Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 58

54K to 57K   out of 172.2K words

an juya mata kan miji kuma dole ta dau mataki. Dole ta san yanda zata yi ta janyo hankalin mijinta ya dawo kanta kafin a saka shi ya koreta.

Abban bai dade da fita ba Jummai ta shigo gidan, don haka ta mikawa Jummai Sumayya tace mata ciwon kai yana damunta. Ta koma dakinta ta rufo kofa, ta zauna a gefen gado ta kafa tagumi.

Jimawa kadan ta tashi ta dauki wayarta ta fara lalube a ciki, har ta zo kan Yaya Murja sai kuma ta fasa dannan kiran. Idan dai Yaya Murja ce ta san hakuri kawai zata bata tace tayi addu a , kuma ai kullum tana addu a itama. Idan kuma ta kirawo Suwaiba itama hakurin zata bata don ita wannan bata ma san menene rayuwar ba.

Haka ta koma ta lalubo lambar Amina, kara daya wayar tayi aka dauka. Bayan sun gama gaisawa tace

 Kawata ina son ganinki yanzun nan, gashi kuma ni bazan iya fitowa ba balle na zo.

Tace

 To nima dai gani a office amma bari mu gani watakila zan iya fitowa nan da minti ashirin haka sai na karaso gidan. Allah yasa dai lafiya.

 Ina fa lafiya, ke dai kawai ki hanzarta ki zo.

Sukayi sallama suka ajiye wayar.

An dauki kamar awa daya domin har ta gaji da jiran Hajiya Amina kafin taji tsayuwar motarta a bakin gate. Cikin kankanin lokaci kuwa Jummai ta buga mata kofa ta sanar da ita isowar Aminan, nan take ta bada umarnin Aminan ta shigo ta sameta a dakin.

Tana shiga ta tura kofar ta karasa ta zauna a kusa da ita tana fadin

 Yaya dai Uwar Sadiku? Ya zan ganki cikin duwa bayan kuma jiya maigida ya dawo? Me yake faruwa ne?

Ta share kwallar da take kwarmin idonta tana ajiyar zuciya yayinda Aminan ta bita da kallon mamaki

 Ni za ayiwa bura uba Aminoni? Tunda ya sauka a garin nan yake min wulakanci saboda wata banzar matarsa; wai ni Abban Sadik ya kalla yacewa hadamammiya yana wani korata daga dakinsa kamar kare.

Ta zaro ido tana binta da kallo, sannan tace

 Daga dawowa Zahra? Ke kuwa me kika yi masa?

 Me aka gaya masa dai zaki ce?

 Allah kawata? Yanzu wannan matar tasa mai kama da abun tausayi ta kai ta kulla wata tsiya haka?

Nan ta karantowa Amina abubuwan da suka faru da yanda take jin janye hankalinsa akayi daga kanta aka saka shi ya zo yana yi mata wulakanci.

Aminan tace

 Ikon Allah, lallai kishiya bata kadan. Shi yasa wallahi ba zan taba bari Habibi ya kara aure ba sai inda karfi na ya kare. Ka rayu da mutum tun bashi da komai amma yanzu yana jin yana da bakin kiranki hadamammaiya, kai maza basu da mutunci!

 Ni yanzu kin san me nake so? Duk inda kudi suke dole na nemosu don kin san munyi da Malam Hatimu zai raba min su gaba daya.

 Hakane. To yanzu ina zaki sami kudin bayan tuntuni kike cewa baki da su, kuma kinga dai nima bani da su.

Tashi kawai tayi ta matsa gaban wardrobe dinta ta bude, ta dauki lokaci tana lalube sannan ta mayar ta rufe. Ta dawo kusa da Aminan ta zauna tana dauke da wani dan akwati mai dauke da sarkoki.

Ta dubi Amina tana dafa akwatin sarkokin tace

 Zan cire wasu daga cikin sarkokin nan ki kai ki sayar min, kafin a gama ciniki na dan sami kaina sai mu sa rana muje wajen Malam. Gara ayita ya kare kawai na gaji wallahi.

Cikin walwala Amina tace

 Yanzu kikayi magana Hajiyata, amma ki zauna yarinya kamar wannan tana ta faman kasa miki hankalin miji ai ba daraja.

Ta bude akwatin sarkokin ta dauko zobenta guda daya na gwal babba ta mikawa Amina. Ta dauko wani karamin saiti na sarka da dan kunne mai karamin kwado ta kara mika mata tana fadin

 Wannan ma na Yusra ne amma a hada dashi a sayar don na san wannan zoben ba zai kai dubu dari ba ma, nawa saitin kuma yayi girma da yawa. A sayar da wadannan abinda ya kama sai na cika tunda ina da wasu  yan kudaden.

Ta karba tana jijjiga kai

 Yanzu kikayi magana Uwar Saddiku, in sha Allah gobe da safe zan kaisu kasuwa. Zaki ji duk wani bayani.

 Shike nan, zuwa nan da kwanaki biyu zanyi kokari mu shirya don na samu muje Gaya tare, nafi so naje gani ga Malam na karanta masa abinda nake so.

Nan suka karasa hirarrakinsu da shirin yanda za su je Gaya wajen Malam Hatimu. Kafin azahar Aminan tayi mata sallama ta tafi.
& & ..

Wajen karfe biyu da Rabi Malam Sule ya dawo da Yusra, Rukayya da Nana daga makaranta; ita Ummi da yake a nursery take tun sha biyu aka dawo da ita.

Suna shiga gidan suka sami Jummai a kicin, Yusra ta dubeta tace

 Jummai ina Mommy?

 Tana sama, inaga dai bata jin dadi yau din nan.

Kafin ta gama jin amsar da Jummai ta bata ta haye saman da gudu, tana shiga dakin ta zauna a gefen gadon kusa da kafar Mommy

 Mommy har yanzu kanki bai daina ciwo ba?

 Um.

Cikin kosawa ta zaro ido tana duban Mommy tace

 Mommy kin san me na gani kuwa?

Kai kawai ta jijjiga mata alamar a a.

Tace

 Mommy Abba ne fa ya kai matarshi makaranta da ita da  yarta, kuma yanzu ma motarsa tana kofar gidan nata na san dauko su yayi ya tsaya yin wani abun a gidan.

Ta tabe baki tana gyada kai

 Yusra duk abinda Abbanku yayi ba zan yi mamaki ba, an riga an juyar masa da tunani sai addu a kawai. Inaga saboda na hana Malam Sule kaita makaranta da baya nan shine yanzu yaje ya kaita don ya bani haushi.

 Hmn! Lallai Abba.

Tayi kwafa tace

 Ki barni da su duk zan yi maganinsu, da sannu zasu dawo hannunna.

 Gaskiya dai abun nashi yayi yawa Mommy.

 Kije kuci abinci kuyi shirin islamiyya kada ku makara.

Ta sauko ta barta tana faman tunani.

Wato saboda ta hana Malam Sule ya kaita aiki shine shi ya dawo ya fara kaita, kwana biyun nan nata ne amma gaba daya a wajen Aisha yake karewa; don ta tabbatar wannan shigar da yayi gidan sai ya kaiwa Aishan kwananta. Lallai yanzu ta sake tabbatarwa da cewa Aisha bata barsa haka ba, don haka itama dole ta tashi tsaye. Kokari zata yi taga sun shirya domin bata jure fushinsa musamman da yake yana da inda zaije a debe masa kewa. Idan suka shirya sai ta fi samun natsuwar aiwatar da abubuwan da take shirin yi.
-------

Kamar kullum yauma Jummai ta gama duk wani aiki na cikin gida, ta fito tana share tsakar gida.

Can daga gefe daya akwai boys quarters mai daki biya; daki daya maigadin gidan ne Malam Sajo yake amfani da shi, daya dakin kuma kwanan nan da Sadik ya shiga SS 3 ne ya gyara saboda idan abokansa sun zo nan suke zama karatu kamar yanda yake fada.
Jummai bata share cikin dakunan, amma idan tana share tsakar gidan takan zagaya har farfajiyar boys quarters din ta share.

 Yan kwanakin nan kullum ta zagaya sharar haka take ganin murafun kwalba kamar kwalbar magani a watse a farfajiyar wajen. Bata san na menene ba amma dai ta san Sadik lafiyarsa kalau kuma Malam Sajo ma bai ce bashi da lafiya ba; kuma koda mutum bashi da lafiya ma ai akalla ayi kwana biyar kafin a shanye kwalba guda ta magani. Amma yanzu kusan kullum sai ta share murafun nan guda uku zuwa biyar.

Haka ta tattara sharar zata kwashe sai kuma ta sa hannu ta tsince murafun kwalabar guda hudu ta rike a hannunta sannan ta kwashe sauran sharar. Ta dauki kayan shararta ta juye a kwandon sharar tsakar gidan wanda yake kusa da gate.

Bayan ta juye ta nufo wajen Malam Sajo wanda yake zaune a gefen fulawoyi yana hutawa.

Tana isowa tace

 Malam Sajo wai ni baka da lafiya ne kwana biyun nan?

Da mamaki ya kalleta yana dan murmushi

 Ni kaina Jummalo? Nan da kika ganni lafiyata ras ai ko ciwon kai na manta rabon da nayi balle ace bani da lafiya. Wani ne yace miki bani da lafiya?

 A a

Ta karasa kusa da shi ta ware hannunta ta nuna masa tana fadin

 Gani nayi  yan kwanakin nan kusan kullum sai na share murafun nan na kwalabar magani a wajen dakin naka, to idan ana da lafiya ai ba za a sha magani ba.

 A to gaskiya dai wannan ba nawa bane, nima dai kwana biyun ina ganinsu. Amma sai dai ko ki tambayi Sadiku da abokansa tunda sune ke zama a daya dakin. Ni kam ai ko bani da lafiya bana shan maganin asibiti Malama Jummai shi ya sa kika ganni gatagau nan.

Tayi  yar dariya saboda yanda yake magana yana jijjiga jiki

 Ai kuwa gaka nan.

Ya kama haba yana sake duban murafun da har yanzu suna hannunta yana fadin

 To amma fa gaskiya ki bincika, ko kuma kiyiwa Hajiya magana ta bincika don gaskiya matasan yanzu abun tsoro ne tunda har magungunan ma sha sukeyi masu bugarwa da wani sirab suke kiranshi ko sirap ni ban rike ba. A dai binciki Sadiku da abokansa.

 Nima zargin da nakeyi kenan, bari mu gani ko zan samu fuska.

Ta koma cikin gida ta adana murafun ta cigaba da aikinta.

Har yamma abun yana ranta, tana so ta yiwa Mommy maganar amma tana tsoro don ta san yanda Mommy bata son laifin Sadiku, sannan kuma ko ta fada idan yazo yace ba haka bane babu abinda Mommy din zata yi a kai.

Sai can bayan la asar lokacin yara sun tafi Islamiyya shi kuma Sadiku bai dawo daga makaranta ba sannan Mommy ta sauko daga sama. Har yanzu tana da sauran damuwa sai dai abun da sauki tunda zuwa yau Talata ta samu Abban yana cin abincinta; damuwarta daya yau zai koma kwanan Aisha. Duk da haka tunda akwai tanadin da takeyi wannan ba damuwa bace.

A falo ta sami Jummai a zaune a bayan kujera tana hutawa saboda babu wani aiki da zata yi.

Bayan sun gaisa ta zauna ta kunna TV, tace

 Jummai ai sai ki fito daga bayan kujerar kiyi kallo kafin aminiyarki ta tashi daga bacci ta isheki da gwaranci.

Ta taso ta dawo kan kafet ta zauna daga gefe tana dariya.

Tana kaunar Zahra saboda yanda take kyautata mata, matsalarta duk da ta yaranta idan ta rasa yanda zata yi haka Uwar Sadiku take wuce mata gaba ayi komai. Ba zata so taga abinda zai cutar da ita ba ko yaranta su sami matsala; duk da tana son aikinta bata son abinda zai rabata da aikin.

Ta tashi ta wuce kicin tana fadin

 Ina zuwa Hajiya.

Jimawa kadan ta fito da murafun maganin nan a hannunta ta tsuguna a gaban Mommy ta mika mata tana fadin

 Hajiya kinga murafun maganin nan, a nan boys quarters na tsinto su,  yan kwanakin nan kuma kullum sai na gansu a shara. Na tambayi Malam Sajo yace ba nashi bane, amma fa kullum sai na gansu na share don yanzu nan haka gobe ma idan nazo shara sai na share wasu.

Ta karba tana dubawa

 Ikon Allah, to na waye?

Ta sunkuyar da kai
 To Hajiya sai dai ki binciki Sadiku tunda kinga yanzu yana shigo da abokai wajen, kuma kin san samarin zamanin nan basa raina abun maye tunda kinga har maganin ma sha sukeyi. Sai ka gama tarbiyyar naka yaron a sami bata gari su bata maka aiki.

 Eh, da wannan. Amma dai Sadiku ya san me yake ba zai sha wannan ba sai dai ko abokan nasa. Bari ya zo muji idan sune ma ai dole ya rabu da su kowa ya koma gidan ubansa ya dinga karatun a can.

 E gara kam a bincika Hajiya, yaran yanzu sai ana sa musu ido.

Ta koma ta zauna suka cigaba da kallonsu.

Suna nan zaune Sadikun ya shigo daga makaranta, Mommy ta tsayar da shi ta nuna masa murafun tana tambayarsa a kansu. A take yace shi bai taba gani ba gaskiya sai dai idan yaran makota ne suke watsowa ta katanga.

Ta gamsu da bayaninsa don haka ta juya ta bawa Jummai murafun tana fadin

 Kin ji ko? Ai dama na san ba shi bane don abokan nasa ma duk na san su. Zai iya yiwuwa yara ne da suke wasa da shi kin san suna yin mota da shi. Kuma idan barnar su Sayyad ta tashi zasu iya watsowa nan din. Kawai ki dinga sharewa idan kin gani.

Ta karbi murafun tana fadin

 To Hajiya, in sha Allahu za a dinga sharewa.

Ta kwashe ta nufi kicin tana zullumi a ranta; domin tabbas bata jin yaran makota zasu jefo wannan murafun tunda ta san yara kanana ne. Ta dai fi zargin Sadikun da abokansa amma dama ta san a wajen Hajiya duk abinda Sadiku ya fada shine gaskiya.

Don haka ta zubar da murafun ta bar maganar tana fatan Allah ya sa abinda Sadikun ya fada gaskiya ne.
__

Kafin ya koma kwanan Aisha saida Zahra ta tabbatar ya sauko daga fushin da yake da ita; da taga kamar ba zai daina shareta ba ma dakanta ta same shi a daki ta bashi hakuri. Harda kukanta duk da dai a cikin ban hakurin ta gaya masa babu abinda tayi da niyya komai ta bayarda dalili. Ya riga ya santa da wannan halin ba zata taba daukar laifinta ba, shi kuma baya son kukanta don haka ya hakura da sharadin ba zata sake yi masa irin haka ba. Dare nayi ya wuce wajen Aisha.
__

Yana fita wajen Aisha a daren ta kirawo Amina don taji yanda akayi da gwal din da ta bayar a siyar. Tayi mata bayani an sayar sai dai gaba daya basu kai dubu dari biyu ba; bata ji dadin hakan ba saboda tana bukatar akalla dubu dari hudu ta tafi da su domin so take ayi mata aiki mai kyau musamman da yake zuwa yanzu duk wani ragowar hakuri da zata iya yi ya kare.

Tace

 To ki ajiye min kudin na san zuwa karshe wata na danyi ciniki wasu sun biya bashi ba zan rasa dubu dari ba, in ya so dubu dari ko rantowa sai nayi.

 Ko kuma ki dan tsara Abban ya baki ba.

 Hmmm! Kawata barshi kawai ai yanzu baya hayyacinsa, zan nemo dai in ya so sai ya biya idan ya shiga hannuna don wannan aiyukan da kayan gyaran da na sha kafin ya dawo duk wallahi sai ya biya.

Suka karasa hirarrakinsu suka ajiye waya.

Haka ta kwana tana tunanin inda zata sami rancen dubu dari.

Suwaiba zata fara tambaya tunda ta san tana aiki kuma ko bata da shi ta san zata ranto mata a wani wajen.
Kawai dai dole ta jira sai karshen wata ta dan hada ciniki, gashi yanzu watan ya kama. Amma bata da wani zabi haka zatayi ta zaman hakuri har karshen wata.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

20

Baifi sati daya da dawowa ba ta gama hada kudin motar da take son siya, don haka ranar da ya kaita ta mayar da Amira gida sai da ta sakashi ya biya da ita gidan Yaya Abubakar. Baya nan don haka ta barwa Anti Fauziya sako kan zata tura masa kudin ta account dinsa.

Duk wannan shirin da take yi bata bari Abban ya sani ba, bata son ta gaya masa don idan ta gaya masa akwai yiwuwar Zahra taji labari wanda ta san sai ta san yanda tayi ta sa ya hana sayen motar.

Sati biyu da gama maganarsu da Yaya Abubakar ya kirawota ya sanar da ita gobe zai kawo mata motar.

Abban yana wajenta amma a daren zai koma wajen Zahra.

Yana zaune a falonta bayan sallar magriba da faranti gireba a gabansa yana ci suna hira tace

 Yallabai gobe fa Yaya Abubakar zai kawo min motata, ka san tun kwanaki nace maka zan sayi mota.

Da mamaki ya dubeta yace

 Ai na zata kin fasa, ni da nace ki bari zan saya muku kowa keda Zahra.

 Haba dai, to yanzu ba shikenan ba na hutar da kai in ya so sai ka sayawa Mommy din kawai tunda ni na riga na saya. Ka san fa tun kafin a fara maganar bikinmu kudin motar suke a hannunsa shi yasa yanzu yana yi min maganar kawai nace ya siyo.

 To Allah ya sa albarka, Allah ya tsare hanya. Ko nima na sami ta zaga gari ko kuma idan na fara neman aure na sami ta tsara bazawarata.'

Ta harareshi, ya kauda kai yana kallon gafe. Ta sa kafa ta dungureshi tana zumbura baki tace

 Bazawara ko?

Yana dariya yace

 Au, ashe fa na cike gidan.

Gaba daya suka sa dariya.

Shima yaji dadin sayen motar amma dai ya so ace ta bari shi ya saya, sai dai hakan ma yayi masa dadi tunda a halin yanzu dama baya son sayawa Zahra mota domin ya kula gaba daya ta canza hali.

Haka suka karasa hirarrakinsu yayi mata sallama ya tafi ya barsu ita da Rukayya.

_

Ranar babu aiki saboda gwamnati ta bayar da hutu. Yana zaune a falon sama ya gama cin abinci tana zaune suna dan taba hira.

19 / 58