Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   13 / 58

36K to 39K   out of 172.2K words

.

Wajen karfe tara saura ta ji shigowarsa, nan da nan ta kintsa.

Yaran su kadai ya samu a falon kasa don haka bayan sun yi masa sannu da zuwa ya basu ledojin da suke hannunsa wadanda kazar Yahuza suya ce a ciki.
Nana ce ta dauke ledojin yayinda Abban yace

 A kaiwa Mommy ta dauki nata tukunna, kafin kurar gidan taga menene a ledar.

Cikin shagwaba Rukayya wadda ta tabbatar da ita yake tace

 Abbaaa!

 Na am, ni ai ban kama suna ba ko?
Sukayi dariya gaba daya suka nufi saman, shima Abban ya bisu a baya.

Tana zaune a falonsa a kan kafet ta mike kafafun ta dorasu a kan filo saboda yanda suke dan kumbura. Daga gefen damanta jug ne cike da zobo yana gumi saboda sanyi yayinda take rike da karamin kofi mai dauke da zobon da alamu sha takeyi.

Suna shiga suka zube a gabanta suna yi mata bayanin naman da Abba ya siyo yayinda Abban ya wuce ya zauna a kan kujerar bayanta. Ta bude ledojin ta dauki nata, ta mikawa Yusra sauran tana fadin

 Gashi nan kowa ya dau daya sai a sakawa Ummi nata a fridge tunda tayi bacci.

Nan da nan suka kwasa sukayi kasa.

Ta sake yiwa Abban sannu da zuwa, bayan ya amsa ya dubi kofin hannunta yace

 Yau kuma zobo kike sha ke kadai abunki?

Tayi  yar dariya tace

 Zobo kam ai na mu duka ne, suma yaran duk sun sha da rana. Bari na dauko kofi na difara maka don ma kada na cika maka ciki ka kasa cin abincin amarya.

Ta kurbe ragowar wanda yake kofin hannunta tana kokarin mikewa, ya dafe kafadarta yana fadin

 Ba sai kin dauko wani ba, zuba min a wannan tunda kin shanye. Kadan zan sha na wuce sai ki cigaba da jin dadin ki.

Ta zuba masa zobon a kofin da ta shanye, ya dauka yana zuka a hankali suna hira.

Sai da shanye kofi guda ya kara rabi sannan yayi mata sallama ya fice.

Tabi bayansa da kallo tana murmushin mugunta; ta san duk daren da ya siyo kaji irin wanna to hirar dare yake so ayi, yanda ya sha zobon nan kuwa ta san wannan hirar ta yau babu abinda zai iya.
-------

Tun da yamma ya sanar da ita kada tayi abincin dare don zai siyo abinci. Shayi kawai ta dafa mai kayan kamshi suka baje a falo suka gama ciye-ciyensu suna hirarrakinsu.

Sai da suka gama komai suka kwanta a nan labarin ya canza, duk yanda ya kai ga sha awarta da son ya kusanceta abun bai yiwu ba. Yayi iya kokarinsa itama tana taimaka masa amma abu yaki, daga karshe itace ta koma tana bashi baki saboda yanda ya shiga tsananin damuwa. A tunaninsa bashi da lafiya, amma kuma babu wani rashin jin dadi da yake ji, haka ya kwana cikin damuwa da tashin hankali.

Da asuba bayan ya dawo masallaci ya sake kokarin gwadawa amma shiru, nan ma haka ta dinga nuna masa ita bata damu ba yayi kokari kawai ya je asibiti a duba shi.

Da gari ya waye ya shirya ya fice office da niyyar idan ya rage aiki zai nemi likitanshi ya ji yanda za ayi. Yanayin aiki da kuma kasancewar babu wani abu da yake masa ciwo sai ya manta, sai da yamma bayan ya tashi daga aiki sannan ya tuna. Yana tunanin yanda za ayi da yammannan ya sami likita sai kuma ya tuna kwanan Zahra ne yau ita kuma dama ba cikakkiyar lafiyace da ita ba, don haka ko bai kulata ba ma babu damuwa.

Haka ya koma gidan.

Kamar kullum bayan ya gama hidimarsa ya kwanta, tana lalubensa yana gocewa saboda baya son abinda ya faru jiya da Aisha ya sake faruwa. Amma kuma a hankali sai yaji kamar zai iya, nan da nan kuwa suka shiga hidima yana jin dadi. Don haka sai yayi tunanin matsalar ta jiya ce kawai abun ya wuce.

Haka yayi kwana biyun nan a wajen Zahra lafiya kalau don haka cikin walwala ya koma wajen Aisha.

Ga mamakinsa duk yanda ya kai ga dagewa tsakaninshi da Aisha sai kallo, haka yayi kwana biyun nan yana mamaki. Ita kuma sai dai ta dinga kwantar masa da hankali tana nuna masa ba komai bane, musamman da yake ya gaya mata zai je yaga likita.

A hankali ya zama kullum idan dai ya shigo yiwa Zahra sallama zai tafi wajen Aisha zai tarar ta ajiye zobo, shayi ko kuma kunun zaki, shi kuma da ta yi masa tayi sai ya sha sannan zai tafi.
& & & ..

Haka rayuwarsu ta cigaba, yaki yaje asibiti musamman da yake yana samun biyan bukata a wajen Zahra. Sai dai yana mamakin yanda akayi ranar da yake wajen Zahra lafiya amma da yazo wajen Aisha sai ya kasa komai.

A cikin tattaunawarsu da Aisha ya sanar da ita idan yaje wajen Zahra baya samun wannan matsalar. A tunaninta asiri ne Zahran tayi amma ta kasa gaya masa, sai dai ta dage da neman maganin karya sihiri.
Musamman ta sami ruwan zamzam take yi addu ar karya sihiri tana sha tana wanka, shi kuma duk wani ruwa da zai sha a gidan nan sai ta yi masa addua ar a ciki amma babu wani cigaba. Yanzu ma an kai matsayin da ta daina bari ya jagwalgwala ta, shima kuma ya daina rawar kai a kanta. Sai dai kullum cikin bata hakuri yake yana yi mata alkawarin zai je asibiti a duba shi amma dai ya kasa zuwa, ita kuma bata bashi kwarin gwiwar yaje asibitin ba saboda ta riga ta yarda sihiri ne, don haka dai ta dage da addu a.
__

Ranar Alhamis Zahra ta tashi da ciwon nakuda sai dai da yake ciwon bai zo mata gaba daya ba ta cigaba da aiyukanta tana yi tana hutawa. Ba kwananta bane amma dai ta riga ta sanar da shi tana nakuda don haka ranar gaba daya a cikin sauraron kiranta yake.

Tun wajen karfe biyar na yamma ya dawo daga aiki, wajen Zahran ya fara shiga bayan ya dubota sai ya koma wajen Aishan tunda yana nan da ta ji wani ciwo sai tayi masa waya.

Sai bayan sallar magriba sannan ta kirawosa, a gurguje ya shirya yayi sallama da Aisha bayan ya sanar da ita idan akwai abinda yaran suke bukata zai ce su karba a wajenta.

Tun wajen karfe bakwai suka shiga asibitin aka shigar da ita labour room, sai wajen karfe taran dare sannan ta haihu.

Dakin da ta haihu ita kadai ce a ciki sai ma aikatan lafiya da likita, likitan yana tsaye a daidai kanta yayinda matron da kuma nurses uku suke daidai kafafunta suna dubawa suna taimaka mata. Tara da minti biyar tayi yunkuri ta haifi yarinyarta santaleliya, a take matron ta yanke cibiya ta dauki yarinyar ta mikowa likita. Ya karba ya dubi Zahra da take kwance yace

 Sannu Hajiya.

Ta amsa tana murmushi.

Ya juyo al aurar yarinyar ya nuna mata yace

 Kinga abinda kika haifa, me kika samu?

Sosai mamaki ya bayyana a fuskarta tace

 Mace?

Likita yace

 Yauwa, gata nan kuma lafiyayyiya Alhamdulillah.

Nan da nan ma aikatan lafiya suka shiga kokarin wanke mai jego da abinda ta haifa, daga baya aka fito aka sanarwa Abban.

Bayan likitan ya fito yayi masa duk wani bayani kuma ya sanar da shi zasu riketa ta kwana in ya so zuwa gobe da yamma za a sallameta.

A hanyarsa ta komawa gidan ya dauko kanwarta wadda zata tayata kwana a asibitin suka wuce gidan. Nan da nan ta zabo mata kaya ta hado mata dan abinda zata ci. Babu yanda bai yi da su Yusra su tafi gidan Aisha su kwana ba suka ki, kananunma sun riga sun fara bacci don haka tace zasu iya kwana. Haka ya hakura ya sa Sadik ya rufe musu gidan suka koma asibiti.

Ko da suka koma asibitin saida ya siyo musu duk abubuwan bukata ya kawo kudi ya bata sannan ya kamo hanyar gidan.

Wajen Aisha ya fara shiga inda dama a nan ya kamata ya kwana, yana shiga yayi mata sallama ya sanar da ita zai kawo mata Rukayya sai ya kwana da sauran yara.

Tace

 Dare yayi wallahi, don Allah ka barta tayi baccinta sai da safe kawai. Idan kuna bukata wani abu kawai ka sanar da ni.

Sukayi sallama ya fita ta rufe kofa.
& & ..

Tunda aka canza mata daki aka gyara Baby aka kwantar da ita a kusa da ita take mamaki, tayi scanning an gaya mata namiji zata haifa yanzu kuma ta haifi mace.

Ta dubi Rahma; wadda kanwace a wajenta wato  yar kanwar babarsu, mijinta ne ya rasu tun yaronta yana karamin kuma bata sake aure ba shi yasa duk irin wadannan abubuwan ita ake kira.

Tace

 Rahama kin san kuwa nayi scanning an ce min namiji zan haifa, amma kinga ikon Allah mace na haifa.

Tayi  yar dariya tace

 Um, ai wallahi Anti abun fa na Allah ne dama likitocin ma lalube suke a duhu abinda Allah ya boye ai mutum ba zai iya gani ba.

 Hhhh! Kin san da ace ba ni kadai ce a dakin haihuwar nan ba Allah cewa zanyi canza min suka yi.

Ta kyalkyale da dariya

 Lallai Anti, kuma kinga gata nan kamar  yayanki don wannan sak yanda kika san Sadiku yana jariri.

 Hmmm!

Ta yarda mace ta haifa kuma tana kaunar yarinyar amma dai tabbas ta saka ran haihuwar namiji, don haka ne ma ya saka komai kayan yara maza ta siya.
Haka dai ta yi ta wasi-wasi har bacci ya kwasheta.
& & ..

Da wuri Aisha ta tashi tunda ta san Zahra bata nan, ta soya doya da kwai yanda zai ishesu gaba daya sannan ta dafa ruwan zafi ta zuba a babban flask, ta dafa shinkafa da miya. Bayan ta gama wajen karfe bakwai saura ta kirawoshi a waya tace ya turo yara su dauki abinci.

Ta san watakila zasu dau lokaci kafin su karaso kuma ta san idan da shi suka taho yana da mukulli don haka tayi sauri ta shiga wanka tunda itama zata je aiki.

Ta fito daga wankan daure da karamin tawul dinta ta ji shigowarsu falon yana mata sallama. Nan da nan ta dauki jilbab dinta ta zura ta fito falon tana amsa sallamar; shi da Nana ne da Rukayya.

Bayan sun gaisheta ta amsa ta nuna musu kwanukan suka fara dauka, ya dubeta yace

 Kin ajiye min nawa ko, a nan zan yi breakfast.

Ta bashi amsa da

 Eh.

Har sun kusa zuwa bakin kofa yace

 Rukayya tunda kowa ya shirya sai ku ci abinci kawai kowa Yaya ta zuba masa na makaranta na san yanzu Malam Sule zaizo sai ku tafi. Kafin ku dawo Mommy ta dawo mana da babinmu.

Suka amsa sannan suka fice.

Aisha ta tambayeshi kwanan masu jego ya sanar da ita basuyi waya ba sai daga baya idan gari ya kara wayewa.

Har zata shige daki sai kuma ta dawo tana fadin

 Bari nayi serving abincin kawai da na sako kaya sai mu ci kada yara su zo suna jirana.

Ta juyo ta kama hanyar kichin yayinda shi kuma ya juyo da kujerar dining table daya ya zauna don ya jira ta. Har ta shiga kicin din kuma sai ta dawo ta tube jilbab din jikinta ta jefa kan kujerar zaman mutum uku, ta cigaba da kaiwa da kawowa tana kwaso abinci daga kicin tana ajiyewa.

Idonsa yana kanta har ta gama, sauri takeyi don haka bata ma kula da yanda yake kallonta ba.

Bayan ta gama ajiye abincin ta bi ta gabansa ta wuce da niyyar shigewa daki. Bata kula da lokacin da ya mike tsaye ba sai ji kawai tayi ya kama hannunta ya dawo da ita ta fada jikinsa. Duk yanda ta so ta kwace kasawa tayi, don ya riketa sosai kuma dama ya gama sanin lagonta.

Wajen wata uku kenan rabonsa da ita, yau din kuma ji yake kamar zai iya biya mata bukata. Ko ma dai menene ba zai iya hana kansa ita din ba a yanzu, ya san abinda take tsoro kuma ya ji a jikinsa babu wannan matsalar don ko daga yanda ya riketa itama ta ji alamun hakan. Da kyar ta lalubo muryarta tace

 Zamu makara fa ni da yara.

Ba tare da ya saketa ba ya fara kokarin lalubo wayarsa a aljihunsa, ta sami damar kara dagewa don ta kwaci kanta bayan ya dauko wayar ya rada mata magana a kunnenta ta kyalkyale da dariya. Tana jinsa ya kirawo Malam Sule yace

 Malam Sule yau Antinsu ba zata aiki ba ku wuce ka kai yara kawai sai ka wuce office ka jira ni.

Nan da nan ya kife wayar ya jefata kan kujerar zaman mutum uku.

Ko ba a gaya mata ba ta tabbatar yau lafiyarsa ta dawo, sai wajen takwas saura sannan ya kyaleta.

Ta dubi agogon bangon dake dakin tace

 La ilaha illallahu, yau ka makarar dani zaka sa principal tayi ta yi min mita.

Yana dariya ya bata amsa

 Shikenan sai kiyi zamanki a gida gobe kya je aiki.

Haka tayi sauri ta shiga wanka, Koda ta fito ya riga ya saka kayansa yana falo yana jiranta.

Haka suka gama breakfast tana mitar ya makarar da ita.

Da taga dai karfe tara ta kusan yi haka ta hakura tayi waya makarantar ta sanar da su ba zata sami zuwa ba.

Daga baya ya shirya ya wuce asibiti ya barta a gidan yana mata dariya.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

14

Har Abban Sadik yaje asibiti yana mamakin yanda akayi yau lafiyarsa ta dawo a wajen Aisha, duk wani lissafi yayi shi amma ya kasa samo amsar. Abu daya ya iya yankewa duk da ya kasa tuna tabbas din abinda ya faru kuma baya son ya zargi Zahra. Yana zargin kamar duk ranar da ya sha zobo ko shayi a wajenta to idan kwanan Aisha ne baya iya komai, domin a iya lissafinsa wannan zobon ne kawai bai sha ba tunda a asibiti ta kwana, shi yasa bai sami matsala ba. Ya yanke shawarar zai sa ido ya gani kuma ba zai sake yarda ya sha zobon nan ba sai dai idan ranar kwananta ne ita Zahran.

Yana isa asibitin aka sallamosu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko su ya dawo da su gida. Nan da nan aka shiga hidima da mai jego.

A ranar ya kamata ya dawo kwananta amma ta san a bisa al ada kamata yayi ta barwa Aisha kwanan sai tayi arba in.

Bata da matsala da hakan don tuni ta kirawo Hajja don ta karo mata maganin da ta bata don ta cigaba da dafa masa zobo; tayiwa kanta alkawarin yanda tayi jegon nan shima haka zai yi.

Tunda yamma ta sanar da shi ta barwa Aisha kwanata har sai tayi arba in, yaji dadi sosai kuma ta kara daraja a idonsa.

Saida ya gama duk abinda yakeyi a cikin gidan sannan ya shiga dakinta yi mata sallama. Ita kadai ce a dakin tana zaune a kan gado domin baby tana bayan Rahma kuma suna falon kasa.
Ya zauna a dai-dai kafarta yace

 Sannu maijego. Ya kike? Ya Baby? Babu dai wata matsala ko?

Ta jijjiga kai

 Ko daya babu.

 To ni zan wuce, Sadiku zai rufe muku kofa sai ya kawo miki mukullan.

Ta dubi flask din da yake kan durowar gefen gado tana gyara zama tace

 Bari na zuba maka shayi gashi yanzu na gama sha nima.

Ya jijjiga kai

 Ai yau bazan sha shayin nan ba don a koshe nake, ki ajiye flask dinki kiyi ta tsiyaya kina sha a hankali.

Tayi  yar dariya

 Kai haba, ai kuwa shayin irin wanda kake so ne.

 Ki daina tempting dina, yau a koshe nake kin san daga wajen liman nake a nan muka zauna aka bankare mana kaji da gurasa muka ci. Abincin daren ma da kyar zai sami shiga yau.

Duk wayonta haka ta hakura ya fita ba tare da ya ko ka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?lli flask din shayin nan ba, yayi mata sallama ya wuce wajen Aisha.

Yana fita ta fara nadama, ta san ba zai iya gane ta saka wani abu a shayin ba to amma me yasa ya ki sha? Gashi sai da ya bari ta barwa Aisha kwananta sannan ya wani ki shan shayin. Saida tayi kwalla saboda takaici; tayiwa kanta alkawarin zasu hadu gobe.
& & & & ..

Da mukullinsa ya bude gidan kamar yanda ya saba ya shiga, tana falo tana karatun littafi da shayi kofi daya a gabanta tana sha. Bayan tayi masa sannu da zuwa sun gaisa ya dubeta yace

 Ina abincinna yunwa fa nake ji.

Ta kalleshi tana dariya

 A a, jegon har ya fara tabaka ne? Yau fa kwanan Mommy ne ko ka manta ne?

 Babu wani jego ai haka akeyi, tunda tana jego ai ke zaki karbi kwanan zuwa tayi arba in don kema idan kika haihu haka zata yi. Don haka ki shirya ina nan har arba in.

Tayi dariya

 Gaskiya dai ka koma, ni ban karbi wannan kwanan ba. Kawai saboda ta haihu sai kuma ka barsu ita kadai da Baby, ina laifi idan ka kwana a can din. Nifa idan na haihu babu wani arba in duk da babu abinda za ayi amma ba zan yafe kwanan ba, ka kwana a nan din dai like just be there ba wai ka tafi ka barni da baby ba wai kai ka

13 / 58