Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 58

135K to 138K   out of 172.2K words

& & &

Ko da gari ya waye ranar aiki ce don haka Abba ya shirya daga gidan Aisha suka fice gaba daya ba tare da ya je gidan Zahra ba. Ya riga ya san babu abinda suke bukata kuma ya yi waya da Malam Ali ya riga ya kai masa yara makaranta.

Babu yanda Aisha bata yi ba ya barta ta rakashi asibitin itama ya hanata, sai dai ta hada breakfast inda ta soya dankalin bature da sauce din kaza sannan ta zuba musu ruwan zafi a flask ta bashi ya kai musu. Yana fitowa ya sayi kayan shayi ya wuce asibitin.
Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga.

Muhammadu yana zaune a kan tabarmar da ya shimfida yana kokarin hada musu shayi da ragowar ruwan da ya zo da shi jiya. Ya ajiye kofunan da suke hannunsa ya tari Abban ya karbi kayan hannunsa ya ajiye. Bayan Abban ya amsa gaisuwar sa yace

 Likitan ya zo ne Muhammadu?

Yace

 Bai zo ba, nurse din ce ta shigo tace yaci abinci zata dawo ta bashi magani.

 To ga abinci nan ka zuba muku ku ci, bari naje na sami nurse din.

Yana fita ya sami waje ya zauna, basu dama yayi suci abinci sannan ya samu yayi magana da Saddikun kafin likitan ya shigo.

Sai da ya basu kusan awa guda sannan ya dawo dakin, lokacin sun gama cin abincin har nurse din ta bawa Sadik maganinsa. Sun gama cin abincin, Saddiku yana zaune a kan gadon yayinda Muhammadu yake zaune a kan tabarmar yana karatu. Bayan Abban ya amsa sannu da zuwansu yace

 Kana da lecture ne yau Muhammadu?

Yace

 A a, sai gobe ne zamu yi test shi yasa nake karatu. Yau ba zan shiga makaranta ba.

 Allah ya bada sa a.

Ya karasa ya zauna a gefen gadon Saddikun.
Muhammadu ya dauki litattafansa ya mike yana fadin

 Abba bari na zauna a nan waje na cigaba da karatun, idan ana nemena Ina nan.

 Ok to kada kayi nisa don yanzu zan tafi.'

Ya ji dadin hakan don dama so yake yayi magana da Saddikun, wanda tun bayan da ya cewa Abban Ina kwana ya sunkuyar da kai bai sake dagowa ba.
Sukayi shiru na dan lokaci babu mai magana, shi Abban yana kallon Saddikun yayinda shi kuma ya sunkuyar da kai ya kasa hada ido da Abban nasa. Jimawa kadan Abban yayi gyaran murya yace

 Sadik me yasa kake son ka kashe kanka?

Ya dago kai idonsa cike da kwalla, suna hada ido da Abban yace

 Kayi hakuri Abba.

Ya sake sunkuyar da kansa yana share hawaye.

Abban ya jijjiga kai yace

 Likitane ya duba ka Saddiku, nurse din da ta shigo ta baka magani bata wuce sa arka ba sai dai ko ta baka shekaru biyu zuwa uku, kalli yayanka Muhammadu yana karatu don ya zama dan jarida, ni da na haifeka public administration na karanta shi yasa kaga na kai matsayin da na kai. Amma kai Saddiku ka zabi zama dan kwaya, ka tara kayan maye ka sha ka fita daga hayyacinka shi kenan abinda kake so Saddiku.

Cikin kuka yace

 A a Abba kayi hakuri.

 Ka daina bani hakuri Saddiku, baka yi min laifi ba. Kanka ka yiwa laifi kuma kayiwa Allah laifi. Ya baka rayuwa kuma ya baka dama ka zama abun alfahari ga al umma amma ka zabi shaye-shaye.

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace

 Wa ya baka kudin zuwa party?

 Mommy.

 Tun yaushe kake shan kwaya?

Ya sunkuyar da kai yayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

 Tun ina SS 2.

 Ka san yanzu jikinka ya saba ba zaka iya rayuwa babu kwayoyin da kake sha ba saboda ka zama addicted ko?'

Bai iya amsawa ba kai kawai ya daga don ya san hakan ne.

 Ina son ka Saddiku, ina son kayi rayuwa a hayyacinka kaima wataran ka zama wani ka tara naka family din cikin nutsuwa. Akwai makarantar da zasu taimaka maka ka daina shan kwaya amma fa makarantar kwana ce, idan likita ya sallameka daga nan can zamu wuce. Idan Allah ya sa ka rabu da addiction din a wata shida sai ka fito ka cigaba da karatunka.

Kai kawai ya dagawa Abban saboda yanda kuka yaci karfinsa.
Suka zauna sukayi shiru har sai da ya daina kukan, Abban yace

 Yanzu ina ne yake maka ciwo?

 Babu ko ina, jikina ne kawai yake ciwo.

Jimawa kadan Abban yayi masa sallama ya fito ya tura masa Muhammadu sanna ya wuce office zuciyarsa cike da damuwa.

Yana tausayin Saddikun sanna kuma yana ganin laifinsa ne da yayi sakaci a kan Saddikun, yana fatan Allah ya bashi ikon ceto Saddikun.

Kafin ya isa office din yayiwa Aisha waya ya sanar da ita ta dafawa Sadik abincin rana idan ta dawo daga aiki idan ta gama ta yiwa Malam Ali waya ya zo ya karba ya kai.
& & & &

Tun safe take jiran shigowar Abban don ta gama shirin zuwa asibiti wajen Saddiku amma har wajen karfe tara bai shigo ba. Wajen karfe tara da rabi ta sa Yusra taje ta dubo gidan Aisha ta kirawo Abban, sai dai bata dade da fita ba ta dawo ta sanar da ita babu kowa a gidan.
Zuciyarta ta kara tafasa saboda ta gaji da abinda Abban yake mata, ita da danta a hanata zuwa ta dubo shi.

Ta dauki wayarta ta shiga daki sannan ta danna masa kira, sai dai har ta gaji da kira bai amsa wayar ba. Ji take kamar ta rusa ihu saboda takaici, ta rasa ma wanda zata gayawa taji dadi. Ta zauna a gefen gadonta ta lalubo lambar Yaya Murja wadda tun jiya take kiran Zahran ita kuma ta ki dauka saboda tana kunyar abinda zata fada mata.

Tana dauka tace

 Zahra ina kika shiga ne ? Tun dare nake faman kiranki. Yusra dai ta ce min kina nan amma me yasa ba kya daukan waya. Kin gan ni a tsaye gidan naki zan taho ko kina asibitin?

Cikin shesshekar kuka tace

 Ina gida. Abbansu ya hanani zuwa asibitin kuma ya ki ya gaya min me ake ciki.

Cikin muryar lallashi tace

 To kinga gani nan zuwa gidan yanzu.

Ta katse wayar ta ajiye.

Wajen sha daya saura Yaya Murja ta shiga gidan, a daki ta sami Zahran ta ci kuka ta koshi. Nan ta bata labarin irin wulakancin da Abban yakeyi mata tun lokacin da aka kwantar da Saddikun a asibiti, gashi ya ma ki ya barta koda ta ji muryar Saddikun. Sai dai duk cikin bayanan da take yi bata gaya mata ainahin abinda ya sa Abban ya ke mata hakan ba.

A iya sanin Murja ta san akwai fahimtar juna tsakanin Zahra da Abban Sadik; duk da a baya bayan nan Zahran tana kokarin ta fahimtar da yayar tata cewa tunda Abban Sadik din ya auri Aisha ya canza mata.

Gaba daya dai ta kasa gane bayanin da Zahran take yi mata a halin yanzu; amma ko ma menene ya za ayi ace mace ta haifi danta kuma ace mata bashi da lafiya amma an hanata ta ganshi kuma an ki ayi mata bayanin halin da yake ciki.

Sai da ta samu Zahran ta tsagaita da kukan san?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 nan ta zaro wayarta daga jaka ta lalubi lambar Abban Sadik din ta kirawoshi.

Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa ta tambayeshi jikin Saddiku sannan ta sanar da shi tana gidansa, ta nemi yayi mata kwatancen inda Saddikun yake a asibitin tana son zuwa ta duba shi. Bai yi mata wani musu ba domin ya san dama za ayi hakan; sai dai ko da ta nemin izini zasu taho da Zahran ya sanar da ita kada su taho da ita idan ya zo zai kaita da kanshi.

Don haka nan take ta tashi kai tsaye ta fito daga gidan ta hau motar haya ta nufi asibitin Malam. Kafin ta isa asibitin Abban ya isa don haka a farfajiyar wajen ta sameshi bayan yayi mata kwatancen wajen.

A zaune yake a kan irin kujerar nan ta dutse don haka itama Yaya Murja sai ta zauna, bayan sun sake gaisawa sukayi shiru tana jiran yace su tashi ya kaita dakin da Saddikun yake. Madadin hakan sai yace

 Ta gaya miki abun da ya sami Saddikun?

Cikin zakuwa tace

 To duka bayanan nata wallahi ba ganewa nayi ba saboda tana cikin damuwa, kamar dai tace jiya da safe ya fita shine aka kirawo ta akace kamar sun ci wani abu suna asibiti. To tace kai kadai ka zo ka ganshi kuma baka bata wani bayani ba, shi yasa ma take cikin damuwa.

Ya jijjaga kai.

Nan yayi mata bayanin ainahin abinda ya faru sannan ya kara da

 Saboda bata son bacin ran shi tana kallo tun yana SS 2 yake shaye-shaye gashi yanzu har ya zama addicted, jiyan da ba dan Allah ya sa da kwanansu a gaba ba da sai dai mu dauki gawarsu. Yau da na fita daga nan kuma makarantarsu naje ashe ma shi ba karatun yake yi ba, tunda jarrabawar da yace mata sun gama ta bashi kudin party harda mota ya tafi an ce guda biyu kawai ya rubuta a cikin paper goma sha daya; kin ga babu maganar karatu ko.

Kallonsa kawai take tana mamaki tana jijjiga kai, tace

 Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ita kuwa Zahra garin yaya tayi haka?

Nan ta gaya masa yanda suka yi da Zahran a kan maganar zargin da takeyi, sannan ta sake bashi hakuri.

Nan ya tashi yayi mata jagora har dakin Saddikun, ta dai samu natsuwa yanda taga Saddikun tunda a hayyacinsa yake har hira ma suka yi kuma ya gaya mata babu inda yake masa ciwo don likitan ma yace da safe zasu sallameshi.
Bayan sun fito ne Abban yake gaya mata ya riga ya sami rehabilitation center da zai kai Saddikun, wanda a yanda ya tsara daga nan asibitin kai tsaye center din zasu wuce.

Tace hakan yayi domin itama tana so taga Saddikun ya zama mutum, sai dai ta roki Abban a kan ya taimaka ya bari Zahra ta ga Saddikun kafin a tafi da shi rehabilitation center din tunda ya ce da ita wata shida zai yi a can kuma shi kadai zai dinga zuwa yana ganinsa. Yayi mata alkawarin gobe da safe zai kawo Zahran ta ganshi inda daga nan zai daukeshi su wuce.

Sukayi sallama ta kama hanyar gida shi kuma ya koma office.
__

Kai tsaye daga asibiti gidan Zahra ta koma saboda yanda take cike da takaicin abun da Zahran tayi. Bayan ta sanar da ita Saddikun yana nan kamar ma lafiyarsa kalau sai kuma ta hau ta da fada.

Sai da tayi mai isarta sannan tace

 Shima kansa Abban haushin ki yake ji saboda yanda kika tsaya kika bari Saddiku ya lalace kuma kika dinga hanashi yayi masa fada, shi ya sa kika ga yayi banza dake. Don haka idan ya dawo ki lallaba ki bashi hakuri tunda gaskiya dai da laifinki don shi da kansa yace ke kika bashi kudin party din. Ki samu ki bashi hakuri don gaskiya yayi fushi sosai, kuma idan an kai Saddikun rehabilitation center ki kawar da idonki a samu ya sami lafiya tunda dai kin tabbatar ubansa ba zai cutar da shi ba.

 Wallahi Yaya wannan wulakancin da yake yawan yi min tunzura shi matarsa take tunda da ai ba haka yake ba.

 Ba zamu iya gane hakan ba sai lokacin da yayi fushi da ke ba tare da wani dalili ba don yanzu kam kin yi abun fushi. Kawai ki gyara kuma ki bashi hakuri.'

Ta riga ta san daman haka Yaya zata ce don haka tayi shiru.

Daga baya YayaMurjan tayi mata sallama ta tafi.
__

Duk yanda yake jin haushin Zahra ya san dole yau ya ganta tunda kwananta ne. Sai da ya gama duk abinda zai yi ya ci abincin dare a gidan Aisha sannan wajen tara da rabi ya shiga gidan Zahra.

Duk yanda ya so ya kyaleta bata bashi dama ba saboda yanda ta sameshi a daki ta saka shi a gaba da kuka tana bashi hakuri. Ta bashi tausayi sannan kuma baya son ganinta a damuwa don haka da wuri ya nuna mata ya hakura. Ya dan ci abincin daren da ta dafa duk da a koshe yake. Haka suka kwana babu yabo babu fallasa.

Gari yana wayewa bayan sun gama cin abinci yara sun tafi makaranta ya daukesu ita da Yusra suka wuce asibitin.
Sai a lokacin Zahra ta sami natlsuwa da taga Saddikun, suka dan taba hira har ta tambayeshi ina motarta. Sai a lokacin ya tuna da motar inda yace mata bai sani ba sai dai ko ta tambayi Abba don wayarsa ma Abban aka bawa kuma har yanzu Abban bai bashi wayar ba. A halin da ake ciki ba zata iya maganar motar ba don lallabawa takeyi ta kankarowa kanta mutunci don haka tayi shiru.

Basu dade ba Yaya Bello ya iso ya samesu, suka gaisa da Zahran sannan ya jajanta mata jikin Saddikun. Shi da Abba suka shiga ofishin likitan, sai da suka fi minti talatin suna tattaunawa sannan suka fito; domin likitan ne ya hadasu da masu rehabilitation center din. Suna fitowa aka rubutawa Saddiku sallama.

Yusra ta taya Muhammadu suka kwaso kwanukan abinci wadanda duk na Aisha ne suka zuba a motar Malam Ali da yake jiransu, Abba ya bawa Muhammadu kudin mota yace ya wuce gida. Har ya kama hanya Yusra tace masa

 Yaya Muhammadu kwanukan ba na gidanku bane ko a kawo daga baya.

Yace

 Ba na gidanmu bane na gidanku ne fa.

Kafin suce wani abu Abba yace

 Na Antinki ne idan kun je gida Malam Ali zai kai mata.

Sai da Zahra tayi da gaske sannan ta danne damuwarta kada Abban ya ga sauyi a fuskarta; wato mutan gidan Bello da Aisha sun fita mahimmanci a rayuwar yaranta shi yasa ya danka musu Saddikun ya hanata ganinsa bayan babu wanda ya haifar mata yaron. Lallai!

Daga gefe guda likitan ne tsaye da Yaya Bello da Abban suna magana, bayan Saddikun ya zuba kayan hannunsa a motar Malam Ali ya karasa ya cewa Abban ya fito.
Abban ya dubeshi yace

 Kaje ka yiwa Mommynka Sallama daga nan zamu wuce da kai makaranta ni da Yaya zamu kai ka.

Ya amsa ya wuce wajen su Mommy din.

Tayi zaton da ita za aje taga makarantar amma Abban yace ba haka za ayi ba su wuce ita da Yusra Malam Ali ya mayar da su gida, shi da Yaya Bello zasu kai Saddikun.

Shi kanshi Abban sai da ya kula da yanda ta fusata, ta shige motar ta rufe domin Yaya Bello ma da ya taho yayi musu sallama sai hakura yayi ya tsaya wajen Abban yayinda Malam Ali yaja motar.

Abba yaja motar shi da Yaya Bellon suka nufi kan titin gwarzo road inda daga nan ne zasu kara neman kwatancen makarantar.

Har suka isa gida Zahra ba tayi magana ba saboda yanda zuciyarta take tafasa; wato yanzu kenan Bello shine zai dinga tsarawa yaranta rayuwa saboda sun mayar da ita  yar iska shi da dan uwansa. Za a kai mata yaro makaranta amma bata ma isa a kaita ta ga wajen ba kenan idan wani abu ya sami Abban Bello ne kawai ya san inda Saddiku yake.

Gaskiya ba zata jure ba, wulakancin ya isa. Bata san me ta tsarewa Aisha da Bello ba suka janye mata hankalin miji, amman dole ta dauki mataki.

UWAR SADDIKU

Written by

Sakina Yazid
(Innar su Amal)

39
Sai da aka bawa su Abban Sadik takardu suka cike sannan aka nuna musu dakin Saddiku, bayan nan kuma aka yi musu bayani cewa ba zasu ziyarceshi ba sai bayan sati biyu. Babu waya a hannunsa don haka aka basu lambar wayar da za a iya kira ayi magana da shi. Mutum biyu kawai ake so wadanda sune zasu dinga ziyartar sa don haka Abba ya sa sunanshi da na Yaya Bello a kan su kadai ne za a dinga bari suna ganinsa. Sukayi masa sallama suka taho zuciyar Abban cike da damuwa yana fatan Allah ya sa kafin ya dawo Saddikun ya fara samun natsuwa.
Haka suka fito suka bar Saddikun shima yana matse hawaye yayinda kwakwalwarsa take kokarin gamsar da shi cewa iyayen nasa basu daina son sa ba.
__

Tunda aka kai Saddiku makarantar nan Zahra ta kasa nutsuwa. A da idan tana cikin damuwa Abban ne yake kwantar mata da hankali, yanzu kuma da take cikin tsananin bukatar hakan yayi burus da ita. Bai taba hanata kwananta ba amma dai babu wata hira da take shiga tsakaninsu; ita tana jin haushinsa kuma tana fushi yayinda shi yake ganin shine ya kamata yayi fushi ba ita ba. A halin yanzu ma kwata-kwata baya jin Zahra a ransa kamar yanda yake jinta a da.

Kusan kwana goma kenan da kai Saddikun amma duk ta rame tana neman fita hayyacinta saboda damuwa da rashin bacci, gashi kullum ta dan sami baccin sai ta yi mafarkin Saddikun a wani yanayi mara dadi.

Ranar asabar ce don haka yara sun tafi tahfiz, don haka ta koma dakinta ta kwanta tunda maigidan ba awajenta yake ba. Tana kwanciya bacci ya kwasheta.

Yana zaune a wani waje mai kyau da haske, shimfidun wajen farare ne tas haka ma kujerun. Yana zaune a kan kujera cikin shigar fararen kaya, sai dai abinda ya firgita ta shine yanda duk kyan wajen da kuma kyan shigar Saddikun kuka kawai yake faman yi yana matse hawaye. Magana

46 / 58