Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 58

129K to 132K   out of 172.2K words

kudin nan kinga ina cikin organizers fa.
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan tace

 Abbanku yace bashi da kudi kuma ka san idan nace masa party zakuyi ma ba zai bari kaje ba, amma idan kana son 30k ni zan turo maka zuwa gobe idan kuma tayi kadan to sai dai kai kaje ka tambayi Abban.

Da sauri yace

 A a Mommy please ki turo 30k din kawai.

Suka dan taba hira yayi mata sallama ya fice.

Yana fatan idan ta bashi dubu talatin din daga baya sai ya san yanda zai yi ya takureta ta kara masa ashirin din.

Party suka shirya su uku shi da abokansa,  yan ajinsu na Jami a ma basu san da wannan party din ba. Ya riga yayi alkawarin dubu dari biyu zai bayar gudummuwar party din. Ya riga ya yagi mafi yawan kudin a wajen Abban ta hanyar karyar abubuwan da aka ce su saya a makarantar, a halin yanzu dubu hamsin din kawai yake bukata ya gama hada kudin su je suyi party dinsu.
& & & ..

Babu yanda ta iya haka ta turawa Saddiku dubu talatin daga kudin da take ta faman tarawa, sai dai duk nacinsa ta ki ta kara masa wasu kudin; ta dai gaya masa ya samo makanike ya sayi gawar motarta da yayi accident idan an biyata sai ta kara masa.

Haka ya samo har mutum biyu, sai dai babu wanda ya taya motar a kan dubu dari ma. Domin duk cewa sukeyi ba zata moru ba don har injinta ma ya tashi daga aiki. Haka ta hakura ta sayarwa da na karshen a kan naira dubu sittin da biyar. Wanda a hakan ma yace sai dai su bashi sati biyu zai kawo kudin sai ya dauki motar.

Sai bayan ya tafi Saddiku ya bishi ba da sanin Mommy ba ya karbe naira dubu goma sha biyar a kan ya kai cikon ya dauko motar.
& & & & ..

Tun bayan la asar ya shirya yayiwa Mommy sallama. Ya dauki motarta ya tafi party; motar da tana kallo yanzu ta zama ta Saddiku tunda da tana kokarin ta sa Abba ya saya masa tashi motar amma yanzu ta san bata da wannan damar.

Kamar yanda Abba ya saba bayan magriba ya dawo gidan. A gidan Aisha zai kwana don haka gidan Zahra ya sauka; bayan ya huta suka dan taba hira ita da shi da yaran. Sai da ya dawo daga sallar isha i sannan yayi mata sallama ya tafi. Kafin ya fita kuma ya sanar da ita idan goman dare tayi Saddiku bai dawo ba tayi masa waya.

Ta san yace mata sun tafi party don haka bata sa rai zai dawo kafin karfe goma na dare ba, don haka wajen tara da rabi ta kulle gidan ta turawa Saddiku message cewa idan ya dawo yayi mata waya tunda ba ciki zai shigo ba a boys quarters dakinsa yake.

Tunda ta kintsa ta kwanta bata farka ba sai karfe biyu na dare; agogonta ta fara dubawa a wayarta taga lokaci.

Nan take ta dannawa Saddiku kira, har wayar ta tsinke bai dauka ba sai kawai tayi zaton ya dawo bacci ne ya kwasheshi tunda ya kwaso gajiya don haka itama sai ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.
__

Tana idar da sallar asuba ta sauko ta bude kofa ta leko tsakar gidan, so takeyi ta tabbatar Saddiku ya dawo gidan jiya. Ga mamakinta babu motarta a tsakar gidan wanda hakan yake nufin Saddiku bai kwana a gidan ba. Ta fito ta tsaya a kan baranda ta kwalawa Malam Sado kira, da gudu ya taho yana rike da carbinsa da yake wiridi. Bayan ya gaisheta ta amsa tace masa

 Malam Sado Saddiku bai dawo gidan nan ba jiya da daddare?

Ya shafa kai yace

 Bai dawo ba Hajiya sai dai ko nan gaba.

Ta koma cikin gidan jikinta a sanyaye.

A kan dining table din kasan ta zauna ta lalubo lambarsa a waya ta sake kira, ringing kawai wayar take yi Amma ba a dauka ba. Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta tuno haka yayi mata wancan lokacin da yayi accident. Nan da nan idanuwanta suka cicciko da kwalla; da sauri ta fara laluben lambar wayar Abbansa. Sai da ta zo kan lambar tasa sai kuma ta tsaya ta kasa kiransa; to yanzu idan ta kirawo shi me zata ce masa? Ce mata yayi idan goma tayi Saddiku bai dawo ba ta kirawoshi amma bata yi hakan ba sai yanzu da safe ta kirawoshi tace masa me? To idan fa accident Saddikun ya sake yi
 Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.

????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
Ta fada a fili yayinda idonta ya cicciko da kwalla. Gashi bata san abokansa ba don haka ma bata da lambar ko daya daga cikinsu. Ta tashi jikinta babu kwari ta koma saman, ta zo daidai kofar dakin su Yusra taji motsinsu. Nan dabara ta fado mata; ta karasa ta tura kofar ta kirawo Yusra. A dakin Yusran ta sameta, bayan ta amsa gaisuwar ta tace

 Yusra yayanki bai dawo gidan nan ba jiya gashi kuma ina ta kiran wayarsa bai dauka ba, ko kina da lambar abokansa da suke party din tare na kirawosu muji?

Da mamaki Yusran tace

 Mommy party sukeyi?

Itama mommy din mamakinta ya karu

 Au baki sani ba? Yace min end of year party zasu yi shi da  yan ajinsu jiya da daddare.

 To gaskiya Mommy ni ban sani ba, kuma a abokansa mutum daya nake da lambarsa. Bari na kirawo shi muji.

Nan ta koma daki ta dauko wayarta ta dawo wajen Mommy din. Ta lalubo lambar Babs wanda dan ajin su Saddiku ne, shima ta sami lambarsa ne saboda yana sonta duk da ita din bata sauraronsa.

Sai da ta zauna a kusa da Mommy sannan ta danna masa kira ta sa wayar a loudspeaker. Yana dauka yace

 Today is going to be a good day tunda ke kika fara kirana Babe, to ya kike?

Tace

 Uhm! Lafiya. Ka san wani abu? Ya Sadik nake nema ka san tun jiya da daddare bai dawo gida ba yace wai  yan class dinku suna end of year party shine nake son naji me ya hanashi dawowa gashi Mommy tana nemansa.

Da mamaki a muryarsa yace

 Party? Gaskiya ba dai  yan class din mu ba sai dai ko wasu friends din nasa, don gaskiya duk mun koma gida ko nima kin ganni a KD.

Sukayi shiru na dan lokaci, jima kadan yace

 Amma bari na tambayar miki su Bigi duk da dai na san ba da su bane amma dai idan har guys din mu ne suka shirya party din to lallai Bigi zai sani.

Sukayi sallama bayan ya sanar da ita idan ya ji wani abu zai kirawota.

Ta dubi Mommy tace

 Kin ji Mommy!

Cike da damuwa tace

 Hmm! Na ji Yusra. Ni haka yace min da 'yan class dinsu don sai da na bashi 20k sannan kuma ya zagaya ya karbe kudin da aka sayar da garwar tsohuwar motata ba tare da ya gaya min ba kuma cewa yayi duk a kan party din ne. To ina ya tafi?

Jimawa kadan ta sallami Yusran don taje ta shirya mata yara su tafi tahfiz.

Haka tayi ta faman jan kafa cikin matsananciyar damuwa har wajen karfe goma saura.

Wajen karfe goma Abban ya shigo don ya dubasu ita da Yaran. Bayan ya amsa gaisuwar Yusra a falon kasa ya haye saman. A dakinta ya sameta tana kashingide a gefen gado, bayan sun gaisa ya zauna a gefen gadon kusa da kafafunta yace

 Ya dai? Jikin ko garin na ganki a kwance.

Ta tashi ta gyara zama sannan ta bashi amsa

 Uhm, babu ko daya. Hutawa dai nake yi kafin  yan gidan su dawo.

 Saddiku har ya fice ko? Ai sun gama exam tunda ke bakya hawa motar yau in ya dawo ya bani mukullin motar ya huta yawon ya isa haka, da anyi magana yace zasu je lecture ko kuma zasu hadu suyi karatu.

Ta dan muskuta

 Um nima haka na gani, bari ya dawo sai na karbi mukullin motar na boye saboda in zan fita.

Suka dan taba hira daga baya yayi mata sallama ya fita; yana mamakin Zahra! Tun tuni yake so ya karbe mukullin mota daga hannun Saddiku amma ta hanashi sai tace ita zata kwace kuma bata iyawa. Lokuta da dama yana mamakita, yanda har yanzu ta kasa gane cewa bata tarbiyyar Saddiku takeyi. Shi yasa har yanzu bai gayamata cewa ba zai biyawa Saddiku kudin registration ba sai ya je makarantar da kansa ya ga result dinsu.

Ta kasa gayawa Abba cewa bata ga Saddiku ba kuma ta rasa wanda zata gayawa gashi har sha biyu saura, ta dai yanke shawarar idan aka yi kiran azahar bata sameshi ba zata gayawa Abbansa.

Karfe Sha biyu da kwata wayarta tayi kara, ta dauki wayar kamar wadda aka yiwa dole sai kuma ta ga sunan Saddiku, sai da zuciyarta ta nemi tsayawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana aka ce
 Hello.

Ba Saddiku bane yake magana, haka dai ta daure ta amsa. Bayan mai maganar ya gaisheta yace

 Don Allah ina magana da mahaifiyar Sadik Yusuf ne?

Cikin hanzari tace

 Eh, ina Sadik din?

 Um gamu nan da su a asibitin Malam Aminu Kano emergency shi da abokansa, suma sukayi tun jiya a wajen party da suka sha kwaya, har yanzu basu farfado ba.

 To gamu nan zuwa.

Ta saki wayar a kan cinyarta daidai lokacin da hawaye ya wanke mata fuska.

Saddiku ya sha kwaya tun jiya ya suma? Yanzu me zata cewa Abbansu, bayan ta gama gaya masa da safen nan Saddiku ya fita.

 Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!

Ta mike tsaye, wayar da take ajiye a cinyarta ta subuce ta fadi kasa ta dauke wayar ta ajiye a kan gadon. Ta karasa gaban wardrobe tana share hawaye ta dauko hijabi ta saka sanna ta dauko jakarta a kan mudubi ta dawo ta dauki wayar ta jefa a ciki ta nufi ficewa daga dakin.

Har ta kama hannun kofar sai kuma ta tsaya ta kasa murdawa; to ina zata? Babu mota a gidan kuma Malam Ali baya nan, shi kuma Abban da yake ba a nan ya kwana ba bata ma san ko yana gida ko baya nan ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta koma kan gadon ta zauna ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. Bata da wata mafita illa ta kirawo Abban Saddiku ta sanar da shi domin idan ma taje asibitin ita kadai a halin yanzu komai zai iya faruwa.

Ta kama gefen hijabin da yake jikinta ta goge hawayenta, tayi ajiyar zuciya ta laluba jakarta ta dauko wayarta. Ta lalubo lambar Abban Saddiku ta danna kira ta kara a kunnenta zuciyarta na dakan uku-uku.
& & & &

Fitowarsu kenan daga gidan Hajiya shi da Yaya Bello, suka shiga motar Abban suka kama hanyar gidan Yaya Bello inda a can zasu ci abincin rana. Yana zura mukullin motar kira ya shigo wayarsa wadda ajiyeta kenan a kusa da giyar motar; ya fasa tayar da motar ya amsa wayar ya kara a kunnensa. Ba tare da ta amsa sallamarsa tace

 Abba Saddiku bashi da lafiya yana asibitin Malam a emergency, yanzu Yayan abokinsa da suke tare ya kirawoni ya sanar da ni.

 Subhanallah! Accident yayi ko me?

 Nima dai ban gane bayanin ba amma dai ba accident bane, nima yanzu zan sami motar haya na wuce asibitin idan kuma kana unguwar sai na shirya mu tafi.

 Ina gidan Yaya kiyi zamanki zan je na gani in ya so mayi waya.

Ya ajiye wayar ba tare da ya saurari amsarta ba.
Ya dubi Yaya Bello da yake gefensa ya sanar da shi abinda ta gaya masa, nan yace su wuce asibitin kawai. Don haka Abban ya tayar da motar suka kama hanya.

Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan a gaban Yaya Bello za a yi mata wannan tonon asirin, ya sami dalilin da zai shiga rayuwarsu ita da yaranta ya hanasu jin dadi.

Sai da tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita halin da ake ciki, duk da bata gaya mata cewa kwaya Saddikun ya sha ba.

Sukayi sallama a kan idan taji abinda ake ciki ta sanar da ita.
& & & &

Har suka isa asibitin Malam Aminu Kano babu wanda yace wa dan uwansa wani abu; shi Abba yana ta mamakin to Saddikun da aka ce masa dazu ya fita meye zai sameshi har a kaishi emergency kuma ace ba accident ba yayinda shi kuma Yaya Bello yake kallon hanya yana nashi nazarin.

A kusa da emergency din yayi parking suka fito suka shiga, sai dai suna shiga kuma ya rasa wanda zai kama. Don haka ya janyo Yaya Bello suka dawo waje ya kirawo Zahra ya tambayeta wanda zasu nema; bayan ta sanar da shi ya ajiye wayar ya kirawo lambar Saddikun sanna suka nufi komawa cikin emergency din.

Yana shiga ya hango wanda yake waya da shi; yaro ne matashi wanda ba zai wuce shekaru ashirin da biyar ba zuwa da shida. Da hanzari ya karaso wajen su Abban,bayan sun gaisa ya mikawa Abban wayar Saddiku yana fadin

 Ga wayar Sadik din.

Ya karba yana fadin

 Wai me ya samesu ne?
Cikin damuwa yace

 To ni dai abokinsu ne ya kirawoni kuma a hotel na samesu wai party sukeyi shine suke competition aka wanda yafi shan kwaya da yawa zasu bashi kudi 250k. Su ukun da suke kwance a nan su suke shan kwayar shine da sauran suka ga sun sume duk suka gudu sai abokinsu daya ya kirawo ni ya gaya min don harda kanina a cikinsu. Shima yana gaya min ya gudu, don yanzu ma likitocin tambayar da suke shine a gaya musu sunan kwayar da suka sha don su san irin abun da ya dace suyi musu amma ni ban sani ba; abokan nasu kuma duk sun kashe waya. Gasu can dai su uku a kwance a sume an dai musu allura.

Yaya Bello yace

 Subhanallah!

Matashin da yake yi musu bayani yace

 Likitan da yake duba su yana wancan office din, ku zo mu karasa sai kuji daga bakinsa.

Yaya Bello yaja hannun Abban Saddiku wanda ya kasa wani katabus suka bi bayan yaron.

Bayan ya gabatar da su a wajen likitan shima likitan irin bayanan da yayi musu ya sake basu, ya dora da

 Matsalar itace bamu san irin kwayar da suka sha ba. Shi daya yaron da ya farfado yace sunan kwayar flash dayar kuma rod, a lussafinsa shi kwaya uku ya sha yayinda su kuma suka sha biyar ko shida. Muna bincike kuma muna jira su farfado mu sami ainahin sunan kwayar domin shine zamu san irin abinda ya dace muyi musu.

Suka yiwa likitan sallama bayan ya sanar dasu idan sun farka za a mayar da su sashen kula da kwakwalwa.

Bayan sun fito daga ofishin suka karasa inda Saddikun yake; yana nan a kwance babu alamar wani motsi a tare da shi idan banda numfashi da yake futarwa a hankali. Suka kare masa kallo Yaya Bello yace

 Allah ya kyauta.

Ya janyo hannun Abban Sadik wanda yake binsa kamar mutum-mutumi suka fito bayan sun yiwa yaron godiya sun sanar dashi cewa suna nan a farfajiyar asibitin idan an bukaci wani abu.

Akwai dan waje daga gefen emergency din da kujerun siminti na zama, nan suka je suka zauna. Suna zama Abban ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yayinda shi kuma Yaya Bellon ya zauna kusa da shi yana nashi nazarin ba tare da yace komai ba.

Sun dauki kusan minti goma haka kafin Abban Sadik ya sauke hannuwansa ya dubi Yaya nasa cike tsananin damuwa yace

 Allah ya sauwake.

 Amin ya Allah.

 Wallahi Yaya ban san yanda aka yi Saddiku ya zama haka ba. Kusan mutum uku ne suka yi min magana a kan na binciki yaron nan, don malaminsu na secondary school ma kai tsaye ya gaya min cewa yana shaye-shaye. Amma duk yanda naso na dauki mataki a kai uwarsa ba zata bari ba domin wasu lokutan ko bari na ganshi ma bata yi. Gashi ko an kama shi da laifi ta iya kare shi, wasu lokutan ma kamar shashantar dani take ta mantar dani al amarinsa. Yanzu ka ga abinda ya faru ko Yaya? Da anyi mata magana sai tace wai ana so a hadani da shi.

Yaya Bello yace

 Sha anin mata ne sai hakuri. Yanzu jira zamuyi ya farfado muji daga bakin likitocin yanda za ayi a taimaka masa don ba zamu barshi haka ba.

Cikin kunan rai ya cigaba

 Ka ga tunda har ya kai ya shiga gasar shan kwaya kenan ya dade yana yi har ta bi jikinsa, kuma ma kudi har naira dubu dari biyu ina suka samo su? Ni dai ban taba bawa Saddiku naira dubu goma ba ma ba balle dubu dari biyu ko fiye. Ina ya sami wadannan abokanma?

Suka cigaba da tattaunawa Yaya Bello yana kwantarwa da Abban hankali yana gaya masa za a samu ya bari in Sha Allahu.

Wajen karfe biyu suka jiyo kiran Sallah daga nesa, Yaya Bello ya dafa Abban yace

 Ba muyi Sallah ba ai

44 / 58