Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 69

30K to 33K   out of 206.1K words

sawa da cosmetics, har sukayi suka gama Samha da Ahmad didn't exchange a word counter suka nufa aka biya kuɗin komai and the goods will be delivered to their residence.

Bayan sun fito daga mall ɗin, wani haɗaɗɗen restaurant Ahmad ya kai su and they each ordered different dishes from different countries,samha tayi ordering ɗin Korean food Salmah Chinese food, Amreesh da Ahmad Arab akayi serving ɗin kowa abinda yake so.Idanun mutane yawanci na akan su, '' wow Zee baby kalli wasu hot guys a can'' wata yarinya da bazata wuce shekaru 18 ba ta faɗa, sauran dake zaune a table ɗin suka juya suna kallon su Amreesh banda wacce aka kira da zee' jin yanda yan uwanta ke yaba kyansu yasa ita ma ta ɗago, ba
Tana da matsakaicin kyau sannan fara kanta yasha multicolored attachment hannayen ta zaƙo zaƙo da artificial nails kayan dake jikin ta did nothing much in covering her body. Gabaki ɗaya surar jikin ta a waje take, sauran sun cigaba da yaba kyan Ahmad da Amreesh,they almost couldn't differentiate wata fi kyau a tsakani, zee' ta sauke idon ta akan Ahmad take taji ta kamu da soyayyar sa kasancewar tana son namiji chocolate color, gabaki ɗaya ji tayi tarasa nutsuwar ta and she just wants to talk to him.

Miƙewa tayi,her friends suna tambayar ta ina zata tace '' i have found my prince charming '' kallon juna sukayi kafin su maida kallon su kanta she was already gone
Tafiya take tana yauƙi tana juya jiki kasancewar Allah ya bata surah me kyau. Some of the men seated there couldn't help but look

Tana ƙarasowa table ɗin su Amreesh directly ta zauna saman cinyar Ahmad tana wani manna ƙirjin ta anasa.
He was stunned, Amreesh pretended kamar besan abinda ke faruwa ba. Salmah was shocked to her bone marrow Samha Kam ƙwa rewa tayi da sauri ta ɗauki ruwa ta kafa kai tana sha, she didn't want anyone to see her tears

Da sauri ƙawayen Zee' suka fara sowa to them what she did abin burgewa ne,suna yi mata kirari suna ƙara fasa mata kai! Ita ko kanta sai ƙara ƙato yake. Salmah ta juyo instinctively ta kalli Samha da tacigaba da cin abincin ta kamar ba komai.
''hi handsome,sunana zeenah,but You can call me Zee in short.!'' ta ƙarashe maganar tana sakin murmushi tare da kai hannunta zata shafa fuskar sa, atunanin ta tayi Nasara ganin yanda ya kasa motsi gabaki ɗaya. Da sauri ya riƙe hannun ta sannan ya ture ta daga jikin sa, ya miƙe tsaye yana huci yace '' how dare You? Baki da Hankali ne huhu? What gave you the guts to sit on me... '' faɗa Dr Ahmad k surfawa sosai. Zee was dumbfounded ganin yanda yake ta masifa and all eyes were on them. No body made a move to help her up not even her friends
Satar kallon sa samha tayi,bata taɓa ganin yayi fushi ba and the sight right now isn't so good but still,haushin sa take ji,ga wani ɗaci da take ji a maƙoshin ta . It just isn't getting away.
And she soon realized Ashe kishi take ji. Bayan ya gama surfafa masifa tsallake ta yayi ya fita daga restaurant ɗin ta bisa da kallo duk da abubuwan da yayi mata da cin zarafin ta da yayi she didn't think it was possible for her to give up,it only made her want him more.
Amreesh ya miƙe offering his hand to Salma,karɓa tayi and he pulled her up,ita ma ta riƙe hannun Samha and they left Bayan payment.

Wasu hawayen baƙin ciki suka fara bin kunci Zee da sauri ƙawayen ta suka ƙaraso,suka miƙar da ita suna bata baki, and they assured her Ahmad will be hers, after all she is beautiful and has all the qualities Dan haka kada ta damu.

Shiga motar yayi ya zauna, he's chest heaving up and down can kuma ya ja tsaki yarinyar ta ɓata masa rai ba kaɗan ba.
Yana nan zaune su Samha suka ƙaraso, everybody got sitted before he drove off.
Ransa ya matuƙar ɓaci, lokaci lokaci Samha ke satar kallon sa but he didn't even look at her
Ganin atmosphere ɗin cikin motar rankowa ba daɗi yasa Salmah ta kalli Amreesh,shima kallon ta yake murya ƙasa tace''let's go somewhere else,kada mu koma gida pls'' ta ƙarashe maganar tana turo baki she looked cute jinjina kansa Amreesh yayi kafin slowly yace '' take us to amusement Park '' ba musu Dr Ahmad ya dauki hanyar Park few minutes later sun ƙaraso. Sauka sukayi,they paid for the ticket before they were let in.
Sosai Samha ta ɗanji daɗi ganin inda suka zo itama Salmah haka, wayoyinsu suka ɗauka, Salmah taja hannun Samha suka shiga suka fara wasa, suka hau ferris wheel,a loopty loop🎡
Sannan suka haw lilo cike da farin ciki suke wasa kafin su fara clicking ɗin pictures, Amreesh da Ahmad suka samu wuri suka zauna suna kallo kawai neither of them said anything
Can sai ga Salmah ta rugo taja hannun Amreesh excitedly,Binta yayi and they continued playing together duk da fuskar sa a ɗaure take,they snapped pictures kafin salmah tasa yaje ya jawo Dr Ahmad ganin an Barsa shi kaɗai, da farko ya ki amma daga baya he joined and it was fun
Ko ina hotuna suke ɗauka ba ƙaƙƙauta wa, se wurin maghrib suka koma gida, yanzu kam Amreesh na gaba Samha baya
,ita da Salmah talking about how much fun they had. Bayan sun dawo gida sunyi sallolin su no body asked for food Dan duk sun gaji kawai everybody retired to their beds. Abubuwan da suka siya had been delivered kowa yaja nasa.
The days that followed suna cike da farin ciki, kullum sai sun fita yawon shakatawa,kuma har yanzu Samha taƙi yima da Dr magana har yanzu haushin sa take ji,shi kuma be never missed an opportunity to assert his love Ako da yaushe yana ƙoƙarin nuna mata soyayya batare da crossing ɗin limits ba. Duk wannan abin Salmah da Amreesh sun yi noticing they just didn't say anything.

SUNDAY****
Tsaye take by the window tana kallon waje,she was wearing a black hoodie and a black trouaer,yanda iska ke kaɗa bishiyoyin nan and they sway side by side, ga wani irin sanyi da ake bankawa, ko ina looks quiet and desolated, ita ma haka take ji,her Black cloth reflects her mood, she was stuck in a whirlwind of romance! She felt lonely she felt miserable and uncertain. Zuciyar ta na mata wani irin nauyi, ga kaɗaici da kewa,kewar Ahmad take sosai duk da bata son ta yarda da hakan,few days ɗin da suka wuce batare da ta masa magana ba,felt
like a punishment not just to him, but to her self.
Turo ƙofar akayi,it was Salmah,tana sanye da wata doguwar rigar material da pink hijab, ƙarasowa tayi ya jawo akwatin Samha ta fara shirya mata kayan ta ciki, tana faɗa ma samha how much she will Miss her,jin bata ce komai ba yasa Salmah dakatawa da shirya kayan ''Sam'' she called out gently, juyawa Samha tayi, alamar tazo salma tayi mata, zuwa tayi ta zauna kusa da ita. Riƙe hannun ta salmah tayi Sannan tace ''faɗamin, me yake faruwa tsakanin ki da Ya Ahmad '' shiru Samha tayi for a while kafin ta sauke ajiyar zuciya Tare Da faɗin ''yace yana sona and I told him to focus on his life's
"Why'' Salmah ta faɗa tana ɗago kan Samha
Miƙewa Samha tayi ta koma bakin taga trying so hard to swallow her cry tace '' yafi ƙarfi na'' in a whisper '' his family might not accept me, and then our relationship has no future!"ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da ya ziraro mata. Kallon ta salmah take kafin tace '' meyasa kike ganin hakan, "?
"Saboda ba muda dangi!!'' Samha ta faɗa
Tasowa Salmah tayi ta tsaya kusa da Samha ''rashin dangi baya nufin ba muda asali samha, kuma sannan sun ƙi mu,to zamu dinga cusa kan mune? They clearly said they want nothing to do with us ya xamuyi? This is not an excuse to reject him Sam, I'm sure ya Ahmad mutumin kirki ne kuma ze riƙe da amana"!!
Salmah ta ƙarashe maganar tana juyo da Samha sannan ta cigaba da faɗin ''tell me,ke bakya son sa?" Kamar jira take aiko Samha ta faɗa jikin Salmah ta fara kuka ''ina son sa, I'm just afraid in the end I will lose him, Ina matuƙar jin tsoro Mah Mah. And I don't know what to do I'm confused '' ta ƙarashe maganar tana ƙara ƙarfin kukan ta.
Salmah ta tausaya ma Samha she patted her back slowly her Saida ta rage kukan sannan ta jawo ta suka zauna bakin gado ta fara share mata hawayen tana faɗin '' i understand how u feel, nima wasu lokutan ina jin tsoron wata rana I will lose REESH, Amma kuma sai nake yin addu'a akan hakan nake kuma tunasar da kaina cewa,the fear is in me,ba lallai bane hakan ya kasance, sannan the more You think about the future the more anxious you become, don't think about the future or the what ifs and buts Samha,komai lokacine and enjoy the present while u can and leave the future to Alhayyul Qayyum, and kowane love story nada nasa ups and downs, take this as yours and face it with courage. Bana so in matsa maki,but I think u should give him the chance he seeks.'' ta gama maganar tana cupping ɗin fuskar samha, jinjina kanta samha tayi tana faɗin ''na gode'' sosai taji daɗin kalaman Salmah and she will heed her advice.













WAYE SHI?(Behind the mask) By autumn 17

Chapter fourteen: you have fallen in love
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?
(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝐹𝑜𝑢𝑟𝑡𝑒𝑒𝑛: 𝑌𝑜𝑢 ℎ𝑎𝑣𝑒 𝑓𝑎𝑙𝑙𝑒𝑛 𝑖𝑛𝑙𝑜𝑣𝑒.

Toilet Samha tashiga ta wanke fuskar ta, ta zo ta taya Salmah arranging ɗin kayan da zata tafi dasu makarantar
''Dan Allah Samha ki kula, banda rashin ji kinji? I wouldn't want anything to happen to you! '' Salmah ta faɗa tana riƙe hannun Samha '' zan kula'' Samha ta faɗa with a mischievous smile
''shi kuma wannan murmushin na mene?'' inji Salmah tana ɗage gira guda,rufe bakinta Samha tayi ta miƙe daga saman gadon tayi ɗan nesa da Salmah sannan tace'' nasan mijin ki yaga nawar in tafi, cuz he obviously feels kamar ina hanashi rawar gaban hantsi humph!! He looks innocent Amma....'' Salmah da tun tuni ta saki baki da ido tana jin abinda Samha ke faɗa tayi tsalle ta dire gaban Samha, ai da gudu Samha ta kwasa tana dariya '' ba zaki tsaya ba?'' inji Salmah as they run around the room, se zagaye ɗakin suke suna dariya
''daga magana se ki ɗau zafi? I'm only stating the truth '' samha ta faɗa tana panting bayan sun tsaya su huta, a matuƙar ba zata Salmah ta cafko ta suka faɗa saman gado suna faman dariya. They looked so happy kamar ba abinda ya dame su a duniya, bayan sun tsagaita suka juyo suna facing ɗin juna,gashin da ya rufe fuskar ta salmah tayi brushing tace'' zanyi kewarki sosai Samha, if I could I would have followed you!" Ɗan taɓe baki Samha tayi sannan tace ''yo ke mai miji,ina daɗin miji zai bari ki bini? Stop pretending girl'' yar karamar duka Salmah ta kai mata tace '' so U have grown up ko? We will get u married"
Da sauri Samha ta tashe zaune ta daga hannayen ta biyu kamar wadda za'ayi arresting tace '' Ah! I'm innocent ooo'' ''silly girl '' Salmah ta faɗa tana ruffling ɗin gashin Samha with a serious face Samha ta riƙo hannun Salmah cikin nata tace '' Mahmah kema ya kamata kiyi ƙoƙari ki kai relationship ɗin ki to the next level, yanda gayen nan yake manne dake,all the times his eyes are on you,baya ganin kowa sai ke,i think he has fallen for you! " Dum Salmah taji gaban ta ya faɗi,he had no feelings,Taya zai so ta? Tasan dacewa koda yaushe idanun sa na kanta amma could that really be considered love? Ita tasan dacewa walau ta yarda ko karta yarda tana son shi and she will do what is necessary to make sure her love is reciprocated! '' kina jina?" Samha ta ɗan jijjiga ta ganin ta lula duniyar tunani, firgit ta dawo,sai kuma ta saki murmushin daya sa dimples ɗinta lotsawa wa,cike da farin ciki ta rungume Samha '' thanks Sam, kuma insha Allah zan yi hakan, and u should also give chance to Ya Ahmad uhm?" Jin jina kanta samha tayi bayan sun rabu,she has already made up her mind

***********

Tun ranar da incident ɗin nan ya faru, Dr Ahmad yashi ga damuwa. He didn't have the chance to properly talk things out with Samha, he's really afraid zatayi misunderstanding ɗinsa.
Zaune suke parlor shida Amreesh, tunda Salmah ta tafi ɗakin Samha Amreesh yake ta Safa da marwa.
Ɗago kansa Dr Ahmad yayi, ganin yanda Amreesh ya wani tsuke fuska abun ya bashi dariya aiko yashiga tuntsire wa
'' oh su zakee masu mata, bankwana fa take da yar Uwar ta shine kawani bi ka damu,hey safa da marwa kake, i really want to see what happens when u have kids, kishin ka is on another level!'' banza dashi Amreesh yayi amma kalma ɗaya da Ahmad ya faɗa yana ta masa yawo akai 'is he really jealous? Does that mean he has feelings?'
Da sauri yazo ya zauna kusa da Dr Ahmad dake kallon sa yace
"You said I'm jealous? Hakan na nufin yanzu nima ina da feelings kamar kowa?" Amreesh ya faɗa looking at Ahmad hopefully, gyara zama Ahmad yayi sannan ya riƙa hannun Amreesh '' can you feel my touch?" Ahmad ya faɗa intently looking at Amreesh Wanda shima kallon sa yake. Bayan kusan minti ɗaya Amreesh ya girgiza kansa '' I can't '' ya faɗa yana haɗe girar sama da ƙasa he was confused, gane hakan yasa Ahmad tambayar sa meya faru
Kamar zai share sai kuma yace '' I sometimes feel her touch,Ina son kasance wa tare da ita '' Ahmad dai kallon Amreesh yake sai kuma yace '' bro you have fallen in love,na faɗi hakan bcuz it's only her whose touch you can feel,and u have such strong emotions towards her'' ya ƙarashe maganar yana matso wa kusa da niyar rungume Amreesh,zaram Amreesh ya miƙe tare da hararar sa, ɗan sosa ƙeyar sa Ahmad yayi '' sorry my bad '' Bai saurare sa ba ya miƙe ya cigaba da Safa da marwar sa, completely yana share abinda Ahmad ya faɗa bai yarda ba.

At exactly 4:30pm, Dr Ahmad ne sanye da wando jeans da riga baƙa polo da wani tsadadden wrist watch a hannun sa, sai zuba ƙamshi yake, tsaye yake kusa da baƙar motar sa Black SUV, ya riga da yagama shirya kayan Samha ciki ita yake jira, daga lokaci zuwa lokaci yake duba agogon sa ganin lokaci na tafiya.

Ɗago kansa ya ƙara yi looking at the entrance for the hundredth time, Salmah ce tafara fitowa, saye take da abaya baƙa, ta yafa gyalen she looked so breath taking idanun ta sunyi jaa alamar tasha kuka sai Amreesh biye da ita, he was dressed in a loosed gray cardigan sai ƙamshi yake, idanun sa ƙyam akan Salmah. Abinda Ahmad ya faɗa na masa yawo a kwanya and he seems to be feeling something new, something he had never felt, Samha ce ta fito last
Dressed in a blue jeans da ya kamata se farar riga mai guntun hannu an rubu ta 'for ever yours'' da glitter purple color tasa Black after dress a sama ta yafa mayafin kamar yanda Salmah tayi, ƙafafun ta sanye da Black colored sandals she looked dashing. Ga wani sassanyan ƙamshi da take turaren Ahmad ne da ta ɗauka ranar wato 'heat'
Kallo guda Dr Ahmad yayi mata ya ɗauke kai, zuciyar sa na bugawa. He didn't like the way she dressed he felt jealous.

Salmah ta ɗan ƙarayin gaba, hakan yasa Samha caught up with Amreesh,hannun rigarsa ta riƙo kallon ta yayi waiting to hear what she will say, sai da ta harare sa Sannan tace'' ga Mahmah nan na bar maka amana,if you bully her kaji rani zan zo in ɗaukar mata fansa, nasan bakasan da cewa mun iya 🥋 taekwondo ba ko? Toh ina tabbatar maka Ni da ita duk mun iya, dan haka ribiti za mu yi maka, wallahi sai mun canja ma kamanni, dan haka Ni kunne yaji,jiki ya tsira'' ta ƙarashe maganar tana jan kunnen ta tare da yin gaba ta barshi tsaye. Her words amused him.
Koda ta isa wurin motar Ahmad da Salmah magana suke, tsaya wa tayi daga gefe har suka gama
Kafin salmah ta juyo ta ƙara riƙe hannun Samha cikin nata, idanun ta na tsiyaya, da sauri Samha ta goge mata,tana girgiza kanta Alamar ta dena kuka, shi dai Dr har ya shige ya zauna Amreesh kuma ya ɗan tsaya not so close to them. Yaga nawar wannan brat ɗin ta tafi, '' I'm already missing you Samha Dan Allah ki kula da kanku!" Salmah ta faɗa tana ƙara rungume Samha
Jin jina kanta samha tayi,she can't promise anything, itama kanta kewar su take ji kawai tana daure wa ne.... hawaye ya cika mata idanu da sauri ta haɗiye hawayen ta raba jikin ta dana Salmah tace '' ki dena kuka Mahmah,ai zan dawo ko?" Jinjina kanta Salmah tayi tare da share hawayen, sannan ta buɗe ƙofar motar ma Samha tana mata bye. Shiga Samha tayi ta rufe ƙofar da murmushin ƙarfin hali. Haka suka cigaba da yima juna bye bye har motar ta fita daga compound ɗin. Fashewa da kuka Salmah tayi dama ita ba tada ƙarfin zuciya kamar Samha, da sauri Amreesh ya ƙaraso ya rungume ta patting her back kafin ya ɗauke ta suka shiga ciki, the house looked empty. Ajiye ta yayi sannan ya tafi kitchen ya ɗebo ruwa a cup ya zo ya durƙasa gaban ta ya miƙa mata karɓa tayi ta sha duka ta ajiye cup ɗin beside her, hannayen sa akan cinyar ta, ya kai hannunsa ya na goge mata hawaye, he

11 / 69