Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   48 / 58

141K to 144K   out of 172.2K words

shi ya saukeshi a kasuwa, suka kama hanya cikin walwala.

Suna isa suka sami Saddikun a shirye da kayansa tsaf a reception yana jiransu, suna shiga aka yi musu iso wajen shugaban center din wanda shine zai basu takardar sallama.

Bayan sun gama gaisawa ya mikawa Abba takardu ya sa hannu ya tura masa; yayi gyaran murya yace

'To Alhamdulillah, Sadik Yusuf ya fita daga harkar shaye-shaye da izinin Allah. Sai dai akwai bukatar a tabbatar bai koma harka da abokansa na baya ba domin  yan shaye-shaye suna da zumunci. Zasu iya sake janshi cikin harkar ba tare da bata lokaci ba. Ba wai hanashi harka da abokai za ayi ba, no, kawai a canza masa environment ko makaranta yanda da kanshi zai sake zabar abokai. Alhamdulillah ma yaron yana da saukin kai domin ya koyi abubuwa da yawa kuma ya haddace wajen izu sha biyar a nan din.

Cikin jin dadi Abba yace

'Alhamdulillahi. In sha Allah za a kiyaye.

Sukayi sallama suka dauko Sadiku suka kamo hanyar gida; sai da suka sauke Yaya Bello a kasuwa sannan suka wuce gidan.

Babu kowa a farfajiyar gidan, duka suna cikin falon kasa suna kallon TV saboda ranar children day ce don haka babu makaranta. Ita kuma Mommy tana falon sama.

Da sallama Saddiku ya shiga falon yana dauke da karamar jakarsa wadda kayansa suke ciki, gaba daya daskarewa suka yi na dan lokaci suka kasa magana. Rukayya ce ta fara mikewa ta sa ihu

'Yaya Sadik!

Kafin ayi wani abu ta mike ta daka tsalle ta fada jikinsa ta rungumeshi tana dariya. Gaba daya su suka taso suka fada jikinsa da gudu banda Yusra wadda ta fito daga dakinsu ta tsaya tana kallonsu tana dariya.

A nan Abban ya shigo dauke da sauran kayan Saddikun yana dariya yace

'An tareka a nan kenan?

Suka karasa ciki gaba daya bayan Abba ya amsa sannu da zuwan da suke masa. Yusra wadda ta zauna a hannun kujera tace

'Yaya Sadik bamu san fa zaka dawo ba don ko dakinka ba a gyara ba, gashi yau Jummai bata nan.

Kafin ta sami amsa ta kalli Rukayya tace

'Ke Rukayya sai kije ki share masa dakin in ya so idan Jummai tazo gobe sai ta kara gyarawa.

Rukayya ta dan bata fuska saboda haka suka saba duk lokacin da ake bukatar wanda zai yi wani aiki to nan da nan Yusra zata ce Rukayyan tayi don ita kusan bata moruwa.

Nan da nan kuma ta dan yi murmushi ta mike tana fadin

 Bari ka gani Yaya Sadik in ba haka ba Ya Yusra bata ki ka kwana a kan kurar ba.

Da sauri ta shiga kicin ta kwaso tsintsiyoyi ta fito ta nufi kofar waje da niyyar ta gyara masa dakinsa na boys quarters. Abba ya mike yana fadin

'Rukayya dakinsa na cikin gida zaki gyara masa nan zai dawo, boys quarters din ma a rufe yake.

Ta amsa yayinda Sadik din ya mike yana fadin
'Bari na gaida Mommy sai na zo na tayaki sharar.

Ya bi bayan Abban wanda ya riga ya haye saman.

Tun da taji ana ihun dawowar Saddiku ta leko ta kafar bene ta hangosu ta koma ta zauna a falon saman tana jiran shigowarsu. Bata hango Saddiku sosai ba amma dai ta ganshi a tsaye don haka ta tabbatar Saddiku ta ya dawo lafiya, yanzu jiran shigowarsa kawai takeyi.

Abba ne ya fara shigowa falon; cike da walwala ta mike ta tareshi. Shi kansa ya dade bai sami irin wannan tarbar daga daga gareta ba, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubeta yace

'Ga danki nan na dawo miki dashi babu abinda ya gutsurar miki shi ko?

Tayi dariya tace

'Ni dama ban ce za a gutsureshi ba ai. Bari na samo maka ruwa.

Ya shige daki yana dariya yayinda ita kuma ta nufi kicin, kafin ta karasa kofar kicin din saman Saddiku ya shigo da sallama don haka ta juyo tana kallonsa tana amsa sallamar cike da farin ciki. Matsowa take tana kare masa kallo yayinda shi kuma yake ta murmushi; ya canza gaba daya. Ya kara girma da kwarjini gashi yayi haske da kiba, harda wani dan gemu wanda da ta tabbatar babu shi. Murmushi kawai take tana kallonsa yayinda ta karasa ta zauna a kujera, ya kula ta rasa abinda zata ce masa don haka yace

'Mommy na dawo.

Ta dafa gwiwarsa tace

'Sannu Saddiku. Ya makarnatar? Lafiya kake ko?

'Lafiya Lau Mommy.'

Suka dan taba hira sannan Saddikun ya tashi ya sauko inda ya shiga dakinsa ya taya Rukayya suka gyara.

& & ..

Dawowar Saddiku ta yiwa Zahra dadi sosai, domin ita kanta ta kula da canjin da aka samu a tare da Saddikun wanda haka yake kara burgeta; ta tabbatar yanzu Saddikunta ya zama mutum sannan kuma yanzu Saddikun ya zama na hannun daman Abban. Domin kusan kullum idan dai Abban yana gida to suna tare, koda kuwa yana gidan Aisha, kuma suna yawan fita tare duk da basa gaya mata inda suke zuwa. Abu daya ne bai yi mata dadi ba yanda Abban ya sanar da ita Saddiku zai sake JAMB kuma BUK zai koma a daidai lokacin da zai zama Yusra kanwarsa tana shirin shiga level 2 ko ma gama level 2 din. Duk da yanda ta kula shi Saddiku wannan bai dameshi ba. Ita a tsarinta ta fi so a mayar da shi Maryam Abacha American University ko kuma a kalla a samar masa wata jami'ar ta kudi amma ba BUK ba; ta san wannan shawarar Bello ce kuma a halin yanzu ba zata iya ja da maganar ba don bata so ta bata wannan walwalar da suke ciki ita da Abban. Don haka zata bari tunda tana sa rai nan da sati biyu zasu je wajen malaminsu ita da Amina ta san da an musu aiki zata samu ta canza komai. A yanzu ma maganar da akeyi ta riga tayi magana da Yaron Malam yayi mata aiki na kwarjini irin wanda yayi mata wancan karon don tana so Abban ya dan fara sauraronta kafin wancan aikin ya fara.

Kwanan Saddiku biyu da dawowa Yaron Malam ya bayar da aikinta aka kawo mata. Ta Whatsapp ya turo mata da sakon yanda zata yi amfani da abun wanda ba tare da bata lokaci ba ta aikata kuma ta bawa Abban ya cinye.

& & &

Tunda lokacin da Saddiku yana asibiti ta tambayi abba motarta yace ta tambayi Saddiku bata sake tayar da maganar ba. Sai yanzu da taga Saddikun ya dawo sannan ta sameshi ta tambayeshi inda ya bar mota. Ya sanar da ita da motar yaje hotel din da sukayi party din amma daga nan bai san yanda akayi da motar ba. Ta so ya tambayi Abban amma ya sanar da ita shi ba zai iya tambaya ba sai dai ita ta tambaya. Tana son motar musamman yanzu da take ganin Saddikun yayi hankalin da zai bar mata motarta, don haka ta shirya zata tambayi Abban inda motar take ko kuma a kalla ya bata wata. Tabbatarwa da tayi cewa tayi amfani da kwarjinin da Yaron malam ya bata sannan kuma ga kayan mata da ta siya a wajen Hajja shi ya kara mata kwarin gwiwar tambayarsa.

& & &
Daga sallar asuba ya dawo, ya riga ya saba baya son komawa bacci bayan sallar asuba. Don haka kawai sai ya zauna a falo ya kunna TV tunda bashi da wani aiki da zai yi. Nan ta fito falon har yanzu tana sanye da rigar baccinta wadda ta dora babbar rigar a kai. Bayan ta gaisheshi ta shige kicin ta hado masa shayi, bayan ta ajiye masa shayin ta zauna a kusa dashi suka cigaba da kallon tashar BBC din da ya kunna.

Jimawa kadan tace
'Yallabai.'

'Na'am.'

Ya juyo yana fuskantar ta, tayi murmushi sannan ta cigaba

'Ni kuwa wai ina motata? Ka san tun Saddiku yana asibiti baka gaya min inda motar take ba.

Ya kurbi shayinsa, ya rike kofin a hannunsa ya dubeta ya kau da kai sannan yace

'Daga baya an sameta a hannun wasu yara, sai dai an sakata a kasuwa an sayar tun tuni.

Ta dan yi gyaran murya

'To yanzu ya za ayi da ni? Ai ko wata sai a dan bani ko na sami ta fita unguwa.

Ya sake kurban shayin sannan ya ajiye kofin a kan teburin da yake gabansa, ya kalleta suka hada ido na dan lokaci yayi murmushi sannan ya dauke kai yace

'Zahra! Kin san daman ba wai ina sha'awar baki mota bane, kin dade da sanin cewa wannan ba ra'ayina bane. Sau biyu ina baki mota ba da son raina ba, kuma duka lokutan biyun saida nayi nadamar baki. Waccan motar ma da Saddiku yayi accident ina cikin gidan nan kika san yanda kikayi da ita ba tare da kin yi shawara da ni ba. Ita kuma ta biyun kinga yanda aka kare. So ni dai ba zan sake saya miki mota ba.

Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuma ya mayar da hankalinsa kan TV din da take gabansa.

Ji????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? mawa kadan tayi gyaran murya

'Hakane. Sai dai ina ga ai yanzu na koyi hankali, kuma in sha Allah abinda ya faru a baya ba zai sake faruwa ba.

'Haka nake fata.

Suka sake yin shiru na dan lokaci, shi yana shan shayinsa ita kuma tana tunanin ta inda zata fara; domin ba zata hakura da mota ba musamman da yake Aisha tana jan mota. Abu daya ne take jin zai sa ta hakura da mota shine idan ya hana Aisha ma hawa mota. Ta dan yi gyaran murya tace

'Hm! Ina ganin tunda ita Aisha tana da tata motar ai nima zai fi zama dai-dai ka bani wata motar tunda yanzu nace duk abinda ya faru na kiyaye; in ya so sai a sallami Malam Ali. Yaran ma ni sai na dinga kaisu makaranta ina daukosu kamar yanda itama Aisha take kai kanta duk inda zata.

Ya kurbe dan ragowar shayinsa ya ajiye kofin, ya fuskanceta gaba daya yace

'Zahra. Kece kika yiwa Aisha dalilin da ta sa kudinta ta sayi mota saboda kin hana direban da na ajiye muku yayi mata hidima, yanzu kuma bata yi min wani laifi da motarta ba balle nace ta daina hawa mota. Ke da kanki ki janyo dalilin da ya rabaki da mota; tare da cewa sau biyu ina saya miki mota ba tare da na sayawa Aisha ko taya ba. Ba zan sake saya miki mota ba, duk inda zaki je direba ya kaiki ko kuma ni na kai ki. Alfarma daya zan iya yi miki shine idan kin sami kudi kema zaki iya sayawa kanki mota sai dai ko kin saya idan motar ta fara barazana ga tarbiyya da lafiyar yarana to za a fitar min da ita daga gida. Mun gama maganar mota ni dake.'

Ya mike ya dauki wayarsa ya shige daki ba tare da ya saurari jawabinta ba.

Ta bi kofar da kallo tana murmushin yake; wato duk wannan ban hakurin da tayi ba za a yafe mata ba kenan? Saboda tsabar wulakanci wai ita yake gayawa ta tara kudi ta sayi mota saboda yana takama ya auro ma'aikaciya mai kudi.

'Hmmm!

Tayi gajeriyar dariya ta mike domin ta san yanda ya saya mata waccan motar ba tare da yayi niyya ba yanzun ma hakan za a sake yi, domin sun gama magana da Amina saura kwana goma sha biyu Ummansu ta tafi Zariya wanda washegarin ranar da ta tafi su kuma zasu je wajen malamansu.

Tana shiga daki ta tuna ya kamata ta turawa Amina kudin da ta hada a account dinta tunda zuwa yanzu ta tabbatar ba zata sake samun wasu kudi kafin nan da lokacin ba. Don haka ta dauki wayarta ta tura naira dubu dari biyu da saba'in zuwa account din Amina. Tana ganin sun shiga ta kirawo lambar Aminan, bayan sun gaisa tace

'Kawata na turo miki 270k gara ki rike a wajenki don wallahi bana jin zan sami cikawa su kai 300k kafin upper week din nan. Wadannan din ma da kyar suka hadu da fizga-fizga sai dai ko bayan an yi aikin lokacin an bude min bakin aljihu.

'To babu komai, nima nan da kyar na hada 200k amma na san zuwa next week zai turo min kudin cefane na next month don haka da su zan yi amfani ya sake bayarwa idan aiki yayi.

Suka yi dariyar mugunta sannan sukayi sallama suka ajiye waya kowacce cike da yakinin burinta ya kusan cika.
UWAR SADDIKU

Written by

Sakina Yazid
(Innar su Amal)

40

Tunda sukayi maganar mota Abba ya zata zai ga Zahran ta canza masa, amma sai ya ga ta cigaba da lallabarsa don haka shima bai nuna mata wani canji ba.

Yau din ranar talata ce kuma ba a gidanta Abban yake ba. Haka ta tashi sallar asuba jikinta babu dadi, ba zata iya cewa ga inda yake mata ciwo ba amma dai ta san bata jin dadi. Kafin ta idar da sallar asuba ta fara jiyo hayaniyar yara suna shirin makaranta. Ta gama azkar dinta ta mike, ta cire hijabin ta ajiya sannan ta fito daga dakin.

A falon saman ta sami Yusra, bayan ta amsa gaisuwarta tace

 Ina Rukayya?

'Tana kicin din kasa tana hada musu abincin makaranta.

'To. Ku gama shiryasu su tafi makarantar zan dan kwanta don bana jin dadi.

'To Mommy. Ni dama bani da lecture yau ba zan fita ba.

'Yauwa, to ga gidan nan idan Jummai ta zo sai kiyi mata bayani. Idan rana tayi a dafa shinkafa da miya.

'To Mommy.'

Ta koma dakin ta kwanta.

Can wajen karfe tara da rabi Abban ya shigo da shirinsa na tafiya office, bayan Yusra ta gama yi masa bayanin Mommy bata jin dadi ya wuce saman don ya dubota.

Tana kwance a dakin, bayan sun gaisa yace

'Yusra tace min ba kya jin dadi, me yake damunki?

Ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tace

'Ni kaina bana ce ba wallahi, ba dai na jin dadi ne amma dai kaina yana dan ciwo don haka na sha Panadol na kwanta.

'Ok. To idan dai kin ji babu hali kiyi min waya sai na zo muje asibiti, kada ki zauna da ciwo haka.

'In sha Allahu ma ba sai na je ba, da na sami bacci zan warware.

'Ok. Tare da Saddiku zamu fita, zan ajiyeshi gidan Yaya Bello akwai wajen da zai kaishi don ya fara koyon gyaran computer kafin admission dinsa ya fito.

'Uhm, to ku gaida mutanen gidan Yaya Bellon.

Ta koma ta kwanta shi kuma ya fice daga dakin.

Ta bi kofar da ya rufe da harara ta ja tsaki a fili tana tabe baki tace

'Bello! Bello! Bello! Na kusa nayi maganin ku gaba daya.

Ta gyara filonta ta kwanta.

& & & .
Har karfe daya ta wuce Mommy bata sauko ba. Lokacin Jummai ta gama abinci ta gyara gidan, itama Yusra tayi sallah har yara sun kusa dawowa daga makaranta. Ta dai san yanzu haka bacci ne ya kwashe Mommy din amma dai ta dade, don haka ta hau saman da nufin ta tashi Mommy din ko don ma tayi sallar azahar.

A hankali ta tura kofar dakin ta shiga da sallama, ta mayar da kofar ta rufe. Yanayin da taga Mommy bai yi mata dadi ba; tana kwance a kan hannunta na dama sai dai ta sauka daga kan filon ta takureshi a jikin gadon. Hular da ta kwanta da ita ta fita daga kanta ta fado gaban gadon sanna ga alamar ta dan turza kafarta a inda kafar take, abun rufar da ta rufe kafafunta da shi rabinsa yana kasa yayinda rabinsa yake jikin kafafun nata.

Da sauri Yusran ta karasa bakin gadon ta durkusa ta tabata tana fadin

'Mommy azahar tayi fa.

Sanyin da ta ji a jikinta ya bata tsoro don haka ta mike a firgice ta rarumi wayar Mommy din ta shiga neman lambar Abba. Bata taba ganin mutuwa ba amma tabbas wannan yayi mata kama da mutuwa, bata son wannan tunanin da kwakwalwarta take biya mata nan take jikinta ya fara rawa. Da kyar ta lalubo lambar Abban nata ta buga, ta ci sa a kuwa wayar tana shiga ya dauka. Kafin ya gama yi mata sallama a gigice tace

'Abba Mommy ce ka zo bata da lafiya.

Kafin yace wani abu ta jefa wayar kan gadon ta fice daga dakin da sauri jikinta yana rawa. A guje ta sauka daga been tana yi tana tsallake wasu, ba tare da ta tantance inda zata tafi ba ta nufi fita daga falon kasa.

Har ta fita sai kuma ta tuna Jummai tana kicin don haka ta dawo da gudu ta shiga kicin din tana haki tana fadin

'Jummai zo ki gani, zo ki ga Mommy.'

Kafin Jummai ta amsa ta ja hannunta don haka ba tare da bata lokaci ba ta bi bayanta da gudu suka nufi sama. Suna shiga dakin Yusran tace

'Kin gani fa Jummai, Kinga Mommy kamar fa bata motsi kinga yanda na fita dazu har yanzu bata motsa ba ko suma tayi?

Jummai ta tsuguna a gaban gadon ta dubi fuskar Mommy din; tabbas mutuwa Zahra tayi. So take ta fasa ihu amma bata so tayi hakan gidan daga ita sai Yusra, don haka ta mike tana fadin

'Bari naje gidan commissioner da gudu na kirawo Mama, Allah ya sa bata tafi asibiti ba. Idan tazo na san zata san abun yi ko kuma su tafi asibiti tunda Abban baya nan.

Nan ta fito ta bar Yusran tana tsaye ta rasa abinda zata yi kuma ta kasa sake taba Mommy. Jummai bata dade da fita ba itama Yusran ta fito daga dakin ta zauna a falon sama tana share hawaye tana fatan Allah ya sa Mommy suma tayi.

Jummai tana fita ta tsallaka da gudu ta shiga gidan commissioner, tayi sa'a Mama bata fita ba tana tsaye a tsakar gida tana bayarda kayanta da za a wanke mata. Cikin gaggawa ba tare da ko sun gaisa ba Jummai tace

'Mama don Allah ki zo ki duba mana Mommy ce ba lafiya, kamar ma ta suma.'

Cikin damuwa tace

'Subhanallahi!

Ta juya ta shiga falonta, ba tare da bata lokaci ba ta fito sanye da

48 / 58