Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 58

51K to 54K   out of 172.2K words

ruwa ba zai shiga wancan tankin ba.

Jijjiga kai kawai yake yana mamaki, to waye zai yi haka?

 To yanzu ya za ayi da wayar kenan.

 Kada ka damu yallabai, ai yanzu za a fiketa a hada ai wannan karamin aiki ne.

Nan da nan kuwa aka gyara wayar, ya sallami mai gyran ya saka kujera a tsakar gidan ya zauna yana tunani.

Ya gaji da zama ya tashi ya shiga ciki ya sanar da Mommy zai je gidan Aisha.

A tsakar gida ya sami Rukayya da Amira suna  yar gala-gala, bayan ya amsa sannu da zuwan da suke masa ya shige ciki.
Tana zaune a kan kujerar dining table tana cin dabino wanda shine yazo da shi yayinda take karatun littafi.

Tayi masa sannu da zuwa bayan ta amsa sallamarsa. Ya karasa ya ja kujera kusa da ita ya zauna yana fadin

 Matar Alhaji, dabino kika saka a gaba haka kina ci kamar wani nama.

Tayi dariya tace

 To me yafi raina.

 Ina naman Sallah na ko baki ajiye min ba.

Tace

 Nama kai, ya za ayi naci na manta da mai gida.

Ta tashi ta shiga kicin, jimawa kadan ta fito da nama a faranti tangaran ta ajiye masa. Ta koma ta dauko kunun aya a fridge ta ajiye tana fadin

 Ga wannan saboda naman ya fi saurin wucewa.

 Yauwa matar Alhaji.

Ta zauna tana dariya. Ya dan ci naman ya kora da kunun aya, bayan ya ajiye kofin yace

 Wannan ma ai naman rago ne, ina naman san yake. Naman ragon ma da ba wani yawa ne da shi ba amma shi kika soya har ya kawo yanzu?

Tayi dariya

 Kai dai kaci nama, bari in sa maka filo a bayan kujerar kada ka fadi saboda santi don naman nan ya ji onga.

Shima dariyar yayi, ya rike hannunta wanda take kokarin karo bayansa da shi ya kalleta suka hada ido na dan lokaci, ta sunkuyar da kanta. Ya kirawo sunanta

 Aisha.

Ta dago suka sake hada ido, yace

 An kawo miki naman Sallah ko ba a kawo ba.

Tayi murmushin yake ta kawar da kai, ta so ace ya bari idan aka kwana biyu ya huta sai ayi wannan maganar amma daga dawowa ya rutsa ta. Tace

 Ba a kawo ba.

Ya saki hannunta ta gyara zamanta, yace

 To a ina kika sami wannan naman?

Ta kalleshi tace

 Nayi layya fa kuma ka sani, a gidan Umma aka yanka aka soya danyen kuma yana freezer na sawa a miya.

 Kice bana baki barwa Umma naman ba gaba daya ragon kika kwaso.

 A a wallahi, Umma kam nama ai sai dai ta bayar don ya ma yi mata yawa.

Ya cigaba da cin naman yana dan janta da hira; sai dai ko ita kanta tana iya gane ransa a bace yake. Suna hirar yana tunani; shekara ta kusan biyu kenan da aurensa da Aisha amma zai iya cewa bai taba bata naman layya ba kawai saboda mugunta irin ta Zahra. Yana mamakin ma yanda ita Aishan wadannan abubuwan basu dameta ba, don bata ma so ayi zancen. Ya tabbatar da Zahra aka yiwa haka tabbas da duk garin nan sai kowa ya ji.

Ya ajiye kofin yayi mata sallama.

Rukayya da Amira suna nan a inda ya wuce su da zai shiga, ya kirawo Rukayya ta taho wajensa da sauri ta sameshi a kan barandar falon.

 Gani Abba.

Ya kama hannunta ya dubeta suka hada ido yace

 Rukayya bayan kwana biyu da tafiyata Hajji Anti tace ki kunna mata ruwa me yasa baki kunna ba?

Ta kalleshi da sauri tana zaro ido

 Allah Abba na kunna, ina shiga gidan ma na wuce baya na kunna.

 To ya akayi gidan Antin naki babu ruwa?

 Wallahi ban sani Abba, nifa ban ma san gidan nan babu ruwa ba sai yau da na dawo.

 Kika dawo daga ina?

Ta zaro ido tare da rufe bakinta saboda ta tuna wannan abu ne da Mommy tace mata kada ta sake Abban ya sani amma bata san yanda akayi tayi wannan maganar ba. Ta kalleshi idonta ya ciko da kwalla tace

 Ba daga ko ina.

Ya ja hannunta ya zauna a kan dakalin da fulawowi suke ciki, ya tsugunar da ita a gabansa ya kalleta suka hada ido. Tayi sauri ta sunkuyar da kanta tana fitar da kwalla.

 Kin san bana son kuka ko Rukayya?

Ta daga kai alamar e, yace

 To maza ki share hawayenki, babu abinda zan yi miki kuma na tabbatar bakiyi min laifi ba.

Ta share hawayen tana murmushin yake.

 Kada kiyi min karya, tunda dama karya ba dabi arki bace gaskiya kawai zaki gaya min.

Ta daga kai alamar to, ya cigaba

 Ina kika tafi da kika dawo yau din?

Da kyar ta bude baki tayi magana saboda ta san zata sha fada a wajen Mommy

 Dama ranar da ka tafi da daddare shine Mommy ta turo Yaya Sadik da Yaya Yusra suka tafi dani tace ba sai na dinga taya Anti kwana ba, shine sai ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?u da safe tace na dawo.

Mamaki ya kara cikashi, yana so ya boye tsananin fushin da yake ciki a gaban Rukayya don haka ya dan yi gyaran murya yace
 Sai me kuma ya faru?

 Shikenan Abba.

 To je ki cigaba da wasanki.

Ta tashi cikin sanyin jiki ta shige falon domin tun tuni Amiran ta shige ta barta.

Shi kuwa Abba kasa tashi yayi daga inda yake zaune, zuciyarshi sai kuna take saboda takaici. Kenan ma bai isa yace ga yanda yake so ayi a gidansa ba idan Zahra bata yarda ba; lallai dole ya nunawa Zahra bata isa ba.

Sai da ya fara gajiya da zaman sannan ya tashi ya fice daga gidan.

Yana bude gate din yaci karo da Malam Sule yana shirin kwankwasa gate din

 Ya dai Malam Sule?

Ya dan rage tsawo cikin girmamawa

 Barka da fitowa Ranka ya dade.

 Yauwa Malam Sule. Nemana ake yi ne na ganka a gaggauce haka?

Ya dan Shafa kai yana sunkuyar da kai

 A a Yallabai, zuwa dai nayi nayi maka bayani kuma na ce ka kara bawa Hajiyan hakuri, duk da dai tace min ba fushi tayi ba amma dai a bata hakurin.

Mamaki yake yana kallon Malam Sule

 Me ya faru da za a bata hakuri?

Ya kalli Abban ya dan zaro Ido, don ya zata Aishan ta gaya masa shi yasa yake sauri yazo ya wanke kansa kada Abban yayi fushi da shi. Ya dan yi gyaran murya yace

 Uhm, Ranka ya dade dama da baka nan ne bama samun tafiya da ita mu kaita makaranta saboda Hajiya Babba tace yara suna makara, to kuma ko nace mata zan dawo na kaita sai tace na bari ta tafi a motar haya.

 Malam Suleman! Kana nufin tunda na tafi a motar haya Aisha take zuwa aiki?

Ya sunkuyar da kai yana shafa keya

 Wallahi Alhaji ba laifina bane, babu bayanin da banyiwa Hajiya ba. To tace yara suna makara, to ba yanda zanyi.

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace

 Shikenan Malam Sule.

Ya sake rankwafawa

 To Alhaji tuba dai nake, a kara bata hakuri. Um idan ba wani aiki ina so naje gida ne.

 Shikenan Malam Sule, babu wani aiki.

Ya zaro mukullin daga aljihunsa ya mikawa Abban yana fadin

 Sai a sanarwa Hajiyan gobe in sha Allah zamu jirata.

Yayi masa sallama ya wuce.

Ya rasa tunanin me zai yi, kenan tunda ya tafi Aisha take zaman hakuri gashi har bari tayi amma bata nuna wata damuwa ba. To kenan ma ba Malam Sule ne ya kaisu asibitin ba da ta ce masa suna asibiti. Tabbas yau dole Zahra ta gane kurenta.

Yana bude gate din gidan zai shiga aka fara kiran sallar la asar don haka kawai sai ya tsaya a fanfon tsakar gida yayi alwala suka jera da maigadinsa suka nufi masallacin da yake nan kan layin.

Bayan an idar da Sallah saida ya tsaya suka gaggaisa da mutane don haka sai wajen karfe biyar saura ya shiga gidan. Yana shiga ya kirawo maigadi yana tambayarsa wanda ya taba injin ruwa, yace

 Wallahi ban sani ba Alhaji, ai kaga ba ni nake kunnawa ba Sadiku ne kawai yake taba wajen nan sai ko kannensa da wani lokacin suke kunnawa.

Ya sallameshi ya karasa cikin gidan, babu kowa a falon domin yaran sun tafi islamiyya. Sadik ne kawai a dakinsa domin tunda ya shiga SS 3 ya daina zuwa islamiyya; sai yace wai karatu yake, ita kuma Mommy sai tace a barshi tunda Shirin jarrabawa yake.

Yana shiga tsakiyar falon ya kwalawa Sadik kira, tana zaune a falon sama da Sumayya a hannunta tana jiyo kiran da yakewa Sadiku ta san wani laifin yayi, ta ja tsaki ta fada a fili

 Daga dawowa mutum ya ishi mutane da fada akan mace sai kace wata  yar gwal.

A birkice Sadiku ya fito daga dakinsa saboda yanayin kiran.

 Gani Abba.

 Wanene ya yanke min waya a injin zuko ruwa?

Bai yi zaton tambayar ba don haka ya dan diririce, idanuwan Abban suna kansa don haka ya sunkuyar da kai yana wani cin magani cikin in ina yace

 Ba ni bane.

 To wane shegen ne idan ba kai bane? Waye yake kunna injin kuma waye ya iya kwance kayan wuta a gidan.

Ya shafa kai yana wasu
 yan fisge-fisge na rashin gaskiya yace

 Abba ni dai ba ni bane, sai dai idan ko bera ne don gaskiya ba ni bane.

Bai yi aune ba sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kumatun yana fitar da kwalla. Abban ya nuna shi yace
 Kaine ka sa reza ka yanke wayar saboda kada ruwa ya dinga shiga tankin gidan Aisha, to Ina tabbatar maka ba zan dauka ba. Gidana ne don haka yanda nake so dole haka za ayi, da kai da duk wanda yake saka ku sani ba zan dauka ba.

Har ya gotta Sadik din zai wuce ya dawo ya tsaya a gabansa yace

 Na sa plumber ya gyara wayar sai ka sake zagayawa ka yanketa tunda kaine ka ajiye ni.

Ya haye saman ya barshi a nan tsaye yana fitar da kwalla saboda takaici; ya manta rabon da Abba ya daukeshi. Tun yana JS 1 da sukayi fada a makaranta Abban ya zaneshi, sai yanzu zai mareshi saboda wannan banzar matar tasa. Dama Mommy saida ta fada zuwa zatayi ta rabasu da Abba; ai dole ma ya koyawa matar nan hankali. Yayi kwafa ya shige daki ya mako kofa.
& & &

Duk abinda ya faru tsakaninsa da Sadiku tana jiyowa, don haka yana shiga falon tace

 Sadik wani abun yayi ko?

Ko kallonta bai yi ba sai da ya kusa shiga dakinsa ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace

 Kizo yanzu, ina jiranki.

Kafin ta amsa ya shige dakin ya mako kofar, don haka ta tashi ta wuce dakinta ta kwantar da Sumayya wadda ta riga tayi bacci.

Ta fuskanci da fada ya shigo don haka itama ranta a bace ta shiga dakin, yana tsaye a gaban mudubi ya rungume hannayensa ita kuma ta wuce gefen gado ta zauna.

Sukayi shiru na dan lokaci, Jim kadan tace

 Gani.

Ya zuba mata ido har saida ta gaji da kallon da yake mata ta kawar da kai.

Yace

 Zahra.

Ta kalleshi, suna hada ido ta sunkuyar da kanta.

Ya cigaba

 Ranar da na tafi Sadik yaje ya yanke waya wadda take kai ruwa tankin gidan Aisha, na barku a kan Malam Sule ya cigaba da kaita aiki tare da  yan makaranta amma tunda na tafi kika hana kika ce yara suna makara kuma basa makara. Na bar Rukayya ta tayata kwana amma ina tafiya kika turo aka kirawota kika barta ita kadai. Na ce a kai mata danyen naman sallah kika hana a bata, kuma waccan sallar ma haka kika sam mata naman shine wannan kika hanata gaba daya. Me yasa? Wanne irin wulakanci ne wannan Zahra? Kika barta tana yawo a motar haya kuma tana sayen ruwa, saboda me?

Maganganun nashi duka sun shammaceta don haka tayi tsamo-tsamo a wajen, ta muskuta kadan ta gyara zama. Ta gagara bashi amsa sai wani muzurai kawai da takeyi, yace

 Ni da gidana ban isa na fadi yanda nake so ayi ba kenan saboda kin ga ina kyaleki ko Zahra? Ba kya ma tsoron koyawa yara rashin kunya kiri-kiri kike aikata abubuwan da basu dace ba a gabansu saboda tsabar wulakanci da raini& '
A fusace ta katseshi

 Kada fa ka zageni! Ai nima sai ka tambayeni kaji ta bakina amma daga dawowa ta gaya maka karya da gaskiya ka zo kana ta fada.

 To a cikin abubuwan da na lissafa wanne ne karyar ai gani ina sauraronki?

Ta muskuta ta cigaba da muzurai tana zumbura baki, gaba daya ya shammaceta. Da ta san za ayi haka da ta tanadi karyar da zata tsara masa, sai dai batayi zaton yana dawowa haka zai gane komai ba. Duk wanda yayi mata wannan munafuncin ma dole ta dauki mataki a kansa don ba zata kyale ba.

Ya gaji da jira tai magana bata yi ba don haka ya cigaba

 To shikenan kinyi yanda kike so nima zanyi yanda nake so, yara kuma ki cigaba da koya musu rashin mutunci. Amma ki sani, kin bani mamaki don a ya da nake dake na zata ko kare na ajiye nace ki tayani kula da shi zaki yi, balle na ajiye matar aure wadda ban ce ki kula da ita ba kawai hakkinta nace a bata amma kika haye Kai saboda hadama. Fice min daga daki.

Ta kalleshi da mamaki kwakwalwarta tana nanata mata  fice min daga daki , yau ita Yusuf yacewa ta fice masa daga daki saboda wata amarya.

Ta tashi cikin sanyin jiki tana kallonsa tana mamaki, sai yanzu ne ma taga tsananin fushin da yake ciki. Dole ta dauki matakin a kan duk wanda yake da hannu a cikin kulla mata wannan munafurcin.

Ta fice daga dakin ta rufe masa kofar.

Tana fita hawayen da take makalewa ya kwace, haka ta barshi yana zuba har ta karasa dakinta ta shige ta turo kofar. Ta zauna a gefen gado kamar wadda aka tunkuda, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana fitar da hawaye masu zafi harda shesshekar.
Wai yau ita Yusuf yake kora daga dakinsa saboda tsabar wulakanci Kuma harda ce mata hadamammiya duk don yana da wata matar. Dole ta dauki matakin a kan Yusuf da wannan matar tasa don ba a isa a zo daga baya ba a rabata da mijinta.

Haka ta karasa wunin cikin kunci, ko da yara suka dawo daga islamiyya haka tace musu bata da lafiya don haka sukayi jugum-jugum.

Ta dafa abincin dare amma ko kallon table din bai yi ba har lokacin kwanciyar bacci.

Bata yi niyyar zuwa dakinsa ba don haka a dakinta ta kwanta, sai dai duk sata irin ta bacci kasa daukarta yayi. Juyi kawai take a kan gadon, zuciyarta sai kuna takeyi saboda takaici. Ga kayan matan da ta sha duk sun hadu sun birkita ta; tun saura sati daya ya dawo aka yi mata kaza ta cinye ga tsumi galan guda wanda shima tsaf ta shanye duk don shirin dawowarsa amma ga da abinda ya dawo mata da shi.

Haka ta kwana tana juyi tana tunanin mafita don dole ta dauki mataki.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

19

Ko da gari ya waye haka Zahra ta tashi da idanuwanta a kumbure saboda rashin bacci, gashi ranar litinin ce don haka dole ta shirya yara zuwa makaranta. Haka ta goya Sumayya ta shiga hidima, da taimakon Yusra nan da nan suka gama.

Karfe bakwai da rabi Malam Sule ya juya mota yana jiransu a tsakar gidan.

Daidai lokacin Abba ya sauko bayan sun gaggaisa da yaran da kuma Malam Sule ya kunna tashi motar ya fice daga gidan. Yana fita daga gate din yaci karo da Rukayya ta fito a shirye, bayan ya amsa gaisuwar ta yace

 Ina Antin suke ita da Amira.

Tace

 Basu gama shiryawa ba shine tace mu tafi.

Yayi mata sallama ya wuce yayi parking a bakin gate din gidan Aisha, ya fito ya shiga ciki.

Amira ce a falo bayan ta gaisheshi ya shige daki inda ya sami Aisha a tsaye ta saka hijabinta ta dauko jakarta. Bayan sun gaisa yace

 Muje na kai ku makarantar.

Da mamaki tace

 Kai da kanka?

Yayi  yar dariya yace

 To ya na iya, na zama direban matar Alhaji.

Suka fito tare har bakin gate, ita da Amira suna cikin shiga motar Malam Sule ya zo wucesu da yara.

Saida Abba ya kai Amira makaranta ya dawo ya ajiye Aisha ya sanar da ita zai zo ya dauketa sai su dauko Amira in ya so sai ya kaita ta mayar da Amiran gidansu kamar yanda ta sanar masa.

Suka yi sallama ya dawo gida.

Duk da ta ajiye abincin safe amma bai ko kalli tebur din ba ya shirya ya fice ba tare da ya bi ta kanta ba.

Tunda take da shi bai taba fushi da ita har ya ki cin abincinta ba sai yau. Tsayawa kawai tayi tana kallon abincin a dinig table bayan ya fice; lallai

18 / 58