Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   49 / 58

144K to 147K   out of 172.2K words

hijabi tace

'Muje na gani Jummai.'

Jummai da Mama suna shiga farfajiyar gidan Abban shima ya tura gate din ya shiga, yana shiga suka juyo yayinda Abban yace

 Dr. an tasoki ko?

Kafin ta amsa ya dubi Jummai yana fadin

'Wai me yake faruwa ne Jummai, me ya sami Mommy din.

Mama ce ta bashi amsa tace

'Shine zamu je mu gani.

Suka shige gidan gaba daya kai tsaye suka haye saman Abban yana biye da su. Suna shiga Jummai ta ja hannun Mama suka wuce yayinda Abban ya tsaya a kan Yusra yana tambayarta

'Yusra me ya sami Mommy din? Kukan me kikeyi?

Bata bashi amsa ba sai hawayenta da yake karuwa. Zuwa yanzu shima hankalinsa ya Kai koluwar tashi duk da bai fahimci abinda yake faruwa ba to amma me zai sami Zahran?

Ya mikawa Yusran hannu yana fadin

'Tashi muje mu gani ga Dakta nan ta zo, yanzu zamu t& .

Muryar Jummai ce ta katse shi yayinda cikin daga murya take fadin

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!

Cikin hanzari ya rabu da Yusran ya nufi dakin, yayinda itama Yusran ta dafa masa baya kamar zata ture shi. Kusan tare suka shiga dakin suka tsaya a gefen gadon inda Mama take kokarin gyarawa Zahran kwanciya. Jummai ya fara kalla wadda take durkushe a gaban gadon da hannuwanta a kanta hawaye yana gudu a kan fuskarta da bakinta a bude. A firgice yace

'Dakta me yake faruwa ne?

Ta jijjiga kai

'Ai sai dai muyi hakuri, Mommy Allah yayi mata rasuwa few hours ago don gashi har ta fara sandarewa.

Zubewar Yusra suka ji wadda tana jin ance Mommy ta rasu ta sume.

Take gaba dayansu sukayi kanta, Mama ta dan tabata sannan ta tallafo kanta ta dubi Abban tace

 Dauketa mu fita da ita daga nan.

Sai da yayi da gaske ya iya daukar Yusran saboda yanda jikinsa yake karkarwa, gashi idanuwansa basa gani sosai saboda yanda hawaye suke fita babu kakkautawa. Kansa yana juyawa kafafuwansa suna neman su kasa daukansa haka ya karasa falo da kyar ya kwantar da Yusra a kan kafet din tsakar falon. Yana ajiyeta ya juyo ya nufi komawa dakin yayi da Mama ta tsuguna a gefenta tana kwalawa Jummai kira

'Jummai bani ruwa.

Cikin sanyin jiki ta fito daga dakin tana share hawaye; fitowar tata tayi dai-dai da shigowar sauran yaran gidan daga makaranta, Rukayya ce kawai bata tashi ba saboda ta tsaya lesson. Turus suka tsaya ganin Yusra a kwance ga Mama a kanta. Ummi ce ta fara magana tana fadin

'Jummai Yaya Yusra bata da lafiya ne na ganta a haka.

Mama tayi sauri tace

'Eh, bata da lafiya amma yanzu zata tashi.

Sumayya tace

 Bari na cewa Mommy mun dawo.

Kafin a bata amsa ta nufi dakin. Mama tayi sauri tace

'Zo Sumy, zo nan ki gani. Ku zauna a nan tukunna Abba ma yana ciki yanzu zai fito.

Cikin sanyin jiki suna karewa kowa kallo suka wuce suka zauna a kan kujerar zaman mutum uku suka jeru kamar masu jiran wani abu.

A hankali Mama ta dinga shafawa Yusra ruwan har aka samu ta farfado, tana bude ido tayi yunkurin tashi Mama ta dafe ta tana fadin

'Yi hakuri Yusra kin ji, kada ki jiwa kanki ciwo kiyi hakuri kiyi tayi mata addu'a kawai.

Ta fashe da kuka tana fadin

'Mutuwa tayi Mama! Wayyo Mommy Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un!

Ta fada jiki Mama wadda ta rungumeta tana fitar da hawaye.

Daidai nan Abba ya fito daga dakin yana share hawaye. Da gudu Ummi ta tashi ta fada jikinsa tana fadin

'Abba ina Mommy ai bata mutu ba ko?

Sauran yaran da suke biye da ita suka tashi da gudu suka shige dakin yayinda Jummai ta bisu da gudu. Itama Ummin sai ta saki Abban ta bi bayansu. Kukansa ya kara tsananta yayinda yake ta maimaita

'Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!

Ya nufi dakinsa ya shige ya turo kofar. Yana shiga ya kirawo Yaya Bello ya sanar da shi sannan ya kirawo Malam Liman ya sanar da shi. Bashi da kuzarin da zai sake kiran wani don haka ya jefa wayar kan gado ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa ya saki hawayen da yake ta faman makalewa.

Yanzu shikenan Zahra ta rasu? Wannan din wacce irin mutuwa ce haka ba tare da wani notice ba. Ya dafe kirjinsa wanda yake kara kuntata yace

'Astagfirullah.'

Ya mike ya shige bandakinsa ba tare da ya san abinda zai yi a bandakin ba.

Daga nan falon inda su Jummai suke zaune da yaran suka jiyo sallamar namiji daga falon kasa. Jummai ta mike ta ajiye Sumayya tana share hawaye ta fice daga falon. Jimawa kadan ta dawo saman, ta karewa yaran kallo; yanda suke a gigice gaba daya bata ga alamar akwai wanda zai iya kirawo mata Abban ba don haka ta wuce ta kwankwasa kofar dakin nasa.

Ya bude yana share ruwan alwalar da yake fuskarsa, yana budewa tace

'Malam Liman ne a falon kasa da mutane suna magana.

Ya daga mata kai ya koma ciki.

Yana shiga ya dauki wayarsa ya kirawo Aisha ya sanar da ita halin da ake ciki, Bai saurari tambayoyin da take yi masa ba ya ajiye wayar ya fito ya nufi falon kasa. A nan falon Abban ya zauna shi da su Malam Liman suna jajantawa suna jiran isowar Yaya Muhammadu da Yaya Bello.

Basu dade da zama ba Rukayya ta shigo, wadda Malam Ali ne ya koma makaranta ya daukota da ya fahimci abinda yake faruwa. Bai gaya mata abinda ya faru ba don haka da ta hango Abba a falo sai ta dafe kirji tayi dan gajeran murmushi, ta kasa magana domin ta kula zaman nasu ba na lafiya bane don haka da gudu ta haye sama.

Yanda ta ga Yusra a kashingide kanta babu dankwalu da Mama zaune a kusa da ita ya sa ta karasa falon da gudu. Ta zube a gaban Yusra ta dafa ta tana haki tace

'Yaya Yusra me ya sameki? Ina Mommy?

Yusran ta kara rushewa da kuka ta matso ta rungume Rukayyan tana fadin

'Mommy ta mutu Rukayya, ta mutu ta barmu.

Da karfi Rukayyan ta banbare Yusra daga jikinta ta tureta, ta fara bin fuskokin  yan uwanta da kallo. Ta kama hannun Mama wanda yake dafe da cinyar Yusra yayinda ta sa hannunta na hagu ta dafe kirjinta tana fitar da hawaye tana fadin

'Mama ai Mommy tana nan ko?

Kafin a bata amsa numfashinta ya fara yin sama don haka Mama ta saki Yusra ta dafe Rukayya tana umartar Jummai ta debo ruwa.

A daidai nan Saddiku ya shigo falon; wanda tare da Yaya Bello suka zo gidan. Ya kare musu kallo na dan lokaci da jajayen idanunsa. Kai tsaye ya shige dakin Mommy. Kallo daya yayi mata ya tabbatar ta mutu, nan ya tsuguna a gaban gadon yana kallon gawar yana fitar da hawaye.

Daidai lokacin da aka fara samo kan Rukayya a lokacin Aisha ta shigo falon saman. Kusa da Jummai ta karasa tana fadin

'Jummai me yake faruwa ne ban gane bayanin Abban ba.

Cikin hawaye Jummai tace

'Wallahi Anti ni yau ko haduwa bamuyi da Mommy ba, Yusra tace min bata jin dadi ta kwanta. Muna kasa ni da Yusra muna hidimar mu Yusran ta shigo ta koma tana ihu Mommy babu.

'Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.

Ta tashi ta karasa kusa da Rukayya wadda Mama take kokarin samo kanta, tana tsugunawa a wajen Rukayyan ta fado jikinta ta rushe da kuka tana fadin

'Anti Mommy! Mammy ta tafi ta barmu!

Rungumeta tayi itama ta fashe da kuka tana bin yaran da kallo na tausayi yayinda rasuwar mahaifinta ta dawo mata sabuwa, don a lokacin bata fi shekarun Rukayyan ba.

Jimawa kadan  yan uwan Zahran suka shigo, su Yaya Murja suka zauna nan wajen yaran yayinda su Yaya Muhammad suka shigo suka duba gawar.
Nan da nan aka sauka da ita falon kasa inda a nan ne su Yaya Murja zasu yi mata wanka da sutura da taimakon malamai mata guda biyu da Malam Liman ya kirawo domin wankan.

& & &
Kafin wani lokaci gida ya dinke da mutane. Nan da nan aka yi mata sutura maza suka dauka aka nufi masallaci domin yin Sallah saboda can ya dan fi sarari domin babu laifi ta sami mutane.

Ana idar da sallah aka kwasa aka tafi makabarta.

Abba da Saddiku suna kan gaba an kama gawa za a saka a rami Saddiku ya saki ya dafe kai, wani daga gefe yace

'Subhanallah! Ku rikeshi zai fadi.

Nan da nan aka dafeshi, aka karasa sakata. Shima Abban da kyar ya jure tsayuwar saboda yanda kansa yake sarawa. Aka sakata aka rufe mutane suka tattaro suka dawo gida.

Haka aka cigaba da karbar gaisuwa. Itama Aisha hutun aiki ta dauka don a gidan makokin take wuni sai dare take komawa gidanta.

A hankali har aka kwana uku. Ranar kwana uku bayan sallar isha'i ana zaune a falon kasa Suwaiba kanwar Zahran ta dubi Yaya Murja tace

'Yaya ba zaki tafi da Sumayya ba kuwa? Ni nayi nayi da ita tace ba zata bini ba kuma wallahi tunda akayi rasuwarnan fa bana jin ta ci abincin kirki.

Kafin ayi magana Sumayya ta noke a bayan Rukayya tace

'Ni ba zani ba.

Aisha ta mika mata hannu ta janyota tana fadin

'Wajena zaki kwana ko?

Ta daga kai alamar eh. Aishan ta dubi Yaya Murja tace, bari a jima kadan idan muka je can sai taci abincin.

Wajen karfe tara Aisha ta mike ta ja hannun Sumayya da Ummi ta yiwa su Yaya Murja sallama ta fice.

Cikin hanzari Yusra tabi bayansu. Motsin da Aishan taji ya sa ta juya, ganin Yusra ya sa ta tsaya don ta zata wani abun zata fada ko ta bawa  yan uwanta.
Ta matso dab da Aishan ta sha gabanta a lokacin da Ummi da Sumayya har sun kusa isa gate don haka suka tsaya daga nan.

Murya kasa-kasa cikin gadara Yusran ta kalli Aisha tar tace

'Ina ruwanki da su da zaki tafi dasu?

Da mamaki Aishan ta bude baki zatayi magana Yusran ta daga mata hannu ta cigaba

'Ki bar ganin Mommy ta rasu ki zata zaki maye gurbinta, baki isa ba kuma ba zaki taba isa ba. Nan ba gidanki bane kada ma ki taba tunanin zan barki ki shiga dakin uwata wallahi kin yi kadan, kuma idan wani abu ya sami su Ummi wallahi sai kin gwammace zama da Mommy da zama da ni. Eye service kawai.

Kafin Aishan tace wani abu Yusran ta wuce ta koma ciki ta barta da baki a bude tana mamaki. Sai da Ummi ta gaji ta dawo ta taba Aishan sannan ta tuna ya kamata su tafi ne.

Ta ja yaran suka fice tunani kala-kala yana yawo a kwakwalwarta.

UWAR SADDIKU

Written by

Sakina Yazid
(Innar su Amal)

41

Ranar da Zahra ta kwana hudu da rasuwa bayan azahar Abba ya sallami mutane, ya sanar da su Yaya Muhammad an tashi daga makoki. A cikin gida ma an sanar da mata don haka nan take aka fara watsewa, itama Amina wadda da ita aka yi zaman kwanaki ukun tayi musu sallama ta tafi. Zuwa la'asar ya zama gidan babu kowa sai Yaya Jummai da Rahma wadanda suka ce sai washegari zasu tafi inda zasu bar yaran da Goggo Binta wadda goggon su Zahran ce; idan an yi kwana bakwai ita kuma zata tafi.

 ----
Ranar kwana biyar gidan ya dan sami natsuwa domin mutane sun yi saukin zama, sai dai da an zo babu dadewa ayi musu gaisuwa a tafi. Yaran gaba dayansu suna cikin tsananin damuwa, musamman masu wayon daga kan Saddiku zuwa Nana. Ummi da Sumayya dai suna dan sakewa sai dai tun ranar da aka kwana hudu Yusra ta hansu bin Aisha idan ta shigo don haka suka rage samun wanda zai saka su a gaba su ci abinci.

Abba yana kokarin kulawa da su don bai koma aiki ba, sai dai shima a cikin damuwar yake wuni. Ya kasa gane abinda yafi yi masa zafi a ransa; mutuwar Zahra ko kuma halin maraicin da yaransa suka shiga. Yana iya kokarinsa wajen basu hakuri sannan kuma ga Goggo Binta ma tana kokari amma duk da haka da damuwa yake ganinsu.

Bayan an idar da sallar isha'i sai da ya siyowa Ummi yoghurt sannan ya shiga gidan. Rukayya ya samu a falo tana kwance kamar mai bacci, sai dai yana shiga falon ta tashi zaune. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya mika mata ledar yoghurt din yace ta kaiwa Goggo nata sannan ta raba sauran ita da  yanuwanta.

Ta karba ta nufi daki domin kaiwa Goggo nata.

Tana karba ya wuce sama, kai tsaye dakinsa ya shige ya turo kofa ya zauna a gefen gado yana tunani. Bai dade da zama ba ya dauki mukullinsa ya fito ya rufe dakin; sai da ya leka dakin Sadik ya sanar da shi kada ya rufe gidan don yanzu zai dawo sannan ya fita.

Gidan Aisha ya nufa; tun ranar da akayi rasuwar rabon da ya shiga gidan nata; sai dai kawai yana ganinta a gidan Zahra. Yau ne kawai zai ce bai ganta a gidan ba.

Da sallama ya shiga falon, tana zauna a kan kujerar zaman mutum uku da waya a hannunta yayinda TV take kunne. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya zauna, ta wuce kicin ta dauko masa ruwan sanyi. Ta zuba masa ruwan a kofi sannan ta zauna a gefensa.

Suka gaisa ta sake yi masa gaisuwa; bayan ya amsa tace

'Ya yaran?

Cike da damuwa yace

 Alhamdulillah. Yau ban ji ki a cikin gidan ba.

Ta kawar da kai tana dan gatsina fuska tace

 Kaina ne yake ta ciwo tun asuba, shi yasa tun safe da na shiga na ga basa bukatar komai na dawo na dan kwanta.

Suka yi shiru gaba dayansu kowa da abinda yake ransa.

Ba wai ciwon kai ne ya hanata zama a gidan ba; ta dai gaji ne da yanda Yusra take yar mata da maganganu tana kokarin sai ta tsokaneta sun yi fada. Tunda Yaya Murja ta tafi Yusran ta daina raga mata sai dai idan bata shiga gidan ba, dama kuma ko da ana zaman makokin ma tana kula da yanda Yusra da Nana basa gaisheta sai dai idan ita ta yi musu gaisuwa. Don haka ma ita a yanda ta shiga yau da safen ta yanke ba zata sake shiga ba sai an kwana biyu.

Abban ne ya mika hannunsa ya shafi kumatunta yana murmushi yace

'To tunanin ya isa haka.

Tayi  yar dariya ta matsa jikinsa ta zauna, ta kwantar da kanta a kan kafadarsa. Suka sake yin shiru na dan lokaci, basu jima ba Abban ya kirawo sunanta. Ta daga fuskarta daga kafadarsa ta kalleshi tana murmushi, da ya tabbatar ya sami hankalinta sai ya cigaba

'Jibi in Allah ya kai mu za ayi kwana bakwai, kuma a ranar zan koma aiki. Zan sa a gyara miki daki a can gidan zuwa next week sai ki koma. Kin ga daman saura wata uku kudin hayar gidan nan ya kare sai na basu gidansu.

Duk da ta san zai yi wannan maganar amma sai da maganar ta shammaceta. Ta dan jijjiga kai domin ta kore damuwar da ta lullubeta, ta lalubo muryarta ta hanyar yin gyaran murya sannan ta muskuta kadan da fuskanceshi tace

'A dai dan kara lokacin ba nextweek ba don na dan kara shiryawa.

'Babu damuwa take your time. Ai ba lallai sai kin kwashe kayanki gaba daya ba a lokaci guda. Idan aka gyara dakin; wanda shima temporary ne kinga sai ki kwashi iya kayan bukatarki a hankali a kwashe sauran. Kafin nan ma kin ga an gama gyara miki daki a saman.

'Uhm, hakane. In sha Allah in na shirya zan maka magana.

'Yauwa. Ki dai shirya da wuri don kin ga Goggo Binta jibi zata tafi, ba zai yiwu a bar yaran su kadai babu Babba a gida ba tunda nima ranar zan koma aiki.

Suka dan taba hira wadda duk yawanci shi kadai yake zancensa, daga baya yayi mata sallama ya koma wajen yaran.

Yana fita ta bi bayansa ta rufe gidan ta dawo ta kintsa tayi shaf'i da witri, ta gyara zama a kan daddumar. Ta daga hannunta ta karanto ayatul kursiyyu da sauran azkar, ta bude baki zata roki Allah amman ta rasa yanda zata jera kalmominta. Sai da ta gaji da rike hannunta a sama ba tare da ta samo kalmomin ba don haka cikin damuwa ta karanto  Rabbi inni lima anzaltu ilaiya min khairin fakeer'.

Ta sauke hannuwanta cike da damuwa da kuma saka rai cewa Allah ba zai jarrabeta da abinda ba zata iya ba. Ya za ayi ta koma wannan gidan? Ba gidan take tsoro ba amma ba zata iya zama da Yusra ba. A zamanta da Uwar Yusra; duk da sai su kusan shekara basu hadu ba; amma sharrin uwarta bai barta tayi zaman aure cikin nutsuwa ba to yanzu me zai faru idan ta fara zama da Yusra? Yarinyar da ta tare ta ido na ganin ido ta gaya mata ba zata barta ta zauna lafiya ba. Gaskiya ba zata iya zama da Yusra ba. Bata san da yaren da zata gayawa Abba cewa ba zata koma gidan ba domin abu ne da aka saba, sannan kuma bata san dalilin da zata bashi na kin komawar ba. Tabbas da ace babu Yusra da Nana to zata koma ta rike masa ragowar yaran; duk da cewa tana sane da halin ko in kula din da shi yake da nata yaran wadanda ubansu ya mutu tun kafin uwar yaransa ta mutu.
Ta san ba zai taba iya yi mata adalci ba tsakaninta da yaransa domin ta gani a gidaje da dama, duk wanda ya tashi cewa zai yi tana cutar marayu. Bata so ta zama silar raba da da uba don haka tana ganin idan aka takura ita kam sai dai ta hakura da wannan auren; tunda ma zuwa yanzu babu wata riba da zata iya nunawa tace ta ci da wannan auren. Haka ta kwanta cikin damuwa saboda abu daya ta sani ba zata iya zama da Yusra a sami zaman lafiya ba.

49 / 58