Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 58

57K to 60K   out of 172.2K words

Wayarsa ce da take ajiye a gefensa ta dauki waka, saida ta dan yi dogon wuya ta leko screen din kafin ya dauke wayar. Sunan A eesh ne ya fito a kan screen din wanda ta san Aisha ce, don haka ta kara nutsuwa ta tada kunnuwanta ko zata tsinci wani abun.

Yana dauka bayan sun gaisa tace

 Yaya Abubakar ne yazo shine yake tambayarka.

 An kawo motar kenan?

 Eh, an kawo.'

 To ma sha Allahu. Bari na dauko tukwici na taho.

Suka ajiye waya ya mike yana dariya.

Ta dubeshi tace

 Tukwicin me kuma zaka bayar?

Da fara arsa yace

 Aisha ce ta sayi mota shine aka kawo mata, ai kinga dole na bayarda tukwici.

Kafin tace wani abu ya shige dakinsa ya barta a zaune.

Tana nan zaune ya fito daga dakin a shirye yayi mata sallama ya fice.

Tabi bayansa da harara har tana kwafa; wato mota ma ya sayawa Aisha kenan? Bayan ta bashi hakuri kuma tana kallo yana zuwa yana kaita aiki yana daukota shine zai saya mata mota ita kuma ta barta da Malam Sule? Tabbas yau za ayi bala i don bazata yarda ba. Ai tun kafin ya auri Aisha take lallabarsa ya saya mata mota amma kullum yana shirya mata zance don haka wallahi dole ma ya zo yaji bayaninta.
& & & ..

A tsakar gidan ya samesu a tsaye da Yaya Abubakar din da kuma Yaya Zainab suna ta duba motar; baka ce kirar Honda Accord ta zamani sai sheki takeyi. Kudin da Aishan ta tura masa naira miliyan dayane da dubu dari ta san bazasu sayi wannan motar ba don haka tana tsaye ta rike hannun Yaya Abubakar din sai faman tsalle take ta kasa tsayuwa guri daya saboda tsabar murna. Ko shi ma Abban da yaga motar yayi mamaki don bai yi zaton Aisha tana da kudin da zata iya sayen wannan motar ba.

Ya karasa suka gaisa sannan ya ja hannun Abubakar suka koma falo, ta kawo musu lemo da cake sannan ta ja Zainab suka dawo wajen motar. Zainab ta dubeta tace

 Allah ya sa dai baki manta tuki ba, don fa tun rasuwar Abban su Abdallah rabonki da tuki.
 Ban manta ba, kuma shima yace zamu dan fita tare na kwana biyu ya tuna min kafin na fara fita ni kadai.

Suka dan taba hira sannan sukayi sallama, Abban Sadik ya kawo naira dubu ashirin sababbi kar ya bawa Zainab yace tayi tukwici.

Nan suka bar Aisha ita da Abba tana ta murna ta kasa barin wajen motar.

Saida aka fara kiran Magriba sannan ya fita masallaci daga can ya koma gidan Zahra tunda dama kwananta ne.

Tunda ya shiga gidan ya kula da yanayinta ya san a kan taji ya ambaci mota ne, don haka shima ya shirya mata. Ta riga ta fara bayyana masa halayenta don haka yanzu kwata-kwata ba zai sake saurara mata ba.

Ta so ta danne ta bari sai yaje sunyi sallama da Aisha idan ya dawo sai ta tada maganar amma ta kasa hakuri.

A zaune suke a falon sama suna cin abincin dare, tuwon ne miyar kubewa danya tayi. Gaba daya hankalinsa yana kan abincin yayinda ita kuma take yafutar abincin tana satar kallonsa. Ta dai kasa daurewa tace

 Wai ni dazu mota ka siya ne naji kana zaka bada tukwici, ban fahimci zancen ba.

Ya hadiye lomar da take bakinsa ya mayar da cokalin cikin kwanon sannan ya dubeta yace

 Bakiji me nace miki ba dazun, Aisha ce ta sayi mota shine Yayyanta suka kawo mata. To kinga ai dole na bada tukwici tunda an kawo mana abun arziki.

Ta ajiye cokalin da take tsikarar tuwon da shi tace

 Ban gane Aisha ta sayi mota ba, ko dai ka saya mata mota?

 Ni ban saya mata mota ba, idan da na saya mata ai tare zan saya muku. Ita da kudinta ta sayi mota sai dai ko idan Yayan nata yayi mata ciko don shima yana da dukiya sosai.

Ta kalleshi yana ta faman zura lomar tuwonsa ba tare da wata damuwa, ta kare masa harara sannan tace

 Kana nufin kace min albashin malamin makarantar ne ya sayi mota? Koko dai kana nufin kace min kun hada baki ka saya mata mota don kayi min wulakanci.

Sai da ya kalleta suka hada ido sannan ya kai lomar tuwonsa, ya ture kwanon ya sha ruwa sannan ya sake dubanta yace

 Ni ban saya mata mota ba domin idan na saya mata mota zan gaya miki don baki isa nayi miki karya ba, Aisha ta siya mota. Idan baki manta ba lokacin da kike ikirarin ta aureni saboda kudina na gaya miki ba haka bane don itama nan da kike gani mai kudin kantace, abun duniya ne bai dameta ba shiyasa kika ga tana rayuwarta haka.

 To naji mai kudi ta sayi mota, ni yanzu ya zakayi dani?

 Yanda na saba yi dake mana! Naga ga Malam Sule nan wanda dama kin hanashi yayi aikinta, kinga yanzu hankalinki kwance iya ke kadai da  yayanki Malam Sule zai dinga yiwa hidima. Ita idan na bata kudin mai sai ta kai kanta inda zata je.

Ta share kwalla

 Amma Abban Sadik tun yaushe nake maka magiyar ka saya min mota shine yanzu zaka zaga ka sayawa amaryarka kuma kazo kana ninkeni bai-bai ko!

Yayi tsaki ya mike tsaye sannan ya bata amsa

 Zahra! Bani na sayawa Aisha mota ba, ita ta saya. Ke kuma ba zan saya miki mota ba saboda na gaya miki bani da ra ayin matata ta ja mota na fi so na sa driver ya kaiku duk inda zakuje. Itama din da kin bari Malam Sule yana kaita inda zata da ba zan bari ta sayi mota ba to amma kin hanashi yayi mata aiki. Ba zan iya daukar mata wani driver din ba kuma ba zan iya barinta tana yawo a motar haya ba kamar yanda bana barinki don haka kinga dole na barta ta sayi mota da kanta ko zan samu na huta da kaita unguwa da daukota. Wannan din tsarinki ne ai tunda da alama haka kika fi so, amma ni babu wata mota da zan siya.

Kafin tace wani abu ya wuce ya barta a zaune.

Ta dauki lokaci tana zaune a wajen tana mamakin maganganusa, ita tunda take da shi ma bata taba tunani ya iya maganganu na tura haushi kamar haka ba.

Tayi kwafa ta mike ta wuce dakinta.

Haka ta kwana ita kadai a dakinta tana tunanin yanda zata bullowa lamarin nan; don tana son mota kuma ba zata taba bari ace kishiyarta tana da mota ita kuma bata da ita ba.
------

Tunda aka ce Aisha ta sayi motar nan Zahra ta kasa samun natsuwa, gashi bata son taja doguwar rigima da Abba tunda bata so ya bata mata shiri. Gaba daya ma yanzu zargi takeyi Abban yana kaiwa Aishan abubuwan da baya kawo mata, don haka a hankali ta samu take tura Yusra da Nana gidan don su gano mata abinda akeyi a gidan.

Aisha bata son suna shiga, musamman Yusra to amma babu yanda zatayi da su saboda gidan ubansu ne. Sai dai kawai idan suka shiga gidan sai ta sa mukulli ta kulle kicin dinta, dama basa shigar mata dakuna don haka suna falo itama sai ta zauna a dining table tana kula da motsin kowa. Basu cika dadewa ba saboda suma suna kula da yanda Aishan take kaffa kaffa da su.
& & & ..

Ranar Juma a ce don haka kamar yanda ta saba tana tashi daga aiki ta wuce ta dauki su Abdallah a makaranta suka je gidan Umma ta hado musu kayansu don gidanta zasuyi weekend.

Duk lokacin da sukayi irin wannan zuwan ta saba sai tayi musu cake ko wani snack, suci su koshi sannan su tafi da shi gidan Umma.

Tunda suka shiga mota yau Farha take mita

 Mama yau ki soya mana kaza da yawa, Umma bata soyawa kullum a miya take ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sawa ba dadi.

Abdallah da yake gaban mota yace

 Mama wallahi karyane, idan an dafa ma da dadi. Kullum fa idan Anti Uwani ta soya na sawa a miya sai ta bamu dai dai.

Tace

 To idan kun yarda na soya muku kaza amma fa ba zan yi muku cake ba, kun yarda?

Take suka hada baki sukace sun yarda.

Tana da kaza a gida amma wannan Abban Sadik ne ya siyo kuma miya takeyi da su tana yi musu peppersoup, don haka a hanya suka tsaya ta siyo kaji gidan gona manya guda hudu sannan suka wuce gidan.

Saida ta gama abinda takeyi wajen bayan la asar sannan ta shiga kicin din, nan da nan ta gyare kajin nan ta sulalasu sannan ta zauna ta fara suya.

Kafin ta kwashe suyar farko Yusra da Nana suka shigo tare da Rukayya. Bayan sun gaisheta duka suka zauna a falo suna kallon TV.

Wajen Rukayya Abdallah da Farha suka samu suka zauna sunata yi mata surutu domin sun saba da ita, ita kuwa Yusar saboda yanda take kyararsu basa ko zuwa kusa da ita. Tana yawan kiransu Agola, ko kuma tace da su sun zo cin arziki kullum sai dai Aishan tayi ta yi musu bayani tana basu hakuri.

Tana kwashe suyar farko ta zubo a tray ta kawo falon kowa a cikin yaran ya dauki guda suka kama ci, Yusra ce kawai tace ta koshi don haka ta koma da yanka dayan nata.

Nan da nan ta gama, tana cikin juyewa a tray don ya sha iska Abban Sadik ya shigo, bayan yaran sun gaisheshi ya wuce kicin inda ya jiyo motsinta.

 Hmm! Dabge ake mana ne nake jiyo kamshi tun daga kan kwana.

Tayi dariya tace

 Kaji ne nake soyawa yara, yau Farha tace basa son cake kaza suke so.

Ya karasa ya sa hannu ya dauka, ta bude fridge ta zuba masa zobo a kofi ta mika masa tana fadin

 Ga wannan a kora.

Ya karbi kofin a hannu daya daya hannun kuma yana dauke da naman da ya fara ci ya fice daga kicin din ya shige dakinsa.

Ta dauki dan faranti ta zuba masa naman ta fito don ta kai masa. Farha ta taso da gudu ta sha gabanta tana fadin

 Mama ki kara min, ki bani gizzard.

 To shiga gashi nan a tray ki dauki gizzard din.

Ta wuce daki yayinda Farha ta shige kicin din da gudu.

Tana shiga dakin ta wuce kan mudubi ta ajiye masa naman tana fadin

 Ga kari.

Ya mika hannu ya kara daukan yanka daya yana dariya yana fadin

 So kike ki cika min ciki idan ban ci abincin Yayarki ba ta hanani sukuni ko?

 Kada ka damu duka zaka cinye cikin ai danyar fata ce bata fashewa.

Sukayi dariya.

A daidai nan ta jiyo Farha ta tsandara ihu, da hanzari ta fito yayinda Abban ya rufo mata baya domin ihun bai yi kama da na lafiya ba.

Tana isowa falon Yusra da Nana suna ficewa suka mako kofar.

Ta karasa da sauri tsakiyar falon inda Farha ke tsaye tana shesshekar kuka Abdallah yana tsaye rungume da ita shima yana kwalla. Rukayya tana shafa kansu tana basu hakuri.

Da gudu Farha ta karasa jikin Aisha tana kara kuka rike da kumatunta, ta dauketa suka karasa kan kujera ta zauna ta dorata a cinya yayinda Abba ya tsaya a bayan kujerar.
Aisha tace

 Me ya faru Farha? Abdallah me aka yi mata?

Yana share kwalla yace

 Yusra ce ta mareta.

 Mari?

Sai a lokacin ta dagata ta duba kumatunta. Yayi jazur musamman da yake Farhan fara ce sosai, ga alamar yatsu nan a fuskar har kan kunnenta.

Ta sake rungumeta saboda yanda take kuka har jikinta yana rawa.

Ta dubi Rukayya tace

 Rukayya me ya faru ne? Har Yusra ta mareta?

Ta sunkuyar da kai cikin sanyi murya tace

 Ban kula ba ina jin dai bayan ta dauko naman ta zo wucewa ta takata shine ta mareta.

Abdallah yace

 Nima ta tureni saida na fadi na buge kaina, kuma tace mana shegu agololo  yan cin arziki.

Ya karasa jikin Aishan yana fadin

 Mama kawai ki mayar da mu gidan Umma, ai muma muna da gida ko?

Abban Sadik ya zagayo ya zauna ya ja Abdallah yana shafa kansa tana fadin

 Nan ma ai gidankune Abdallah kaji, bari naje naji yanzu zan gamu da Yusran.

Ya fice ya bi bayan Yusran.

Yana shiga ya samesu a falon kasa suna zaune da Mommy suna mayarda maganar.

Bayan ya amsa sannu da zuwansu yace

 Yusra me yasa kika mari Farha?

 Abba takani tayi, nayi mata magana tace min me siffar karuwai shi kuma Abdallah ya kawo min duka wai zai tare mata.

Mommy tace

 Kai daga jin wannan maganar ka san fada akeyi a gabanta tana ji tunda karamar yarinya kamar wannan ai bata kai ta san menene karuwa ba. Kuma idan banda cin fuska da wulakanci tana auren uban Yusra amma ta dinga ce mata me siffar karuwai, kawai saboda tana takamar ka daure mata ginda. Idan ita yaranta cikin gari suke rayuwa wadannan ai a nan muke da su cikin GRA a ina zasu koyi zagi irin wannan?

Ta mike ta haye sama ta barshi a nan.

Ya dubi Yusra yace

 Bana son karya Yusra, ita Farhan ce ta gaya miki haka?

 Wallahi Abba haka tace.

Nana tace

 Nima ina ji.

Ya zauna yana jinjina zancen; tabbas yaransa basu iya zagi ba kuma basu saba yi masa karya ba, amma gidan su Aisha a cikin gari yake unguwar kofar Nassarawa; duk da dai suna da rufin asirinsu amma ya san tabbas babu mamaki idan Farha ta iya zagin.

Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya tashi ya fice.

Yana fitowa daga gidan aka fara kiran sallar magriba don haka kawai sai ya wuce masallaci, sai da aka idar da Sallah sannan ya dawo ya shiga gidan Aishan.

Rukayya ce a falo ita kadai tana homework, bayan ya amsa sannu da zuwan da tayi masa ya wuce dakin Aishan inda ya hango fitila.

Tana zaune a kan dadduma da hijabi, da alama Sallah ta idar. Farha tana kwance a kan daddumar gefen Aishan yayinda Abdallah yake zaune a kusa da ita da alama tare suka idar da Sallar.

Ya karasa ya zauna a gafen gado, kallon da take masa kallone me cike da tuhuma domin tana so taji dalilin da yasa aka mari Farha.

Yayi gyaran murya yace

 Yusra tace Farha ce ta zageta, kin san su basu saba zagi ba shi yasa zata ji haushi har tayi over reacting. Kin san basu saba zagi ba mu a nan amma tace Farha tace mata me siffar karuwai, kinga wannan ai ko wa aka gayawa zai ji haushi. Ki dinga yi musu fada, itama Yusran nayi mata fada.

Cikin sanyin murya tace

 Toh.

Ta sunkuyar da kanta tana kallon daddumar da take kai, ya san ba zata sake yi masa magana ba don haka ya tashi ya fice daga dakin ya shiga dakinsa.

Mikewa tayi ta fara hada musu kayansu; gara ta mayar dasu inda ake kaunarsu. Ya za ayi ace Farha ta san karuwa kuma har yana wani fada yaransa basa zagi saboda nata yaran ne ba a musu tarbiyya don haka su suka iya zagi. Ba tun yau ba tana kula da yanda Yusra ta tsani Farha; shi kanshi Abban tana kula da yanda yake nuna kishinsa idan su Abdallah suka zo. Idan yaga tana hidimarsu ya dinga nuna kamar shi ta share shi kenan, gaba daya dai ta kula ya fi natsuwa idan basa nan.

Ta dai kau da kai ne ga abun saboda bata so aure ya rabata da yaranta; yanzun ma kuma bazata bari aure ya shiga tsakaninta da su ba.
Jimawa kadan ta gama hada musu kayansu ta janyo karamin akwatin ta fito falo yaran suna biye da ita. Ta ajiye akwatin a bakin kofa ta wuce kicin ta sami roba ta juyo kazar da ta soya musu tazo ta ajiye a kusa da akwatin. Ta shige dakin Abban tana rike da mukullin mota ta tsaya bayan ya amsa sallamarta tace

 Zan je na mayar da su Abdallah gida.

Ya tashi daga kashingiden da yayi ya dubeta da mamaki

 Daga dan wannan abun da ya faru, ki barsu su gama kwankinsu ranar Lahadi sa tafi. Yusra nayi mata fada ba zata sake dukan kowa ba.

 Babu komai, sun fi so su tafi. Zan mayar dasu din ai yanzu zan dawo.

Bai ga alamar zata fasa ba kuma baya son rigima da ita don haka yace

 Allah ya tsare, sai kiyi sauri kafin dare yayi sosai. Bari na taso na fice sai ki rufe gidan tunda ba nan zan kwana ba.

Kusan tare suka fito falon, ta dubi Rukayya tace

 Ki bi Abbanki Rukayya, idan na dawo zan masa waya sai ki dawo.

Sai da ya rufe mata gate sannan ya kama hannun Rukayya suka nufi gida. Yana mamakin irin wannan fushin na Aisha, ita idan akayi abu ko magana bata fiya son yi ba sai dai kawai ta yi shiru tayi ta faman fushi. Yanzu ya san sai ya kai sati yana lallabata kafin ta bari su dawo yanda suka saba.

Suna dab da shiga gidan ya cewa Rukayyan

 Wai da gaskene Farha ta cewa Yayarki Mai siffar karuwa?

Da sauri ta bude bakinta ta rufe da tafin hannunta

20 / 58