Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 58

42K to 45K   out of 172.2K words

bude, batayi mamaki ba da ta gansu don ta san sai wani abun ya biyo baya.

Babu yabo babu fallasa Rahma tayi mata sallama don haka ta wuce ciki bayan ta cewa Rahman Bismillah. Suka karasa falo suka zauna, ita Yusra sai faman muzurai takeyi tana murgude baki shi kuwa Sadik ko zaman ma bai samu yayi ba, tsayawa yayi a kansu yana muzurai kamar wani soja. Ta bi su da kallo, har zata cewa Sadik din ya zauna sai kuma ta fasa don ba ita ta hanashi zaman ba. Bata son kallon da yake mata; tunda take a rayuwarta bata taba kallon idon mutum taga zallar kiyayya ba kamar yanda take gani a idon Sadiku.

Rahma ta katse mata tunanin tana gaisheta, babu izgilanci ko alamar fushi a maganar Rahman don haka itama ta dan saki jiki suka gaisa ba yabo ba fallasa.

Rahman tace

 Yar taki ce tace ta fasa murfin tukunya kuma sai tazo da maganganu marasa dadi, shine nazo na ji wai me ya faru ne?

Kamar ba zata yi magana ba, ta dan kauda kai tana murmushi sannan tace

 Haba dai murfin tukunyar me? Abinda kaima a hannunka yana fashewa.

Nan ta mayar mata da abinda ya faru da kuma sabulun da ta kama Yusran da shi, tace

 Murfin tukunyar bai dameni ba kwata-kwata amma ace yarinya kamar Yusra ta san yanda zata bi ta cutar dani saboda ina auren babanta ai kinga dole na zata aikota aka yi.

Mamaki ya cika Rahma, ta juya ta kalli Yusra. Yanda yarinyar tayi tsamo-tsamo ya tabbatar mata lallai ta aikata. Ta mayar da dubanta ga Aisha tace

 Ikon Allah! To don Allah kiyi hakuri, wallahi abune na yarinta don na tabbatar babu yanda za ayi Mommy ta turota tayi wannan aika-aika. Kuma na tabbatar da taje bata gaya wa Mommy din abinda tayi ba, ta dai ce ta fasa miki murfin tukunya kinata fada. Zan yiwa Mommy din bayani in naje, yara ne sai hakuri in Sha Allah na san haka bazata sake faruwa ba.

 Hmmm! Babu komai ai ya wuce.

Rahma ta mike tana fadin

 Bari mu koma.

Sukayi mata sallama suka fice.

Gaba daya yaran haushin Rahma suke ji saboda su zuwa sukayi ayiwa Aisha rashin mutunci amma ta zauna tana bada hakuri.
Koda suka koma wajen Mommy din haka Rahma ta zauna tayi mata bayanin abinda Yusran ta aikata; sai dai daga yanda Mommy din take bata amsa ta san bata gamsu ba. Domin daga karshe ma cewa Rahman tayi sharri ne Aishan takewa Yusra, itama bata san sharrin Aishan bane shi yasa ta kama zancen.

Haka ta taso jiki babu kwari ta sauko daga falon saman tana jiyo hayaniyarsu. Tabbas daga wannan dan bayani da suka mayar ta gamsu ko da ba Mommy ce ta sa Yusra wannan aika-aika ba to da saninta aka aikata; haka ta zauna tana mamakin yaushe Zahra ta zama haka, ta watsar da tarbiyyar yaranta saboda kishi.
& & &

Ko da ma su Rahma basu zo ba dama Aisha bata yi niyyar gayawa Abban Sadik abinda ya faru ba, ba ayi abun a gabansa ba kuma zuwa yanzu ta fahimci Zahra mace ce da ta iya juya zance don haka ta barwa ranta abun. Amma idan suka gaya masa wani abu to tabbas da shi da su bazasu ji dadinta ba.

Sai dai itama Mommy din ta gane idan ta kai masa wannan maganar abun zai zama kamar ta kai karar kanta ne, don haka itama sai tayi shiru. Suma yaran ta gargadesu kada su gayawa Abbansu kuma kada su gayawa Rukayya wadda lokacin da akayi abun tana daki tana hadda.
& & & .

Wajen fiye da sati biyu kenan rabon da ya sha zobo a wajen Mommy, musamman da daddare. Don haka yanzu normal yake harkarsa, duk yanda yake so yana samu a wajen Aisha tunda ita Zahra tana jego. Baya son ya zargeta da zuba masa abun da zai taba lafiyarsa amma dai yana so ya tabbatar ko don ya gane abunda ya haifar masa da wannan matsalar.

Tun kafin ya karaso unguwar ya yiwo mata waya yace ta ajiye masa shayi in ya zo zai sha kafin ya wuce tunda kwanan Aisha ne.

Da murna ta tashi da kanta ta shiga kicin don dama tunda ta haihu ko zobon zata hada masa bata bari Rahma tayi kuma ko ya sha ko bai sha ba da kanta take zubar da sauran ba tare da mutan gidan sun sani ba.

Nan da nan ta dafa shayin ta juye a flask ta hada da kofuna biyu ta kai dakinta tunda yanzu mafi yawancin lokuta idan ya dawo tana dakinta.

A dakin kuwa ya sameta, tun kafin ma yace ina shayin ta zuba masa. Ya zauna a kan dadduma ya jingina da gadonta yayinda ita kuma take kan gadon. Yana shan shayin suna hira; a zuciyarsa yana fatan abinda yake zargi kada ya tabbata. Yana ji a jikinsa cewa Zahra ba zata iya cutar dashi ba ko da kuwa don kishi ne.

Sai wajen tara da rabi sannan yayi mata sallama ya tafi; yana ta mamakin yanda yau din take ta walwala fiye da  yan kwanakin baya, tana ta faman kakalo hira har ya shanye shayin.

A wannan daren duk yanda yake bukatar Aisha kasa yin komai yayi, sai jagwalgwala ta kawai da yayi. Sosai ta firgita saboda da ta fara murna cewa matsalarsu ta kare, don haka saida ya dauki lokaci yana kwantar mata da hankali yana bata tabbacin ya riga ya sami magani don haka daga wannan daren ba za a sake samun irin wannan matsalar ba.

Haka suka kwana tana fatan Allah ya sa da gaske yake ya sami maganin yayinda shi kuma yake matsanancin mamaki na yanda za ayi ace Zahra tana zuba masa wani abu a shayin don ya kasa kusantar Aisha.

Wayewar garin ranar ya kama kwananta ne ita Zahran, har dare yayi ya shiga wajen nata. Yayi niyyar ya tunkareta da maganar abinda take zuba masa a zobo amma kuma har suka kwanta bacci yana wasi-wasi.

Duk saukin kanta da halayenta masu kyau da yake so amma fa bata taba karbar laifinta; haka zata saka shi a gaba suyi ta musu a kan lallai sai ya fahimci ba itace mai laifi ba sai dai idan wani ne mai laifin. Don irin wannan ma ya san ba zata taba yarda tace ta saka masa abu a zobo ba, idan taga dama ma haka zata sa kuka ta juya zancen a kan cewa shine zai zargeta tayi ta rigima har sai ya bata hakuri.

Haka har gari ya waye sai dai kawai kallonta da yake yana mamaki; sau biyu tana tambayarta me yasa yake kallonta shi kuma sai yace mata babu komai.

Haka ya kare wannan kwana biyun ba tare da yace mata komai ba.
Kuma duk cikin kwana biyun nan batayi zobo ko lemon tsamiya ba, shayi ma kuma da bai nema ba bata bashi ba. Sai na safe kawai wanda yace a daina saka komai a ciki a dinga bashi ruwa kawai zai hada shayinsa da kansa.

Ranar da zai koma kwanan Aisha ranar ne tayi zobo, lafiyayye sai kamshi ne yake tashi ga sanyi har gumi jug din yakeyi. Duk yanda yake son zobon nan haka ya hakura, har ta cika masa kofi ya dubeta yace

 Kai ba zan sha zobon nan ba, bana jin dadin cikina sai dai ko wani lokacin.

Suka cigaba da hirarsu a dining table, shi yana cin abinci ita kuma tana taya shi hira da yake lokacin wajen karfe biyar ne don haka ita ta riga taci abincinta na rana. Ya dubeta ya tura mata kofin zobon yace

 To ai sai ki shanye wannan da kika zuba.

Tayi  yar dariya tace

 Ni kam na sha nawa, wannan ai naka ne. Sai dai idan baka sha ba na ajiye da daddare na sha.

Ya cigaba da cin abincinsa; dama bai yi zaton zata sha ba tunda ta san ta saka wani abun a ciki don tabbas ya san da babu wani abun a ciki da tuni ta shanye zobon nan.

Ya kusa gama cin abincin Sadik ya shigo daga makaranta, ya riga ya shiga SS 2 don haka idan aka tashi daga makarantar yana tsayawa lesson sai biyar suke tashi. Bayan yayi musu sannu da gida ya dubi jug din zobon nan yana gumi yace

 Abba in dauko kofi in sha zobonka, wallahi zafi nake ji yau an yi rana.

 Ai ba ma sai ka dauko kofi ba dauki wannan ka sha.

Abban ya bashi amsa yana nuna wanda Mommy ta riga ta zuba masa a kofi.

Da sauri Sadik ya karaso da niyyar daukan kofin, kafin ya karasa ta balla masa harara tana kokarin buge masa hannu

 Naka zobon ai yana kicin da abincinka ka shige ka dauka.

 Mommy wai na sha wannan din kafin na cire uniform.

 To ki barshi mana tunda ba sha zanyi ba.

Abba ya fada yana kokarin daukar kofin ya mika masa, tayi wuf ta rigashi daukewa tana fadin

 Allah ba zai sha ba sarkin rashin kunya, yaje ya sha nasa.

Sadik ya jefa jakarsa kan kujerar falon ya shige kichin yana gunguni, ta mayar da kofin ta ajiye tana ta wani kumbura.

Sai da ya gama cin abincin tsaf ya dubeta yace

 Zahra.

 Na am.

Ta amsa da alamun jikinta ya dan yi sanyi.

Ya kalleta suka hada ido, ta kau da nata idon saboda yanda yake kallonta kamar yana kokarin karanto wani abu a zuciyarta.

Yace

 Ko dai akwai wani abu a zobo nan ne wanda ba Sadiku aka zubawa ba ni aka zubawa.

Ta dan dirirce sai kuma tayi kokari ta waske

 Ban gane ba? Kamar me kenan? Bayan ga irin zobon nan Sadiku ya debo daga kicin kuma ya sha.

 To me yasa ba zai sha wannan ba kema kuma ba zaki sha ba?

Ta dan bata rai sannan tace

 Gani nayi ai ba tarbiyya bace na zubawa ubansa abinci shi kuma ya dauka ya sha, a kofin ma da na zuba maka. Amma idan kana so lallai ya sha zaka iya kiransa ka bashi, ni dai ba zan sha ba tunda na gaya maka bana bukata. Me zan zuba maka a zobon? Shekaru goma sha kana shan zobona ban taba zuba maka komai ba sai yanzu? Saboda dai ni babu abinda zanyi na burgeka. Ai shikenan!

Ta tura kujerar ta mike ta bar masa waje ta nufi dakinta, ya bi bayanta da kallo yana mamaki.

Dama ya san haka zatayi domin hakan ne dabi arta a duk lokacin da bata da gaskiya, ya karasa cin abincinsa ya tashi ya shige dakinsa.

Ya saba bata hakuri idan sukayi irin haka sai dai yau ya ci alwashin ba zai bata hakuri ba don shima ta bashi haushi da mamaki. Bayan sallar isha i ya gama shirinsa ya sameta a daki yayi mata sallama ya nufi wajen Aisha.


UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

16

Tun daga lokacin da Aisha ta kama Yusra tana zuba mata sabulu a abinci sai kuma ta samu saukin fitnar Zahra, sai dai ita Aishan ta kasa sakewa da yaran gaba daya har Rukayya. Ko da Rukayyan ta zo tayata kwana sai tayi ta kula da ita tana kula da motsinta musamman a kitchen.

Tun wannan lokacin kuma sai fitnar Zahra tayiwa Aishan sauki, duk da bata fasa aniyar raba Aisha da Yusuf ba ta dai bari ne kawai tana jira ta tara kudin da zata iya bawa Malam Hatimu yayi mata aiki. Sannan kuma tunda Hajja ta bata maganin nan ta boye a bayan wardrobe ta sami natsuwa tunda duk abinda take so yayi mata yana yi, sannan kuma ko fada zai mata a kan wani abu da zarar ta bata rai sai ya fasa.
-------

Kwanci tashi har shekara ta zagayo an fara lissafin azumi, tunda aka ce azumi saura sati hudu Abban Sadik ya fara maganar kayan Sallah.

Saida ya gama magana da Zahra tayi masa total gaba daya har na Aisha, ya tabbatar mata da anyi albashi zai saka mata kudin.

Yana zaune a falon Aisha ta tada kai da cinyarsa suna hira, ya mika hannu ya dauki wayarsa yace

 Au, bari na turawa yayarki kudin kayan sallarku don na huta, sai kuma a shiga hidimar azumi.

Ta dauke idonta daga kallon TV din da take kallo tace

 Wai Mommy?

 Eh, kin san sallar ta matso.

Ta tashi zaune ta sashi a gaba

 Don Allah ni dai kada ka tura da nawa, ka turo min kudin zamu saya tare da su Zahida kaga waccan babbar sallar ma haka sukayi anko babu ni.

Yayi  yar dariya

 Yanzu ku kayan sallar ma sai kunyi anko? Mata masu gari. To gaya min lambar sai na tura miki naki ita sai na tura mata nata da yara.

Tana gaya masa kuwa nan take ya tura mata dubu dari kudin kayan sallarta, sannan ya tura wa Mommy nata da na yaranta.

Bayan ya je gidan ne take tambayarsa taga kudi amma basu cika ba; yayi mata bayani cewa Aisha ta karbi nata zasu saya da  yan uwanta. Babu yanda ta iya haka ta hakura da shirin tsiyar da tayiwa Aisha domin duk mitar ta yace mata shi ya riga ya gama wannan maganar.
& & ..

Cikin azumi ya sanar da Mommy yana shirin zai je aikin Hajji kuma da ita zai je, a take ta fara murna. Tayi masa godiya sosai sannan tace

 Amma wallahi da ma Umrar azumi ka biya min, ka ga zuwana Hajji biyu fa zan so zuwa Umra, musamman ta azumi. Kuma ka ga ma yanzu Sumayya bata isa yayeba.

Ya danyi tunani yace

 Hakane, to babu damuwa. Sai muje Hajin da Yaya Bello in ya so kafin karshen shekarar sai na biya miki Umrar ko ba zan je ba sai kuje da Sadiku. Ita kuma kanwarki badi sai muje Hajin da ita.

Nan take ta sake cika da murna tunda taji yace zai biya mata suje ita da Sadik, tana ganin kamar ma idan ta saka shi a gaba da naci ya hada harda Yusra in ya so su tafi ita da yaranta. In ya so Hajin da yace zai je da Aisha kuma ta san yanda tayi a ka bar zancen don tana ji a jikinta kafin shekara war haka ma ta samu an yi mata aikin nan an kada mata Aishan.
& & ..

Saura kamar sati hudu tafiyar alhazai Aisha ta fara laulayi, amai da jiri babu sassauci. Suna zuwa asibiti aka tabbatar ciki ne da ita sati hudu, aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.

Tun a hanya yake tsokanarta domin da ya fidda rai da yaga aurensu har ya haura shekara ko batan wata bata taba yi ba. Yana kaunar Aisha sosai don haka yake so ta haifa masa yara ko guda biyu ne, sannan ne zai tabbatar jininsa da tsokarsa ta gaurayu da ta Aisha.

Don haka suka dawo gida suka cigaba da rainon cikinsu; duk da bayan ta fara shan magungunan da aka bata laulayin yayi mata sauki tunda tana zuwa aiki kuma tana harkokinta sosai.

Sati biyu da zuwansu asibiti ya kama ranar da jirgin su Abba zai tashi.

Tsaf Abba ya gama shirinsa yayinda Malam Sule da Yaya Bello suke jiransa a mota, ya sa Rukayya a gaba ta hada kayanta, ya kaita gidan Aisha yace ta zauna a nan har sai ya dawo daga Saudiya sai ta koma wajen Mommy. Ya sanar da Mommy din kuma ta dinga duba masa Aisha don tana dauke da juna biyu. Yayi mata sallama ya fice suka kama hanya.
Yana fita ta mike ta fara zarya a falon, wato don ma raini ita yake gayawa yayiwa amaryarsa ciki ta kular masa kafin ya dawo? Tayi kwafa, in sha Allah wannan cikin sai ya bare kafin ya dawo.

A take ta dauki wayarta, har ta lalubo lambar Hajja zata kirawo sai kuma ta fasa, ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai.

Bayan ta sanar da shi cewa wancan aikin fa tana nan tana hada kudinsa sannan ta dora da bayani

 Malam yanzu ciki ne da ita amma gaskiya ina so ne a lalata cikin, kwata-kwata bana so ta haihu na fi so yanda ta shigo ita kadai ta fita ita kadai kawai.

Yayi  yar dariya

 Wannan karamin aiki ne, yara ma zasu iya yinsa. Akwai laya da za ayi aiki a ciki a baki ki samu ta tsuguna a kan layar nan, idan dai ta tsuguna to kafin awa daya cikin ya rabu da jikinta.

 To Malam yanda za ayi ta tsuguna din shine matsalar don ka ga ma ba gidan mu daya ba.

 Kada ki damu, ko yara ki bawa su jefa mata a masai. Na san masanku na tangaran ne layar kuma mai sulbi ce ana jefawa ko ba a kora ba zata wuce, idan dai ta tsuguna a kan wannan masan cikin nan sai ya fita daga jikinta.

Tayi murmushin farin ciki, yayi mata bayanin kudi Naira dubu goma sha biyar. Nan take tana ajiye waya ta tura masa kudin da alkawarin washegari zai taso yaro ya kawo mata har gida ita kuma zata sallami yaron.

Cikin walwala ta karasa wunin ranar domin dama babban abinda yake firgita ta shine Aisha ta tarawa Yusuf wasu yaran. Ta ci alwashin ko sau nawa yarinyar nan zatayi ciki sai ta barar da shi muddin Malam Hatimu yana raye.
---------

Tunda Abban ya kaimata Rukayya Rukayyan take ta magiya don Allah suyi cake tunda gobe da akwai makaranta kuma yanzu ta dawo na ta huta da dafa abincin makaranta.

Haka

15 / 58