta fi so tun da aka hanata cin shinkafa. Anisa ce ta dauko musu plate ta kai musu daki don yau Hajiyan gaba daya ta ki fitowa falo. Haka suka saka ta a gaba ta dan ci tuwon kadan tace ta koshi, sai shayin goruba da aka hada mata ta shanye kofi guda.
Ta koma kan gadon ta kashingida ta barsu zaune suna  yan hirarrakinsu a tsakaninsu.

Sai da akayi sallar isha'i sannan suka yi mata sallama suka tafi suka barta da Anisa da mai aikinta kamar yanda suka saba.

& & &

Tun ranar da Zahra taje gidan Yaya Murja ta dawo ta aikata duk abinda yayan ta bata shawara; tunda ta fuskanci a halin yanzu bata da wata mafita da ta wuce hakan. Don haka babu laifi Abban Sadik din yana dan sauraronta duk da dai har yanzu bai ce mata komai a kan Saddiku ba.

Kwananta ne yau don haka yana dawowa daga gidan Hajiya ya tsaya a gidan Aisha yayi mata sallama sannan ya wuce gidan Zahra.

Kamar yanda suka saba karfe goma sun gama komai ya rufe gida, shi da ita ma sun yi shirin bacci.

Tana kwance idonta a rufe domin bacci ya fara daukanta yayinda shi kuma yake zaune a gefenta da computer dinsa a kan cinyarsa yana aiki. Karar wayarsa ce ta farkar da ita, ta gyara kwanciya yayinda ya kai hannu kan durowar gefen gadon ya dauki wayar. Lokaci ya fara dubawa ya ga karfe sha biyun dare har da minti goma; sai da gabansa ya fadi domin ya san ba lafiya ba tunda yaga Yaya Bello ya kirawoshi a wannan lokacin.

Yana kara wayar a kunnensa kafin yayi wata magana Yaya Bello wanda kana jin muryarsa zaka san kuka yake yace

'Yusufa Hajiya lokaci yayi, sai dai muyi hakuri.

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!

Katse wayar kawai yayi ya ajiye computer dinsa ya mike a dai dai lokacin da itama Zahran ta tashi zaune tana tambayar abinda ya faru. Ya dubeta yana fitar da kwalla yace

'Hajiya ta rasu, yanzu zanje na gani.

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Allah Sarki.'

Sukayi shiru na dan lokaci yayinda ya cigaba da kokarin saka kayansa. Ya dauki mukullin motarsa ya nufi kofa, ta mike tana fadin

'Allah yayi mata Rahama, Allah ya hada fuskokinmu a aljannah.'

'Amin.'

 Zamu taho da safe ni da yaran.

'Ku bari sai mun yi waya tukunna, zan turo Ali ya kai ku.

Yayi mata sallama ya fice.

& & ..

Kafin gari ya waye labarin rasuwar Hajiya ya zagaya gari. Karfe tara na safe aka gama hadata aka kaita makwanci. Sai da aka dawo daga makabarta sannan Abba ya sanar da iyalansa su taho, don haka gaba dayansu suka taho. Itama Aisha saida ta biya ta dauko Amira sannan suka wuce saboda ko ba komai ta samu wadda zata debe mata kewa a gidan.

Kafin yamma gida ya cika da dangi da abokan arziki, domin Hajiya Balaraba mace ce mai mutane sosai. Allah bai bata haihuwa da yawa ba domin yara hudu kawai ta haifa, kuma da yake ita kadai ce matar mahaifinsu sai suka zama basu da  yan uwa. Duk da haka tana da dangi da yawa, domin mahaifinta yayi aure-aure kuma ya tara yara su goma sha takwas. Lokacin da tana da jajayen sawunta yanuwanta da suke mafi yawansu mazauna Sumaila ne suna zumunci da ita sosai, sai dai daga baya bayan rasuwar mahaifinsu Yusuf din da dukiyar ta kare a hankali kowa ya janye jikinsa. Yanzu kuma da aka sami labarin rasuwarta kowa ya zo ana ta kuka ana tuna alkhairinta lokacin da tana da hali.

Duk yaranta suma sun hallara da  yayansu, Ummulkhairi ce kawai bata iso ba wadda a Lagos take zaune inda aure ya kaita. An riga an sanar da mijinta rasuwar wanda yayi alkawarin shi da ita zasu biyu jirgi kafin magriba zasu iso.

& & ..

Tun Hajiya tana da lafiyarta ta bar wasiyyaa cewa idan ta rasu kada ayi mata zaman makoki, amma saboda  yan uwanta wadanda suka taho daga Sumaila da kuma Ummulkhairi da yaranta su biyar wadanda sai sunyi sati biyu sannan zasu koma Lagos haka aka hakura aka yi zaman na kwana uku. Duk wanda ya tambayi Saddiku haka Yaya Bello yake cewa yana makaranta suna jarrabawa shi yasa ba a gaya masa rasuwa ba.

Ranar da aka kwana uku da safe Yaya Bello da kansa ya shiga har cikin gidan ya sanar da mata cewa bayan azahar zai sa a kawo mota za a mayar da su Sumaila. Duk yanda Yaya Saratu ta so ya bari a kai bakwai bai ma saurareta ba. Itama Ummulkhairi da taji wannan sanarwar take ta sanar da shi tana so ita da yaranta su wuce gidan Yusuf su karasa kwanakin nasu a can. Don haka ta karfin tsiya Yaya Bello ya sallami kowa aka share makoki.
Azahar nayi shima Yaya Bello ya tattara iyalansa a gaba suka koma gida tare da Najma  yar wajen Ummulkhairi. Iyalan Abba suka shiga mota Malam Ali ya ja suka tafi, shi kuma Abban ya dauko Ummulkhairi da yaranta wadanda zasu karasa hutunsu a gidansa. Yaya Saratu kawai suka bari a kan ita sai da yamma zata tafi sai a bar mai aikin Hajiya da kuma Innani kanwar Hajiya tare da Anisa wadanda sai daga baya zasu tafi.

& & & .

Lokacin da su Zahra suka bar gidan makokin Ummulkhairi ta sanar da ita suna nan zuwa ita da yara, don haka suna shiga gidan ta sa aka fara gyara musu dakin baki na falon kasa. Sai dai suna shiga unguwar Abba ya ajiyesu a gidan Aisha yace su sauka a nan tunda kusa ne sa dinga shiga wajen Zahra da yaran.

Nan da nan Aisha ta shiga hidima da su.

Yana shiga gidan Zahra tana zaune a falon kasa yayinda Jummai take goge dakin. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ta ce

'Ina Anti Ummun? Tace min tare zaku taho.

'Eh tare muka taho suna gidan Aisha na san nan din ma da anjima zaki gansu.

Bai saurari abinda zata ce ba ya haye saman; ba zai iya sauraron komai ba saboda yanda ya gaji kuma ga damuwa.

Ta kawar dakai tana mamaki; yanzu kenan ba zai ma bari ta sauki bakinsa ba! Ta tashi itama ta haye saman.

Haka aka gama jimamin rabuwa da Hajiya kowa ya koma harkokinsa, mutanen Lagos ma suka gama hutunsu suka koma gida.

 -----

Dole ta saka Zahra tana yin amfani da shawarwarin Yaya Murja tunda ko babu komai ta san sai ta kwantar da kai a wajen Abba sannan zata sami kudin zuwa wajen Malami. Tunda dama da business dinta take samun kudi kuma a halin yanzu babu zancen wani business domin duk ta cinye kudin.

Yanda take ganin walwalar Abban ta san cewa Saddiku yana lafiya tunda ya gaya mata yana zuwa duboshi kuma yana yi masa waya. Shima Abban ya sami natsuwa ne saboda yanda yake ganin cigaba a wajen Saddiku; rehabilitation center din sun bashi rahota a yanzu da Saddiku ya kai wata biyu a hannunsu an samu an raba shi da miyagun kwayoyin; yanzu aikin gyaran dabi'unsa ake yi da kuma karatun islamiyya da ake biya musu. Wannan ya sa Abban ya kara sakewa da Zahran duk da bai sanar da ita inda Saddikun yake ba.

& &

Mahaifiyar Amina ta fara samun lafiya sannan kuma a halin yanzu akwai kanwar Aminan wadda take karatu a Sudan ta zo hutu, don haka tana gidan Aminan kuma tana kula da Umman nasu. Don haka suke cigaba da shirye-shiryen zuwa wajen boka; domin Amina ta samo musu sabon boka.

Yau ranar asabar ce kuma da yake ana cikin hutun makaranta kullum yara suna gida, don haka ta gaji da hayaniyarsu tana so ta dan fita. Gidan Amina take son zuwa don ta san a nan ne zata samu a saurareta kuma a bata irin shawarwarin da take so. Ba a gidanta Abban Sadik ya kwana ba don haka sai wajen karfe goma na safe ya shigo gidan. Bayan ya gama abinda zai yi da zai fita ta tambayeshi izinin fita wanda ba tare da wani bata lokaci ba ya bata dama.

Nan da nan ta shirya, ta sallami yaran sannan ta barwa Jummai abincin rana da abincin dare don batayi niyyar dawowa da wuri ba. Ta fito Malam Ali ya ajiyeta, ta sallameshi domin Aminan zata mayar da ita gida idan sun gama.

Sai da ta fara gaisawa da Umman su Aminan ta yi mata ya jiki sannan suka zauna a falo suna gaisawa da Aminan. Basu jima a falon ba suka koma dakin Aminan. Nan suka baje a kan kafet din da yake tsakar daki, Raihana kanwar Aminan ta zo ta kawowa Zahra ruwa da lemon roba suka gaisa sannan ta fice ta ja musu kofa.

Bayan sun dan taba hirarsu ta duniya Zahra tace

'Aminoni ina cikin damuwa wallahi ba zaki gane ba, yanda kika ganni nan daurewa kawai nakeyi amma komai ya tsaya min.

Ta yi dan gajeren murmushi mai ciwo, tace

'Baki kai ni damuwa ba Uwar Saddiku! Idan banda Daddy ya raina ni ya za ayi ace ina zaune nan a Kano yana Abuja yana bin matan banza; harda wadda aka ce shi ya ajiyeta kamar matarsa yake mata komai. Kuma duk abun nan ya hana ni zuwa Abujan kuma sai yayi wata biyu bai zo ba, da ya zo kuma dama kwana biyu ne zai ce yana da aiki don haka nan da nan zai koma. Ni zai yiwa tozarci!

Ta dan zaro ido

'Ikon Allah! Kai Jama'ah wallahi maza basu da mutunci.
'Ki bari kawai kawata. Akwai wani malami da aka hadani da shi kuma shima an ce aikinsa yana yi sosai, gashi bashi da nisa don an ce nan cikin unguwa uku yake. Kawai dai aikinsa da tsada.

'To ai haka zamu je don kin ga ni ma na kusa hada 300k, ina ga ko bata isa an gama aikin ba zata isa a fara. In ya so idan ana bukatar ciko sai na bada dakunnen Rukayya a sayar.

'Nima kusan na hada kudin, kin san akwai aikin da za a yiwa Ummanmu a asibitin koyarwa na A B U. To Raihana ce zata zauna da ita, so nake sai sun tafi asibitin kafin a sallameta sai muje mu gama duk abinda zamu yi. Saura sati shida, kada ki damu kawata kafin azumin bana komai ya dawo dai-dai.

'Ina ga ma mu dan kara don ni so nake sai ya dawo min da Saddiku tukunna, ina jin shi kuma saura sati biyu ya dawo. In ya dawo na ganshi sai na fi samu nutsuwa, kai da danka saboda zalunci a hanaka ganinsa!

Suka cigaba da tattauna yanda zasu fitowa matsalolinsu.

Sai da akayi sallar la'asar sannan Zahra ta shirya Aminan ta mayar da ita gida.

__

Kwanci tashi Saddiku yayi wata shida a rehabilitation center, kuma yau Alhamis yau ce ranar da za a daukoshi a dawo da shi gida. Cikin walwala Abba ya shirya tunda ya riga ya dauki hutu ba zai je office ba a ranar, bai gayawa kowa cewa yau zai dawo da Saddiku ba ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.

Sai da suka kama hanya sannan Yaya Bello ya sanar da shi cewa idan sun dauko Saddikun

47 / 58