Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 58

39K to 42K   out of 172.2K words

gama aikinka, tab!

Kallonta yake da mamaki

 To yanzu ya za kiyi dani.

 Abinci zan baka kaci ka koshi ka koma can in an kwana biyu ka dawo.

Duk yanda ya so ya tsara Aisha ta karbi kwanan nan ki tayi, haka ta dafa masa taliya ya ci ya koshi ya sha shayi sannan tayi masa sallama ta rufe kofarta ya koma wajen Zahra.
& & .

Ko da taji shigowarsa luf tayi kamar mai bacci domin tazata wani abun ya dawo dauka.

Sai da ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya kirawota a waya domin da baiga Rahma ba yayi tunanin ko a dakinta zasu kwana. Ta zata ya riga ya fita don haka ta dauka tana mamaki.
 Ina nan fa, a nan zan kwana.

 A a, me ya faru kuma ka fasa?

Yayi  yar dariya yace

 Kanwar taki bata karbi kwanan ba.

Nan yayi mata bayani kamar yanda Aishan tayi masa, suka ajiye waya tunda dama kiranta kawai yayi don ta san a gidan zai kwana.

Har bacci ya kwasheta tana tunanin wauta irin ta Aisha, ya za ayi abata miji kwana arba in tace a barshi? Ko yanzu ma da akayi haka ta san idan dai Aishan ta haihu ko da tsiya-tsiya sai an bata kwana arba in din nan tunda ita haka taga ana yi.
& & & .

Kwanansu daya da fitowa daga asibiti Aisha taje barka da kayan barkarta da ta tanada cikin leda; kayan baby ne masu kyau da tsada. Sai da ta tabbatar yana gidan ta shiga domin tuni ta sha jinin jikinta da matar nan.

Bayan la asar ne suna zaune ita da shi a falonsa da Baby a hannunsa Rukayya ta shiga falon da sallama ta sanar da Mommy zuwan Anti Aishan. Har ta mike zata tashi ya cewa Rukayyan ta hawo da Antin nan mana. Kafin tace wani abu Rukayyan ta fice, bata dade ba suka dawo tana dauke da ledar yayinda Aisha take biye da ita.

Babu laifi suka gaisa da Zahran da yake a gabansa me, aka mika mata Baby ta dauka ta sa albarka. Suka dan taba hira gaba daya har Abban Sadik din, ta turawa Zahra ledar tace

 Ga wannan babu yawa, Allah ya rayata ya kara lafiya.

Tare suka amsa da Zahran da Abban Sadik.

Tayi musu sallama ta sauko ta koma gida, zuciyarta fari fes saboda yanda tayi barkarta a gabansa tunda ta san Zahran bata yi mata komai a gabansa.
& & ..
Saida aka kwana biyar sannan ya sanar da su sunan yarinya, ya saka mata Sumayya. Da kyar Aisha ta daure ta sanar da  yan uwanta sunan inda ta nemi Yaya Zuwaira da Yaya Zainab su zo amma kada su taho da yara don bata son fitna.

An ci burin wannan sunan kuma an shirya taro inda aka gayyato mutane da yawa, dangin Abban Sadik din ma haka suka zo da yawansu saboda Yaya Saratu aka bawa goronsu na gayyatar ta tabbatar ta hado kansu sannan suka taho.

Aisha ta riga ta tambaya ko akwai aikin da zata tayasu amma Zahra tace mata babu domin komai bayarwa za ayi a yiwo daga waje, don haka ranar sunan ba tayi shirin tafiya gidan da wuri ba. A tunaninta ma  yanuwan Abban zasuyi ta shigowa gidan nata amma har shadaya babu wanda ya shigo. Batayi mamaki ba domin dama ta san babu wanda yake kaunarta a danginsa, tun lokacin da suka je da Zahra gaba daya suka ki sakewa da ita. Duk da sun je ita da Abban sun bawa Hajiyan hakuri amma har kawo yanzu basu saki jiki da ita ba.

Sai wajen sha biyu saura sannan Zuwaira da Zainab suka iso, ba tare da bata lokaci ba suka shirya tare da Aishan suka wuce gidan sunan.

Tun daga bakin gate Rukayya ta hangosu, da gudu ta karasa ta kama hannun Aishan tana yi mata sannu da zuwa, ta gaida su Yaya Zuwaira sannan ta wuce gaba suka bita a baya.

Tun daga falon duk  yan uwan da Rukayya ta san basu taba haduwa da Aishan ba sai tace musu

 Ga amaryar Abbanmu.

Haka har suka wuce falon sama inda Mommy take, su Yaya Saratu ma duk suna wajen anata hira.

Suka karasa kusa da Mommy Aisha ta zauna kusa da ita su Yaya Zainab din ma suka zauna.

Gaisheta sukeyi suna mata barka amma da kyar take amsawa tana wani dauke kai.

Suka juya wajen Yaya Saratu wadda itama da kyar take amsa gaisuwar.

Yaya Murja ce kawai ta sauraresu da girmamawa, ragowar mutanen da suke wajen suka cigaba da hirarrakinsu babu wanda yake bi ta kansu. Don haka suma suka gyara zama suka fara kus-kus dinsu su kadai.

Basu dade da zama ba wata dattijuwar mata ta shigo, tun daga kafar bene take zabga kirari tana guda

 Uwar gida Uwar Saddiku, kinyi taki kinyi ta raggo. Uwargidan Yusuf maki gani ido ya makance. Yanda duk kika dama haka za a sha Uwargida ta Uban Sadiku ko mahassada sun ki. Haihuwa kyautar Allah, ba rawar kai bace ba iyawa bace, ke Allah ya zaba uwar SADIKU matar Yusufa& .
Yaya Saratu ce ta fara mikewa ta lika mata naira dubu tana fadin

 Kin min daidai, babu karya a cikin zancenki uwar Sadiki taci dubu sai ceto.

Abun nata ya fara yawa kuma duk wanda ya san Aisha kishiyarta ce ya san da ita akeyi. Yaya Murja ce ta mike ta dauki kudi a jakarta ta ja matar sukayi kasa ta sallameta.

Bata dade da fita ba su Aisha suka mike Yaya Zuwaira ta karasa kusa da Zahra ta ajiye mata kudi naira dubu goma tace a siyawa Baby sabulu. Sukayi musu sallama suka fito.

A gidan Aishan suka karasa wuninsu suna jajanta mata zama da wannan matar don ko su kansu sun kula da yanda ita da  yan uwan Yusuf din basa ko kaunar Aisha.

Tun tuni Aisha ta san dangin Yusuf basa sonta amma sai yau ta kara tabbatarwa, don zata iya cewa a  yan uwansa matar Yaya Bello ce kawai ta saurareta sai kuma Innani wadda ita din  yar uwar Hajiya ce.

Haka aka gama taro aka watse, abincin sunan nan kuwa Aisha ko kalarsa bata gani ba domin lokacin da suka fito daga gidan ba a fara rabo ba kuma da aka fara babu wanda ma ya tuna da ita duk da an kaiwa makota abincin gida-gida.
& ...

Wajen sati biyu da gama taron suna sai Yusra ta tsiri shiga gidan Aisha, haka kawai da rana ko da daddare musamman idan Abbansu yana gidan sai Yusra ta shigo. Wata rana ita kadai take shiga wata rana kuma ita da kannenta. Hatta Rukayya saida tayi mamaki saboda Yusra bata taba shiga gidanba amma sai gashi yanzu kusan duk ranar da Abbansu yake gidan sai ta shiga.

Amma da zarar Abban ya zauna an kawo abinci aka ce ta zo ta ci sai taki, tace ita ta koshi. Sai dai kawai su zauna a falo suna kallon TV.

Yau shinkafa da miya Aisha ta dafa ta hada salad ga kuma zobo. Tare suka zauna da Abban suka fara cin abincin, sai dai da kyar ta hadiye lomar farko saboda dandanon miyar bai yi ba. Ta ajiye cokalin tana jira taji mai zai ce.

Shi din ma da kyar ya hadiye wanda ya saka a bakinsa ya dubeta yace

 Yau me ya sami miyar ne?

Tace

 Wallahi nima na ji, na zata ma bakina ne.

Kamshin miyar ya canza gaba daya, gashi yana wani santsi da dandanon mara dadi. Dole ta dauke wannan miyar ta kawo musu mai da yaji suka ci abincin nan domin bata ma da wasu kayan miyan gashi abincin dare ne.

Haka suka kwana tana mamakin abinda ya bata mata miya, har gari ya waye bata gane ba don haka ta cigaba da harkokinta.

Bayan an kwana biyu kuma ranar asabar tayi tuwon shinkafa da miyar gyada da rana shima ga mamakinsa yanda waccan miyar tayi wannan ma haka tayi.

Dandanon babu dadi ga shi kuma har wani bashi miyar takeyi, dole ta tashi tayi sauri ta kada musu miyar kuka suka ci tuwon.

Sanda ta ajiye abincin dare tana kula da Abban Sadik sai da ya dandana kadan sannan ya saki jiki yaci.

Daga baya kuma suna zaune a falo suna hira da daddare yake tambayarta

 Wai kuwa kin gane abinda yake bata miki miya, ko kayan kamshi da kike sakawa ne?

Cikin damuwa tace

 Wallahi ban gane ba, bana jin kuma kayan kamshin ne amma dai zan cigaba da dubawa.

 Ya kamata dai ki kula sosai, idan ma wani abune yake shiga abincin sai ki mayar da hankali ki gyara.

 In Sha Allah.

Ta kula da yanda yake kokarin ya zargi ko tana saka masa wani abun a abinci wanda hakan ya sosa mata rai, sai dai itama ta rasa abinda yake faruwa da miyar tata.

Haka ta cigaba da kula ko zata gane.

A  yan kwanakin nan saida abincinta yayi irin haka wajen sau biyar, domin har dafa duka tayi wadda ta dinga yi musu kanshi da kumfa kamar sabulu.

Gaba daya ta shiga damuwa, amma ta kasa gane inda matsalar take. Gashi Abban Sadik ya fara hakura da abincinta sai yaje waken Zahra yaci. Don haka ta mayar da hankali take ta rokon Allah ya yaye mata kuma ya nuna mata abinda yake faruwa kada taje ta cutar da su ita da Abban Sadik din.
& &

Ranar Alhamis ce, kamar yanda suka saba a kwanakin nan Yusra ce da Nana a zaune a falon Aisha bayan sallar la asar. Kallon TV sukeyi ta tashi ta shiga kicin ta dora abincin dare; tuwon miyar kuka ta dora wanda bayan ta sa komai a wuta ta fito daga kicin din ta shige daki.
Tana shigewa Yusra ta dubi Nana tace

 Ki zauna a nan kada ki taso bari na samo ruwa na sha.

Tayi sauri ta fada kichin din.

Da gaggawa ta karasa kusa da cooker, ta kai hannu ta dauki murfin tukunyar miya ta ajiye a gefe. Ta zaro 'yar farar ledar da ta ke daure a jikin siket dinta ta bude, da sauri ta debi abinda yake cikin ledar ta barbada a miyar ta juya ta kulle ledar ta rike a daya hannunta. Ta dauki murfin tukunyar wanda murfin glass ne tana kokarin rufe tukunyar, bata san yanda aka yi ba murfin ya subuce ya tarwatse a kasa. Karar faduwar murfin ya sa Aisha ta karaso kichin din da gudu wadda dama tana hanyar dawowa kicin din, itama Nana da sauri ta karasa kicin din.
Yanda Yusran take kallonta tana rawar jiki ya sa ta san bata da gaskiya, ta karasa a hankali tace

 A a, Yusra me kikeyi kuma a nan zakije ki kona kanki?

Tana karasawa ta kula da ledar da take hannun Yusra, ita kuma tana ganin hankalinta ya kai kan ledar tayi sauri ta fara kokarin boyewa.

Da sauri Aishan ta cafke hannunta ta dauki ledar tana budewa da mamaki tana fadin

 Yusra! Me kuma kike saka min a miyar?

Tayi tsuru-tsuru tana kallonta tas tana wani murguda mata baki tace

 ba komai.

Ta fara kokarin juyawa ta fita daga kicin din Aishan ta daka mata tsawa, take ta tsaya.

Ta kwance ledar ta duba sosai tana yi tana shanshanawa; idan dai ba kuskure tayi ba to sabulu ne sai dai an gurza shi kamar da abun gurza kubewa. Ta gyada kai; tabbas sabulu ake saka mata a abinci  yan kwanakin nan da abincinta yake baci. Ta dubi Yusra tace

 Sabulu Yusra? Kike zuba min a miya saboda mugunta ko me?

Ta sunkuyar da kai tana gunguni.

Aisha tayi murmushi tace

 Hhhh! Ba ni kike cuta ba Yusra, ubanki kike cuta saboda dai sabulu ba abinci ba kuma tabbas zai iya illata lafiyar mutum musamman mutum mai shekaru kamar Abbanki. Ni ubana ya mutu na san menene maraici, ba abune mai dadi ba amma ke naki uban kike so ki dinga bawa sabulu saboda ki illata shi. Na san Mommy ce ta turoki, don haka idan kin je ki gaya mata nace tsohonki kike zubawa sabulun yana ci, idan kuwa ya mutu ku ya macewa ku da ita domin kune kaf danginku babu wanda ya kaishi kudi balle ku sa rai wani zai kula daku kamar yanda yake yi. Garin zalunci zaku cutar da kanku a banza.

Ta kama hannunta ta saka mata ledar ta danke mata tace

 Gashi nan idan kin je kice mata nace abinda tayi min Allah yayi mata kuma kema haka.

Ta murguda baki ta ja tsaki sannan ta fizge hannunta ta fice daga gidan tana huci, Nana tana biye da ita.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

15

A fusace suka shiga gidan, Anti Rahma ce a zaune a falo da Baby a hannunta. Ta bisu da kallo bayan da suka nufi hawa sama tace

 Ke Yusra meye zaku shigo gida babu sallama ko baki ga mutum a falon bane?

Ta share kwalla tana zumbura baki, ba tare da ta juyo ba tace

 Mommy nake nema.

Suka karasa hayewa saman ba tare da sun ce mata komai ba.

Tana zaune a falon Abban tana kallon TV tana shan romon kaza, suna shiga suka zube a gabanta Yusra ta kifa kai a cinyarta ta fashe da kuka. Ta dafa kanta da mamaki ta dubi Nana tace

 Meye haka kuma? Nana me aka yi mata?

Ta zumbura baki sannan tace

 Mommy Anti ce fa, ta zageta ta zagi Abba harda ke ma ta zaga kuma tace Yaya Yusran ta gaya miki.

Da mamaki ta tambaya

 Anti Rahma?

 Matar Abba mana.

 Aisha? Lallai matar nan rainin nata ya isa! Me tace miki?

Yusra ta dago kanta, kafin tayi magana Nana tace

 Tace zamu kashe ubanmu kuma kowa a danginmu ba masu kudi bane sai shi, harda cewa ita babanta ya mutu.

Yusra ta bude tafin hannunta ta turawa Mommy ledar garin sabulun wadda dama ita ta bata ita, nan da nan ta dauke ta zura a bayanta. Yusra tace

 Mommy garin na rufe tukunyar ne to dama non stick ce mai murfin glass shine murfin ya fadi ya fashe tazo tana ta maganganu.

Ta mayar wa da Mommy duk maganganun da Aishan ta fada.

Suna cikin wannan maganar Anti Rahma ta hawo sama ta zauna a kan kujera tace

 Me aka yiwa Yayan ne?

Cikin fushi Mommy tace

 Ita da matar ubanta ne, kawai saboda ta fasa murfin tukunya shine za a zageta a gaya mata maganganun banza har ana cewa ta zo ta gaya min saboda raini.

Rahma ta taya su jimami da mamakin yanda murfin tukunyar zai sa ayi haka, tace

 To ai murfin tukunyar bai fi karfin uban Yusra ba da za a zageta a kai kwanukan nan da kai da kanka ma kake fasawa shine harda zagi. Kai wasu matan dai sun kwashe kayansu daga gaban ma aiki.

Sukayi shiru na dan lokacin, jim kadan Mommy ta zabura ta mike ta tsallake su ta wuce daki, jimawa kadan ta fito da mayafi ta dubi su Yusra tace

 Ku tashi muje, sai na ji uban da ya tsaya mata.

Sadik ne ya shigo yana rike da hannun Ummi yana karasa shigowa yace

 Mommy kowa yana cikin gida wannan yarinyar tana baya tana ta faman wasan kasa, kalli jikinta fa.

Rahma ta sha gaban Mommy tana mika mata Sumayya tana fadin

 Haba Yaya, ai bata isa kije ba saboda wannan maganar. Riketa muje sai na ji uzirinta, ai idan kika je raini sai ya shiga tsakani.

Ta karbi Sumayya ranta a bace; bata so Rahma ta hanata ba don da sai ta tafi da yaran ta sa Sadik ya mammari Aishan.

Tunda Abbansu ya daina shan zobonta a kan kullum sai yace cikinsa yana bashi matsala ta shiga damuwa saboda ta san yana samun biyan bukatarsa a can. Don haka ta fito da wannan dabarar domin ta san idan ranshi ya baci wajen abincin dare to daren ba zai yi dadi ba. Da farko gishiri tayi tunanin a dinga karawa sai kuma taga ai idan gishiri ne da an ci za a gane ta fi son abinda idan ya ci zai zargi ko wani abun ne na asiri aka zuba masa; don haka ta sami sabulu.

Ta dubi Rahma tace

 Da kin bari naje in ga idon mara kunya.

 Ai bata isa ba wallahi, wutsiyar rakumi ai tayi nesa da kasa.

Mayafin Mommy din ta karba ta yafa ta dubi Yusra tace

 Muje Yaya.

Mommy ta dubi Sadik wanda Nana ta gama yiwa bayanin abinda ya faru tace

 Ka bisu kaima saboda naga matar nan saitin ta yana gocewa.

Rahma tace

 Yayi zamansa ma na isheta.

 Gara dai ya biku, kuje Sadik.

Haka Rahma ta wuce Yusra, Nana da Sadik suka bita a baya suka nufi gidan Aishan.
& & ..

Su Yusra suna fita Aisha ta zubar da miyar, ta gyara wajen. Har zata dora sabuwar miya sai kuma taji hankalinta bai kwanta da tuwon ba ma don haka sai ta sauke ta sheka masa ruwa tunda daman rude kawai tayi.

Ta fito daga kicin din ta zauna a falo da niyyar idan tayi sallar magriba ta dafa musu jollof kawai.

TV a kunne take amma bata gane me ake fada a TV din tunani kawai take tana mamakin me ta tsarewa Zahra.

Tana nan zaune aka buga kofa don haka ta tashi ta

14 / 58