Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 58

30K to 33K   out of 172.2K words

take ta yi masa sannan ya juya ya wuce gaban wardrobe ya debo kayan baccinsa ya fara canzawa.

Tace

 Idan ka shirya na saka abincin dare.

 Ok, yanzu zan sauko.

Ta juya ta fice daga dakin cike da takaici bashi hakurin da tayi.

Bayan sun gama cin abinci suka zauna a falonsa suka dan taba hira, da ta kula ya fara jin bacci ta tashi ta shige dakinta ta sake shiryowa ta sa rigar bacci ta fito ta shige dakinsa.

A dabi arsa baya neman matarsa sai yayi bacci kai daya, lokacin dare ya raba sosai kuma dukansu sun rage baccin. Ga mamakinsa yau yana kwanciya ta fara lalubensa, bai kawo wani abu don wannan ba bakon abu bane tunda matarsa ce; kawai dai ya san ta saba jira sai sun rage baccin musamman da yake mafi yawa cin lokuta kafin ya kwanta ita din bacci ya dauketa.
Haka sukayita fama; yana yi yana mamakin yanda yau gaba daya take kamar a gigice tunda ya riga ya saba shi yake sarrafata kuma a hankali yanda yake so. Bai yi mamaki sosai ba don ya san akwai abubuwan da mata suke Sha musamman don wannan harkar, don haka yake tunanin itama wani abun ta sha.

Suna gamawa kamar yanda ya saba ya zare jikinsa yaje yayi wanka, bayan ya fito ya tabata yace mata taje tayi wanka ko kuma tayi alwala idan ba yanzu zata yi wankan ba. Haka ta tashi taje ta wanko jikinta tayi alwala ta fito ta sake kwanciya.

Can cikin dare baccinsa yayi nauyi ta sake lalubarsa, kamar a mafarki ya farka. Ya gyara kwanciya yace

 Yau bakya jin bacci kenan?

Tayi  yar dariya ta amsa

 Um.

Suka cigaba. Baya son ya rasa sallar asuba a masallaci don haka suna gamawa ya tashi yayi wanka, itama ta tashi tayi nata wankan lokacin wajen karfe uku da rabi na dare. Suka koma suka sake kwanciya.

Ko da yaje masallaci ya dawo yaci burin biyan bashin baccin da ya ci, saida yayiwa sakatarensa message yace masa zai dan makara don ya samu yayi bacci sannan ya koma ya kwanta.

Tana idar da sallah itama ta dawo ta kwanta, yayi zaton bacci zasuyi kamar yanda suka saba don wani lokacin sai wajen karfe shida take tashi ta shiga kicin don shirya  yan makaranta.

Tana kwanciya ta laluboshi, duk yadda ya so ya kyaleta kasawa yayi; ba wai saboda yana bukatarta a wannan lokacin ba sai don yana ganin matarsa ce ba zai iya kyaleta ba musamman da wannan bukatar. Suna gamawa lokacin har shida ta gota don haka a gurguje ta mayar da kayanta ta wuce kasa don shirya  yan makaranta. Ta fuskanci gajiyawarsa wanda dama haka takeso; so take ta sauke masa duk wata sha awa da yake da ita saboda idan yaje kwanan Aisha sai ya kwanta yayi ta baccin a can ba tare da ya kusanceta ba.
Tana fita daga dakin ya tashi ya shiga wanka, bayan ya fito daga wankan ya zauna a kujerar gaban mudubi ya kafa tagumi; me ya sami matar nan ne? Ko ma me ta sha gaskiya yau ta jigata shi. Bacci yake so ya koma amma ya hakura saboda yana tunanin idan ta sameshi a kwance bayan yara sun tafi makaranta to lallai zata sake nemansa shi kuwa ya san ba zai iya ba. Don haka nan da nan ya shirya ya sauko dai-dai lokacin yara sun fice.

Ta saka mishi abincinsa wanda yana gama ci yayi mata sallama ya fice, gidan Aisha ya shiga don ya dubata inda ta sanar da shi sati mai zuwa zata koma aiki. Yayi mata sallama ya fice bayan ya sanar da ita zasu dinga fita da yara idan Malam Sule ya ajiyeta sai ya wuce da su.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)


12

Kwanakin nan biyu haka Abban Sadik yayisu babu baccin kirki saboda yanda suke kwana hidima, har Allah-Allah ya dinga yi kwanan Zahra ya kare ya koma wajen Aisha.

Ranar da zai koma wajen Aisha kuwa da wuri ya dawo daga wajen aiki, ana cikin kiran sallar isha i .

Wajen Zahra ya wuce kai tsaye, bayan sun masa sannu da zuwa ita da yaran ya amsa ya dubeta yace

 Bari na wuce don yau a gajiye nake wallahi, don Allah da zarar karfe tara tayi ki rufe gidan nan kar a sake budewa sai da safe.

 To in Sha Allah zan rufe.

Yayi musu sallama ita da yaran ya fice.

Ta bi bayansa da kallo tana murmushin jin dadi, domin aikin da tayi ta san yau din nan idan banda bacci babu abinda zai iya.

Hakan kuwa aka yi; ita Aisha bata kawo komai domin bata da matsala da hakan, suka kwana suna baccinsu har asuba. Ko da gari ya waye haka suka gama hirarrakinsu ya shirya yayi tafiyarsa aiki.

Har saida aka sake kwana bayan ya dawo daga masallaci sannanne wani abu ya shiga tsakanin sa da Aisha, a nutse yanda ya saba kuma yanda yake so suka farantawa juna. Da dare yayi kuma ya koma kwanan Zahra.

Yana fargaba da addu ar Allah ya sa yau bata sha abinda ta sha wancan karon ba don gaskiya ya fi so yaji dadi yana cikin hayyacinsa.

Yanda akayi wancan karon din kuwa haka aka sakeyi, babu yanda ya iya haka ya dinga hakura da baccinsa. Saida ya koma wajen Aisha sannan ya maimaita mata yanda yayi.

Haka suka cigaba da yi duk da ita Aisha bata dauki abun a matsala ba, sau dayan nan ya isheta musamman da yake yana daukan lokaci ya tabbatar bukatarta ta biya. Haka rayuwa ta cigaba.

Zahra bata taba shiga gidan Aisha ba kuma bata turo yaranta, tunda tana amarya dai data tura Yusra da waya ta dauko mata hoton falon bata sake tura su ba. Rukayya ce kawai take zuwa tayata kwana, itama don babu yanda Zahran zata yi ne. Sai kuma Allah ya sa Aishan da Rukayya jininsu ya hadu sosai, don haka Rukayyan take jin dadi zuwa kwana; duk da dai idan gari ya waye ta fito daga gidan Mommy hanata komawa takeyi har sai wani daren.
_

Yanda ya saba duk karamar sallah kaya kala uku yake yiwa kowa, tsakanin Zahra da yaranta. Idan kuma babbar sallah ta zo to kaya kala daya yake musu, sannan kuma ya kawo sa da rago wanda za a yanka na layya.

Ranar asabar ce don haka yana gida da yamma, suna zaune shida Zahra a falonsa suna hira; da yake yaran duk sun tafi islamiyya. Ya dubeta yace

 Sallah fa ta matso, ya za ayi ne da kayan sallarku?

Tayi  yar dariya

 Yanda aka saba mana, ka san dai a wajena ake siya ko business din nawa ya dan samu cigaba.

 Hakane, to zan tura miki dubu dari da hamsin, yara kowa dubu ashirin ke kuma hamsin. In ya so sai ki kawo muku abinda kike so, ita kuma kanwarki itama sai na tura mata hamsin din.

Ta langabe kai

 Haba yallabai, to ita ba zata yi min cinikin ba? Ka turo har natan mana na dai san ba zai wuce leshi ba. Za a kawo su kala-kala in ya so sai tazo ta zaba.

 E kuma kinga hakan ma zaifi, ta huta da shiga kasuwa.

 Kwarai kuwa. Amma gaskiya da zaka karawa yara ko da dubu biyar-biyar ce ka san fa kayan yanzu sun dan kara kudi.

 A a hakan ma zai isa. Kin san fa Babbar Sallah ce dole sai na tanadi abun layya. Ni ban ma sani ba na siyo sa kamar yanda na saba ko kuma na siyo muku raguna dai-dai ke da kanwarki yara kuma a basu biyu.

 Haba dai, ai sa ya fi auki. Idan ka siyo mana sa daya da rago ya ishemu gaba daya idan muka hadu muka soya sai a raba. Sai dai idan ita Aishan ta fi son rago sai a bata nata.

 A a na san bata da matsala, bari dai naje kasuwar naji farashin dabbobin tukunna sai ayi wanda ya samu.

Suka gama hirarrakinsu daga baya ta barshi a nan ta shiga kicin dora abincin dare.
& & ..

Sallah saura sati biyu Aisha ta tashi da wani zazzabi, da kanshi ya kaita asibiti. Aka yi mata duk wasu gwaje-gwaje da suka dace, aka tabbatar bata dauke da juna biyu, sai dai malaria don haka aka rubuta mata magunguna suka kamo hanya.
Har suka zo gida yana tsokanarta a kan shi ya fara murna har ya gama shawara idan mace ta haifa Aisha zai mayar idan kuma namiji ne Muhammad. Haka suka tsaya a chemist aka yi mata allurai sannan suka dawo gidan.

Kwana biyu ta fara warwarewa, da daddare suna zaune a falo ya mike kafafunsa ta tada kai da cinyoyinsa ta kwanta suna hira kuma suna kallon TV.

Yace

 Wai Sallah ta kusa ke ko labarin kayan Sallah ba kya yi balle na abun layya.

Tayi dariya tace

 Wai da yake ba ni zanyi ba, kuma na san mai yi yana sane da lokacin.

 Lallai ne baki da matsala. To akwai leshina a wajen yayarki, gobe sai ki shiga ki zabi daya. Kin san tana sayar da kayan sawa shi yasa kawai nake sayen kayan sallar a wajenta.

Ranta ya sosu, Yaya za ayi yace matarsa ce zata saya mata kayan Sallah ko an gaya masa ita babu masu sayar da kayan a danginta. Bata son ta ja maganar yaga kamar ta damu; kuma da yake tana da ragowar kaya a akwatin lefenta sai abun bai dameta ba sannan kuma akwai leshi da suka siya ita da  yan gidansu wanda daga Switzerland suka tura kudi aka siyo musu don nata ma yana wajen tele inda Zahida ta kai musu dinki, don haka tace

 Ka gani ni dai ina fama da kaina gobe ban san yanda zan tashi ba, idan ka je kawai ka zabo min wanda ya burgeka.

 Ah bari ma kawai na kirawota ta turo min hotunansu sai ki zaba ko?

Kafin ta amsa ya daga waya ya kirawo Zahra, wadda a take ta turo masa hotunan leshin ta Whatsapp.

Irin leshin nan ne mai hade da mayafinsa, ta san kudinsu basu wuce dubu ashirin da biyar ba. Bata raina ba, sai dai kuma leshin baya burgeta kwata kwata. Tabbas da anyi shawara da ita ba za a saya mata wannan leshin ba domin ita da a bata wannan gara a bata leshi marar mayafi ko ma atamfa. Ta duba su gaba daya ma kalolin ba wani kyau sukayi ba amma dai ta zabi wani kalar ruwan toka mai fulawoyi ruwan goro.

Ana kawo leshin ta kaiwa Hajiya tace a bawa Zahida ta kai mata dinki zasuyi waya.

Sai ana i gobe Sallah ya sanar da ita sa zai yanka da rago, kuma zuwa zatayi su soya tare a gidan Mommy in an gama soyawa sai a raba a dibarwa kowa nasa. Tsarin bai yi mata ba domin tun bayan zuwansu gidan Hajiya bata son shiga harkar Zahra, sai dai bata son tayi masa musu kada yaga kamar kullum itace take fara bashi matsala. Don haka tace babu komai hakan yayi.
Ta san Zahran ce ta shirya masa hakan kuma ta san don a cuceta ne, amma zata tsaya taga gudun ruwansu tukunna.

Amma dole a sake wannan tsarin don ba zata dauka ba.
------

Kudin kayan sallar da ya turo mata a ciki ta samu ta fidda dubu ashirin kudin aikin da Hajja tace zata yi mata; domin ko leshin da ta bawa Aisha ma dubu ashirin da biyar take sayar da shi amma a kan dubu hamsin ta bawa Abban.

Nan da nan ta kirawo Hajjan ta sanar da ita kudi sun samu, tayi mata alkawarin zata kawo mata aikin ana saura kwana uku Sallah.

Ranar asabar kuwa sai ga Hajja, bayan sun gaisa ta zaro farar kwalba irin ta fiya-fiya. Tarkace ne kawai a cikin kwalbar sai wani guntun tsoka da aka sokawa allura ga kuma takarda wadda ke dauke da rubutun larabci a jiki wadda aka nannade aka sakata a tsaye. Ta mikawa Zahra kwalabar tare da wata mitsitsiyar kwalbar baka tace

 Kin gansu nan; wannan babbar ki sami singiletinsa wadda ya saka yayi gumi a jikinta ki gutsiri dan mitsitsi ki saka a ciki. Idan kika saka sai ki juye man da yake cikin wannan kwalbar ki mayar ki rufe. Ki samu waje mai duhu ki boye kwalbarki; idan kikayi haka to zaki sha mamaki don ya daina musa maganarki kuma duk abinda zai bata ranki ba zai yi shi ba.'

 Allah Hajja.

 Ai sai dai idan bakiyi yanda nace ba, amma tabbas idan kinyi yanda nace to baki da matsala.

Sukayi sallama tana ta jin dadi.

Ranar a wajenta ya kwana don haka singiletin da ya cire ita ta samu ta yanka ta hada kamar yanda aka umarceta. Ta samu waje a dakinta bayan wardrobe ta boye kwalbar. Ta kwana tana walwala da farin ciki.
Ranar Sallah ba a wajen Aisha yake ba, amma dai ya sa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nar da ita da safe zasu tafi da tuwon Sallah don su kaiwa Hajiya idan an sauko idi don haka itama ta zuba nata.

Tun dare Rukayya ta tayata ta gama miyar taushenta sannan ta hada zobonta mai dadi. Asuba nayi ta dora tuwo, da yake ba yawa ne da shi ba nan da nan ta gama. Suka gyara gidan tare da Rukayya suka yi wanka. Atamfa ta saka sabuwa kar dinkin doguwar rigar mai matukar kyau, tayi kwalliyarta sannan suka budade gidan da turaren wuta.

Zuwa karfe bakwai da rabi sun gama komai don haka Rukayya tayi mata sallama a kan zata je gida don kayanta suna can.

Bata dade da fita ba ya shigo tare da Sadik; tunda aka kawota yaune rana ta farko da Sadik ya shigo gidan kuma yaune rana ta biyu data taba ganinsa, don ko a unguwar bata hangoshi. Bata son yanda yake mata wani kallo mai cike da raini, amma dai haka ya gaisheta ta amsa.

Abbansa ya wuce daki tabi bayansa.

Basu dade da shiga ba suka fito, ta basu abincin gidan Hajiya a flask da kuma zobo a kula suka kama hanya.
& & &

Ya riga ya sanar da ita tsarin yanda suyar naman Sallah zata kasance, ya gaya mata ranar Sallah ake farawa a karasa washegari don haka idan an yanka za a zo ayi mata magana.

Sai wajen sha daya aka turo Rukayya ta kirawota, nan take ta canza kaya suka tafi tare da Rukayyan.

Masu aiki ne su biyu Uwar biyu da kuma Hansatu, sai Jummai, sannan kuma ga Asiya wadda itace  yar autar su Zahran wadda ta koma hannu Yayansu Muhammad tun bayan rasuwar mahaifiyarsu. Ana ta aikace-aikace, su Hansatu suna kokarin hura wuta, ta karasa suka gaisa da Mommy babu yabo babu fallasa. Su Jummai ma duk suka gaggaisheta, amma tana kallon Yusra bata gaisheta ba kuma babu wanda yace wani abu. Ta zauna ta kamawa Jummai nama suka cigaba da yankawa.

Murahu biyar aka dora don haka aikin nasu ya fara da sauri. Gaba daya naman san gida aka shigo musu da shi, sai raguna guda uku. Ya raba rago daya da rabi aka bayar sadaka a waje, aka sake shigo musu da rago daya da cinyoyin na biyun.

A take Mommy ta ware naman da za ayiwo musu dambun nama ta bayar aka tafi kaiwa.

Ragowar kuma ana soyawa ana kulle wani ana kai mata freezer.
Duk kaskon da aka sauke za a watso naman a faranti ace kowa ya taba, haka har magriba suna aiki. Babu laifi an soya da yawa don haka ana yin Sallah Mommy tace a barshi haka gobe a karasa.

A gajiye Aisha ta dauki  yar jakarta da ta shigo da ita tayi musu sallama ta koma gida.

Ta gaji, bata taba yin aikin sa ba don ita kullum raguna ake yanka musu. Ta so ace an bata nata naman tayi yanda take so da shi amma da yake wannan ne karon fari ta hakura; amma tabbas bazata sake wannan aikin hadakar ba. Danyen naman da taga ana sakawa a freezer tayi zaton za ace ga nata amma bataji an ce ba, tana jira taga goben tukunna.

Ranar ma ba a wajenta zai kwana ba don haka ita da Rukayya suka kwana. Tun bakwai na safe yayiwo mata waya yace su taho an fara aiki; da kyar ta tashi suka shirya suka fice. Tana sane taki cin abinci suka fice. Suna zuwa suka dan taba aikin ta fuskanci tayi kamar awa daya tana aiki ta cewa Mommy zatazo gidan tayi breakfast yanzu zata dawo. Ta fice ta barsu a ranta ta san ba zata koma ba don ta gaji.

Tana shiga gida taci abincinta ta koma bacci.
Sai can wajen azahar Zahra ta sami Abban Sadik din ta ce masa ya je ya turo musu Aisha saboda aiki yayi yawa. Take ya tashi ya nufi gidan.

Tsit gidan kamar babu kowa, don haka ya wuce daki. Tayi dai-dai a kan gado tana baccinta don ko motsinsa bata ji ba, saida yayi gyaran murya ya zauna a gefen gadon sannan ta farka.

Ta mutssike idonta tace

 A a sannu da zuwa.

Bayan ya amsa yace

 Lafiya dai ko, anata aiki ashe kina nan kina bacci.

Ta yatsina fuska tana daga kwance

 Jiri naji yana kwasata ga kaina yana ciwo shi yasa na zo na kwanta, ka san zazzabin nan ba wai ya gama sakina bane.
 Eh hakane.

Ya kai hannu ya taba wuyanta

 To kin sha Panadol?

 Eh, na sha kafin na kwanta da yake ban dade da kwantawa ba ka shigo.

 Ok, to sannu. Kwanta, bari naje sai nayi musu bayani.

Yayi mata sallama ya

11 / 58