Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 58

27K to 30K   out of 172.2K words

zuba ta dora a dining table ta koma daki ta yiwo wanka ta shirya, har ta fito bai fito ba.
Don haka ta zuba nata abincin ta zauna ta kunna TV tana ci tana kallo.

Ta kusan cinyewa ta ji motsinsa, yana shigowa falon ta gaisheshi ya amsa ba yabo babu fallasa. Kan table kawai ya wuce ya zauna zai fara cin abinci, ta tashi ta hada masa shayi ta zuba masa abincin kamar yanda ta saba sannan ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta.

Yana gama cin abincin ya tashi ya fice ba tare da yace mata wani abu ba, duk da dai ta san gidansa ya tafi.

Yana zuwa bakin gate din gidan Malam Sule yana sauka daga acaba, ya karasa da sauri ya kwashi gaisuwa.

Abban ya matsa gefe ya ce

 Yauwa Malam Sale, dama Ina nemanka. Ni jiya wai ya akayi kuka tafi gidan Hajiya ba tare da Aisha ba?

Ya shafa kai

 Ranka ya dade ai mata sai hakuri, rashin fahimta ce aka samu ni kuma na rasa yanda zanyi da su ranka ya dade. A dai bata hakuri.

 So nake ka gaya min tsakanin da Allah Malam Sule don Allah kada ka boye min, me ya faru? Ya akayi baku tafi da Aisha ba?

A hanakli malam Sule ya koro bayani, yayi masa bayanin abinda ya faru har zuwa lokacin da suka dawo. Ya dora da

 To kaga yallabai babu yanda zanyi, kuma ai bai kyautu Ina tuki ace ta zauna a gaban mota ba, ai ko Yusra ta girma kamar haka ai ta shiga baya na tuka ta balle matarka ta aure ranka ya dade. Amma a dai yi maslaha yallabai lamari ne na kishi.

Ya jijjiga kai kawai yace

 Nagode Sule, nagode.

Ya juya ya bude gate din suka shiga.

Kansa ya kulle gaba daya; yanzu ya za ayi Zahra tayi haka, kuma sannan jiya ta zauna ta tsara masa zance yaje yanata yiwa Aisha fada. Ya tuno yanda take kallonsa lokacin da ya hakikance yana fada.

A zatonsa ya san Zahra shi yasa ya kama zancenta don bai zata zata yi masa karya ba, ashe ma bai santa ba. Ranshi yayi matukar baci; babban damuwarsa yanda ta dora Hajiya a kan karya har take jin haushin Aishan, ya san kawo yanzu kaf danginsa sun ji zancen nan.
Ya karasa cikin gidan ya shiga da sallama.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

11

Ranar asabar ce don haka yana shiga ya samesu a falo ita da Yusra, Nana da Ummi domin ragowar basu tashi ba. Da gudu Ummin ta rungumeshi tana masa oyoyo, gaba daya suka gaisheshi. Itama Mommy tayi masa sannu da zuwa ya amsa ba yabo babu fallasa, ta san dai akwai matsala daga yanayin yanda ya amsa ba tare da bata lokaci ba ya haye sama. Nan take ta tashi ta haye tabi bayansa.

A zaune ta sameshi a dakinsa a kan kujera, ta wuce ta zauna a gefen gado tace

 Ya kwanan amarya?

 Alhamdulillah.

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace

 Zahra, me yasa kika yi min karya?

Taji wani banbarakwai, mamaki ya kamata

 Uhm, karya kuma?

 Eh, kika ce min Zahra kin binku tayi ku tafi gidan Hajiya bayan cewa kikayi ta shiga gaban mota?

Tayi tsuru-tsuru, ta sunkuyar da kai zuciyarta cike da takaicin kiranta makaryaciyar da yayi

 To motar ta cika, gaban motar ne kawai da waje aka ce ta zauna kuma taki.

 Amma kin san gaban mota ba wajen zamanta bane tana matar aure, don me Yusra ko Nana bazasu shiga gaban motar ba?

Ta sha kunu ta kauda kai, sukayi shiru na dan lokaci yana kallonta yana sauraron amsarta. Tace

 To yanzu kafi kishin matar da ka auro kwanannan a kan yaranka, naga dai suma sun balaga ko?

Mamakinsa ya karu

 Oh! Da baki san sun balaga ba kike barinsu suna shiga gaban motar idan zaku fita ko kuma idan za a kaisu makaranta? Ko kuwa sai jiyan suka balaga?

Ta murgude baki ta kawar da kai

 Gaskiya bana so, kada ki sake yi min irin wannan. Ba zan dauka ba, yara su shiga gaban mota ku ku shiga baya idan ba haka ba wallahi zan dau mataki a kai kuma matakin ba zai yi miki dadi ba.

 Uhm, yanzu dai zugo ka tayi dani da Hajiya kazo kace mu makaryata ne kenan.

Yayi yake cike da takaici

 Karyar dai da kika biyawa Hajiya, ai Hajiya bata san me ya faru ba sai abinda kika gaya mata. Kada ki sake yi min irin wannan na gaya miki.

Kafin tace wani abu ya fice daga dakin yana saukowa ya fice daga gidan ya nufi gidan Aisha.

& & ..

Yana shiga ya sameta a kicin tana wanke-wanke, yanda bai yi mata sallama ba bata sa rai zai ce mata ya dawo ba. Ga mamakinta sai ya karaso kichin din yace

 Na dawo.

Ta juyo tana rike da kwanon da take wankewa tace

 Sannu da zuwa.

Ya amsa yayinda ta juya ta cigaba da wanke-wankenta shi kuma ya shige ciki.

Har yayi wanka ya fito tana kicin din, tana hada kayan abincin rana saboda idan ranar tayi sai kawai ta dora. Ya leko kicin din tana tsaye tana yanka kabeji, yace

 Har yanzu ba a gama ba?

Ta juyo tace

 Um, aikin ne da yawa.

 To sannu da aiki.

Ya koma falo ya zauna ya kunna TV, yana kallo amma hankalinsa baya wajen, yana ta tunanin yanda zai yi da Aisha don ya kula fushi takeyi da shi. Yana sane da cewa jiya bata kwana a dakinsa ba amma shima a jiyan fushi yayi saboda abinda aka ce masa tayi, saida ya ji daga bakin Malam Sule da kuma yanda Zahran tayi masa da yayi mata magana sannan ya san bai kyautawa Aisha ba.

Yana nan zaune ta zo ta wuce daki, yayi zaton zataje ta dauko wani abun ne yaji shiru bata fito ba har wajen minti talatin. Don haka ya tashi ya bi bayanta; dakinsa ya fara dubawa bata ciki sai dai kawai ta gyara dakin don haka ya wuce dakinta.

Tana zaune a kan gadonta ta mike kafa da novel a hannunta tana karantawa, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ta gyara zama ta dan matsa don ya sami wajen zama sosai.

Yayi gyaran murya yana ta wani murmushi da yake bata mamaki tunda a saninta fushi yake da ita don ko da zai fita bai ko kalleta ba.

Yace

 Um, ya kika zauna a nan? Yau ba kallon Zee World don ne?

Ba tare da ta kalleshi ba tace

 Um, karatu nakeyi.

Suka yi shiru na dan lokaci yana kallonta, yaga dai bazata kulashi ba, ya kirawo sunanta

 Aisha

 Na am.

Ta bashi amsa ba tare da ta dago kanta ba.
Ya kalleta yayi murmushi ya zare littafin da take karantawa daga hannunta. Ta dago suka hada ido, ta bishi da kallo ba tare da ta ce komai ba. Bata da niyyar magana don haka yace

 Fushi kikeyi dani ko Aisha? To ai shikenan na ji gaskiyar zancen a bakin Malam Sule don haka komai ya wuce. Kawai dai idan irin wannan ta sake faruwa ba tafiya zakiyi ba sai ki yi min waya ki sanar da ni tukunna.

Cikin halin ko in kula tace

 To, in sha Allah zan kiyaye.

Ta mika hannu ta dauki littafinta a kan cinyarsa tana kokarin budo shafin da take, ya sake zare littafin daga hannunta yana fadin

 To kuma ai sai a daina fushin ko?

 Ni dama ba fushi nake ba.

 To ki taso muje falo inda muka saba zama, ai naga ko a can ma kina yin karatun ko.

Ta gyara ta sauko daga kan gadon, ta dauki littafin nata a kan cinyarsa ta nufi falon. Yayi murmushi kawai ya biyota a baya; tabbas ya san Aisha tana da miskilanci amma bai yi zaton zata iya yi masa fushi haka ba. Suka dawo falon ta sami waje kujerar zaman mutum daya ta zauna ta cigaba da karatunta shi kuma yana kallon TV.

Duk yanda yaso ya jata da hira ta ki bashi hadin kai, gajerun amsoshi take bashi da basu wuce e ko a a ba, ko kuma tace Um. Har ya gaji ya koma ya sa mata ido yana mamakin wannan dogon fushin.

Suna nan zaune har sha biyun rana tayi, ta tashi ta shige kicin ta dora abincin rana. Ta kusan gama abincin ya ce mata zai je masallaci ya dawo.

Yana ficewa ta ajiye masa abincin rana a table tayi sauri ta cinye nata, ta wuce dakinta ta kwanta. Tana jin shigowarsa tayi kamar bacci takeyi, don haka ya kyaleta ya zauna yaci abincinsa shi kadai.
& & &

Inda Abban Sadik ya fita ya bar Zahra nan ta zauna tana takaici; wato Yusuf har ya auro matar da zata sa yace mata makaryaciya. Dole ne ta dauki matakin don bazata zauna da wannan yarinyar ba, shima Malam Sule kuma dole ya bar mata gidan don ta san karshenta shi ya fadawa Abban Sadik yanda akayi; dama tana sane da yanda yake kokarin kin bin umarninta.

Ta ji dan danshi a kwarmin idonta, ta kai yatsanta ta taba wajen ta kalla; hawaye ne. Ta jijjiga kai cike da takaici; tabbas yanda ta fitar da wannan kwallar sai ta fitar da Aisha daga rayuwar Yusuf ko da kuwa Aishan tsafi takeyi. Tabbas yanzu ta kara gasgata maganar Malam da yace ba haka suka barshi ba.

Kamar an mintsineta ta tuna bata ma yi magana da Malam ba tunda ta nemi layar nan ta rasa, don haka ta mike ta nufi dakinta. Tana shiga ta saka mukulli ta kulle kofar saboda kar yara su dameta. Ta zauna a gefen gado ta dauki wayarta ta kirawo Malam Hatimu.

Bayan ta gama yi masa bayanin batan layar yayi  yar dariya yace

 Allah sarki, masu ita sun dauke kenan Hajiya, ai kunyi sakaci. Sannan kuma yarinyar ta zo da sa a watakila kuma da nata hatsabibancin, amma ba zata iya damu ba duk taurin kanta.'

Cikin kosawa tace

 To yanzu ya za ayi Malam?

 Eh, kada ki damu akwai aiki wanda za ayi kuma aikin nan zai rabata da mijinki har abada, ke ko bayan ranki bazasu sake hada inuwa daya ba. Ammafa gaskiya aikin yana da tsada sosai, yauwa.

Cikin farin ciki tace

 Kada ka damu Mallam, ko nawa ne zan biya ayi wannan aikin indai zai yi yanda kace.

 Ai Hajiya aiki kamar yankan wuka, sai dai kudin aiki naira dubu dari uku da tamanin zai kama komai da komai.

Ta dan dauke wuta saboda jin yawan kudin; to a ina ma za a ta sami wadannan kudin, ta danyi gyaran murya ta cigaba

 Malam babu kuma wani ragi da za a samu?

 Gaskiya Hajiya a hakan ma anyi miki ragi, don kinga aiki biyu za ayi. A mallaka miki ruhin maigidan ta yanda sai yanda kikayi da shi ita kuma a nesanta ruhinta da nashi ba zasu sake sha awar kasancewa da juna ba.

Ta jijjiga kai, tabbas tana son wannan aikin amma bata da kudi a yanzu

 To shikenan Malam, zan yi kokari na hada kudin nan da wani lokaci in sha Allah zan nemeka.
Sukayi sallama tana tunanin inda zata sami wadannan kudin don gaskiya a halin yanzu bata da kudi. Jarinta na business dinma da takeyi ta dan yi musu gibi so take ta sami dama ta tambayi Abban Sadik. Bata da wata kadara sai sarka da dankunnen gwal nata da na yara kuma gaskiya ba zata iya sayarwa ba. Amma ko a jikin Abban Sadik din zata san yanda zatayi ta sami kudi.

Haka ta wuni tunani har dare yayi, tana ta lissafin yanda zata sami wadannan kudaden. Zuwa dare dabara ta fado mata, don haka nan da nan ta nemo Hajja mai kayan mata. Gaba daya ma ta manta da matar nan don kafin ma Aisha ta tare ya kamata ta nemeta ta hada mata masu zafi amma da yake ta sa ran auren ba zai dade ba sai ta manta.

Nan suka gama magana da Hajja a kan a hada mata masu zafi kamar na naira dubu hamsin don so take gaba daya ta mantar da Abban Sadik kowacce mace. Aka yi mata lissafin dubu saba in da alkawarin in dai ta tura kudin a lokacin to gobe da azahar za a kawo mata sakonta.

Bata da kudi amma saboda akwai abinda ta shirya haka ta kwashe kudin nan a account dinta na business ta turawa Hajja, ya zama saura abinda baifi dubu ashirin ba a account din. Tana tunanin da ta fara aiki da kayan nan sai ya biya kudinsu.
& & &

Haka suka wuni Aisha taki kula Abban Sadik, tace masa ba fushi take ba amma kuma taki ta saurareshi idan tayi murmushi to ita da waya ne. Haka har dare yayi.
Tana yin sallar isha i ta kwanta a dakinta tsaf da niyyar bacci, don haka shi kadai ya zauna a falo yana kallon TV.

Bayan karfe tara ya fita ya dubo wajen Zahra sannan ya dawo, ya shirya ya wuce dakinta.

Duk yanda ta so ya kyaleta a daren nan saida ta sallama masa, haka ya dinga tsara mata kalamai na lallashi a kunnenta har ya samu ta huce.

Sai da safe ya gaya mata zasu shirya asabar mai zuwa ya kaita ta sake gaida Hajiya kuma su bata hakuri.
_

Kamar yanda sukayi alkawarin da Hajja washe gari sai gata ta zo da kanta. Ta yi sa a lokacin da ta zo yara suna islamiyya don haka babu kowa a gidan sai ita, duk da haka dai a dakin baki ta sauketa suka zauna suka turo kofa.

Nan Hajja ta baje kaya tana bayani; kayan da ta hado mata sun kai rabin ledar bagco ga kuma tsumi a galan. Ta zauna tayi mata bayani dalla-dalla tana rubutawa; bayan sun gama Hajja tace

 Hajiya Zahra ai idan akayi maka kishiya baka zama haka, gyara zakiyi na musamman idan ba haka ba sai ki ga wankin hula ya kaiki dare. Yaran nan na yanzu masu ido a tsakar ka, wallahi kada ki saurara mata.

Ta kama haba tace

 Hmm! Ni da na gani Hajja, yarinyar daga zuwanta har ya canza min, jiyan nan dana kirawo ki nan ya kare min tijara saboda ta tsaro masa zance. Ai dole sai na tashi tsaye.

Ta matsa kusa ta dafa gwiwarta tana magana kasa-kasa

 To kinga akwai wani ma..

Ta zura hannu a jakarta ta zaro wani dan kulli a farar Leda, ta cigaba

 Kin gan shi nan ba ma bawa masu kishiya ma saboda idan kikayi amfani da shi ba zai sake jin dadin wata mace ba sai ke, gashi dubu goma ne amma ki bada biyar saboda wannan cinikin da kika yi min.

Ta karba tana juyawa, tana fadin

 Allah Hajja?

 Allah Hajiya. Ai idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka. Idan ma kina bukatar wani taimakon akwai aikin da mukeyi sai yanda kika yi da maigidan, idan ma sakinta kike so yayi zai yi.

 Allah Hajja? Kin san nifa bana son aikin nan da akeyi da aljanu.

 Kema kin san aikina Hajiya, wannan din ma da zan kawo miki ayoyi ne da kanki ma zaki gani. Naira dubu ashirin kawai zaki bayar shikenan an gama.

Nan take suka kulla ciniki, suka rabu a kan idan ta sami kudin zata nemo Hajja. Ita kuma Hajjan ta sake tabbatar mata da idan dai tayi aiki da wadannan kayan da ta kawo mata ko naira dubu dari ta nema sai ya bata.
& & ..

Ta riga ta san da fushi ya fita daga gidan gashi yau din dai a wajenta zai kwana. A sanin da ta yi masa ta san da fushinsa zai shigo don haka ta yi duk wani shiri na tarbarsa.
Duk da yanzu din itama ta so tayi masa fushin amma dole ta hakura saboda abubuwan da ta shirya; duk da daman ta riga ta saba bata son fushinsa, ko da shine yayi mata laifi da zarar yayi fushi zata fara bashi hakuri.

Tunda Hajja ta tafi tasamu ta sha tsumin nan ta koshi, ta bi sauran kayan duk tayi amfani da su, don haka kafin ma yazo ta fitni kanta.

Yana son shinkafa da salad don haka ta shirya fried rice da kaza ga lafiyayyen salad, ta jera a table.

Sai wajen tara da rabi ya shigo gidan, Yusra ce kawai a falo da Rukayya suna homework. Yana shigowa Rukayya ta shirya, suka fice ya rakata don ta taya Aisha kwana sannan ya dawo ya rufe kofa.

A falonsa ta sameta, ya shiga da sallama. Bayan ta amsa sallamarsa ta mike tana masa sannu da zuwa. Ya amsa ba yabo babu fallasa, ya wuce daki. Ta bishi da sauri, don haka kusan tare suka shiga dakin

 Yallabai.

Ta kirawo sunansa murya a mariraice.

Ya juyo ya dubeta sannan yace

 Menene?

Ta kara marairaicewa tayi kasa da murya

 Ka san dai fushinka baya min dadi, don Allah kayi hakuri in dai nice ba zan sake ba.

Ya juyo gaba daya ya tsaya yana kallonta, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa. Yadan matso kusa da ita sannan yace

 In dai baki sake ba ya wuce.

 In sha Allah ba zan sake ba.

Ya mayar mata da murmushin da

10 / 58