Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 58

126K to 129K   out of 172.2K words

ta shiga bandakin don yin fitsari. Tana sabule pant din da yake jikinta ta ga jini, nan da nan hankalinta ya tashi. Tayi fitsarin ta fito tana kokarin fita daga dakin kuma mararta ta kara tsanantawa da ciwo don haka ta koma ta durkusa a gefen gado.

Ta lalubo wayarta daga kan gadon ta kirawo Abban Sadik wanda yake office dinsa. Bayan ta sanar da shi halin da ake ciki yace ta shirya ya zo su je asibiti domin Malam Ali ya fita dauko Sumayya da Ummi daga makaranta.

Nan ya sameta a gefen gado tana faman dagewa saboda ciwo, ya kamata ta saka hijabi sannan ya rikota suka sauko. Jummai bata san halin da ake ciki ba sai da suka sauko; tayi mata sannu da fatan samun lafiya suka wuce asibiti.

Suna zuwa asibiti aka samu likita ya dubata saboda yanayi halin da take ciki. Scanning likita ya turasu wanda da kyar Abba ya riketa suka je dakin da akayi mata, aka bashi takardar ya rikota suka koma wajen likitan.
Cikin hanzari likitan ya karbi takardar ya fara dubawa, bayan ya gama dubawa ya kalli Abban yace

 Alhaji sai dai ayi hakuri, yaro ne a cikinta namiji amma Allah yayi masa rasuwa shi yasa take bleeding. Yanzu zamu dubata mu taimaka mata ta haifeshi sai ayi masa sutura.

Abban ya goge fuska yace

 Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, ikon Allah.

Nan take ita kuma ta fashe da kuka yayinda mararta take kara kartawa. Nan da nan likita ya kirawo ma aikatan jinya yace su saka ta a dakin labour room. Shi da Abban suka bi bayansu.

Aka shige da ita yayinda Abban ya tsaya, jimawa kadan ya lalubo waya ya kirawo Yaya Murja ya sanar da ita sannan ya kirawo Aisha da Yaya Bello ya sanar da suma halin da ake ciki.

Ba tare da bata lokaci ba Yaya Murja ta iso asibitin,nan suka tsaya ita da Abban suna ta jira. Sai wajen karfe uku na yamma sannan aka samu ta haifi yaron babu rai.

Likita ya dauki yaron ya mika mata yace

 Sannu Hajiya, kin ganshi ko. Allah ya kawo wasu masu albarka.

Ta share hawaye tace

 To likita me ya kashe shi?

Ya mayar da gawar ya ajiye ya dubeta yace

 Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki damu Hajiya wannan ba wani bakin abu bane a wajen mace mai haihuwa tunda ma ke kina da wasu yaran wannan ba zai zama matsala ba.

Nan ya barta da ma aikatan suna gyarata ya fito waje.

Bayan an gama shiryata aka fito da ita aka bata daki inda likita yace zasu riketa zuwa gobe saboda jininta ya dan hau. Aka nade gawar yaron aka bawa Abba. Bayan ya tabbatar an bata daki sun zauna ita da Yaya Murja ya sanar da ita zai je ya kaiwa Yaya Bello gawar ayi mata sutura sannan ya karbo musu abinci a gida.

Abba yana fita Yaya Murja ta matsa kusa da Zahra tace

 Kiyi hakuri ki share wannan hawayen, in da rabo sai kiga kin haifi wani amma kina ta kuka sai kace karamar yarinya.

Cikin shesshekar kuka tace

 Yaya ya za ayi yaron da bai fi sati biyu ba aka duba aka tabbatar min kalau yake kuma yanzu ace ya mutu?

Da mamaki Yaya Murja take kallonta tace

 Hmm! Saboda ke baki taba yin bari bane shi yasa kike cewa haka. Ya za ayi ba zai mutu ba tunda rayuwarsa tana hannun Allah. Ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu bane, ke da kike da yara shida ai sai dai kawai ki cigaba da godiya ga Allah da fatan Allah ya sa wahala ta zama kaffara.

Ta janyo flask din da tazo da shi ta had a mata shayi mai kauri ta sakata a gaba saida ta shanye. Jimawa kadan likita ya shigo yayi mata allura, kafin ya fita bacci ya fara fuzgarta don haka ta hakura ta kwanta ba da son ranta ba. Yaya Murja ta zauna a kan kujera tana jiran zuwan Suwaiba wadda tace zata biya ta taho da Rahma saboda jinya.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

37

Tun kafin Suwaiba ta fito daga gida ta kirawo Rahama, sai dai bata dauka ba. Don haka ta kirawo Innar su Rahman don ta sanar da ita zata zo sai ta dauki Rahma su wuce.

Rahama tana daki a kwance tana kallon wayarta da taga Suwaiba ce taki dauka, haka kawai jikinta ya bata gidan Zahra zasu ce taje ita kuma tayi alkawarin ba zata sake komawa wannan gidan ba.

Tana jiyo Inna ta fara magana da Suwaiba a waya tayi tsalle ta fito tsakar gidan, bayan Inna ta ajiye waya tace

 Inna na gaya miki ba zan sake zuwa gidan nan ba, wallahi duk wani mutunci da kika ga tana yi idan mutum bai taba yaranta bane. Ni dai gaskiya bana son zuwa gidan nan.

Inna ta jijjiga kai

 Hakuri zakiyi, ko iya asibitin ne kije ki zauna da ita in ya so da an sallameta sai ki dawo. Tunda dai kin ga suna kallonki kina yiwa yayyenki irin wannan hidimar, hakuri zakiyi, yanzu Suwaiban zata karaso.

Haka Inna ta sakata a gaba tana bata baki, ba tare da bata lokaci ba Suwaiba ta zo suka wuce asibitin.

Nan suka zauna a asibitin har magriba.
Ana idar da sallar Magriba Abban ya shigo, ya kawo musu abincin dare sannan kuma ya tahowa Zahra da wayarta wadda ta bari a gida lokacin da suka taho asibiti. Suna gaisawa Yaya Murja da Suwaiba sukayi musu sallama suka tafi. Jimawa kadan Abba ya yiwa Rahma sallama ya tafi ya barta da Zahra wadda take ta bacci saboda alluran da ta sha.

Sai da yayi magana da likita kafin ya bar asibitin inda likitan ya tabbatar masa zasu sallameta da zarar blood pressure dinta ya dawo dai-dai kuma ta daina ciwon kai wanda take ta korafinsa tun bayan da ta haihu.
& & & &

Tun a daren Abba ya sanar da Aisha, tayi maganar abincin safe ya sanar da ita Yaya Murja tace za a kai musu don haka ta bari idan yamma tayi sai ta dafa musu abincin dare suje tare su dubota; idan ba a sallameta ba zuwa lokacin.

Ta sanar da mutanen gidansu wanda kafin wani lokaci Hajiyanta ta yiwa Hajiyan Abban waya ta jajanta mata sannan kuma suka sa cewa gobe zasu je asibitin su dubota.

Suma su Yusra tunda Abban ya dawo gida suke ta tambayar labarin Mommy, don haka yayi musu alkawarin gobe ko bai je da su duka ba zai je da wasunsu idan dai ba a sallameta ba.
----------

Sai wajen karfe biyu Abba ya kirawo Aisha ya sanar da ita ta dafa wa Zahra abinci zai zo da anyi sallar la asar su wuce asibiti. Nan da nan ta fada kicin ta dafa farfesun kaza sannan ta dafa shinkafa ta dafa macaroni tayi miyar dage-dage wadda ta sha nama sannan ta hada coleslaw. Ta sami flask ta cika musu da ruwan zafi saboda shan shayi.

Bayan ya fito daga office ne ya kirawo Yusra ya sanar da ita cewa su shirya ita da kannenta in ya dawo zasu je asibiti, tunda ranar Juma a ce babu islamiyya. Nan da nan Jummai ta tayasu suka shirya ta tambayesu ko za a dafa wani abun Yusran tace Abba yace Anti Murja ce take kaiwa.
---------

Sai da ya tsaya a wajen Aisha ya ci abinci sannan Aisha ta shirya cikin abayarta mai kyau ta rufe kanta da mayafi mai kalar olive green ta dauki 'yar jakarta sannan suka fito. Suna fitowa ta zare mukullan motar daga aljihunsa tana dariya tana fadin

 Ka gaji da yawa, bari na tukamu.

Yayi dariya yace

 Za dai ayi min wayo a more min mota.

Itama tayi da dariya.

Suka karaso gaban motar ya bude booth yana fadin

 Zuba abincin a nan da yara zamu je sai su zauna bayan motar.

Suka zuba abincin ya zauna a gaban motar ta ja suka fito daga gidan.

Tayi parking a kofar gidan Zahra, Abban ya fita ya shiga don ya fito da yaran.

Gaba daya su sun riga sun shirya don haka yana shiga suka fito yana dauke da Sumayya yayinda yake rike da hannun Ummi ragowar suna biye da shi. Sai da Yusra tayi turus da ta hango Aisha a motar Abba tana tukawa, ya karaso da su duk suka shiga bayan motar.

Rukayya ce ta fara gaida Aisha wadda ta juya tana amsawa, suka suka gaisheta har Yusra saboda Abban ya riga ya shiga motar. Ta ja motar suka kama hanya.
Sai da suka kamo hanya sosai yacewa Aishan idan sun zo kan tin gidan gwamna ta tsaya zasu sayi fruit. Don haka suna zuwa  yar kasuwar nan da take kusa da Yahuza suya ta tsaya; da hannu ya yafito mai fruit din wanda ya taho da guda. Yayi masa lissafin lemon, ayaba da kuma apple na kusan dubu bakwai yace a saka a leda kuma ya taho da POS machine ya karbi kudin.

Nan da nan mutumin ya juya da hanzari ya dauki leda ya fara cikawa yayinda shi kuma Abban ya gyara zama ya fara laluben aljihunsa don dauko wallet dinsa wadda ATM card dinsa suke ciki. Sai dai ga mamakinsa babu komai a cikin aljihun; ya dan yi tunani yana rike da aljihun ya kalli Aisha wadda take kallonsa yace

 Kin san na baro wallet din a falo!

Tayi murmushi tana dubansa, cikin rada tace

 Kanata santin shinkafata.

Yayi dariya yayinda ta mika hannu inda kafarsa take ta dauko jakarta, ta zaro ATM card dinta ta mikawa Abban a daidai lokacin da mai fruits din ya karaso dauke da manyan ledodi guda biyu.

Abban ya fita ya karbi kayan ya saka a booth yayi amfani da katin Aisha ya biya kudin sannan ya dawo ya zauna, ta ja motar suka wuce.

Abban ne a kan gaba har suka hau benen da dakin da aka kwantar da Zahran yake, suna biye da shi sai da aka zo bakin kofa saboda ya san Rahma tana ciki ya ja baya yace duka su shige. Ummi ce ta bude kofar suka shige gaba daya.

Rahma da Yaya Murja suna zaune a kan tabarma daga gefe yayinda ita kuma take gefe guda yayinda ita kuma Zahran take kwance a kan gadon tana danna waya.

A hankali ta tashi ta gyara zamanta yayinda suka karasa suka tsattsaya a gefen gadon, ta dan muskuta Yusra ta dauki Sumayya ta dora mata a gefen gadon. Aisha ta karasa shiga dakin da sallama Abban yana biye da ita. Ta wuce ta zauna can daga kusa da Yaya Murja yayinda shi kuma Abban ya ja kujerar da take ajiye daga daya gefen ya zauna.

Ya gaida Yaya Murja da Rahma yayi musu ya mai jiki sannan ya mike ya karasa wajen Zahran ya tsaya a bayan yaran.

Itama Aishan suka gaisa da Rahma da Yaya Murja tayi musu yaai jiki, ta mikawa Yaya Murja kwandunan da suka zo dasu tayi musu bayani. Suka dan cigaba da hira Yaya Murja tana tamabayarta mutanen gidansu.

Bayan ya gama tambayar Zahra jikin nata ya juya yayi wa Yaya Murja sallama ya dubi Aisha yace

 15 minutes, ina jiranku a mota.

Ya mika mata hannu kamar mai karbar wani abu, ta zura hannu a jakarta ta dauko mukullin motar ta saka masa a hannunsa ya juya ya fice bayan yayi wa su Yaya Murja sallama.

Bayan ya fita Aisha ta mike ta matsa kusa da gadon suka gaisa da Zahran sannan ta yi mata jaje tare da ya jiki. Da kyar take amsa mata tana ta faman harararta don haka itama ba tare da bata lokaci ba ta koma ta zauna.

Suna hira jefi-jefi da su Rahma tana kula da agogon wayarta, minti goma sha biyar suna cika ta yiwa Yaya Murja sallama ta dubi yaran tace

 Rukayya ku zo muje 15 minutes din yayi kada mu bar Abba yana jira

Ta fice.

Jimawa kadan yaran suka fice bayan Yaya Murja ta tasa keyarsu.
Su Zahra basu dade da fita ba Amina ta shigo, bayan sun gaisa Yaya Murja tayi musu sallama ta tashi yayinda Rahma ta bita don tayi mata rakiya.

Amina ta dubeta tace

 Na ga mutuniyarki sai wani sheki takeyi tana ta yiwa miji iyayi, na ga ma itace take tuka motar saboda kauna.

Ta ja tsaki

 Hmm! Haka Yusra take gaya min ana ta soyayya a hanya. Ki barni kawai Amina! Yarinyar nan ta raina ni wallahi. Na tabbatar da hannunta a wannan haihuwar da nayi babu rai shine ta zo ta nuna min ta kwaci mijinta. Wallahi Amina sai nayi maganin yarinyar nan.

 Hmmm! Kinga dai yanzu ki kwantar da hankalinki ki sami lafiya, sai ki san yanda zakiyi ki tattaro kan kudi don kinga akwai wani malami da za a hadani da shi kwanan nan kuma an ce aikinsa babu wasa. Kin san ina ta fama da Abban Asiya ina so na dauki hutun aiki na bishi Abuja yana ta faman gocewa, zargin da nakeyi wata ya ajiye a can shi yasa ko da tsiya-tsiya sai na je.
Suka cigaba da hirarrakinsu suna shawarar yanda za a yi a sami kudi aje wajen Malami, daga baya Rahma ta dawo don haka suka canza hirar.
___

Kwana daya Zahra ta kara a asibiti aka sallameta, suna dawowa gida Rahma tayi musu sallama ta koma gidansu.

Duk wani ban baki da ban hakuri likitocin sun yiwa Zahra shi domin likita ya tabbatar mata idan ta cigaba da zama da damuwa zata haifarwa kanta da hawan jini na din-din-din, sai dai ita bata ga yanda za ayi ta kwantar da hankalinta ba. Duk wata kulawa Abba yana bata sai dai har yanzu tana ji a jikinta cewa ya san abubuwan da ta shirya kallonta kawai yakeyi.

A hankali tana kara samun lafiya tana cigaba da tunanin hanyar da zata bi ta sami kudi. Bata son ta siyar da babbar saitin gwal dinta amma dai ta fara tunanin sayar da na yaran. Bata son ta tambayi Abba kudi domin bata ga fuska ba duk da komai yana yi mata kamar yanda ya saba sai dai kawai ita din ta kasa sakewa.

Haka dai rayuwarsu ta cigaba.
---------

Kwanci tashi har an kai wajen wata uku da haihuwar da Zahra tayi babu rai, basu samu sun je wajen boka ba saboda har yanzu mahaifiyar Amina a kwance take; domin kusan za a iya cewa ta zama sai dai a kwantar a tayar. Don haka babu halin Amina tayi nisa musamman da yake tana matukar kaunar mahaifiyar tata. Haka ta hakura tana kallo mijin nata yana can Abuja ga shi Asiya tana kawo mata rahotannin cewa yana tare da matan banza a can din amma babu yanda zata yi don ya ma hanata zuwa Abujan gaba daya.

Hankalin Abba ya dawo jikinsa don haka ya nemi kudi ya sake fara business din sa; sai dai wannan karon duk wani abu da zai yi na harkar business din sai idan yana gidan Aisha ne yake yi domin ko wayar abokan kasuwancin nasa baya amsawa idan yana gidan Zahra.

Haka kowa ya cigaba da rayuwarsa.
__

Tun tuni aka samarwa Saddiku da Yusra admission a jami ar Maryam Abacha American University wato MAAUN; Yusra tana karantar Business Administration yayinda Saddiku yake karantar Accounting. Da yake kwanci tashi babu wahala gashi a halin yanzu har suna zana jarrabawar zango na farko wato zasu gama level 1 su shiga level 2.

Tunda suka fara jarrabawa Saddiku yake gayawa Mommy ta karbar masa kudi a wajen Abba naira dubu hamsin zasu hada suyi end of session party. Sai kaucewa zancen takeyi saboda ta san yanzu bata da dama a wajen Abban yayin da shi kuma Saddikun yake sake dagewa da yi mata naci. Haka dole ya sakata tayi masa alkawarin ko da Abban bai bashi ba ita zata bashi ko da bai kai dubu hamsin din ba.
Kudaden da take hadawa domin suje wajen boka su kadai ne a account dinta domin ta hada kusan dubu dari biyu; garwar motarta da akayi accident wadda take ajiye a tsakar gida ita take jira ta sami mai siya ta hada kudin sai suje.

Wanna magiyar da Saddiku yake mata a kan kudin party ma ya kara mata kaimi wajen ganin ta dawo da hankalin Abban kansu, bata son ganin yaranta a cikin damuwa musamman Saddikun.
---------

A dakinta ya sameta tana zaune a kan dadduma ta idar da sallar isha i, bayan ta amsa sallamarsa ya wuce ya zauna a gabanta kamar mai daukar karatu. Ta dan kare masa kallo; zuciyarta tana so ta yarda lallai Saddiku yana shaye shaye; to amma bata ga lebensa da hannayensa suna yin baki ba irin na 'yan wiwi. Abinda bata gane ba shine shi din ba hayaki yake sha ba kwayoyi yake sha masu tsada da kuma dauke hankali nan take. Ya kwantar da kai yace

 Mommy baki turo min 50k din ba, gobe fa zamuyi final paper kuma ranar Saturday zamuyi party din.

Tunda ya zauna dama ta san abinda zai tambaya kenan, ta jijjiga kai tana murmushi

 Ku yanzu ba za ma ku iya tsayawa ku ga result ba kafin kuyi party din idan fa ba ku ci jarrabawar ba.

 Haba Mommy, ai duk mun ci. Kin san a ajin wasu foreigners ne don haka ana gama exam kowa zai tafi gida shi yasa zamuyi party din. Kusan kowa ma ya biya mu uku ake jira. Don Allah Mommy ki karba min

43 / 58