Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   39 / 58

114K to 117K   out of 172.2K words

tasiri take kula da motsin Aisha, musamman ta sami mai aikin gidan commissioner wadda dattijuwa ce take sa mata ido tana kular mata da motsin Aishan. Tana so ta san lokacin da Aishan zata bar gidan. Zuwa yanzu kusan watanni goma an sanar da ita Aishan tana na; ta kasa gane wanne irin naci ne wannan. Miji baya kula ki amma ace ba zaki bar masa gida ba? Ta dai bata daga nan zuwa babbar Sallah ta san in Sha Allahu zuwa lokacin ko bata gaji ba to tabbas kudin hayar gidan zai kare.

Maganar boka ta tuno da ya ja layi guda biyu yace mata tafiyar Aisha da Yusuf mai tsawo ce; yanzu haka tsawon kenan kuma in Sha Allahu sai ta ga karshen wannan tafiyar.
__

Kwanci tashi har azumi ya karaso; duk wani abu da Aisha take bukata na azumi haka ta dauki Amira suka je suka siya, kuma da yake Yaya Abubakar ya san halin da take ciki ranar da aka ga watan azumi sai ga sako ya aiko mata. Buhun shinkafa, dankalin bature, doya, kifi da suga haka aka kawo mata.

Ranar goma sha takwas ga watan azumi jirgin su Hajiya zai tashi tare da Aisha. Ranar sha biyar ga wata ta shirya suka tafi gidan Hajiya ita da Amira; bayan ta kwashe duk wani abu mai amfani nata saboda bata barwa kowa ajiyar gidan ba. Sai da ta kulle ko ina tayi addu a sannan suka fito, har zata saka kwado a gate din ta tuna duk wanda ya zo yaga kwado daga waje ya san babu kowa a gidan don haka sai ta fasa saka kwadon kawai ta kulle da mukullin. Babu wanda take harka da su a kan layin don haka bata bukatar yiwa kowa sallama, ta ja motarta suka bar unguwar.

Ranar da aka dauki azumi na sha takwas da safe Aisha da kanta ta dauki Abdallah da Farha ta kaisu gidan Umma, kakarsu ta wajen Uba. Ba karamin dadi Umma taji ba don dama sun dade basu je mata kwana ba. Sukayi sallama a kan sai bayan Sallah idan ta dawo zata zo ta daukesu. Da yamma jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki, tana tsakiyar Hajiyanta da Anti Uwani.
____

Ranar da aka kai azumi na ashirin da biyar Baba Salamatu wato mai aikin gidan commissioner ta shigo gidan Zahra. Lokacin yara duk sun tafi masallaci sallar asham sai Jummai wadda take aiyukanta a kichin yayinda Mommy din take hutawa a falon sama. Bayan sun gaisa da Jummai ta hau saman ta kirawo Mommy.

Nan da nan ta sauko saboda ta san akwai labari tunda Sala ta zo. Bayan sun gaisa tace

 Hajiya ina ga kanwarki dai ta bar gidan na fa.

Ta ji dadi sosai a ranta, amma sai ta waske tace

 Allah Sala, ko dai unguwa ta tafi.

 Kai gaskiya ba unguwa ta tafi ba Hajiya. Don Kinga fa tun azumi na kusan goma na daina ganin motsinta, almajiran ma da suke zama kofar gidan jiya sun tabbatar min bata nan don farkon azumi kullum da magriba sai ta basu sadaka amma yanzu an kwana biyu basu ga motsi a gidan ba.

Ta dan yatsina fuska

 Allah sarki, to na gode Salamatu. Dan jirani ina zuwa.

Ta karasa tana mikewa tsaye, ta haye sama ta barta a nan.
Jimawa kadan ta sauko ta zauna a inda ta tashi, ta mikawa Salamatu naira dubu tana fadin

 Ga abun sadaka kya sayi ko dan sabulu.

Nan da nan ta washe baki da addu a tana ta faman godiya, tayi mata sallama ta fice.
& & & .

Cikin walwala suka tashi ranar idi, nan da nan aka shirya yara kowa ya sha kwallaiya. Karfe takwas saura Abba ya fito ya zuba su a mota suka wuce masallacin idi.

Kafin su dawo an sauke tuwon Sallah.

Sai da kowa yaci ya koshi sannan Mommy ta ware na makota, Jummai ta dauka suka tafi tare da Nana da Ummi. Gidaje uku suka kai, gidan commissioner ne na karshe kuma shine cikon na hudun. Bayan sun gaisa da matarsa wato Dr. Maimuna wadda ake kira Mama suka bayar da tuwon, aka juye aka basu kwanukan da kuma tukwici.

Salamatu ta dauko kwanukan ta biyosu suna  yar hira da Jummai kamar zata yi mata rakiya. Kasa-kasa suke yin maganar don haka Ummi da Nana da suka wuce gaba basa jinsu. Salamatu tace

 Wai ni Jummalo amaryar gidanku auren ya mutu ne?

Jummai tace

 Babu mamaki fa, don na manta rabon da maigidan ma yayi rabon kwana da ita; ko ba ayi shekara ba an kusa. Ina ga sakinta yayi ko kuma dai wata matsala aka samu.

 Gaakiya da alama, tunda kin ga ta bar gidan fa tun farkon azumi. Yanzu haka dai auren ya kare. To ko Uwar dakinki ce ta kar auren ne?

Ta dan zaro ido

 Ke salamatu! To ni ban sani ba in kin shiga gidan kya tambayeta.

Ta tabe baki

 Au na manta ke fa ba a sukan uwar Saddiku a gabanki ko. To ku gaida gida.

Tayi musu sallama suka wuce.

Tun daga wannan lokacin gulma ta fara yawo a unguwar cewa Abba ya saki Aisha.

Bayan da su Nana suka dawo ne kuma Malam Ali ya kwashesu da tuwon gidan Hajiya suka tafi kai mata. Mommy ta riga ta gayawa Yusra cewa idan Hajiya ta tambaya Ina abincin gidan Aisha tace tare suka yi don haka suna ajiye tuwon ma kafin a tambaya Yusra ta cewa Hajiyan

 Tare sukayi tuwon da Mommy da Anti Aishan.

Ta yashe baki

 Ai gara hakan ya fi.

Bata jin dadi sosai saboda ciwon diabetes wanda tun goman karshe ya tasar mata saboda an hanata azumi tace sai tayi, don haka ta san ba cin tuwon zata yi ba. Nan ta bawa Yusra umarni ta kaiwa Anisa ta ajiye a kicin. Ta gyara kwanciyarta ta kara muryar rediyonta yayinda su kuma yaran suka fito tsakar gida suka cigaba da hidimominsu.
_

Bayan Sallah da sati daya su Aisha suka dawo Nigeria; tayi sallah kuma tayi addu a a kan Allah ya karya wannan kulli da aka yi tsakaninta da mijinta, sannan kuma ta roki Allah ya saka mata ko ma waye yake mata wannan zaluncin kuma Allah ya toni asirin me yi mata hakan.

Tabbas ta sami natsuwa kuma ta dawo da wani sabon karsashi na zaman jiran lokacin da wannan asirin zai karye, in Sha Allahu ko zata rabu da Yusuf to ba yanzu ba sai dai idan ya dawo hayyacinsa yace ta tafi to tabbas a lokacin zata tafi.

Kwanansu biyar da dawowa Aisha tana hutawa a gidan Hajiya; an dauko su Abdallah duka ta basu tsarabarsu har sun je gidan  yanuwanta yawon zumunci.

Suna zaune a rumfar da take farfajiyar gidan suna hirarrakinsu, Hajiya ce a kashingide a kan tabarma yayinda Anti Uwani ke zaune a kusa da ita. Ranar laraba ce don haka Farha da Abdallah suna islamiyya. Aisha ta fito daga cikin gidan bayan tayi musu sannu da hutawa ta zauna a kusa da Anti Uwani. Bata dade da zama ba ta dubi Hajiya tace

 Hajiya gobe ni da su Abdallah zamu je gidan Yaya Zainab, daga nan zan dauko  yata ranar Juma a sai mu koma gida.

Sai da Hajiyan ta tashi zaune sannan ta bata amsa

 To Allah ya kaimu goben. Baku yi magana da Yayanki bane?

 Tun last week dai da yazo, ranar da muka je gidansa har muka taho bai dawo ba kuma da ya zo nan shekaranjiya bana nan, amma idan bai zo ba zan kirawoshi kafin mu tafi.

Tayi gyaran murya tace

 Uhm! To ai munyi magana ba zaki koma gidan Yusufa ba tunda ko kin koma dake da wadda bata da miji duk daya kuke. Ki zauna a nan, ba zamu kashe miki aure ba, duk lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya zo ya daukeki ku koma.
Tuni idonta ya cicciko da kwalla tace

 Hajiya don& .

 Ba shawara na zauna yi dake ba, idan ke baki san ciwon kanki ba mu muna kishinki. Na gama magana babu inda zaki koma har sai Yusufa ya zo nan da kanshi sai ku tafi.

Da kyar ta bude bakinta tace

 To.

Ta tashi jikihta babu kwari ta koma cikin gidan, kai tsaye dakin Anti Uwani ta wuce ta fada kan gado ta sa kuka.

Tana shigewa Anti Uwani ta dubi Hajiya tace

 Yaya don Allah ku bar maganar nan, ku bar yarinyar nan ta koma gidanta tunda ita ta ji ta gani. Idan tana can ma sai tafi dagewa da addu a amma yanzu idan an rike ta a nan ba zata nutsu ba tunda ta fi son can din. Idan babu hali ma ni sai na koma can na dinga tayata zaman zuwa lokacin da komai zai warware.

 Uwani ki kyaleta, ai ba sallamarta mukayi ba kawai don mun mata aure.

 Ni dai Yaya gaskiya ki barta ta koma, shima Abubakar din zai zo ya same ni.

Bata saurari Hajiyan ba ta tashi ta bi bayan Aishan.

Kai tsaye dakinta ta wuce don ta san a nan ne zata sameta. Ta zauna a gefen gadon ta dafa bayan Aishan tace

 Yi hakuri Shatu, Abubakar din zai zo ya same ni. Wannan abun ba komai bane face jarrabawa kuma da izinin Allah zai wuce, mu da muka je har kasa mai tsarki muka roki Allah a kan wannan lamarin ai ya kamata a ce mu barki ki zauna a dakinki zuwa lokacin da komai zai warware.

Ta share kwallarta da zanin gadon ta mayar da kanta ta kwantar a kan cinyar Anti Uwani sannan tace

 Gara na zauna a can ni dai, kuma ina ji a jikina wannan matsalar ta kusa zuwa karshe in Sha Allah. Kuma Anti Uwani ita matarsa so take na bar gidan kin ga yanzu idan ta bude ido taga bana nan ai ta ci nasara ko?

 Kada ki damu ki cigaba da shiri in Sha Allahu don ranar Juma ar zaki koma, idan ma sun ki saurarata har gidan baffanki zan je na kirawoshi ya mayar dake don na san ba zai goyi bayan wannan aika-aikar ba.

Haka ta dauki lokaci tana lallashinta.
& & & ..

Washegari da yamma suna zaune sai ga Baffa, Suhail ne babban yaronsa ya kawo shi saboda shi tun tuni ya hakura da tuki saboda baya gani sosai daga nesa, don haka idan zai fita sai ya jira yara.

Bayan sun gaisa da Hajiya da Anti Uwani yace

 Kwana biyu, kin san idona ya ki ina ta so nazo na ganku to yara duk kowa ya bazama nema babu lokaci.

Tace

 Babu komai Baffa, ai dama komai lokacine. Allah ya kara lafiya ya ja kwana.

 Amin ya Allah.

Suna nan zaune suna hirarrakinsu Aisha da su Abdallah suka shigo, sun dawo daga gidan Anti Zainab.

Bayan ta gaida Baffa yace

 Yanzu kika zo Shatu da magaribar nan, ba kya gudun kiyi dare a hanya? Ya maigidan naki? Ina fatan dai komai ya warware.

Ta sunkuyar da kai tace

 Lafiya kalau.

Anti Uwani tace

 Ai tunda muka dawo daga Umra dama bata tafi ba.

 Garin yaya? Ina fatan dai ba matsalar nan ce ba.

Hajiya tace

 Itace dai har yanzu babu wani cigaba, don shi yasa ma nace ta zauna a nan idan ya dawo hayyacinsa ya zo su tafi.

Da mamaki Baffa yace

 Ikon Allah! Ko da yake malamin da na sa yake addu a ya gaya min abun zai iya daukar lokaci amma komai daren dadewa zai yi karshe.

Ya kalli Aishan yace

 Shatu da kinyi hakuri kinyi zamanki a can tunda ance min an baki mai tayaki kwana, jarrabawa ce ta ubangiji kuma idan kina can din ai sai abun ya fi saurin warwarewa.

Ta sunkuyar da kai, Anti Uwani tace

 To ai Yayan ce ta hanata komawa ita da Abubakar, amma ita ai tana son ta koma gidanta kuma nima na goyi da bayan hakan an dai fi karfinmu ne kawai.

Baffa ya kalli Hajiya yace

 Gaskiya a barta ta koma Hajiya, ai hakuri akeyi. Kuma wannan abun in Sha Allah zai warware in Sha Allah.

Ya kalli Aisha yace

 Ki koma Shatu kiyi zamanki, sai dai idan shine yace ki tafi to tabbas muma ba zamu barki ki zauna ba. Amma yanzu hakuri zakiyi ki zauna gaba daya mu cigaba da addu a.

Anti Uwani tace
 Dama gobe tace zata koma, tunda an yi haka in Sha Allahu goben sai muje na rakasu ita da Amiran.

Baffa ya dubi Hajiya yace

 Ayi hakuri Hajiya in Sha Allah komai zai wuce.

 Um,shikenan Baffa. Dama gani nayi tana can tana zama kamar me zaman kanta shi yasa nace ta dawo gida, amma in Sha Allah goben zata koma.

 Yauwa.

Aishan ta tashi ta wuce daki inda su Abdallah suke can suna wasansu.

Hajiya da Anti Uwani kuma da Baffa suka karasa hirarrakinsu, sai dab da magriba Baffa yayi musu sallama ya tafi.
Yana fita Hajiya ta dubi Anti Uwani tace

 Kun sami yanda kuke so ai sai kije ku fara shiri ke da  yar taki ko?

Ta mike tana dariya tace

 Eh, bari muje mu hada kayanmu ai zaman aure ba wasa bane kuma kowa da jarrabawarsa.

Ta wuce daki tana dariya.

Cikin daren nan Anti Uwani ta taya Aisha suka hada kayanta. Washe gari Juma a wajen karfe goma suka kama hanya tare da Anti Uwanin suka tsaya suka dauki Amira sannan suka wuce.

Sai da suka gama gyara gidan tsaf sannan Anti Uwani ta hau mota ta koma gidan Hajiya, ta bar Aisha da Amira.

Gaba daya Aisha ta manta basu siyo burodin karin kumallo ba gashi kuma basu da indomie a gidan. Don haka da safe wajen karfe takwas da rabi Aisha ta bawa Amira kudi ta siyo musu burodi da kwai su karya.

Tana fitowa daga gate din gidan su kuma su Yusra sun fito daga gidansu zasu tafi tahfiz don ranar aka koma hutu. Yusra ta balla mata harara, ita kuwa tayi dariya ta dagowa Rukayya hannu wadda ta mayar mata da murmushi ta daga mata hannu itama. Ta wuce ta barsu a nan Yusra tana ta faman hararar Rukayya.
--------

Tun bayan da ta haifi Sumayya bata sake yin wani tsarin iyali ba, ba wai ta damu da haihuwar bane amma tabbas a halin yanzu idan ta zo ba zata Hana ba. Duk da har yanzu Aisha bata haihu ba amma dai tana so ta haifi da namiji sannan Kuma tana so ta cika gidan da  yaya.

Tun cikin azumi take jin jikinta babu dadi, lokacin da ya kamata tayi al ada har ya wuce bata sha azumi ko daya ba don haka zuwa yanzu tana da yakinin ciki ne da ita. Lafiya kalau take daukar ciki ta haihu don haka ta yanke shawarar ba zata je asibiti ba har sai cikin yayi wata hudu, zuwa lokacin idan aka yi scanning za a iya gaya mata mace ne ko namiji.

Tun kafin yaran su tafi tahfiz Jummai ta zo, don haka suma tafiya ta sallami Jummai da ayyukan da zata yi mata ta haye sama ta kwanta a dakinta. Bata Dade da kwanciya ba Shima Abban yayi mata sallama ya wuce gidan Hajiya.

Yana fita bacci ya kwasheta.

Bata farka daga wannan baccin ba sai wajen Sha biyu da kwata lokacin da yara suka dawo daga tahfiz wanda shigar Sumayya da Ummi dakin shine ya farkar da ita. Bayan sun gama yi mata sannu da gida tace su sauko wajen Jummai su ci abinci sannan su kunna TV suyi kallo. Suna fita daga dakin ragowar yaran ma suka shigo sukayi mata sannu da gida sannan suka fice
Yusra ce ta karshen shigowa ta sami waje a gefen gadon ta zauna, ta dubi Mommy din wadda har yanzu take kwance tace

 Mommy kika ce matar Abba ta tafi?

Cikin halin ko in kula tace

 Eh, tun cikin azumi ma kuwa.

 To gaskiya Mommy ko dai bata tafi ba ko kuma ta dawo don gaskiya yau na wannan mara kunyar  yar tata ta fito daga gidan, don har hannu ma ta dagowa Rukayya.

Ta tashi zaune ta kalli Yusra yayinda mamaki ya bayyana a fuskarta

 Ikon Allah, to dama tana nan ko kuwa dawowa tayi?

 Ina ga dai Mommy azumi taje tayi a gida shine ta dawo.

Ta jijjiga kai

 Um! To shikenan idan kin sake ganin motsi a gidan kiyi min magana.

Ta amsa sannan ta tashi ta fice daga dakin.

Duk da Yusra ta san cewa uwarta tana bin malamai amma bata san itace tayi abinda Abba ya daina kula Aisha ba, ba wai ta dauka bin malaman kuskure bane. Hasali ma a wajenta shine dai-dai tunda Mommy tace tsari ne ake nema musu. Lokacin da taga Abba ya daina kula Aisha tayi zaton asirin da Mommy tace musu ta yiwa Abban ne ya karye shi yasa ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ya manta da ita, don haka yanzu da ta ganta tsoro take ji kada ta sake yiwa Abbansu wani asirin duk da ta san Mommy a tsaye take a kansu.
Yusra tana fita daga dakin ta gyara zama ta kafa tagumi; Aishan nan wai me take nufi ne? Kusan shekara guda miji baya zuwa inda kike amma kin ki fita daga rayuwarsa? Wannan din wanne irin naci ne?

39 / 58