Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   53 / 58

156K to 159K   out of 172.2K words

karanta aya ko hadisin da yace dole idan kina auren mutum ki rike masa yaran da baki haifa ba, hasali ma har aka gama bayanin masu riko babu matar uba a ciki to na me za ace sai ta yi? Idan yana so ta rike masa su kuma ai matarsa ce sai yayi amfani da dabara ya lallabata ba wai ya nuna mata isa ba. Kuma idan sun sabauta Aishan ai yaranta suka cuta da mu da muka haifeta, tunda shi ubansu aure zai kara ya cigaba da rayuwarsa.

Cikin sanyin jiki Hajiya ta dafa hannun Anti Uwani tace

'Hakane. Bari dai gari ya waye Baffa yazo, idan aka bi abun a hankali za a sami mafita in sha Allah.'

Jimawa kadan Anti Uwani tayi mata sai da safe ta tashi ta koma daki; dukansu zuciyoyinsu babu dadi. Ita Hajiya ba da son ranta ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar auren ba wadda take cike da jarrabawa kala-kala ga rashin haihuwa, ita kuma Anti Uwani abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata tana tunani babu yanda za ayi ta bari Aisha ta shiga irin rayuwar da ita tayi.

Haka suka kwanta bacci kowa da abinda yake ransa.

Rayuwar auren Anti Uwani ce gaba daya ta dinga dawo mata; abubuwan da tace ba zata sake tunawa da su ba balle su sa mata damuwa amma yau sun hanata bacci.
Shekaru kusan talatin tayi a gidan miji amma iya shekarar farko ne kawai zata ce tayi a nutse. Tunda ta shekara bata haihu ba dangin miji suka fara takura mata, tun baya biye musu har shima ya fara damuwa. Kuma babu wanda ya taba cewa taje asibiti sai dai ayi ta bata tsimi tana shanyewa, haka tayi ta shan rubutu da tsimi wani daga gidansu wani kuma daga wajen dangin mijin. Ga kuruciya a tare da ita don bata fi shekaru Sha biyar ba a lokacin. Shekara uku a gidansa ya kara aure; yarinyar kuwa tana tarewa ta sami ciki. Haka aka mayar da Anti Uwani kamar mai aiki a gidan; kwashe amai, wanki, girki duk itace idan kuma dare yayi maigidan yace wajen amarya zai kwana kada wani abu ya sameta. A haka cikin damuwa da hantara suka cigaba da zama da matar nan har ta haifa masa yara biyar duka mata, daga baya ya saketa ya kwace yaransa tunda dama ko da uwarsu tana nan ma duk wata hidimarsu da ta gida Anti Uwani ce take yi. Bayan ita ya auro wata wadda ita kuma tana shigowacta haifa masa yara biyu maza. Haka Anti Uwani ta cigaba da bauta mata saboda da zarar ta ki yin wani abu sai maigidan yace tana bakin ciki don Allah bai bata haihuwa ba. Daga karshe tana zaune a tsakar gidan tana hura wuta zata dora abinci yayinda amaryar gidan take janyowa maigidan ruwan wanka a rijiyar tsakar gidan karamin yaron gidan mai shekaru kamar bakwai yayiwo tsokana ya shigo gidan da gudu basuyi aune ba sai ji sukayi ya fada rijiyar nan. Nan take uwarsa tace Uwani tana kallonsa ya fada rijiyar bata rikeshi ba. Shi kuma maigidan yace idan dai yaron ya mutu to ya saki Uwani saki uku. Da kyar aka dauko gawar yaron daga rijiyar inda a nan take maigidan ya kora Uwani gida.
Bayan wanna kuma ta auri wani mutum wanda shi kuma lafiya suka zauna don shi bai hadata da iyalansa ba ma suna gari da ban da ban, shekara tara da aurensu Allah ya karbi rayuwarsa. A nan wancan ya dawo cikin zawarawa ita kuma tace gaba daya ma ta gama aure a duniya tunda ko babu komai a lokacin ta tsufa.

Da kyar bacci ya kwasheta tana tuna rayuwarta ta baya kamar mai kallon fim.

 ----

Bai san tsawon lokacin da ya dauka a zaune a kan dining table din ba, gajiya kawai yayi da zaman ya tashi jikinsa babu kwari ya hau saman. Kai tsaye dakinsa ya wuce, yana shiga ya zauna a gefen gadon ya dafe kansa da hannuwansa. Motsin da ya jiyo daga daya gefen gadan shine ya janyo hankalinsa, ya sauke hannuwansa ya kalli bangaren da ya jiyo motsin. Rukayya ce a takure a kasa daga gefen gadon ta hada kai da gwiwa; sai a lokacin ya tuna shi ya ce tazo ta jirashi a daki.

'Rukayya.'
Ya kirawo sunanta.

Ba tare da ta dago kai ta dubeshi ba ta amsa a gajarce

'Um.'

'Taso ki zo nan.

Ta taso tana goge fuskarta wadda tayi ja gaba daya saboda kuka; duk da zuwa yanzu babu hawaye a fuskarta. Ta zagayo ta dawo gabansa ta tsuguna tana kallon kasa. Ya kare mata kallo na dan lokaci cikin damuwa, ya mika hannuwansa ya kamo nata hannuwan wadanda suke ajiye a kan gwiwarta ya rike tafukan hannunta a cikin nasa ya sake kiran sunanta. Ta amsa a gajarce tare da daga Ido ta kalleshi ta mayar da idonta kasa. Yace

 Me ya hadaki da Yayarki kuke fada haka?

Kafin ta amsa ya cigaba

'Kin san bana son karya don haka gaskiya zaki gaya min.

Cikin sanyin murya tana kokarin danne hawayen da yake shirin kwace mata tace

'Cewa tayi bana son Mommy.'

'Ba kya son Mommy? Yusran ce tace haka?

Kai kawai ta daga masa alamar eh.

'To me ya sa zata ce ba kya son Mommy?

'Saboda zamu je gidan Anti Aisha ni da Ummi?

Ya saki hannuwan nata yana jijjiga kai yace

'Ban gane ba Rukayya, kiyi min bayani sosai. Me ya hadaku fada? Me yasa don zaki je gidan Anti Aisha za a ce ba kya son Mommynki?

Sukayi shiru na dan lokaci, shi yana sauraronta yayinda ita kuma take tunanin yanda zata yi masa bayani ba tare da ta fadi laifin Mommy ba. Shirun ya dan tsawaita kuma ta san ita yake jira tace wani abu, ta share kwalla daga idonta sannan ta fara yi masa bayanin abinda ya faru har ya sa suka fara fadan. Bayan ya gama sauraronta yace

'To zuwa gidan Antin ne ya zama yiwa Mommy rashin biyayya ko kuwa wa yace mata zaki sake uwa ne?

Bata son yanda yake turata kan bayanan da zasu shigo da Mommy cikin maganar amma ta san dole ta bashi amsa. Ta kosa da tsugunon sannan kuma bata son maganar, haka ta sake share kwalla ta cigaba da bayani.

Tayi masa bayanin yanda Mommy ta hanata zuwa gidan tunda ya auro Aishan sannan tace

'Kuma yanzun ma ba zama zanyi ba, zuwa zanyi na gani ko akwai kayan da zan tayata kwasowa tunda ka ce mana zata dawo shine ita kuma ta fara gaya min maganganu.

Yayi shiru na dan lokaci yana so ya hada zantukan gaba daya ya basu ma'ana, sai dai kansa gaba daya ya cushe sai sara masa yake. Da kyar ya daga kwayar idonsa ya kalli Rukayyan saboda yanda duk wani motsi na kwayar idon nasa yake kara masa ciwon kai. Yace

'To kiyi hakuri, idan kin je gidan Aisha ba yana nufin zaki sake uwa bane don babu wanda yake iya sake uwa, sai dai Aishan itama uwarku ce gaba daya tunda kinga yanzu nan zata dawo ta dinga kula da ku. Amma bana son ki sake yiwa wani irin dukan da kika yiwa yayarki, rashin hankali ne zaki iya jiwa mutum ciwo.

'To Abba.'

'Tashi kije, kada ki sake kulata kuyi wani fadan idan ta yi miki wani abu ki zo ki gaya min ko ki gayawa yayanku.

'To.'

Har ta kama hannun kofar zata bude ya sake kiran sunanta, don haka ta dawo ta tsuguna daga gefe. Yace

 Akwai wani abu da Anti Aishan takeyi ne wanda yasa Mommy din bata son kuje wajenta?

'Wallahi Abba babu wani abu, haka kawai ne sai Mommy din taga kamar Antin zata cutar damu kuma wallahi ba haka bane. Ita kuma Yaya Yusra sai ta dinga zugata ba zata bata hakuri ba.

Ya jijjiga kai ya sallami Rukayya wadda ta fito daga dakin ta rufe masa kofa.

Gaba daya kansa ya kulle; tabbas ya san Zahra bata son Aisha kuma ya san akwai lokutan da take hana Rukayya zuwa gidan amma bai san abun ya kai haka ba. To ko shi yasa Aishan tace ba zata zauna da Yusra ba? Watakila wani abune na kiyayya da Yusran take bayyanawa Aishan yasa take jin ba zata iya zama da ita ba. To amma ai babu inda zai kai Yusra don haka dole Aishan tayi hakuri ta zauna da yaran gaba daya. Zai yi magana da Yusran zuwa da safe kuma zai sakata a gaba suje ta bawa Aishan hakuri in yaso ma sai ta tayata kwaso kayanta kafin su Rukayyan su dawo makaranta ta dawo gidan.

Sarawar da kansa yakeyi tayi yawa don haka ya mike ya matsa gaban karamin fridge din da yake dakin ya bude ya dauki ruwa sannan ya koma gaban mudubi ya dauki Panadol ya hadiya. Ya shiga bandaki ya yiwo alwala da nufin yayi sallar Magriba wadda bai yi ba ya tsaya rabon fada gashi har ana kiran isha'i; sai dai yanda yaji da ya fito ya tabbatar ba zai iya yin sallar a lokacin ba.
Don haka ya kwanta a gefen gadon ya dafe kai tare da rufe idanuwansa.

& & .
Washegari da wuri ya tashi duk da kasancewar ranar asabar ce. Karfe bakwai na safe ya sauko daga saman, yaran gaba daya suna kan dining table suna cin abinci domin akwai tahafiz wadda karfe takwas saura kwata ake shiga. Yusra ce kawai wadda bata tashi daga bacci ba bata wajen amma har Saddiku ma yana zaune. Bayan ya amsa gaisuwar su ya tambayesu Yusra inda suka tabbatar masa bata tashi daga bacci ba. Surutunsu ya sa Jummai ta fito daga kicin inda take aiki, ta tsuguna ta gaisheshi. Bayan ya amsa ya koma ya haye saman inda Rukayya ta bi bayansa da abincin safen sa ta ajiye masa a table din saman ta sauko.

Ya shige dakinsa ya kashingide a kan gado ya fada tunani; tabbas yana bukatar mace a gidan don da ace da mace a gidan wadda ba  yar aikin gidan ba da ya san yanzu yana bacci amma dole ta sa kullum sai ya tashi ya tabbatar yaran sun shirya sannan idan sun tafi makaranta shima ya shirya ya fita nasa aikin. Ya san Aisha karfe takwas take tafiya islamiyya don haka bari zai yi sai bayan azahar lokacin ta dawo yaje suyita ta kare. Domin shi yau din nan yake son ta dawo gidan.

Har bayan azahar yana gidan yana sauraro ko zai ji shigowar Aisha amma bai ji motsinta ba. Don haka wajen karfe uku bayan yara sun tafi islamiyya ya shirya ya nufi gidan Aishan da shirin zai je yaji abinda ya hanata dawowa, da shirinsa na wucewa gidan Yaya Bello bayan ya gama da Aishan.

Har ya isa gidan yana mamakin wannan taurin kan na Aisha.

Da mukullinsa ya bude gate din ya shiga, yana zuwa kofar shiga falon yaganta a garkame da kwado. Mamaki ya rufe shi; tunda yake da Aisha bata taba fita ba tare da ta tambayeshi ba. To daga islamiyya ne bata dawo ba ko Kuma wani wajen ta wuce bata gaya masa ba?

Har ya saka mukulli zai bude kofar sai yaga idan ya shiga ma babu abinda zai yi don haka ya juya ya fice daga gidan ya nufi gidan Yaya Bello yana san ra duk ma inda taje kafin ya dawo ta dawo in ya so sai yaji.

A farfajiyar gidan ya sami Yaya Bellon yana zaune yana shan fura da  yar autarsa Minal wadda zazzabi ya hanata zuwa islamiyya. Bayan Minal ta gaisheshi ta shiga gidan ta karbo masa kofi don ya sha furar, tana ajiyewa ta koma cikin gidan.

Bayan Abban sun gaisa da Yaya Bello suka cigaba da hirarrakinsu. Yaya Bello ya dubeshi yace

'Ya yaran? Aishan ta koma wajen nasu?

Cikin yanayi na damuwa yace

'Wallahi Yaya bata koma ba, sai wasu dokoki da ta kafa na shirme. Ni gaba daya ma na kasa fahimtar ta. Wai ita bazata rike yaran duka ba sai dai dole na cire Yusra da Nana su bazata iya zama da su ba.

'Ah, kamar Yaya? Wannan ai zancen banza ne ma. To su Yusran da Nana gidan marayu zaka kai su kenan ko ya take so kayi dasu?

'Wallahi Yaya nima dai na kasa fahimta.

'To kuma bata baka wani dalili ba?

'To basa dai jituwa da Yusra, ita kuma Nana zaka iya cewa ko uwarsu bata kai Yusran iko da ita ba. Kuma da Zahran ma ai basu sami wata jituwa ba tunda ka ga abinda ya faru har na shekara ban shiga gidan Aishan ba ko ba a fada mata ba Zahran take zargi kamar yanda kowa ma ita yake zargi. Da wasu abubuwa dai na cutarwar da rashin kunya da tace ana aika Yusran tana yi mata. Don haka tace ma wai Yusran ta tareta bayan rasuwar Zahran ta gaya mata ba zata barta ta maye gurbin uwarta ba.

Ya daga hannuwa ya yarfe kamar mai Shirin fada yace

'Ai ka ji! Duk shirme ne nasu na mata. Nawa Yusran take da Aishan zata ce ta rasa yanda zata yi da ita? Wanna ma ai ba wani abu bane, idan ka koma sai ka hadasu ka jawa yaran kunne a gabanta. Kuma in ta dawo nan din ma ai ba kyalewa zaka yi ba, duk wanda yayi ba dai-dai ba sai ka dau mataki kuma gidan ma sai ka sa ido tunda yanzu babu irin muguntar fa da mata basa yiwa dan kishiya.

'Hakane. Sai na koma gidan yanzu zan saka ta a gaba mu koma can din.

'Gara haka, Kai ma ka huta da biyan kudin hayar. Amma idan kace zaka biye ta tata sai ta tarwatsa maka iyalin don haka ma kada ka saurara mata. Idan ba zata zauna maka da wadannan marayun yaran ba yanzu kam bata da wani amfani a wajenka.
Suka cigaba da hirarrakinsu Yayan yana kara karfafa masa gwiwa lallai kada ya kyale Aishan dole ta koma ta kula masa da yaran.

Sai wajen karfe biyar na yamma sannan Abba yayi masa sallama ya kama hanyar gidan. Yana shiga unguwar ana kiran sallar Magriba don haka kai tsaye masallaci ya wuce. Sai da aka idar da sallar Magriba sannan ya wuce gidan Aishan. Kamar dazu haka ya tarar da gidan a rufe, cikin tsananin mamakin inda Aishan ta tafi ya sa mukullinsa ya bude kwadon ya shiga falon. Dakinta ya fara shiga inda ya hangi akwatunanta na saman wardrobe babu guda uku a cikinsu, ya karasa ya bude wardrobe din ya tarar ta kwashe mafi yawancin kayan sawarta. Yayi murmushi yana tunani yanzu haka ta riga shi dawowa ta hada kayanta ta koma can gidan, don haka cikin kwarin gwiwa ya fito ya nufi gidan.

Duka yaran suna zaune a falon kasa; kafin ya karasa shiga ciki Sumayya ta taso da gudu tayi masa oyoyo. Bayan ya shiga ya zauna sannan ya dubi Jummai wadda take tsaye da leda a hannunta tana jira ya dawo ta tafi gida yace

'Jummai zaki tafi ko?

'Eh Alhaji dama jira nake ka shigo sai na tafi tunda Yayansu ma bai dawo ba tukunna.

'To babu laifi. Aisha bata shigo bane?

'Eh gaskiya bata zo nan ba.

Mamakinsa ya bayyana, yayi sauri ya wayance ya sallami Jummai ta fice bayan ta yiwa yaran sallama shi kuma ya haye sama yana ta mamakin inda Aisha zata tafi harda kwashe kaya haka ba tare da ta sanar da shi ba.

Ya zauna a gefen gado ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ba tare da bata lokaci ba ya lalubo lambar Aishan ya danna mata kira. Har aka fara kiran sallar isha'i yana nan zaune yana faman kiran wayar amma ba a dagawa, haka wayar zata kari ringing har ta katse. Cikin kosawa da damuwa ya mike ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya nufi masallaci yana ta tunani kala-kala; to ina Aishan ta tafi? Me ya hanata daukan wayars?

Yana daf da shiga masallacin dabara ta fado masa, don haka ya tsaya ya lalubo lambar Zahida ya kirawota. Bayan sun gaisa ya tambayeta yayarta. Nan take ta sanar da shi Aisha tana gidan Hajiya, yayi mata sallama ya ajiye wayar.

Ya mayar da wayar aljihunsa yana murmushin yake; wato Aisha gidansu ta tafi kenan saboda ba zata rike masa yara ba? To wannan wacce kalar fitna ce? Wai dama haka Aishan take ko kuwa wani ne yake zugata? To idan ma don yaranta ne ai yace ta kwasosu su dawo gidan tare? Shi dai bai taba ganin inda mutum yana da mata taki rike masa yara ba, ko da kuwa shegu ne balle yaran da aka san uwarsu. Yana nan tsaye yana mamaki ba tare da ya sami amsar tambayoyinsa ba aka tayar da Sallah, don haka ya mayar da wayar aljihunsa ya karasa masallacin ya shiga sahu cike da damuwa.

Ana idar da sallah ya koma gidan, a nan ya tarar Saddiku ya dawo don haka yayi musu sallama ya shiga mota ya nufi gidan su Aishan. Duk da bai san me zai je yayi ba amma dai yana jin gara yayiwa iyayenta bayani don yana kyauta zaton zasu goya masa baya.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

44

Tun a wannan daren Hajiya ta kirawo Abubakar ta sanar da shi ga Aisha a gida don haka gobe yazo da safe don a sami mafita. Suna ajiye waya ta kirawo Baffa, bayan tayi masa bayani yace to shima da safen zai zo don bai kamata a bari ta sake kwana ba ba tare an bi diddigin abun ba.

Ko da gari ya waye da yake Baffa ya saba sammako tun kafin su gama karin kumallo ya iso gidan, Anti Uwani ta zubo masa dafadukan taliya da kunun tsamiya. Ya sanar da ita ya riga ya ci abinci kafin ya fito sai kunun kawai ya debi rabin kofin ya zauna a falon yana sha yana jiran isowar Abubakar don yace ya fi so ayi a gabansa.

Wajen karfe takwas da kwata shima Abubakar din ya iso. Nan suka hadu a falon Hajiya da ita Hajiyan, Anti Uwani, Baffa da kuma Yaya Abubakar. Har Hajiya ta fara yiwo bayanin abinda ya kawo

53 / 58