Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   50 / 58

147K to 150K   out of 172.2K words



 -----
Washegari ranar Lahadi haka ta wuni zuciyarta babu sukuni saboda waccan maganar da take mata yawo a rai. Ta so ace ta je islamiyya da ta tambayi malamarasu ko akwai wani hadisi ko aya da zasu sa dole ta rike masa yaran da ba ita ta haifa ba, amma saboda rasuwar ta bari sai wani satin zata koma islamiyya.

Tuk kafin azahar Abban ya kirawota ya sanar da ita ta ajiye masa abincin rana don haka nan da nan ta dafa taliya da miyar kifi ta jera a table, sannan ta hada zobo ta saka a fridge.

Sai wajen karfe uku ya shigo, yana shigowa ta sa masa abincin. Sai da yaci ya koshi don kusan tunda akayi rasuwar nan bai zauna ya ci abinci ya koshi ba sai yanzu. Da aka kirawo sallar la'asar ya fita masallaci, bayan ya dawo yace mata zai yi bacci ne kada a tasheshi. Yana shirin shigewa dakin tayi gyaran murya tace

 'Nima ina son zuwa gidan Hajiya, ko naje in ya so sai na dawo kafin magriba?

'Eh, sai kin dawo. Lafiya Hajiyan take dai ko?

'Lafiya kalau, na ga su Yaya Zainab ne kawai suka zo gaisuwa babu ita duk da na san gwiwarta tana ciwo amma dai munyi waya da ita. Ina so dai naje na gani.

'To babu laifi, ki gaishe min da ita da su Abdallah.

Ya shige dakin yayinda ita kuma ta mike ta shige nata dakin domin ta shirya.

& & ..

Tana shiga gidan Hajiya ta tarar da Anti Uwani da Zahida suna zaune a falo suna hira. Bayan sun gaisa ta dubi Zahida tace

'Ke kuma me kike a gidan mutane da yamman nan?

Tayi dariya

'Ke zan tambaya, ku da kuke zaman makoki.

'Hmmn! Ai an share makokin ma. Ina Hajiya da yaran na ji shiru?

Anti Uwani tace

'Hajiya tana daki, inaga bata idar da azkar ba shi yasa bata fito ba. Yaran kuma Abban Afra ne ya fita dasu wai zasu je sayen kaya za ayi kaltaran menene a makaranta.

Zahida tayi dariya tace

'Cultural day fa ake cewa Anti Uwani.'
Ta kawar da kai tace

'Oho duk daya.

Ta juya wajen Aisha tace

'Ya marayun  yayan naki? Kuna lafiya ko?

 Lafiya Alhamdulillah.

Jimawa kadan ta mike ta shiga daki wajen Hajiya.

A zaune ta sameta a kan dadduma da kafafunta a mike, bayan sun gaisa tayi mata ya jiki suka dan taba hira sannan ta taso ta dawo falon. Bata dade da zama ba Anti Uwani ta tashi ta shige dakin da Hajiya take.

Anti Uwani tana shigewa Zahida ta taso ta dawo kusa da Aisha, tana zama Aishan ta dubeta tace

'Kin shako gulma kenan bakinki yake motsi.

Ta zumbura baki tace

'Oh ni, wai na sake jajanta miki rasuwar yayarki.

 Sai dai yayarki ba ni ba.

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan cikin murya me dauke da damuwa tace

'Hida kin san me Abban Sadik yace?

Ta dan zaro ido ta gyara zama tace

'Me yace?

'Wai na tashi daga gidan da nake na koma gidan Zahra saboda yara.

Da mamaki Zahida tace

'To da me kike tunani? Ai ko wanene ma haka zai yi tunda kinga wancan nasa ne kuma yanzu bashi da wata mata a ciki.

'Hmm! Baki gane ba Zahida. Nifa ba zan iya zama da yaransa ba gaskiya, ba wai ina nufin dukansu ba a'a. Idan aka dauke Yusra da Nana to bani da matsala da sauran yaran. Amma ba zan iya zama da Yusra ba, ke ko gwadawa ma ba zan yi ba sai dai ayi min duk abinda za ayi Amma ba zan zauna da Yusra ba.

Mamakin Zahida ya karu, tace

'Yusran wai zata kai shekara nawa ne da kike tsoronta har haka?

 Sha takwas ne idan tayi yawa sha tara. Ba wai tsoronta nake ji ba amma Zahida yarinyar nan tabbas idan ta sami dama zata iya poisoning dina na mutu. Ko bata kashe ni ba kuma ba zata taba bari mu zauna lafiya da ubanta ba, nutsuwar da yake son samu ba zai samu ba. Kinga kuma duk abinda ya faru da shi da duk masu kallo cewa za ayi ina musgunawa marayu.

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan ta cigaba

'Zahida kin san dai tunda na auri mutumin nan uwar Yusra bata barni na yi rayuwar aure ta shekara daya ba tare da wata matsala ba ko, to wallahi wannan yarinyar ta fi uwarta sharri. Kuma da bakinta ta tare ni ta gaya min ba zata taba bari na zauna lafiya ba muddin na tare a gidansu. To ba wai ina jin tsoron abinda zata yi bane ina jin tsoron kada ta kureni na ce zan rama don ramuwar tawa ba zatayi kyau ba, gara kawai kar a fara.

'To yanzu ya zaki yi? Tunda dai shi ga abinda yace.

'Ban sani ba Zahida, don ban ma gaya masa ba zan koma ba. Ce masa kawai nayi sai ma gama shiryawa, amma tabbas ba zan zauna da Yusra ba.

'Ai kuwa akwai rigima tunda dai kin san ko sakin uwarsu yayi kece zaki rike yaran nan balle mutuwa tayi.

Aisha ta dan zaro ido ta gatsina baki tace

'To wa ya dora min? Ai babu inda Allah yace dole sai na rike masa yaran da bani na haifa masa ba don kawai Ina aurensa. Don haka sai dai ayi duk wacce za ayi.

Zahida ta jijjiga kai tace

'Ai kuwa akwai rigima.

A dai-dai nan Abdul da Farha suka shigo tare da Abban Afra suna rike da ledodi. Nan suka zube kayan suna nunawa mamansu yayinda shi kuma Abban Afra ya sanar da Zahida ta gayawa Hajiya zasu tafi.

Ba tare da bata lokaci ba Hajiyan ta fito tare da Anti Uwani suka yi musu sallama suka tafi. Suna fita itama Aisha ta mike tana shirin tafiya, Hajiya tace

'Au dama lekomu kawai kikayi? Ba dadewa zakiyi ba.

'Wallahi Hajiya gani nayi baki sami zuwa gaisuwa ba shine nace bari na zo na duba kafar, ko abincin dare ma ban yi ba.

 Ga kafa nan dai yanda kika barta. Gara kam ki tafi tunda yanzu gida ya zama ke da yara kar ki dinga lattin abinci.

Tayi musu sallama ta fice, tana tunanin maganar Hajiya. Wato su sun ma zata ta tare da yaran ne ko me, don taga kowa maganar yaran kawai yake mata kamar yanzu itace uwarsu.

Tana shiga gidan aka fara kiran Magriba, ta leka dakin Abban ta hangoshi yana nan yana bacci. Don haka ta karasa ta tasheshi saboda magriba. Tana yin Sallah ta fada kicin, nan da nan ta tuka tuwon semovita miyar kuka wadda ta sha busasshen kifi da nama. Ta hada ta ajiye a kan table sannan ta shiga wanka.
Bayan ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta zauna tana jiransa. Karfe tara saura ta kalli agogon, har yanzu bai shigo ba? To ko ba zai ci abincin bane? Ta sake kallon wayarta sannan ta mayar da ita ta ajiye. Bata son ta kirawoshi domin bai saba ce mata zai dawo ya saba ba, ta san ba lallai ya kwana a wajenta ba domin tunda akayi rasuwar a can yake kwana kuma bata da matsala da hakan amma dai ta kasa gane dalilin da zai sakata ta dafa abinci kuma yaki zuwa. Har ta gaji da karatun wasikar jaki bai shigo ba don haka ta zuba abincinta ta fara ci.

Ko rabin abincin bata ci ba ta jiyo motsinsa a gate, ba tare da bata lokaci ba ya shigo falon da sallama. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubeta yana murmushi yace

'An gaji da jirana ko?

Ta yi gajeran murmushi

'Yunwa nake ji shi yasa.

Ta fara kokarin mikewa ya dakatar da ita yayinda ya ajiye wayar hannunsa da mukullai a kan kujera ya nufi dining table yana fadin

 Yi zamanki ki gama zan zubo abincin, nima yunwa nake ji.

Ta cigaba da cin abincinta yayinda shima ya zubo abincin a faranti ya dawo inda take ya zauna suna ci suna hira. Bayan sun gama cin abincin ta hada kwanukan ta kwashe sannan ta kawo masa shayi, ta zauna suka cigaba da hira.

Wajen sha daya saura ta mike tana hamma tace

'Ni kam bari naje na kwanta idan zaka fita kayi min magana wallahi bacci nake ji.

Ba tare da ya kalleta ba yace

'A nan zan kwana ai, nima yanzu zan shigo.

Da mamaki tace

'Yaran fa?

'Ai Goggo Binta tana nan, sai jibi ne zata tafi. Ina tunanin ma na lallabata ta kara mana ko sati ne kafin nan kin gama shiryawa tunda kin ga idan tace dole jibi zata tafi to fa ko baki shirya ba dole ki koma can din in ya so a dinga kwashe kayan a hankali.

Tace

'Uhm! To sai ka shigo.

Ta shige dakin ta barshi a zaune.

Haka ta karasa shiryawa cikin sanyin jiki domin idan aka ce jibi zata koma gidan Zahra to tabbas akwai rigima don ba zata koma ba. Gashi ta rasa da kalaman da zata yi masa bayanin cewa ba zata koma ba don ta san ba zai fahimceta ba; a halin yanzu ma bata jin akwai wanda zai fahimceta. A iya shekarun da tayi a rayuwa ta ga matan aure da dama wadanda yaran miji ke hanasu zaman aure wadanda ba a taba yi musu adalci, bata jin nata labarin zai babanta. Wani lokacin sai taji kamar ta koma ta fara zama da su ta gani ko zaman zai yiwu, amma zuciyarta tana tuna mata idan ta fara sai ta fi shan wahalar bari don haka gara ma kawai kada ta fara.

Tana nan kwance tana karanta wasikar jaki ya shiga dakin ya sameta. Ba tare da wani bata lokaci ba ya shirya ya cimmata a kan gadon, lokacin har ta fara gyangyadi. Sai dai da yake ta san bukatar da ta kawoshi kuma ita din ma tayi kewarsa haka ta biye masa suna raba dare suna biyan bashi.

_

Tun kafin Abban ya sanar da Aisha zata koma gidan Zahra ya sanar da Jummai. Ya bata umarni a fitar da duk wasu kayan da suke dakin Saddiku ya kwashe ya kai gareji a gyara dakin don nan Aisha zata zauna kafin a gyara mata daki a sama. Nan da nan ba tare da bata lokaci da ta shiga aiki.

Tunda Rukayya taji wannan labarin ta kasa boye murnar ta, do da kanta ta dinga taya Jummai fitar da kayan dakin nan har aka gama. Yusra tana kallonsu tana kwafa musamman ya da taga????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  Rukayyan tana ta rawar jiki.

Ranar litinin wadda tayi dai-dai da kwana shida da mutuwa ranar Abba ya umarci yara da suyi hakuri su koma makaranta. Musamman Aisha ta tashi da safe ta dafa musu abincin makaranta sannan tayiwa Abban waya ya turo Rukayya ta daukar musu. Haka ta zuzzuba musu kowa ya dauki nasa in banda Nana wadda tace ita indomie zata dafa.

Tun wuri Yusra ta dawo daga tata makarantar don haka ko da sauran yaran suka dawo wajen karfe biyu da rabi a gidan suka sameta. Bayan sun ci abinci Jummai ta taimakawa Nana, Ummi da Sumayya suka shirya suka wuce islamiyya. Basu dade da fita ba Rukayya ta shiga dakinsu na kasa inda ta sami Yusra a kashingide a kan gadonsu tana chatting a waya. Kai tsaye ta nufi wajen da ta ajiye jakar makarantar ta ta bude ta fara zaro littafanta. Yusra ta dubeta tace

'Ke bazaki islamiyyar bane?

Ba tare da ta dubeta ba tace
'Eh, sai next week idan mun gama CA test a makarantar, yanzu ma karatu zan je nayi a gidan Anti sai dare zan dawo.

Yusran ta tashi zaune a kan gadon a dai-dai lokacin da Rukayyan ta mayar da jakar ta rufe ta mike da litattafai a hannunta tana shirin ficewa daga dakin.

Yusran tace

'Kuma karatun ne ba zaki iya yi a nan ba duk fadin gidan nan dole sai kin je gidan da aka hanaki zuwa.

Cikin halin ko in kula tace

'Eh, a can zan yi karatun sai dare zan dawo.

'Lallai! Wato ke tun kafin ma Mommy ta kwana bakwai da barin duniya har kin fara karya dokokin da ta kafa miki ko, kamar daman jira kikeyi ta mutu ki koma inda ta hanaki zuwa.

Cak ta tsaya a inda take ta juyo ta kalli Yusran yayinda idanuwanta suka cicciko da kwalla; kalaman yayar tata sun yi matukar yi mata ciwo a zuciya sai dai bata da wata amsa da zata iya bata. Ta ja hijabin jikinta ta goge kwallar da ta fado fuskarta ta juya ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin. Tana fita ta tsaya a bayan kofar ta rasa me zata yi; tafiya zata yi kamar yanda tayi niyya ko kuwa ta hakura ta zauna a nan tayi karatun? Sai dai ta san idan ta zauna a gidan to da zarar Sumayya ta dawo daga islamiyya karatun ya kare. Domin a wajenta take zama kuma ko me take bukata haka Yusra zata ce taje Rukayya tayi mata.

Ta share hawayenta ta wuce tsakar gida inda ta jiyo motsin Goggo Binta da Jummai, ta sanar da su ta tafi gidan Anti Aisha sannan ta wuce cike da damuwa.
& & &

Yanda Aishan ta ganta cikin damuwa ya sa ta zata damuwar rasuwar ce don haka ta saka ta a gaba ta dinga bata baki tana yi mata nasiha har ta samu ta sami natsuwa. Ta sakata a gaba ta fara karatun wanda kusan tare suka yi shi.

Sai da akayi kiran Magriba tayi sallah taci abinci sannan ta koma gidan. Bata kula Yusra ba har dare yayi suka kwanta.

& & & .

Ranar Talata da safe kamar yanda Abba ya saba bayan ya shirya zai fita aiki ya tsaya a falo wajen Goggo Binta domin ya gaisheta. Bayan sun gaisa ta sanar da shi cewa gobe zata tafi, ba zata sami damar kara kwana ba. Sai dai tayi masa alkawarin idan an kwana biyu zata dawo. Nan ya nuna mata babu damuwa goben idan ta shirya Malam Ali zai kaita har can Sumaila shi da Saddiku, ya tabbatar mata da cewa kafin ma ta tafi Aishan zata dawo gidan.

Yayi mata sallama ya fice aiki.

Ya san Asiha ta riga tafi aiki don haka sai bayan da ya zauna a office sannan ya dauki waya ya kirawota, ya sanar da ita ya kamata da ta koma gida ta hada kayanta don daga yau zuwa gobe da safe yake so ta koma gidan Zahra saboda Goggo Binta zata tafi.

Bata iya ce masa komai ba sai dai tace masa idan ya dawo sayi maganar.

Sukayi sallama suka ajiye waya.

Haka ta karasa wunin ta a makaranta tana tunani rigimar da za ayi domin ita abu daya ta sani; ba zata zauna da Yusra da Nana ba domin Nana duk abinda Yusra ta sakata shi take yi.

__

Tun bayan rasuwar Zahra da Yaya Murja ta koma gida take tunanin makomar yaran. Ta yi tunanin Abba zai sa Aisha ta dawo gidan domin kula da su to amma hakan bai kwanta mata a rai ba. Bata san Aisha sosai ba sai ta hannun Zahra, a iya wannan sanin kuma bata taba jin wani alkhairi a kan Aishan ba. Hasali ma Zahran ta nuna musu cewa Aisha tana da sharri sannan kuma tana bin malamai sosai don ta mallake gidan. Don haka take jin bai kamata a bar ta da yaran ba sai dai idan hakan shi kadai ne zabinsu. Tana da labarai da yawa na irin haka yanda matar uba take mayar da yara kalar tausayi saboda rashin uwa kuma zata yi iya yinta ta tabbatar hakan bai faru da yaran Zahra ba; duk da ta san abu ne maii tsananin wahala.

Sun yi waya ta san gobe Goggo Binta zata tafi don haka yau ta tashi da niyyar zuwa gidan suyi sallama. Gidan Suwaiba ta fara zuwa don su tafi tare.

A dakin Suwaiban suka zauna ita Suwaiban tana canza kaya suna hira. Cikin damuwa Yaya Murja tacewa Suwaiban

 Jiya da mukayi waya da Yusra tace Abbansu yace Aisha zata koma gidan amma dakin kasa ya sa a gyara mata.

Suwaiba tace
'To Yaya ai idan ma dakin Ya Zahran yace ta shiga ba wani abu bane, na san ma hakan za ayi. Watakila dai yana jira ne ya sami lokaci a kwashe kayan a raba tun da ko ana so ko ba a so kayan da suke nata ne sun zama na magada.

'Hakane. To ni zaman nake ji; kin san fa duk labaran da muke ji a kanta ba masu dadi bane, kamar dai daga abubuwan da Zahran take fada matar tana da fitna ga sharri.

Suwaiban ta dawo ta zauna kusa da ita a gefen gado ta fuskanceta tace

'To Yaya mu ya zamuyi? 'Yaya dai nashi ne don haka yanda yake so haka zai yi da su. Don kuwa kin san babu makawa ita zai bawa rikon yaran nan wanda hakan shine daidai.

Cikin damuwa Yaya Murja tace

'Hakane. Ni da tunanina ko ayi masa magana idan ba damuwa ya auri Rahama, kinga dama ta saba zama da yaran shi kuma ya saba zama da mata biyu shikenan sai ta rike yaran  yar uwarta.

Ta dan zaro ido

'Yaya kada fa ki manta shi ba dan uwanmu bane don haka bamu da uko da shi, kuma ita Rahman idan bata yarda ba fa?

'Ai ba mu zamu yi masa magana ba, idan muka kaiwa Baffa shawara su sai su shawarceshi. Ita kuma Rahma ni bana ma jinta; ya za ayi taki yarda ma? Kalli fa shekarun da ta dauka babu aure, ai ina ga ko musu ba zata yi ba tunda ko babu komai ta san ba zata je gidan Zahra ta sha wahala ba.

'Hmm! Kada dai ki ballo ruwa Yaya.'

Ta mike ta saka hijabinta tana fadin

'Mu tafi Yaya don ina son na dawo kafin  yan makaranta su dawo.

Suka fice suka nufi gidan Zahra.

Lokacin da suka je gidan yaran duka suna makaranta sai Goggo da Jummai, suna nan zaune a falon kasa suna gaisawa Saddiku ya fito a shirye. Bayan sun gaisa suka

50 / 58