Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   41 / 58

120K to 123K   out of 172.2K words

juna kamar wasu baki.

Ta bude baki zata yi magana yayinda Yaya Bello ya janyo Abban suka nufi cikin, bata da wani zabi don haka ta wuce gaba suka bita a baya domin idan ta tsaya wajen ma ba zai isa su wuce ba.

A falon suka ci karo da Anti Zalihan ta mike tsaye tana fadin

 A a, kin tsintosu Aisha.

Babu wanda ya amsa mata don haka ta matsa Abban Sadik da Yaya Bello suka zauna a kujerar zaman mutum uku yayinda ita da Aishan suka zauna a kujerun zaman mutum daya. Yaya Bello ya dubi Aishan yace
 Aisha me yake faruwa ne, kamar mamakin ganin juna kukeyi ke har kina share kwalla. Me yake faruwa ne?

Bata sami bakin bayar da amsa ba saboda hawayen da take ta faman tokarewa ne ya kwace ya wanke mata fuska gaba daya, ta sa hannu ta fara share hawayen.

Cikin tsananin damuwa da mamaki Yaya Bello ya gyara zama yana dubansu daga wannan ya dubi wannan. Yace

 Yusufa wai me yake faruwa ne? Kayi min bayani.

Ya sa hannu ya goge fuskarsa yana muttsike ido kamar wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude baki yace

 Yaya babu komai fa, na dai dade ban ga Aishan bane kawai.

Ya dubi Aishan wadda ta sunkuyar da kai tana share hawaye yace

 Ikon Allah! To yaji tayi ko rabuwa kuka yi amma baku sanar ba.

Gaba daya su suka yi shiru kowa yana ta faman zare ido, itama Anti Zulaiha sai kallonsu take tana mamaki don bata ma fahimci kan zancen ba. Yaya Bello ya katse shirun ya dubi Aishan yace

 Aisha me yake faruwa ne? Ya sake ki ne ko me ya faru?

Ta share hawaye tace

 A a bai sake ni ba, ya dai kusa shekara biyu bai zo gidan da nake ba shi yasa muka dade bamu hadu ba.

Yaya Bello ya sake shiga rudani, ya kalli Aishan ya kalli Yusuf din. Aisha ta sake share hawaye, ta bashi labarin yanda abubuwan suka faru. Binta kawai yake da kallo yana mamaki. Ya dubi Abban Sadik din yace

 Yusufa kai kuma kana auren mace kawai sai baka ganta ba kuma ba zaka nemeta ba?

Ya share gumi yace

 Wallahi Yaya ni kaina har yanzu ina mamaki, don ni sai yanzu ma fa da na ganta na tuna da ita. Na kasa gane me yake faruwa ma gaba daya wallahi.

 Ikon Allah! To ni kaina ma ban fahimceku ba. Amma Yusufa ya za ayi ace kai da matarka kuma ga gidan da take kusa da daya gidan amma kace wai ka kusa shekara baku hadu ba. Wannan din wacce irin rayuwa ce?

 Wallahi Yaya nima sai yanzun nake mamaki, kamar ma gaba daya mantawa nayi da wani bangaren na rayuwata. Gaba daya ma na kasa ganewa.

Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa. Jimawa kadan Anti Karima tayi gyaran murya tace

 Gaskiya Abban Muhammad ni ina ga ka kirawo Malam Sama ila tunda yau asabar watakila yana gida, domin wannan abun yayi kama da aljannu ko shaidanu. Gara ka gane kan komai a dauki mataki kafin su bar nan su sake komawa ruwa.

Yace

 Hakane gaskiya, bari nayi masa waya na san yanzu zai shigo in sha Allah.

Ya dauko waya ya kirawoshi, yace masa yana bakin titi zai fita amma yanzu zai dawo.

Sukayi shiru suna jiransa.

Jimawa kadan Yaya Bello ya kasa hakuri ya kirawo Muhammad yace masa ya fita waje da zarar Malam Sama ila ya zo su shigo tare. Yana fitowa suka hadu suka shigo ya nuna masa falon.

Bayan sun gaisa Abban Muhammad yayi masa bayanin abinda yake faruwa, ya rufe da

 To Malam Sama ila abun ne naga kamar na mutanen boye, to shine nace gara ka zo muji ko da akwai abinda za a taimaka da shi.

Yayi shiru yana jijjiga kai, jimawa kadan yace

 To gaskiya Alhaji wannan bayanin da kayi min ya fi kama da sihiri, Allah ne ma ya takaita abun. Watakila kai din kana da wata kariya ko kuma gidan naka na da makari shi yasa da suka shigo suka ga juna. Tunda idan ban manta ba lokacin da na yiwa Asma u rukiyya na baka taimako kala-kala naka da na yaran.

 Hakane. To yanzu ya za ayi Malam? Na iya barinsu su koma gidan don ni gaskiya ina tsoron su koma su sake mantawa.

Suka sake yin shiru na dan lokaci.

Jimawa kadan Malam Sama ila yace

 Akwai Malam Audurahmanu, kai ka san shi ai wanda yake zuwa mana limancin sallar dare da azumi. Sai dai shi a unguwar koki yake, shine ya kware a aikin sihiri ni dai ka barni da rukiyya idan aljani ya bayyana a jikin mutum.

 To ai sai mu tashi muje in dai zamu sameshi yanzun.

 Zamu sameshi tunda ko baya gida makarantarsu kusa da gidan ne

Yaya Bello ya dubi Abban Sadik yace

 To kaji ai sai ka tashi muje ko?

Cikin sanyin murya ya amsa
 To Yaya, yanda kace.

Gaba daya suka mike suka fito, har sun kusan fita Yaya Bello ya koma yacewa Anti Karima

 Ina ga ki dauko mayafi muje saboda ita Aisha din kya zauna da ita.

Don haka ta saka hijabinta suka shiga motar Abban Sadik Yaya Bello ya tuka suka kama hanya.

A makaranta suka sami Malam Audurahmanu, babu dalibai don an tashi  yan islamiyya don haka ya nuna musu aji suka zauna.

Bayan Malam Sama ila yayi masa bayani ya tambayi Aisha itama tayi nata bayanin, shi kuwa Abban Sadik da aka tambayeshi ma kasa bayanin yayi; abinda yake tunawa kawai shine ya dade bai ga Aishan ba kuma ya san bai saketa ba.
Malam Audurahmanu ya dubi Yaya Bello yace

 Ina zuwa.

Ya fita daga ajin.

Jimawa kadan ya dawo dauke da robar ruwa karama guda biyu da kuma wani mai a 'yar roba kamar ta Robb. Ya mikawa Aisha robar ruwan guda daya yace ta shanye, ta kalli Anti Karima ta daga mata kai don haka tayi Bismillah ta shanye. Ya mikawa Abban Sadik din dayan yace shima ya shanye, ba tare da wani musu ba ya shanye.

Ya dubi Yaya Bello yace

 Ayoyin karya sihiri ne, sune matakin farko za a sha na kwana bakwai.

Aisha tace

 Ni dama tunda abun ya faru kullum sai na tofa ayoyin na sha sai dai a ruwan fanfo ne ba na zamzam ba.

Malam yace

 Ma Sha Allahu to shi ya sa ma abun baiyi wani tasiri sosai a kanki ba, karanta min ayoyin naji.

Nan take ta karanta masa ayoyin ba tare da wani kuskure ba.

Yana murmushi yace

 Ma sha Allah, in dai kika rike wannan babu wani sihiri da zai yi tasiri a kanki, ko yayi ma na dan lokaci ne tunda Allah yana jarraba bawa da abinda ya so.

Ya mikawa Abban Sadik  yar robar hannunsa yace ka lakaci wannan ka shafa a kanka. Ya karbi robar ya rike amma ya kasa ko budewa, jujjuyata kawai yakeyi yana kallonta. Kafin yace wani abu Yaya Bello ya karba ya bude, ya lakaci man da yake ciki ya muttsike a hannunsa ya cire hular Abban Sadik din ya kama kan nasa ya shafe masa man tas. Nan da nan idonsa yayi ja ya fara neman birkicewa, Malam Sama ila da yake gefensa ya dafe shi ya fara karatu.

Ba a fi minti biyar ba yayi atishawa ya dawo dai-dai. Ya goge gumin da yake fuskarsa, Yaya Bello ya mika masa hularsa ya saka yana ta faman satar kallon Aisha wadda suke zaune a gefe daya ita da Anti Karima.

Malam Audurahmanu ya mike yana fadin

 Bismillah Malam Bello.

Ya bi bayansa suka fice.

Sai da suka shiga ofishinsa suka zauna sannan Malam yayi gyaran murya ya dubeshi yace

 Wato Malam Bello sihiri ne aka yiwa dan uwanka don a rabashi da mai dakinsa, aljanine aka saka masa wanda gaba daya yake hanashi tunawa da ita. Saboda yanda aljanine yake tare da shi kuma duk ma wanda ya so ya tuna masa ita to ba zai yarda su hadu ba. Amma Allah ya kawo makarin abun tunda ka ga wannanan man da ka shafa masa a kansa kamshin mutuwa yayiwa aljanin don haka ba zai sake dawowa ba. Sai dai da yake yana da wata matar kuma ga maganganun da ta gayawa wannan din za a iya cewa itace tayi wannan aika-aikar; duk da dai bai halatta a zargeta ba domin shaidanu makaryata ne. Amma yanzu idan kun tafi to a barshi ya cigaba da kwana gidan ita waccan din, zan bayar da ruwan tofi da zai dinga sha tsawon kwana bakwai kuma da addu oi. Sannan a samu ko shi ko wani a dinga karanta bakara a dakin da yake kwana. In Sha Allah bayan kwana bakwai din sai ku dawo sannan sai ya koma rabon kwana kamar da.

Yaya Bello ya jijjiga kai yana mamakin yanda Zahra zata yi haka, tunda yake bai taba jin matar da Hajiya take yabo kamar ita ba, don ko matarsa da ita aka fara aurowa Hajiya bata sonta kamar yanda take son Zahra.

Nan suka koma ajin, bayan sun koma ya sake yi musu bayani gaba daya kuma ya gaya musu kada su zargi kowa balle a sami wata sabuwar fitna don shaidanu haka suke so.

Ya basu umarni suje su cigaba da addu a komai zai dawo dai-dai, ya sake bawa Aisha hakuri sannan sukayi sallama suka tafi.
Sai da suka fito sannan Aisha ta tuna da Amira, take ta buga mata waya tace ta zauna ko a library ne ta jirata nan da awa daya zata karaso.

Gidan Yaya Bellon suka koma inda sai da sukayi Sallah suka ci abinci sannan Aisha tayi musu sallama ta ja motarta ta tafi.

Duk yanda yake tsananin son magana da Aisha haka ya hakura ta tafi, sai dai ya bari kawai idan ya fito daga gidan Yaya Bello sai yayi mata waya ko yaya ne yaji muryarta tunda Malam yace kada yaje gidan da take.

--------
Saida ta dauki Amira sannan suka wuce gidan, tana shiga tayi wanka ta canza kaya sannan ta zauna ta kirawo Hajiya ta gaya mata abinda ake ciki. Nan take Hajiya ta bata shawarar ta yi sadaka kuma ta cigaba da addu a. Haka tabi  yan uwanta da kira duk ta sanar da su su cigaba da tayata addu a.

Duk da Malam yace kada ya zo gidanta sai an kwana bakwai wannan bai hanata walwala ba, tunda dai an warware matsalar. Haka ta kwana tana Sallah da addu a cikin walwala.

---------

Tunda Aishan ta fita Abban Sadik yake kokarin cewa zai tafi amma Yaya Bello ya hanashi, ya kula gidan Aishan yake son zuwa kuma Malam yace kada yaje sai an gama addu a. Nan ya rikeshi har saida sukayi Sallar Magriba kamar yanda ya saba. Ya jaddada masa addu oi da kuma karatun kur ani wanda Malam yace yayi sannan yace

 Idan bakayi karatun kur ani a dakin ba ni zan iya dauko Malam muzo muyi maka karatun ka dai sani don haka ka tabbatar kayi abinda Malam yace.

Sukayi sallama ya kama hanyar gidan.

Saida suka kusa shiga unguwar sannan ya sami waje yayi parking, ya zaro wayarsa da nufin ya kirawo Aisha. Ga mamakinsa babu irin binciken da baiyi a wayar ba amma babu lambar Aisha, ya budo Whatsapp ma ya duba ko zai sami chats din ya dauki lambar daga nan amma bai samu ba. Gashi dama ya san bai taba haddace lambarta ba lambar Zahra kawai ya haddace kuma da kunya ya kirawo wani yace a bashi lambar Aisha bayan tana gidansa. Haka ya gaji ya hakura zuciyarsa babu dadi ya kama hanyar gidan.

Ta gaban gate din gidan da Aishan take ya wuce, sai da yayi slow ya karewa gidan kallo yana mamakin yanda ya dade bai ga gidan a wajen ba domin kullum ta nan yake bi idan ya dawo daga aiki. Haka ya wuce gidan Zahra yana mamakin wannan abun.
-------

Yanda ta saba taryarsa cikin walwala idan ya dawo haka tayi masa; Saida ya huta yayi sallar isha i sannan ta kawo masa abincin dare. Binta kawai yakeyi da kallo domin abubuwan da suka faru yau tabbas sun haifar masa da wasi-wasi game da wacece Zahra; canza masa akayi ko kuwa dama can haka zuciyarta take. Baya jin zai iya tunkarar ta da wannan zancen a yanzu musamman da yake Malam yace kada su tada wata tarzoma kuma da dan sauran shakkarta a zuciyarsa. Don haka ya barwa tashi zuciyar wannan batun.

Haka tayi ta hidima da shi tana jansa da hira, domin tun da ta gane ba zata iya zuwa a raba shi da  yan uwansa yanzu ba sai ya zama duk lokacin da ya wuni wajensu idan ya dawo haka zatayi ta kokarin faranta masa rai domin ya gane ta fi su sonshi.

Bata ga alamar damuwa a tattare da shi ba sai dai ta kula da yanda tunaninsa yake yin nisa daga inda take, haka dai tayi ta fama. Ko da suka kwanta ma duk yanda ta kai ga dagewa haka ta hakura ta barshi domin gaba daya nuna mata yayi bacci yake ji ba zai iya ba. Bai fiya kin sauraron bukatarta a wannan lokacin ba don haka ta kwana cikin damuwa da fatan Allah ya sa ba wani abu Yaya Bellon yayi masa ba.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

36

Tun bayan da suka dawo daga gidan Malam Aisha ta fara shirin tarbar Abba, tunda tana ji aka ce bayan kwana bakwai zai fara rabon kwana.

Duka labulayen gidan ta bayar aka wanke, suka share ko ina suka gyara ita da Amira. Ita kanta sai da gidan ya bata sha awa saboda akwai abubuwa na gyaran gidan da ta dade bata yi ba.

Musamman ta sami lokaci suka je sayayya ita da Amira saboda kayan gyaran fatar ta duk sun kare bata sayi wasu ba.

Nan da nan gida ya dau kamshi.

Ranar Alhamis taje saloon aka yi mata gyaran jiki da kitso, tsaf aka goge mata fata ta fara sheki.

Ita kanta bata san irin tarbar da zata yi masa ba domin gaskiya tana jin haushinsa sai dai tayi shirin ne don tana so ya sameta yanda take so.
-------

Ranar Juma a da su Abba suka je wajen Malam ya sanar da su gobe su zo tare da Aishan. Anti Karima Yaya Bello ya sa ta kirawota ta sanar da ita, don haka da gari ya waye bata je islamiyya ba sai ta jira karfe goma tayi ta wuce gidan Yaya Bello.

Daga can suka hadu suka wuce wajen Malam.

Nasiha ya sake yi musu sannan ya basu addu oin da kuma turare wanda yace Aisha ta turara shi a gidanta yau din nan kafin maigidan ya shiga. Suka yi masa sallama suka koma gidan Yaya Bello.

Sun dauki lokaci suna hirarsu ita da Anti Karima sannan tayi musu sallama ta fito, ta sami Yaya Bello tare da Abban Sadik a falon. Ta yiwa Yaya Bello sallama tare da godiya sannan ta fice.

Da hanzari Abban Sadik din ya mike ya bi bayanta, ta zauna a mota tana kokarin saka mukulli ya bude kofar gaban motar ya zauna kafafunsa suna waje.

Hannunta yana kan sitiyarin motar ta kawar da kai ta dubi daya gefen, ya dubeta yayi murmushi. A can kasan makogoronsa ya kirawo sunanta

 Aisha.

Yanayin muryar tasa sai da yasa taji kiran kamar a tsakar kanta. Ta juyo ta dube shi ba tare da ta amsa ba. Murmushi ya sake yi mata sannan yace

 Kiyi min abincin dare yau a nan zan kwana.

A hankali tace

 Toh.

Ya sa hannu ya dauki wayarta wadda take ajiye a kusa da giyar motar, ya lalubo lambarsa ya danna kira. Sai dai ga mamakinsa lambar ta ki shiga wanda ya sa ya gane blocking din lambarta akayi a wayarsa. Nan da nan ya dauki tasa wayar ya duba jerin blocked numbers, yana kalla kuwa ya gane lambar tata domin dama haddacewa ne bai yi ba. Nan take ya cireta daga blocking kuma ya mayar yayi saving.
Suka dauki lokaci a zaune a haka; shi yana faman kare mata kallo ita kuma ta ki kallonsa kuma taki magana.

Jimawa kadan ya kirawo sunanta yana murmushi, ta juyo ta kalleshi ba tare da ta amsa ba. Suka hada ido, ta dauke kanta yayinda shi kuma yayi mata murmushi. Yace

 Bari na barki ki tafi, sai na shigo.

Tace

 A dawo lafiya.

Sai da yayi kokawa da zuciyarsa sannan ya fita daga motar, kafin ya gama shigewa cikin gidan ta ja mota ta kama hanya.

Yana shiga cikin gidan bayan ya zauna ya lalubo lambar account dinta ya tura mata Naira dubu hamsin. Bayan kudin ya tafi ya tura mata sakon text message

 Ban san me ake bukata ba a gidan amma na turo 50k kiyi cefane kafin nazo.

Ya ajiye wayar suka cigaba da hirarrakinsu.
& & & &
Babu yanda Yaya Bello bai yi da shi ya tafi da wuri ba saboda ya kula da yanda yake dokin ganin Aisha, amma Abban Sadik yaki tafiya har sai da sukayi Sallar la asar sannan yayi masa sallama ya tafi.
Kai tsaye gidan Zahra ya wuce.

Yaran duk suna islamiyya don haka ita kadai ce a falo tana zaune tana ta cin goriba. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya dubeta yace

 Yau kuma goruba kika samu?

Tace

 Wallahi. Yarane suka siyo zasu tafi

41 / 58