Uwar Sadiku Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sakina Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 58

33K to 36K   out of 172.2K words

fice.

Yana shiga ya wuce falo, don haka mommy ta bishi. Yana kokarin kunna TV tace

 Abban Sadik lafiya dai Aishan bata dawo ba?

 Uh, bata jin dadi ne. Jiri take da ciwon kai kin san bata gama warwarewa ba tayi zazzabi kwanan na.

Ta hadiye malolon da ya taso mata ta yage baki tace

 Mhmm! Ko dai kanwata ciki ne da ita ne ake mana laulayi a fakaice.

Yayi dariya yana shafa kai

 A a Babu wannan zancen tukunna, zazzabi ne dai kawai.

Suka dan taba hira sannan ta tashi ta wuce dakinta, tana shiga ta zauna a gefen gado cike da damuwa; tabbas cikine da Aisha don jiyan ma tana kula da yanda take abubuwa jikinta babu kwari. Tab, ya za ayi ta bari a haihu da mijinta, gashi ta cika gida da yara mata yanzu idan Aishan ta haifi maza uku ko mutuwa yayi sai ta fita gadon arzikin da aka tara da ita. Gaskiya ba zata yarda ba.

Ta shafa hannunta inda aka saka mata inplant na family planning; tabbas da an koma aiki zata je a cire mata wannan abun don ya zama ko da bata sami hanyar lalata cikin Aisha ba to sai dai suyi haihuwar tare. Ba zata sha wahalar talaucin Yusuf ba kuma ya tara dukiya a fi ta gado. Haka ta zauna tayi ta tunani har saida Nana ta shigo kiranta ta sanar da ita an sauke wani ta zo ta nuna wanda za dora sannan ta taso ta fito.

Zuwa la asar sun gama soya duk naman da za a soya, sai su Jummai da suke ta faman gyara wajen. Danyen naman kuma duk an lode a babbar freezer.

A falon kasa ta zauna ta dibarwa Hajiya nata naman cikin wata babbar roba mai murfi! Duk da Hajiyan ma ya yanka mata rago a gidanta amma haka suka saba sai an kai mata. Ta sami  yan bakaken ledodi ta zubawa su Jummai nasu tunda dukansu ta basu danye da yawa sun kai gida sannan kuma biyansu zata yi kudin aikinsu.

Ta dauko kwanon samira mai kamar girman langa tuwo da miya ta zuba naman har ta cika sannan ta rufe sannan ta dauko roba irin ta take away din nan ta zuba kayan ciki ta rufe.

Ta dubi Rukayya wadda take zaune tana ta cin naman tace

 Rukayya dauki ki kaiwa matar ubanku.

Tace

 Anti Aisha?

A fusace mommyn tace

 Ba ita ba ni, kuma idan kin je ki zauna tunda uwarkice.

Ta gane sakon don haka nan da nan ta dauka ta fice.

A falo ta sami Aishan tana zaune tana kallon TV tana shan zobo da cake. Bayan ta sake gaisheta ta mika mata kwanukan tace

 Wai gashi inji Mommy.

Bata zata nama bane a tunaninta ko abinci ne don haka tace da Rukayyan ta ajiye a kan dining table. Bayan ta ajiye ta kuma ce mata

 Ki debo zobo a fridge ki sha, ga cake nan a kan dining table ki dauka.

Ta shiga ta debo zobon ta fito ta dauki cake din ta wuce ta zauna a kujerar zaman mutum daya. Ta kurbi zobon sannan tace

 Anti kikayi cake din bana nan, ina so fa na koya Anti.

 Kada ki damu in dai cake ne next time in zaki tayani kwana sai mu bi dare mu yi miki na zuwa a school ko? Sai dai fa ina tsoronki a kicin kin yi kankanta fa. Shekarunki sha daya fa, bar ganin kinyi tsawo.

 Kai Anti, Allah zan iya. Ai dai kema kin ce ina da natsuwa don haka kin san ba zan yi barna ba ko?

 Tabbas kina da natsuwa Rukayya, in sha Allah za muyi cake mai dadin gaske kuwa.

Saida ta shanye zobon nan suna hira sannan ta tuna da gargadin da akayi mata ta tashi ta fice ta koma gidan.

Bata dade da fita ba Aisha ta tashi ta bude kwanukan, ta bude baki tana mamaki; kada dai ace duk naman nan da aka soya wannan ne rabonta, ko kuwa dai daga makota aka aiko da wannan din.

 Ikon Allah.

Ta fada a fili tana mamaki da dariya. A yanka sa guda kato da rago amma a sammata wannan, ai ko su Jummai ta san sun cancanci kason da yafi wannan. Amma dai zata jira tunda yau maigidan a nan zai kwana taji bayani.
Ta mayar da kwanukan ta rufe ta barsu a wajen.
& & ..

Sai bayan sallar isha i ya shigo gidan, kamar yanda ya tsira  yan kwanakin nan haka ya mike a kan kujerar zaman mutum uku ya fara gyangyadi. Har ta gama jera masa abincin dare ta zo ta tsaya a kusa dashi bai ji motsinta ba; ta rasa gane wannan yawan gyangyadi da baccin da yake mata  yan kwanakin nan, sai kace wanda yake kokawa da zaki a office din. Tabbas da ace shine matar da zata ce ciki ne da shi. Tayi gyaran murya ta zauna a hannun kujerar tace

 Habibi abincin daren fa, ko har kaci a mafarki?

Ya tashi zaune ya dungure mata kai yana fadin

 Sai dai idan mafarkinki nakeyi kika bani abincin a mafarki, ba dama mutum ya kashingida sai kice yana gyangyadi.

Tayi dariya

 Uhm, to a dai taso aci abinci kafin na cinye abuna.

Saida suka gama cin abinci suna hira sannan yace mata

 Dan debo min naman nan mana, Zahra tace ta raba an kawo miki naki ko?

Ta kalleshi da mamaki tace

 Au wai wannan shine rabon nawa?

Kafin ya amsa ta mike ta dauko kwanukan nama ta ajiye ta zauna tace

 Kaga fa abinda Rukayya ta kawo, wallahi na zata ma daga makota ne.

Mamaki ya bayyana a fuskarsa yana buda kwanon da robar, yace

 Wannan din shine rabon naki?

 To ni dai shi aka bani. Shiyasa nima na zata daga makota aka kawo. Wannan nama ai ko su Jummai kason su ai ya kamata yafi wannan balle ni, duk da ban san yanda tsarin yake ba.

Yayi shiru yana mamakin wannan rabo na Zahra, domin ko yanzu da zai fito ya ga nama zai kai fanteka biyar a falon sama kuma ya san akwai wani ma a kicin.

 Bari idan naje yi musu sallama maji yanda aka yi.

Nan ya sa naman a gaba, kafin wani lokaci ya ci rabi.
& & ..

Sai wajen goman dare sannan ya tafi wajen Zahra don yayi musu sai da safe. Babu kowa a falon sai Sadik yana kallon TV yana cin nama da burodi. Bayan yayiwa Abban sannu da zuwa ya amsa ya wuce sama.

A dakinta ya sameta tana kwance a kan gado sai dai ba bacci takeyi ba, bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta nade kafarta don ya sami wajen zama.

Yace

 Gajiya ce ta sa kika kwanta da wuri yau?

 Wallahi kuwa, duk jikina ciwo yakeyi.

 Sannunku da kokari, Allah ya maimaita mana.

Suka yi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

 Kika ce min an raba nama an bawa Aisha nata?

Da mamaki ta amsa

 Eh, Rukayya ta kai mata, sai dai idan shirme tayi.

 Bana jin, na dai ga naman ne a  yar Samira don ko kafin na fito ma na cinye rabinsa. Duk wannan naman ya za ayi kuma ace wannan ne rabonta, ko ba ke kika zuba bane.

Ta bata rai

 Ikon Allah, na kula kai dai idan dai a kan Aisha ne ba zan taba burgeka ba. Gani nayi ita kadai ce a gidan nata, idan ta cinye wannan ba sai ta turo a kara mata ba? Kai kuma ai ga naka can na ajiye maka a dakinka kamar yanda muka saba. Nan fa mu shida ne ni da yara ga masu aiki, baki da danginka duk nan suke shigowa kuma a nan zasu ci ga makota ma duk a nan zan dibar musu. Naman Sallah kuma dama ina yaga wani auki da mutum zai zata zai samu da yawa?

Binta kawai yake da kallo yana mamaki, so yake yayi mata fada amma ya rasa me ya hanashi.

Cikin sanyin murya ta shafe kwalla daga idonta tace

 Kayi hakuri idan rabon da nayi bai yi maka ba, ka kwashi naman gashi can a falo ka kai mata ta raba in ya so ta aiko mana da kason mu.

Ta sake share hawaye tana shirin kwantawa, yace

 Wannan duk ba abun kuka bane, shikenan a barshi haka. Allah ya maimaita mana. Ni na tafi sai da safe.

Kafin ta amsa ya tashi ya fice daga dakin, ta bi bayansa da kallo tana mamaki don ta zata fada zai yi kuma sai taga ya fice. Tayi murmushi da ta tuno da aikin da Hajja tayi mata; tabbas aikin ne ya fara ci da ta san baran-baran zasuyi don ba zata bashi naman ba.

Dama tana sane tace a nan za su soya naman don kawai Aishan tayi mata aiki ne don bata isa taci kamar rabonta ba.

UWAR SADDIKU

Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)

13

Tunda ya shigo gidan ta gane bashi da nutsuwa, bai yi mata maganar naman ba don haka itama sai kawai ta kyaleshi. A nan kan dining table a nan kwanukan da aka kawo naman suka kwana, har ta saka musu abincin safe suna nan bata dauke ba.

Kwai kawai ta soya suka hada da shayi da burodi suke karyawa, suna yi suna hirarsu cikin walwala. Ya dubi kwanon yace

 Naman nan inaga in na fita zan bawa Malam Sule danyen nama ya kawo miki, sai ki soya ki barshi a nan kya yi amfani da shi tunda ko babu komai naman sallah ai ka bawa baki.

Da mamaki ta dubeshi

 Nama kuma, haba dai! Me yayi zafi?

 To duk sun rabe wancan naman, akwai dai danyen nama a babbar freezer a can idan zaki yi miya ki dinga turawa a karbo miki. Wanda za a kawo din kuma sai ki soya.

 Hakan ma yayi, amma ba sai an kawo wani danyen nama ba. Kasan na gaya maka nayi layya a gidan Umma ko? To wallahi ta ajiye min nama danye da soyayye, don nice ma nace su barshi a can idan naje na taho da shi da tuni an kawo shi.

 Zaki dai kwashewa Umma nama, bayan ga naki a nan.

 Ba haka bane, ka san fa raguna hudu aka yankawa Umma naman ma ai ya yi mata yawa; ga na Yaya Abubakar, ga nawa ga kuma na mijin Zahida sannan daga gidan Baffa ma cinyar sa aka kawo.

Haka dai ya hakura da batun naman.

Sai bayan azahar ta shirya sukaje tare ya ajiyeta a gidan Umman, nan yara suka hadu akayi ta murna. Tayi matukar kewarsu don haka ta sanar da Umma duk ranar Juma a zata dinga daukarsu daga makaranta su dinga yin weekend a wajenta, in ya so ranar Lahadi da yamma sai ta dawo da su.
_

Kamar yanda ta daukarwa kanta alkawarin ana sallacewa taje aka cire mata abun family planning din da ta saka, don haka ko al ada batayi ba bayan an cire ta sami ciki. Shi kanshi Abban Sadik din bata sanar da shi da cikin ba ta bari sai ya kai kamar wata hudu; saboda bata so ta gaya masa ya gayawa Aisha kada ta cutar mata da ciki.

Duk wata tambaya da zata yiwa Rukayya a kan alamun ciki a tattare da Aishan Rukayyan ta tabbatar mata ba haka bane. Sai dai bata yarda da hakan ba; gani takeyi kamar Rukayyan ce bata gane ba. Don haka har saida cikin nan yayi wata uku sannan ta sanar da Abban Sadik wanda daman ya riga ya gane kyaleta kawai yayi.

Tunda ta san ta sanar da shi cikin nan kuma bata ji ya ce Aisha ma tana da ciki ba sai ta tsiri fitna; kullum akwai abinda zatace ya sa Aishan ta dafa mata daga karshe kuma idan an dafa bata ci sai ta san abinda tace bai yi mata ba. Da kanshi ya gane hakan ya daina biye mata.

Namiji take so ta haifa don haka sosai ta dage da addu a Allah ya sa namiji ne a cikinta, sai da cikin ya kai wata biyar sannan taje aka yi mata hoto wato scanning inda aka tabbatar mata namijin ne.
--------

Kwanci tashi cikin Zahra har ya kai wata bakwai, ya riga ya fito sosai gashi da alama yaron da yake cikin nata yana da nauyi sosai. Dole yasa take hakura da kusantar Abban Sadik kamar yanda take so, ya zama sau daya a mafi yawancin dare wasu lokutan ma kuma idan yaga yanayinta haka yake lallabata suyi bacci ba ayi komai ba.

Babu abinda yake bata mata rai a rayuwarta kamar ta tuna cewa Yusuf yana da wata matar da zai iya biyan wannan bukatar da ita. Ta fiso ace ita kadai Yusuf zai iya kusanta, idan kuma ta kama dole sai an hada da wata to ta zama itace a sama.

Yanzu da bata iya yi masa yanda take so tabbas ta san ranar kwanan Zahra kwana sukeyi suna faranta ran juna, watakila ma shi yasa a mafi yawancin kwanta yake lallabata suyi ta bacci kawai; duk da tayi masa bayani sau babu iyaka cewa zata iya don babu inda yake mata ciwo amma ya ki ya saurareta.
& & ..

Ita da Jummai ne kawai a gidan saboda yara duk sun tafi makaranta, maigidan kuma daman ba a wajenta yake ba. Jummai tana kasa tana ayyukanta yayinda ita kuma take zaune a falon sama tana kallon TV.
Jummai ce ta kwankwasa mata kofa ta sanar da ita zuwan Hajiya Amina, nan da nan ta bayar da umarni ta hawo sama. A nan fridge din saman ta samar mata ruwa da lemo suka zauna sun hirarrakinsu.

 Kinyi nauyi kawata, kin rike wuta sosai fa.

Amina ta fada tana dariya.

Itama dariyar tayi sannan ta bada amsa

 To ke kuwa ya za ayi a zo gidana kuma a fini iyawa? Ai ba zai ma yiwu ba. Kin san cikin ma da na dauka tana da shi ashe babu komai in gaya miki.

 Ke kawata?

 Allah kuwa, kuma kin san nayi scanning an tabbatar min namiji ne a ciki na.

Ta zaro ido tana murmushi

 Kai amma na miki murna kawata, finally. Ina ma biyu ne maza.

 Kada ki damu dayan ma yana tafe in sha Allah. Yanzu kawai damuwata na san a ranar kwananta kashe dare suke suna harka tunda in ya zo nan sai yayi ta wani faman nuna min tausayi na yake ji wallahi duk jarabata haka nake kyale mutumin nan saboda takaici. Ko da yake na san dama haka yake idan ina da ciki da ya fara girma yake rage wannan bukatar, to amma yanzu kin ga ai ba kamar da ba da nake ni kadai.

Amina ta harareta tana fadin

 Kai kawata, kina faman motsi da kyar ki dinga tausayin kanki mana. Ki barshi kawai wallahi damarsu ce, amma da kin haihu ki nemi Hajja ta hadaki da kyau sai ki koma aiki.

Haka suka cigaba da hirarrakinsu har wajen azahar sannan Aminan tayi mata sallama ta tafi.

Ta kula Amina ba zata taimaka mata wajen karkato Abban Sadik ya rage kusantar Aisha ba don haka ta barta da zancen, amma bata fasa tunanin mafita ba don tayi lissafi ta ga daga yanzu zuwa tayi arba in akwai wajen wata biyar kenan da zai je yayi ta kusantar Aisha tana nan tana kallo.

Gashi ba gidansu daya ba balle ta gane me yake faruwa idan ya shiga dakin Aishan.  Yan kwankin nan idan yayi mata sallama ya tafi haka take kasa bacci saboda takaici. Da haka ta yanke shawarar zata nemi Hajja ko da akwai abinda zata iya bata tunda dai ta san tana da abubuwan da idan aka sakawa mutum a abinci za a tayar masa da sha awa don haka ta san na kashe sha awar ma ba zai gagara ba.

Bayan ta gama yiwa Hajja bayanin duk wata damuwarta tace

 Hajiya kenan, Uwar Saddiku baki da wasa. Kada ki damu akwai abinda zan taho miki da shi kawai ki tanadi dubu goma da kuma kudin montana shikenan.

Sukayi sallama da alkawarin da yamma zata zo.

Yamma tana yi kuwa sai ga Hajja. Nan suka zauna a falonta, bayan sun gaisa tace

 Hajja, kin san me nake so? Wallahi so nake idan kina da wani abu wanda kika san baya cutarwa amma dai ya zama ko da ya je wajen matarsa ba zai iya komai ba, a kalla zuwa lokacin da zan haihu na dawo normal sai mu cigaba da karawa.

Tayi dariya tace

 Uwar Sadiku kenan, kin san kan tsiya. To akwai abinda zan baki, shayi kawai zaki dafa dashi ko zobo idan dai ya sha babu abinda zai iya komai kokarinta sai bayan akalla awa goma Sha biyu. Ke wasu ma har awa ashirin da hudu. Kedai aikin da zakiyi kawai shine ki san yanda zakiyi duk ranar kwanta ya sha wannan hadin musamman bayan magriba.

Ta karbi kullin da Hajja ta miko mata tana dariya tace

 Yauwa ta wajena, bashi dai da illa ko?

 Babu wata illa, da zarar ya dauki lokaci zai fita daga jikinsa ya cigaba da harkarsa normal.

Nan suka gama magana ta kawo kudi ta sallameta.

Cikin walwala ta karasa wunin ranar; ko babu komai ta san abinda yake hanata bacci ya kau don haka yau akwai bacci harda minshari.
& &

12 / 58