Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 58

111K to 114K   out of 172.2K words

bayansa da kallo cike da takaici; tabbas wannan bakin ciki ne muraran ina ruwan wani Yaya Bello da kai yara karatu shi da ba da kudinsa za a kai yara makaranta ba. Kuma ya za ayi yace ta yiwa Bello magana. Kaf danginsa babu mutumin da yake mata kwarjini kamar Bello, ita gara ma ace ta yiwa Hajiya magana a kan ace ta yiwa Bello.

Ta ja tsaki ta mike a fusace ta shige dakinta.

Yaya Bello bai saba yi musu shisshigi a al amuransu ba, kwata kwata ma sau daya ya taba bata haushi lokacin da ya sa sunan Rukayya ba tare da yayi shawara da ita ba. Amma yanzu tana zargin yawan zuwan da Abban yakeyi gidansa a nan yake zuwa ya zazzage masa cikinsa shi kuma ya sami damar yi musu shisshigi. Yanzu ta riga ta gama gayawa danginta da kawaye cewa yaranta Dubai zasu tafi karatu yanzu kuma ya zo ya sa a fasa. Su kansu yaran bata san yadda zasu dauki abun ba musamman Saddiku. Ba zata iya yiwa Bello magana ba amma tabbas zata san yadda zatayi don ita kanta ta fi gamsuwa da karatunsu a Dubai din.

Tana jinsa ya fita, sai dai duk da bai gaya mata inda zai je ba ta san gidan Hajiya zai je kuma daga nan yaje gidan Yaya Bello.

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito daga dakin ta wuce falo ta dauko wayarta ta koma dakinta ta zauna a kan gado. Ta lalubo lambar Yaron Malam ta danna masa kira; domin tana ganin gara kawai a toshe mata bakin Yaya Bello ya fita daga idonta.

Tana daf da tsinkewa ya dauka, bayan ya amsa sallamarta yace

 Hajiya yi hakuri ina kan wani aiki ne, idan kina son magana dani da gaggawa ki turo sako ta Whatsapp idan ba haka ba kuma da na gama aikin zan kirawo ki.

Kafin ta amsa ya katse wayar.

Ba zata iya jira ba don haka ta budo Whatsapp ta fara tura masa sakon voice note

 Yaron Malam wani aiki nake son ayi min. Akwai wani wan mijina wanda ya fara yi min shisshigi ni da yarana saboda ya ga danuwanshi ya fara samun kudi. Ina so a kawar min da idonsa daga kanmu ko kuma ma a hana dan uwan zuwa inda yake.

Bayan ta tura wannan kuma ta rubuta wani sakon ta tura

 In ka gama aikin mayi magana.

Ta tura sannan ta fice daga dakin.

Sai can bayan la asar sannan Yaron Malam ya kirawota; tayi masa bayanin abinda take so wato Yaya Bello ya fita daga harkarta. Yayi mata alkawarin zai yi mata aiki inda suka amince zata tura masa naira dubu talatin kudin aiki. Suna ajiye waya ta tura masa kudin, bayan kudin sun shiga ya sake kiranta ya sanar da ita yaga kudin, sannan yace
 Bayan kwana biyar ki sake tayar da maganar, in Sha Allah ba zai sake yi miki shisshigi ba.

Sukayi sallama tana cike da jin dadi.
---------

Saida ta bawa maganar sati biyu sannan ta sake tayar da ita. Sai dai abinda ta sakankance zai faru ba shine ya faru ba, domin Abba yana nan a kan bakansa. Ya jaddada mata cewa yara babu inda zasu je karatu suna nan a Nigeria sai dai idan Yaya Bello ya yarda. Ya sanar da ita cewa jiya ma sun yi magana da Yaya Bello kuma yace da zarar result dinsu ya fito a bashi akwai wanda zai bawa a samar musu admission a BUK ko Northwest.

Sosai hankalinta ya tashi don ta zata an bar wannan maganar. Duk yanda ta so ya saurareta ya ki, sai dai ya bata dama taje ta sami Yaya Bello idan har yace a kai yara Dubai to za a kaisu amma muddin bai ce ba to suna nan a BUK.

Ranar da sukayi magana ranar Juma a ce da daddare don haka ranar asabar wajen karfe takwas na safe ta dauki mota ta wuce gidan Yaya Bello; ta gaji da wannan fin karfin gara taje taji da kanta musamman da yake yaron Malam yace mata yayi aiki a kansa.

Lokacin da ta shiga gidan daga Yaya Bello sai Umman su Muhammad wadda, suna zaune a falo suna karin kumallo domin yaran gidan duk sun tafi tahfiz sai Muhammad kawai da Shukuriyya wadanda sune manya kuma su  yan Jami a ne.

Bayan sun gaisa Umman Muhammad ta kwalawa Shukuriyya kira daga kicin tace

 Shukuriyya kawowa Antinku wainar geron idan kin kwashe.

Ta dubi Zahra tace

 Bari a kawo miki wainar geron.

Ta mike tana fadin

 Shigo mu koma ciki.

Zahra tayi murmushi tace

 Ki barmu a nan ma daman wajen Yaya nazo, sai dai ko muje ya gama cin abincin tukunna.

Ya kurbe ragowar kununsa ya ajiye kofin yace

 Na ma gama, kuyi zamanku. Ya yaran nawa? Duk lafiya kuke ko?

 Lafiya Alhamdulillah, duk suma sun tafi tahfiz.

Sukayi shiru na dan lokaci alamar yana sauraronta. Ta gama nukunukunta tace

 Yaya dama a kan maganar yara ne, Saddiku da Yusra da suke WAEC yanzu. Mun gama magana da babansu za a sama musu admission a Dubai kuma an fara shirye-shirye yanzu ya zo yace wai BUK zasu yi. To kuma Yaya yaran duka suna da kokari su don saura ma kadan a sami admission din yace a bari.

Yayi gyara murya don ya so ya fuskanci inda zancen ya dosa

 Eh, munyi magana da shi don nine ma nace masa ya barsu su fara a nan din idan sun fito da sakamakon mai kyau sai su tafi kasar waje karatun degree na biyu. Ina ganin kamar hakan zai fi tsari da tarbiyya musamman a wajen ita Yusra din. Kuma karatun ma na nan ai ba gagararsu zai yi ba kamar yaune zaki ga sun gama musamman da yake dukkansu suna da kokari sosai.

 Uhmm!

Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro.

Har yanzu ta kasa gane dalilin da yasa mutumin nan yake mata kwarjini, duk inda ka tsaya a gabansa sai ya sha gabanta ya cika maka ido. Yau din nan zuwa tayi ta kora masa jawabi amma gashi ta kasa, tayi zaton ma zata ga ya rage kwarjini saboda aikin da akayi a kansa amma sai taga kamar ma kara masa kwarjini aka yi.

Umman Muhammad tace

 Hmmm! Ka san dai karatun a can yafi a nan nutsuwa da sauri Alhaji, sai dai kawai da yake kayi maganar taribiyya amma fa da banbanci.

Yayi gajeriyar dariya yace

 To ai komai lokacine, yaran da wataran ma da kansu zasu kai kansu duk inda suke so a duniya musamman shi Saddikun da yake namiji.

Tayi gyaran murya tana murmushin yake

 Bari na tafi don nayi sauri na koma.

Suka mike kusan lokaci guda ita da Umman su Muhammad a dai-dai lokacin da Shukuriyya ta fito dauke da tray ta doro waina da kili_kuli.

Nan da nan Umman ta karba ta koma kicin din ta juyo a roba ta fito mata dashi sai dai kafin ta zo har ta ja mota ta tafi. Ta dubi Yaya Bello da yake tsaye a bakin kofar falon tace

 Laa! Kuma sai ka barta ta tafi bata karbi wainar ba Alhaji ai abun marmari ne kuma mutum ya gani.
Yayi murmushi

 Bata so karba ba. Ba zuwa tayi muyi magana ba zuwa tayi ta yi min rashin kunya kuma bata isa ba. Ina jin ya gaya mata na hana ya kai yara waje karatu shine ta zo kuma bata sami yanda take so ba, ko baki kula da yanda take magana bane?

 A a ina kula sai dai da yake ni tunda ya kara aure haka muke da ita, da kyar take kulani don haka ni bata ma damuna shi yasa yanzun ma na zata nice bata son gani ashe kai din ma ka shiga gonarta.

Ya juyo ya dawo cikin falon ta biyoshi a baya tana mita

 To kai kuwa Baba ka kyalesu mana, tunda yana da kudin.

Ya zauna sannan ya bata amsa

 Ba zan kyalesu ba! Yusufa ai danuwana ne kuma idan yaransa suka lalace dole abun ya shafi zuri armu. Da ma wasu nutsattsun yara ne da sai ace, musamman shi Saddikun. Bari su gama a nan din tukunna muga hankalinsu.

 Ai shikenan, Allah ya bada sa a.

--------

Tunda ta dawo daga gidan Yaya Bello Abba yaga yanda take cika tana batsewa ya san bata sami yanda take so ba, don haka ya kawar da kai kamar bai ganta ba. Haka ta karasa wunin tana ta faman kunci, tunaninta ma yanda zata gayawa yaran musamman Saddiku wanda yake ta faman murna yana gayawa abokansa wadanda yanzu yawanci suna level 2 cewa shi Dubai zai tafi kuma ba zasu rigashi gama degree ba.

Sai dai shi Abban yaji dadin wannan hukuncin kawai dai yana mamakin yanda tafi shakkar Yaya Bello fiye da shi.

Bayan Sallar isha i ne suna zaune a falon sama har yaran suna hirarsu, Yusra ce ta shigo da sallama daga falon kasa. Kujerar da take kusa da ta Abban ta zauna, bata jima da zama ba tace

 Abba wai yaushe zamu yi jarrabawar ne? Wadda kace zamuyi don samun admission a Dubai din.

Ya kalleta

 Oh, Mommy bata gaya muku ba ko? Ai an fasa zuwa Dubai din, na yanke hukunci da ke da Yayan naki kuyi first degree a nan BUK in ya so idan kun gama sai ku tafi duka kasar da kuke so don yin second degree. So yanzu idan result ya fito BUK za a nema, daman kin ga ita kuka cike a JAMB form ko?

Nan take idonta ya ciko da kwalla, Mommy wadda take zaune a kusa da shi ta tashi ta shige dakinta. Yusran ta zumburo baki

 Abba! Haba Abba, don Allah Abba ka bari mu tafi.

 An gama magana Yusra, nan din ma degree zakuyi irin na can so babu wannan zancen. Amma nayi miki alkawarin idan dai kika fita da first class to in Sha Allahu ko ban biya miki ba zan nemar miki scholarahip ki je UK ma kiyi masters kinga na can ya fi daraja.

Ta share zafafan hawayen da suka gangaro kan fuskarta, ta tashi ta shige dakinsu na sama ba tare da tace masa komai ba. Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai, ya san abun da haushi amma bai ji dadin yanda tayi masa hakan ba sai dai ya san wannan din dabi ar uwarsu ce. Ya cigaba da hirarsa da suaran yaran, sai daga baya suka tashi kowa ya tafi makwancinsa.

Tun kafin gari ya waye Yusra ta sanar da Saddiku abinda Abba yace, nan da nan ya rikice. Ya sami Mommy a dakinta ya sa mata kuka; yana tsugune a gabanta Yusra ta shigo ta zauna a gefen gado kusa da Mommy din. Ta kalli Saddikun ta kawar da kai, tace

 Mommy don Allah ki yiwa Abban magana mana, wai me ma yasa zai canza magana bayan an gama maganar nan?

Taja tsaki ta kawar da kai

 Wai ubanku ne Bello yace ba zaku je Dubai din ba sai dai BUK, nima babu yanda banyi dasu ba don jiya ma da safe da na fita gidan Bellon naje. Yace wai a barku saboda tarbiyya, ko kuma tsabar bakin ciki ne oho! Tunda yaransa BUK sukeyi to dan kowa ma yayi BUK.

Saddiku ya dubi Mommy yace

 Wallahi Mommy na dade da sanin mutumin nan dan bakin ciki ne, ina ruwansa tunda ba da kudinsa za a je ba?

Yusra tace

 Uhm! Yanzu ai sai ya zuba ruwa a kasa ya sha tunda zamu zauna muyi BUK kamar yaransa. Mtsewww! Na tsani dan sa ido wallahi.

Saddiku ya dora hannuwansa a kan gwiwar Mommy yace

 To yanzu Mommy babu abinda zaki iya yi a kai?
 Da zan iya da tuni nayi, ka san shi da bakin taurin kai.

Ya dafa kansa da hannuwansa biyu

 Amma gaskiya ya cuceni Mommy, duk friends dina na gama gaya musu zan tafi Dubai amma gayen nan ya sa aka fasa. Allah ya isa wallahi.

Tace

 Ka barni da shi, zan yi maganinsa kwanannan.

Nan suka gama hirarrakinsu suna ta zagin Yaya Bello. Daga baya suka sanar da Mommy cewa idan hakane ta yiwa Abban magana su in ba za a kai su Dubai din ba to sun fi son Maryam Abacha University. Duk da bata san yanda zai dauki wannan zabin nasu ba amma tayi musu alkawarin zata yi iya yinta taga a kalla sun sami nan domin ko babu komai dai kada suyi Jami'ar da  yayan Bellon suke yi wato BUK.
__

Kwanci tashi har an fara yiwa azumi lissafin abinda bai fi wata daya ba. Zuwa yanzu duk wanda ya ga Aisha ya san tana da damuwa, sai dai duk yanda  yan uwanta suke so su rabata da gidan Yusuf ta ki yarda. Suna nan dai ita da Amira, duk da bata rasa komai ba amma rashin ganin Abban yana damunta. Ko a hanya bata ganinsa, kusan kamar ma dai suna rayuwa a mabanbanta duniyoyi.
Bata taba fasa addu a da sadaka ba, ga addu ar karya sihiri wadda kullum sai tayi kuma Hajiya ma sai ta yi ta aiko mata da ruwan. Tun tana lissafin kwanaki har ta gaji ta daina; abinda ta rike kawai shine Allah ya amsa addu arta lokaci kawai ake jira.
& & & ..

Ranar Juma a ce kuma da yake ta kama ranar hutun aiki Zuwaira, Zainab da Aisha da Zahida gaba daya su da yaransu sun hallara a gidan Hajiya. Don haka sai kaiwa da kawowa akeyi, Farha da Abdallah wanda yake shirin zana common entrance suma suna nan a cikin dangi. Mijin Zahida ne ya bawa Hajiya kujerar Umra wadda zasu tafi cikin azumi don haka kowa murna yakeyi.

Can wajen karfe biyar na yamma lokacin kowa ya fara shirin tafiya Yaya Abubakar shima ya shigo tare da babban yaronsa Abulkhairi. Bayan sun gaisa ya dubi Anti Uwani yace

 Anti Uwani family meeting kuke yi ne aka wareni?

Tayi dariya tace

 A a wa ya isa ya wareka? Nan da ka gansu duk dadin baki suka zo su yiwa  yar uwata zata tafi Umra su samu ta tafi dasu ni kuwa ina kallonsu da ni zata duk a Nigeria zamu barsu.

Yayi dariya yace

 Ai kuwa a Nigeria zaku barsu Anti Uwani don kema da taki kujerar nazo.

Zahida tayi caraf tace

 Allah Yaya da gaske.

Ya daga kai

 In Sha Allah na ma gama biyan kudin sai su tafi tare, nima don dai ban dade da komawa sabon office bane da dani za a.

Nan take Zahida ta zabga guda, kafin ta dire Yaya Zainab ta harareta tace

 To sarkin bidi a, da an yi motsi sai ki kama wani nanannen hanciki.

Suka kyalkyale da dariya.

Nan suka hau sabuwar murna gaba daya. Hajiya ma sai tafi Anti Uwanin murna domin sai da ta matse kwalla saboda jin dadi. Haka ta dinga sakawa Abubakar albarka tana addu a Allah ya kara masa arziki.

Haka Anti Uwani ma sai ta rasa inda zata saka ranta don murna, tayi ta sa musu albarka tana musu addu a. Ta matsa kusa da Hajiya ta dafa ta tace

 Yaya, Yaya Kinga dana ko? Na rasa bakin godiya Yaya. Tunda kika haihu ban taba kukan rashin haihuwa ba, kullum godewa Allah nake da bai bari na sha wahalar goyon ciki ba kika sha mana wahalar ke kadai kika haifo min  yaya. Gashi nan kinyi shuka sai girbar alkhairi nakeyi hankalina kwance.

Hajiya tayi dariya tace

 Naga alama kam to ina binki bashi kenan na wahalar nakuda.

Suka sa dariya gaba daya

 In Sha Allah idan naje sai nayi dawafi sannan nayi miki addu a Yaya; yanda kuke so na Allah ya soku fiye da haka kuma Allah ya karramaku fiye da yanda kuke karramin.

Ta fara share kwalla, Zahida ta dafa bayanta yayinda Hajiya tace

 To ga  yarki nan baure sarkin kuka zata tayaki muna murna zaku saka mu kuka.

Suka sa dariya gaba daya.

Ana idar da sallar Magriba duk suka watse suka bar Aisha da Amira wadanda sai bayan sallar isha i zasu tafi.

A nan falon Hajiya suka ci abinci suna ta hirarsu, sai da aka idar da sallar isha i suka tashi tafiya. Lokacin Farha tayi bacci don haka Abdallah da Anti Uwani suka rakosu farfajiyar gidan.
UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

34

Babu yanda Zahra ta iya, tana ji tana gani aka fasa kai yaran Dubai karatu. Ta dai samu ta karfin tsiya ta takura Abban ya amince zai saka su a Maryam Abacha University. Yayi magana da Yaya Bello shima ya amince da haka, tunda dama abinda yake gaya masa shine ya kasance yaronka yana kwana a gida har sai ka ga yanayin fahimtarsa a rayuwa tukunna. Don haka nan da nan aka fara shirin shiga MAUN.

Sai dai kawai ta yiwa kanta alkawarin sai ta kai Yaya Bello wajen boka don ta fuskanci tunda yanzu dan uwansa ya kara kusanci da shi to lallai hukuncinta zai ci gaba da cin karo da nasa. Yanda take jin yanzu ta sami Abba a hannunta bata jin zata sake bari ya subuce mata, duk wata hanya da zata bi sai ta bi don ta tabbatar babu wanda ya sha gabanta a wajen Abba. Domin a yanzu ma gani takeyi kamar Abban yana bawa Yaya Bello wasu kudade ne.
__

Tun lokacin da ta gane aikin boka yayi

38 / 58