Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 58

96K to 99K   out of 172.2K words

kama ranar zasu wuce Dubai kuma har ranar bai gayawa Zahra ba.

Kaf suka shirya kayansu ana yin sallar Magriba suka bi jirgi sai Dubai.

Sai da suka sauka a hotel suka huta sannan ya bude data.

Yana bude data kuwa kiran Zahra ya shigo kamar tana jiransa, a lokacin Aisha tana wanka. Ya amsa wayar ya fice daga dakin, ya dawo falon kasa wato reception na hotel din ya sami kujera ya zauna.

Bayan sun gaisa ya tambayi yaran, duka suna kusa da ita don haka ta bashi suka gaisa da kowa har Saddiku. Bayan ta karbi wayar suka dan taba hira, jimawa kadan yace

 Yauwa ban gaya miki ba na wuce Dubai din fa, itama Aishan muna tare da ita a nan din tare zamu dawo.

A dan razane tace

 Um ban gane ba. Kace ita nan gida zata wuto?

 Eh. Na canza shawara daga baya tunda itama ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai din kawai sai muka wuce.

 Um, Allah ya bada sa a.

 Amin.

Yanda yaji muryarta ta canza nan take ya san da sauran bayani, ya san idan ta fara mita abun zai daukesu lokaci don haka nan take yayi mata sallama ya kashe wayar.
& & & &

Kwanki biyun farko da sukayi a Dubai shi kadai yake fita tare da wanda aka hadashi don ya raka shi kamfanin da zai yi sayayya. Yana fita Aisha take komawa bacci, domin dama ta tara bacci a Saudiyya. Haka ya kwana biyu yana yawo ita kuma tana hutawa, don ko abinci har dakin ake kawo mata.

Sun riga sun gama magana da Aisha a kan ya saya mata waya in ya so ita kuma sai tayi tsaraba da kudinta; don haka fitarsu ta farko ya sayo mata Samsung hadaddiya mai tsadar gaske.

Suna komawa daki ta kasa hakura, saida ta kunna wayar nan. Suka hadu sukayi launching sabuwar waya.
Wayar ta hadu sosai kuma camera tana fitar da hoto don haka sai ya zama duk inda suka je haka zasuyi ta hotuna.

Sun hutu kuma sun ji dadi domin Aisha zata iya cewa bata taba jin dadin zama da shi ba kamar a wannan lokacin. Shi kansa yaji dadin tahowa da ita saboda yanda take jiyar da shi dadi kuma tana saka shi walwala, don haka ya saki kudi sukayi ta yawo suna sayayya. Hotuna kuwa Allah ne kawai ya san yawan wadanda Aisha ta dauka a sabuwar wayarta; wasu a dakin otel, wasu a wajen cin abinci, wasu a wajen sayayya wasu ma a kan hanya kawai. Ko wanne kuma sai ta makale a jikinsa take dauka ko ta sami masu wucewa tace a daukesu.

Ranar da suka kwana uku a Dubai rana suka je wani club na larabawa, wajen an yi masa tsari ne kamar a Sahara. Sanna ga rakuma da dawakai birjiki duk wanda kake so shi zaka hau, kuma abinci kala kala na larabawa. Wajen yayi matukar burge Aisha.

Tunda suka shiga wajen suke daukan hotuna.

Bayan sun gama hutawa rana ta fadi tace zata hau doki, suka karasa aka hada musu doki. Ita bata iya doki sosai ba don haka da ta hau wani balarabe ya ja linzamin dokin suka zagaya.

Daga baya Abba yace ta dawo su hau doki daya don su zagaya sosai.


Nan da nan ta sauka ta koma kan dokin Abba; ta zauna a gabansa ya rungumeta ta baya sannan ya ja doki suka kama hanya. Suna tafiya sunata hira da dariya.

Saida suka zagaye wajen tas.

Bayan sun dawo wani balarabe ya nuna musu hotunansu da yayi ta dauka a camera dinsa wanda idan suna so biyanshi zasuyi sai ya tura musu. Nan take ta mararaicewa Abba ya biya aka tura hotunan wayarta.

A gajiye likis suka koma dakin sai dai zuciyarsu fari tas saboda wunin ranar yayi musu dadi.

Washegari Aisha tana bude Whatsapp taci karo da sakon Zahida na murya wato voice note, nan da nan ta bude tana saurara:

 Wai mutum yana Dubai amma ba zai tura mana hotuna ba, to wallahi ni ko kasuwar garinmu naje sai na ishi duniya da hoto balle na hau jirgi na keta hazo. Ko da yake ma Yusuf din zan tambaya nake bata lokaci.

Saida ta gama dariya sannan ta zabi hotunansu wajen kala goma ta tura mata. Ta cigaba da dube-dubenta a waya.
_

Duk da bacin ran da take ciki na tafiyar da yayi da Aisha Dubai bata fasa shirin tarbarsa ba kamar yanda ta saba; maganar Dubai ma ta riga ta bawa zuciyarta hakuri. Kawai dai ta yiwa kanta alkawarin ko da tsiya ko da tsiya-tsiya idan zai kuma fita kasar nan ko ina ne sai ya je da ita.

Hajja ta kawo mata kayan mata wadanda cikinsu harda na mallaka, duk ta fara amfani ma da su. Sai dai jiya da suka yi waya da Amina ta sanar da ita akwai wasu kaya da aka kawo mata daga Nijar, idan ta tashi daga office zata kawo mata su lallai ta gwada don ta bata tabbacin sai sun sa mata mutum sambatu.

Wadannan kayan kawai take jira tunda jibi zasu dawo.

& & & .

Ma aikatar kudi ta jiha ne inda Amina take aiki. Su biyu ne a office dinta ita da abokiyar aikinta sai dai kowacce da teburinta. Daga gefe guda kuma akwai kafet karami wanda nan ne suke Sallah ko kuma su dan mike idan suna hutawa.

Yau ma a nan suke zaune, ita Amina tana rubuce-rubucenta yayinda Hadiza ke ta faman kalle-kalle a waya.

Sunayi suna hira jefi-jefi.

Hadiza ce ta budo wani status a wayarta tana kalla tana murmushi, can kuma a fili tace

 To Amin, muma Allah ya kaimu wannan sharholiya.

Amina tace

 Keda wa?

Ta dan matso tana nuna mata abinda ta gani a wayarta; mata da mije ne a kan doki yana rungume da matar suna ta dariya, ita kuma matar tana rike da kofi me straw tana zukar wani abu daga ciki. Yana wucewa wani ya fado suna tsaye ya rungumeta nan ma dariyar suke, shi yana sanye da kananan kaya ita kuma tana sanye da abaya. Bayan ya wuce wani ya fado yana kwance a kan yashin ita kuma ta tada Kai da bayansa tana ta dube-dube a wayarta. A kasan hoton karshe an rubuta  sharholiya made in Dubai. Allah ya maimaita mana.
Wani status din ya fara budowa Aminan tace

 don Allah mayar dashi na kara gani; matar kika sani ko mijin?

Tayi  yar dariya

 Wallahi babu ko daya. Ina jin a group ma fa muka hadu da matar nan kuma fa ban san ko itace a hoton ba ko  yaruwarta ce don bamu taba haduwa ba sai dai a group. Kawai dai sun burgeni.

 Sunanta Aisha ko?

 Gaskiya a a, sunanta Zahida M. K don haka take sawa a WhatsApp name dinta.

 To wannan ta hoton dai sunanta Aisha kuma kishiyar kawata ce don hotunan nan ma hada baki sukayi da mijin ya tafi da ita suka bar Uwar gidan a nan tana fama da yara.

Ta zaro ido

 Ke Amina?

 Wallahi kuwa, wannan tafiyar ta munafunci ce. Uwargidansa ya rainawa hankali don maganar da nake miki ma suna can sai jibi yace mata zasu dawo.

 Kai kawata maza  yan bura uba ne! Wato Uwargida jakar gida an barta a gida an tafi da amarya Dubai sharholiya. Kai Allah ya shiga tsakaninmu da irin wadannan kishiyoyin, ki gama wahala da miji a zo a nuna miki iyawa.

A nan ta saka Hadizan ta tura mata hotunan wayarta tunda dama idan ta tashi daga office di??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n gidan Uwar Sadikun zataje.

Tunda taga hotunan nan ta kasa zama a office din, sosai ranta ya baci don tana taya Amina jin zafin wannan tafiyar da aka yi babu ita. Taci sa'a ana yin sallar azahar ogansu ya fice daga office din don haka itama ta fice ta nufi gidan Zahra.

A falo ta sameta tana hutawa yayinda Jummai take aikace-aikacenta da goyon Sumayya. Kafin su gaisa ta jata falon sama, bayan sun zauna ta ajiye mata ruwan sanyi da lemo. Suna gama gaisawa Zahra tace

 Wai ya na ganki kamar a fusace ne, ina dai fatan kin taho min da tsumin?

 Na taho miki da shi. Wani abun takaici na gani wallahi. Ni wai ba cewa kikayi kwana biyu Abban Sadik zai yi a Dubai bane?

Ta tabe baki ta kawar da kai

 Haka yace. Amma ai daga baya na gaya miki ya tafi da amaryarsa wai wani idan ya dawo naji bayani, don haka yanzu kwana bakwai zasuyi shine sai jibi zasu dawo. Ai duk wannan shirin da nake yi sai ya ji daga gareni don wallahi ina binsa bashin zuwa Dubai.

 Hmmmn! Sai ma kinga abinda na gani sannan zaki tabbatar kina binsa bashi. Yana can suna ta sharholiya shi da kanwarki baki gani ba kamar wasu saurayi da budurwa.

Ta budo wayarta ta nuna mata hotunan da Hadiza ta tura mata; tana kalla tana jijjiga kai zuciyarta tana zafi saboda takaici.

 Ni zai rainawa hankali! Sai yanzu ma na gane babu wani business da yaje yi wallahi kawai hutawa ya dauki amaryarsa ya tafi ya barni a nan da yaransa. Tunda mutumin nan ya tsara tafiya Hajjin da matar nan na san ya shirya raina min hankali wallahi. Kawai daga kara aure mutum ya zama wani karamin munafiki, komai zai yi sai boye-boye? Kin san ko Hajjin ma ban san yana shirin tafiya ba sai da ya zama saura sati daya su tafi ya sanar da ni.

Ta dafa cinyarta

 Kada ki damu kawata na karshe sukeyi, wannan hotunan ma gani nayi kamar kin yarda da zancensa shi yasa nace sai na nuna miki. Amma kada ki wani damu da sun dawo za ayi maganinsu.

 Hmmmn!

Nan suka cigaba da hirarrakinsu, daga baya ta bata tsumin da ta kawo mata sukayi sallama ta tafi ta barta tana takaicin hotunan.

Hotonsu a kan dokin nan yayi matukar tsaya mata a rai don ita bata ma taba sanin Abban ya iya hawa doki ba.
__

Jirgin safe suka biyo don haka wajen sha daya na safe suka sauka a gida Nigeria. Malam Ali yana jiransu a airport don haka nan da nan suka gama clearance suka dauki kayansu gaba daya aka zuba a mota suka kamo hanyar gida.
Suna shiga unguwar Abba yace ya kai su gidan Aisha don haka can ya kaisu suka sauka ya sauke musu kayan gaba daya. Duk da gidan ya dan yi kura amma haka Abban ya tayata suka karkade dakinsa yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya nufi wajen Mommy.
& & & .

Tunda Malam Ali ya shiga dasu gidan Aisha yara suka kai mata labarin Abba ya dawo yana gidan Anti; bata yi zaton haka ba don ta zata a gidanta zai sauke jakar tsarabarsa amma duk da haka sai ta daure. Ta tare yaran gaba daya ta hanasu fita don so take tayi kamar bata san ya dawo ba.
Sai dai kafin ya gama wanka ya zo ranta har ya gama baci; kenan wani abun ya tsaya yi a wajen Aisha.

Tana zaune a falon sama tana ta faman cika tana batsewa ta jiyo yara suna ta murnanr dawowarsa bayan da ya shigo gidan. Sai da ya gama hirarsa da yara ya rarraba musu chocolate din da ya riko sannan ya hau saman ya sameta.

Da kyar ta daure ta amsa sallamarsa; ya fahimci damuwarta saboda dama tun lokacin da yace mata ga su a Dubai shi da Aisha ta daina kiransa a waya sai dai shi ya kirawo, Kuma da ya kirawo sai ta hadashi da yaran. Don haka ya shiryawa duk wata rigimarta.

Bayan sun gaisa ya tambayeta gida da yara ta tashi ta dauko kunun aya ta ajiye ta cika masa kofi, ta koma ta zauna a inda ta tashi kusa da shi. Sai da ya kwankwade kunun ayan ya ajiye kofin sannan ya dubi fuskarta.

Sai cika take tana batsewa tana ta faman harare-harare. Ya mike tsaye yana magana cikin halin ko in kula

 To ni bari na koma dama akwai inda za mu dan& & & .

A fusace ta mike tana harare-harare

 Ban gane ka koma ba, ina kenan kuma? Shikenan mu& '

Ya kama hannunta wanda ya sha kunshi yayinda ta kara shan kuna, yayi taku daya ya matso gabanta sosai yace

 To ai na ga kamar baki ji dadin dawowata bane shi yasa da zan dan koma na baki waje ko.

Ta murgude bake zatayi magana, kafin ta bude baki ya sumbaci lebenta yayi dariya

 Allah ya nuna min ranar da za a daina murgude min bakin nan na rashin kunya.

Ta zumburo baki, ya sa hannu ya kara janyota jikinsa. Duk wata tsiwa da ta haddace zatayi ya goge mata haddarta, haushinsa take ji amma ta kasa ture shi. Yace

 Na san dai kinyi kewata da yawa, to ba gani na dawo ba kuma shikenan sai a tare ni da murguda baki sai kace wani wanda bashi da galihu. Ai dole na koma tunda dama jakata a kulle take idan kika shirya sai na dawo.

Shiru kawai tayi ta kwanta a kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta. Tayi kewarsa kamar yanda shima yayi kewarta. Suna nan a tsaye suka ji motsin hawowa saman wanda kana ji ka san Ummi ne da Sumayya. Tayi gyaran murya ta dan ja baya don ta tabbatar shi ba sakinta zaiyi ba, tace

 Yara fa suna nan.

Ya ja baya ya koma ya zauna.

Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu shi da ita da Yara.

Jimawa kadan ya mike zai shiga daki, yace

 Ayi abinci da ni fa a nan zan kwana.

Ya shige dakin bayan ta amsa; yana so yace tayi abinci da Aisha amma yana tsoron fitna, don ya kula duk lokacin da yayi mata maganar Aisha to da fada suke rabuwa don haka ya hakura.
& & & &

Bayan sallar la asar ne suna zaune gaba dayansu a falon a kasa ana ta hira, ya duba agogo lokacin karfe biyar da kwata. Ya san dai zuwa yanzu Aisha ta dan huta don haka ya dubi Mommy yace

 Bari muje da yara mu yiwa Anti sannu da zuwa, yanzu zamu dawo.

Ya dauki Sumayya ya tasa yaran gaba daya har Saddiku suka nufi gidan Aisha; domin ya san idan ba haka yayi ba bazasu je ba, shi kuma baya jin dadin wannan zaman da sukeyi kamar suna gaba da juna.

A zaune take a falo tana hutawa lokacin da suka shiga; cikin fara a dalwala ta karbesu.

Bayan ta amsa gaisuwar kowa taki amsa gaisuwar Rukayya don haka bayan kowa ya gama magana Rukayyan ta sake cewa

 Anti sannu da zuwa.

Ta harareta tace

 Bazan amsa ba Rukayya, sai yanzu kika zo inata nemanki.

 La Anti wallahi aiki nakewa Mommy shi yasa.

Ummi tayi caraf tace

 Abba kaga Anti tayi fushi da Yaya Rukayya.

 Shikenan sai muyi ta dariya.

Aisha tace tana rungumo kafadar Rukayyan

 To mun shirya, dama ba fada bane.

Sukayi dariya gaba daya. Saddiku ne kawai bai saka musu baki a hirarsu ba yana zaune da hannusa wanda bai gama warkewa ba a rungume yana ta muzurai.

Ta tashi ta shiga daki, jimawa kadan ta fito da kaya ta ajiye ta koma ta sake dauko wasu ta fito ta ajiye sannan ta zauna. Ta janyo hannun Sumayya wadda take kan cinyar Abbanta, ta noke alamar ba zata zo ba. Ta dauko  yar tsana daga leda ta mika mata sannan ta mika mata alawa a 'yar karamar roba. Ta mika mata hannu tace
 To zo mu shirya.

Ta sake nokewa, tayi dariya tace

 Sumayya kiwa.

Ta bawa Saddiku takalmi sau ciki, Yusra da Nana da Ummi kuma kowa ta bashi abaya da agogo.

Akwai keken dinki mai aiki da wutar NEPA dan matsakaici na dorawa a kan tebur, ta janyo kwalin ta mikawa Rukayya tace

 Chief fashion designer, ga keke.

Nan take tasa ihu, ta sunkuci kwalin ta mikawa Abba cikin murna tace

 Abba ka ga.

Kafin ya amsa ta juyo tace

 Anti nagode, kayan sallarki zan fara dinkawa.

Tana dariya tace

 Umm! Wannan dai mayi magana daga baya idan kin dinka na  yar tsana dai mayi magana.

Duk gaba dayansu sukayi mata godiya, har sun mike ta mikawa Rukayya Leda tace kin manta da taki abayar. Abba ya karbar mata duka yaran suka wuce suka barshi a nan yana dauke da Sumayya. Ya dubeta yace

 Wannan ai ke baki sayowa kanki komai ba yara kika siyowa, na zata ma kanki kika siyowa keken dinki.

Tayi dariya

 Ai ni bana son dinki itace take so, tunda suka je gidan Zahida da sallah ta gano kekuna kuma Zahida tayi mata alkawarin zata koya mata dinki shikenan ta kasa nutsuwa kullum dinki.

Yayi mata sallama ya bi yaran a baya.

Yana shiga gidan ya tarar da su a falo sun baje gaban Mommy.

Rukayya sai murna take ta kasa zama guri daya saboda keken nan wanda ta riga ta fitar da shi daga kwalinsa.

Ya ajiye Sumayya ya wuce sama, ya shiga dakinsa ya kwanta don ya huta.

Da sallama ta shiga dakin, bayan ya amsa sallamarta ta zauna a gefen gadon wajen kafarsa. Ya gyara kwanciyarsa yana kallonta alamar ita yake sauraro saboda ya san wannan zaman da magana.

 Mun ga tsaraba yara suna ta godiya.

 To ma

33 / 58