Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 69

24K to 27K   out of 206.1K words

laka, she felt so embarrassed da abinda ya faru ɗazu, gaban madubi ta tsaya ta shafa lotions ɗinsa sannan ta fara ƙoƙarin kwashe gashin ta,amma ta kasa gashi duk ta gaji. Buɗe ƙofar Amreesh yayi ya shigo suka haɗa ido ta madubi, sauke idanun ta tayi , ajiye hijabin dake hannun sa yayi saman gado kafin ya isa inda take,'' let me help '' ya faɗa yana zaunar da ita saman kujerar gaban madubi
Ɗan ranƙwafo wa yayi,hakan yasa ta ɗan riƙe numfashin ta,yana lure da hakan amma se kawai ya miƙa hannunsa ya dauki comb ya fara combing ɗin gashin ta his light touches sending shivers down her spine
SE da yagama sannan yayi styling ɗin gashin style me kyau. Murna tayi sosai bayan ya gama and she looked at it through the mirror
Shi dai ya ja gefe yana kallon yanda take murnar and he felt something shima kamar farin ciki

Bayan ta gama yaba kitson ta dawo kusa dashi holding his hand idanun su cikin na juna '' thank you '' tace tana sakin murmushin daya sa dimples ɗinta lotsawa ''uhm'' kawai ya faɗa yana shafa kanta, lumshe idanun ta tayi Sannan ta rungume sa,
Tsaye yayi without making any efforts to hug her back. Ɗago kanta tayi Sannan tace '' ya akai ka iya?"
''mama na ta koyamin'' ya faɗa looking distant. Ita da bata fahimci yanayin sa ba taƙara cewa ''yaushe za ka kaini in ganta''
''she's no more" ya faɗa yana kallon ta
''sorry'' ta faɗa hugging him tighter,shiru su biyu suka yi listening to each other's heart beat
Ganin lokacin sallah yayi yasa suka yi disengaging from the hug sannan ta riƙo hannunsa they both entered the toilet together sukayi alwala tare
Bayan sun fito excitedly tace ''idan ka dawo daga Masallaci, let's cook together pls'' ta ƙarashe maganar holding his arm making a very cute and irresistible gesture

''okay'' ya faɗa, tsalle ta fara tana faɗin ''thank you''

Fita yayi daga ɗakin daidai Dr Ahmad yana fitowa shima
Dariya Dr Ahmad ya fara, Amreesh ya tsuke fuska yayi gaba abinsa
Saida dr Ahmad yay me isar sa Sannan yabi bayan Amreesh tare suka fita.
Bayan Amreesh ya fita ɗakin su ta ruga taje ta kwaso kayanta, ta dawo da su ɗakin Amreesh
Sannan ta kabbarta sallah.
***********************
Lokacin da Salmah ta sauko bayan tagama Sallah,samu tayi duk suma suna ƙasa dr Ahmad da Amreesh ina one sit Samha on the other tana kallon cartoon, Amreesh da Dr Ahmad kuma suna magana
''Yaushe zaka koma office?'' Dr Ahmad ya tambayi Amreesh daya kafe wuri guda da ido
Jin tambayar Dr Ahmad,batare da ya kallesa ba yace 'monday' 'okay' Dr Ahmad yace Sannan ya maida hankali ga cartoon ɗin da Samha ke kallo
Kallon ta yayi daidai ita ma ta ɗan saci kallon sa,suka haɗa ido ,ɗauke kai tayi tana faman tsuke fuskar ta
Shi dai bai ce komai ba.

Ƙarasowa parlorn Salmah tayi,jin Amreesh zai koma office duk taji bata ji daɗi ba, gaida wa sukayi da Dr Ahmad,
Kafin ta je wurin Amreesh tana turo baki tace'' baka faɗamin zaka koma office ba ai'' ta ƙarashe maganar kamar zatayi kuka,ɗan satar kallon ta Samha tayi jin yadda take maganar
She really wanted to laugh, and idan ya tafi Ba ga taba? Me yasa mahmah zata wani damu?
Kallon ta Amreesh yayi kafin ya miƙe ya riƙo hannun ta suka tafi kitchen,Samha da Dr Ahmad sukayi exchanging ɗin glances each with their thoughts
Dr Ahmad yaji daɗi sosai there's really a massive improvement a condition ɗin Amreesh, ita kuma Samha she felt jealous Saboda,meyasa yanzu attention ɗin Mah-mah yafi karkata akan sa? Miƙewa tayi zata bi su, Dr Ahmad yayi saurin riƙo hannun ta se kiciniyar ƙwace hannunta take, amma takasa, se baki take, she really amused him,with a single pull ya jawo ta, ta faɗi zaune gefen da tana huci,'' calm down my lady'' Dr Ahmad ya faɗa yana kallon fuskar ta with an amused face ya ƙara da faɗin ''ki bar su,su sha love mana uhm? Don't be the jealous one!" A fusace tace '' I'm not jealous, he's taking my sister away! Duk kulawar ta, ta koma akan sa we rarely spend time together,koda yaushe yana nan biye da ita like a tail!!" Ta ƙarashe maganar tana kuka,its really rare to see her cry. Jikin Dr Ahmad ya yi sanyi ganin yanda take ƙoƙarin riƙe hawayen ta she meant every word she said daga ƙoƙon zuciyar ta
'' I'm sorry'' ya faɗa
''Bakomai '' ta faɗa tana share hawayen ta ganin Hakan yasa,yayi ƙasa da murya yace '' I Will love you,idan kin bani dama'' kallon sa tayi da sauri,se kuma ta fara ƙoƙarin ƙwace hannun ta ''dan Allah samha'' ya faɗa yana marai raice fuska
''sake ni'' ta faɗa tana hararar sa
Sakin ta yayi ta matsa nesa da shi
Amreesh lokacin da suka isa kitchen,ɗaukar Salmah yayi ya aza ta saman counter yana goge mata hawayen da suke ta zuba kamar an buɗe tap
''tell me,me yasa kike kuka?" Ya faɗa yana tsaya wa tsakanin ƙafafun ta, his blue eyes fixated on her
ƙasa tayi da kanta ba tare da wani ɓoye ɓoye ba tace '' I'm already missing you '' ta faɗa her teary brown eyes into his blue ones,kunya ta ji sosai,tana ƙoƙarin maida kanta ƙasa yayi saurin riƙo haɓar ta and she refused to meet his gaze
''look at me '' ya faɗa in a low and sexy tone,ɗagowa tayi daƙyar suka sake haɗa ido yace'' acikin kwanakin da suka rage before I resumed, I will b yours'' ya ƙarashe maganar yana ƙara matso da fuskar sa gab da tata har suna jin numfashin juna,ga wani irin luguden da zuciyar ta keyi,they stared at each other intently something like magnet pulling her in kafin slowly she placed her lips on his....








WAYE SHI?(Behind the mask) By autumn 17



Chapter eleven: His own family

Holding his head with her hand to deepen the kiss, wani irin baƙon abu ne ke ziyartarsa, it's something new and strange,baima San Taya ze iya describing ɗin abinda yake ji ba,he was still trying to understand his feelings when suddenly she disengaged kamar nepa ta leƙo ta koma.... ɗago kansa yayi and they stared at each other,wata irin kunya ce ta kama Salmah, share wa tayi Sannan tayi cupping ɗin fuskar sa, suna kallon juna,still smiling tace '' faɗa min,did you feel it"?
Bai ce komai ba se kunnen sa da yayi ja '' Are You blushing?'' ta tambaya tana haɗiye dariyar ta,ƙasa yayi da kansa yar dariya tayi tana rungume kansa to her chest Sannan tace ''kada ka damu,if you don't feel it now,wata rana zakaji more than just a kiss'' ta ƙarashe maganar tana shafa kansa, ita bata San da cewa bawai yayi shiru bane saboda yana jin kunya ko baiji komai ba,kawai dai saboda he didn't know how to describe what he felt,he was unsure.
Bayan wani lokaci, they disengaged, Salmah ta sauko daga saman counter ɗin tana faɗin '' yunwa nake ji, let's cook''
Buɗe drawer tayi,ta ɗauko neatly folded aprons guda biyu pink and white color, dawo wa tayi inda yake tsaye da murmushi a fuskar ta,tsaya wa tayi gaban sa Sannan ta warware apron ɗin tayi masa alamar ya duƙo saboda ya fita tsayi, ɗan ranƙwafo wa yayi ta saƙala igiyar a wuyan sa Sannan tayi rounding ɗin hannunta around his waist and tie the ropes, tsintar kansa yayi da riƙe numfashin sa why? Her chest was rubbing on his, and her scent? It was doing something weird to him....''done'' ya tsinkayi Muryar ta, wani irin ajiyar zuciya ya,ya sauke,pink apron ɗin ta warware ta bashi with a sheepish smile on her face, karɓar apron ɗin yayi his blue orbs fixated on her, murmushin ta ya ƙara faɗa lokacin da ya matso kusa,yayi mata kamar yanda tayi masa, hannun sa a ƙugunta ya ƙara matso da ita jikin sa,her chest oh his,haɓarsa a kafaɗar ya,runtse idanun ta tayi, her hands slightly gripping on his waist, ga wani irin feeling da take ji a cikin ta,it was butter flies fluttering in her tummy! '' done'' ya faɗa saitin kunnen ta
Matsa wa tayi da sauri,tana ɗan rarraba ido,har ta ji kunya. 'what were you thinking ' ta ayyana aranta tanajin kunya sosai.

Shi dai kallon ta yake, what's with the sudden change
'' kina lafiya?'' ya tambaya yana dafa kafaɗar ta
Yar dariya tayi Sannan tace 'of course I'm fine,mu fara girkin, grilled chicken, fried fish da jallop rice.'' ɗan dakatawa tayi Sannan tace ''duk ka iya wannan?" Bai ce komai ba,ya nufi fridge ya ɗauko everything they needed

Ita kuma tana taimaka masa da dauko wannan ɗauko wancan,
Ɗan tsira masa ido tayi,he looked so sexy and perfect husband material,ganin zai juyo da sauri ta juya ta fara juya kifin, kafin ta fara jefoma masa tambayoyi kala da iri, and he found himself answering each patiently.

*************SAM-MAD***** yayi mamaki sosai ganin har yanzu basu fito ba,se kuma ga ƙamshi na tashi,taɓe baki Ahmad yayi yana gulmar Amreesh a ransa,wai tunda suke Amreesh never made any efforts to cook,Amma yau gashi harda su jan matar sa ya shige kitchen,shi game mata! Amma duk da haka yana cikin farin ciki sosai.

Tun tuni Samha sai cika take tana batsewa,time to time Ahmad ke kallon ta yana riƙe dariyar sa, the girl is something else, soon enough ƙamshi ya cika ko ina.

A can kitchen ɗin kuwa, Salmah da Amreesh were having the best times of their lives,yanda Salmah take basa labari akan child hood ɗin su,he found it incredibly interesting.

Soon the food was ready and they begun arranging it on the dining,
Har sungama, Salmah zata je takira su, Amreesh ya riƙo ta juyowa tayi suka haɗa ido, jawo ta yayi gently,ya zaunar da ita on one of the seats,yace'' zan kir....'' rufe bakin ta yayi da yatsan sa, ya zauna on the seat next to hers sannan yace '' idan suna jin yunwa,zasu zo'' ya ƙarashe maganar yana zuba mata abinci a plate ɗin gaban ta. Ya ɗau cokali ya fara bata abaki, it tasted delicious
Se ga samha da Ahmad suma sun zo, suka zauna kusa da juna suna facing ɗin su Amreesh
'' su zakee masu mata'' Ahmad ya faɗa teasingly,yi Amreesh yayi kamar beji abinda Ahmad ya faɗa ba ya cigaba da ba Salmah abincin baki,she obviously looked so shy,ita ko Samha sai rolling ɗin idanun ta take. Taja plate ta zuba ma kanta everything served on the table
Dr Ahmad yaɗan matsa kusa yace '' nima azuba min my lady'' samha ta haɗiye abincin da ke bakin ta batare da ta kalle sa ba tace '' baka ji yunwa ba'' ɗan shafa ƙeyarsa yayi,biting his lower lip sannan yace ''let me help my self''
Ya ɗau ki plate ya zuba ma kansa ya fara ci.

Ganin Amreesh yana ta bata abincin kuma shi baci yake ba yasa ta karɓi cokalin daga hannunsa ta fara basa, kallon su Samha tayi ta taɓe baki 'wai gardi guda dashi ake basa abinci a baki' ta ayyana aranta tana hararar Amreesh da bai masan tanayi ba. His only focus is on his wife dake blushing,kumatun ta sun wani yi ja. Idan ta miƙo spoon ɗin ,he will hold it along with her hand and take it to his mouth yana mata kallon ƙasan ido.
Abinda ke bata kunya ke nan.
''soyayya ruwan zuma ce yara kusha...'' Dr Ahmad ya faɗa yana tuntsire wa da dariya, this further embarrassed Salmah, samha da takaici ya cika ta,tace ''abincin ma bai yi daɗi ba'' ta gama maganar tana taɓe baki da kuma ƙara kai wata loma.
Ahmad yaɗan waro idanu and he looked at Amreesh da ya ɗan ɓata fuska, he looked funny, ''abincin Bai yi daɗi ba?" Ya tambayi Salmah yana ɗan turo baki, ba tare da yamasan yanayi ba. And damn, he looked cute.

Salmah ta ɗan ƙifta idanun ta several times, kafin ta buɗe bakin ta zata amsa,samha tayi sauri tace '' yo ka tambayi matar ka? Isn't it obvious she will take ur side? Ka tambaye Ni Ko Dr!'' ta ƙarashe maganar da murmushin gefen baki tana jingina da kujerar.

Har yanzu yana kallon Salma waiting to hear her response. He was a top chef and idan tace abincin yayi daɗi then it's fine idan kuma tace akasin hakan,zai sake komawa kitchen ya dafa wani till she is satisfied
'' abincin yayi daɗi sosai'' Salma ta faɗa tana kallon sa kafin ta juyo suka haɗa ido da samha, kashe mata ido guda samha tayi kafin tace'' ai dole ki faɗi haka,amma a tambayi Dr Ahmad'' Dr Ahmad jin an kira sunan sa ya ɗan yi tsuru,he didn't know which side to take, idan za'abi gaskiya abinci yayi daɗi,amma if he supports Amreesh? Ya tabbata samha will eat him raw... Kowa anyi shiru ana jiran abinda Dr zai faɗa,yaɗan sosa ƙeyar sa , smiling nervously yace'' uhm... abincin be ji magi ba'' jin hakan yasa samha sakin faffaɗan murmushi me kyau tana kallon Amreesh. Ba wai ta tsane da bane, but kamar yanda ta kushe girkin Dr Ahmad,ai bazata yabi nasa ba. And the look on his face was satisfying. Kallon Ahmad yayi,da sauri dr Ahmad ya jefa masa apologetic look da ɗan riƙe kunnuwansa Alamar ban haƙuri.
Kauda kansa yayi and his eyes fell on salmah, data ɓata fuska tana kallon samha dake ƙara zuba abinci cikin plate ɗin ta,'' toh idan abincin beyi daɗi ba meyasa kuke ci? '' ta tambaya tana faman harararsu
Dariya samha tayi tace ''so protective, relax,yunwa,ai batassn sabo ba ko?" Samha ta ƙarashe maganar tana kai lomar abinci baki
Shima Dr Ahmad ya ƙara shaƙe plate ɗin da abinci ya na ci. Sai da samha ta gama cin abincin tayi nak sannan ta fara bada points akan dalilin da yasa tace abincin bai yi daɗi ba, shima Dr Ahmad tace ya faɗi nasa dalilan,he copied almost everything she said... Ita ma salmah ta fara bada nata hujjoji,tana ƙare Amreesh soon dining ya dawo debating flat foam kowa na tofa albarkacin bakinsa banda Amreesh da yayi shiru
He was observing everything,wani irin yanayi ya shiga,? He was happy yes, that must be it. Yana farin ciki, he is starting to have feelings. Duk da farin cikin da yake ji is faint, Amma still he is happy,he felt an emotion for the first time in 25 years. Dalili? Well saboda waɗannan mutanen dake tare dashi a yanzu, and for the first he felt he has a family, his own. Cuz su duka ukunan they are what turned his house into a home, rayuwar sa dake cikin kaɗaici into something amazing. And his eyes fell on Salmah, yanda take depending ɗinsa, yaji wani abu me girma game da ita acikin zuciyar sa.
'' kuma Abu mai mahimmanci, mijina shi yadafa abincin so it has yi be delicious!'' ta faɗa tana riƙe hannunsa and at the same time looking into his eyes with a smile on her face, wannan simple gesture ɗin ya ƙara narkar da zuciyar Amreesh. Shima ita yake kallo intently,kalan idon sa na canjawa to a golden one.
Dr Ahmad ne ya fara clapping da ƙarfi sannan yace '' weldone Mrs. A Zakee, gaskiya bamuda abin faɗa yanzu,Ni dai nayi surrender,cuz I'm speechless".
Murmushi sosai Salmah tayi tana jin farin ciki,ta gane cewa Amreesh ma yayi farin ciki saboda kalan idon sa sun canja
Da ƙyar samha ita ma ta yarda tace abincin yayi daɗi

Bayan an gama cin abincin an gyara ko ina, parlor suka koma, suddenly Dr Ahmad yayi switching ɗin TVn to PS, Salmah da samha sunyi mamakin ganin PS ɗin, they hadn't notice it before, dama kuma sun iya ps games, kafin abinda ya faru da family ɗin su ,they had one. Bayan ya dai dai ta komai ya kawo pad ɗin,it's a team game, hakan yasa boys vs girls team

The game begun,sai gashi an ci girls team kusan sau biyu, gyara zama sukayi and soon enough anci boys team 4:2
Suna ta murna
Another round begun and this time,gabaki ɗaya boys team basu ci komai ba saboda Amreesh gabaki ɗaya hankalinsa na akan Salmah he wasn't paying attention
Dr Ahmad yayi faɗa har ya gaji but still... switching ɗin team mates sukayi samha da Amreesh, Salmah da Ahmad,aka cigaba da fafatawa, samha kaɗai keyin komai Amreesh dai har yanzu hankalinsa na kan Salmah, idan ya danna pad ɗin,se dai ma ya taimaka a cinye su...samha was frustrated,
Haɗa ido Salmah tayi da Amreesh,nan take yace ayi switching ɗin team again,aiko Dr Ahmad ya tuntsire da dariya yace'' ai se ka faɗa mana abaka matar ka,ba wai kasa mutane suna faɗuwa ball tsuke fuska Amreesh yayi
Slowly Salmah ta miƙe ta zauna kusa da shi samha kuma ta koma kusa da Dr Ahmad ''its You and me my lady'' Dr Ahmad ya faɗa lokacin da samha ta zauna kusa dashi. Rolling ɗin idanun ta tayi tana ƙunƙuni

Another round of the game begun,an daɗe kafin salmah tayi ma team ɗin su samha 1 :0 and she did it alone saboda Amreesh bai ma iya game ɗin ba and he still wasn't concentrating
Harara samha ta Banka ma Ahmad,da sauri ya gyara se gashi sun zo 1:3 suka ci-gaba da fafatawa, idan Amreesh yaga za'a ci team ɗin su sai yayi restarting ɗin game ɗin kuma ya tsuke fuska ba damar complain.
Haka suka cigaba da game ɗin har lokacin Asr, suka tashi 4:6 team ɗin su samha won.

Bayan an dawo daga Sallah they continued har dare yayi,sai wuraren ƙarfe tara sannan they called it a night
Gabaki ɗaya ranar suna cikin farin ciki
Samha ta shiga ɗakin su directly gado ta haye ba jimawa Bacci yayi gaba da ita.
Dr Ahmad sai da ya fara yin wanka sannan ya hau gadon shima nan take Bacci yayi gaba dashi.
Tare suka shigo ɗakin, Amreesh ya wuce bayi ita ko Salmah ta cire hijabin da ke jikin ta kafin ta haye gado ta kwanta, tana kallon ceiling murmushi kwance a fuskar ta,

9 / 69