Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 69

117K to 120K   out of 206.1K words

san menene yayi drawing ɗin attention ɗin sa gare ta ba,but she effortlessly seduced him, maybe saboda yanda take ɗaukan kanta ne? Or her sexy aura? Ko appearance ɗinta ne he wasn't sure.
Ta wutsiyar idon ta samha ta hango shi yana tunkaro ta amma sai ta yi kamar bata ganshi ba,he holds no importance.
Tsayawa yayi daidai ita yana kallon smooth chocolate complexion ɗinta,lashe baki yayi ya miƙa hannun sa da niyar rungumeta yana faɗin '' sorry for your loss '' swiftly Samha ta kwashe albasar da ta yanka, ta matsa gefen da girkin ta yake avoiding his hug, kallon hannun shi dake sage a iska yayi kafin ya kalleta,wani irin irritation yaji yana taso masa amma sai ya danne.

Samha ta cigaba da aikin gaban ta kamar ba kowa wurin ita kaɗai ce,wani attempt yake ƙoƙarin yi ya jiyo footsteps a stairs hakan yasa stylishly ya fita daga kitchen ɗin kafin Mahma ta ƙaraso

Ganin Xiao ya fito daga kitchen yasa Mahma yi masa wani dogon kallo kafin ta shiga kitchen ɗin '' what was he doing here?" Mahma ta faɗa tana rungume hannayen ta a ƙirjin ta, kusan bayan minti ɗaya Samha tace slowly '' wa kenan?" Wuri Mahma ta samu ta zauna tace '' wancan wanda ya fita '' buɗe tukunyar abincin Samha tayi ta zuba albasar sannan tace '' i didn't notice '' daga haka bata sake cewa komai ba,itama Mahma sai tayi shiru kawai. Few minutes later Samha ta zubo musu acikin plate ɗaya ta kawo dining suka zauna su biyu suna ci, unlike da,there used to be four of them...the house looks and feels empty now. Bayan sun kammala cin abincin su Mahma tayi wanke wanke sannan suka dawo parlor suka zauna kusa da juna suna kallo


Da daddare Mahma tayi insisting sai sun jira Aliyu ya dawo kafin su kwanta duk da Samha bata so ba haka ta zauna tare da ita suna jiran shigowar Aliyu,har tara tayi ta wuce,goma tayi ta wuce har wurin ƙarfe ɗaya shiru ba Aliyu ba labarin sa

Jan Mahmah Samha tayi suka wuce ɗakin su, daga nan kuma abin ya zama routine, kullum sai sun jira Aliyu but he never came

Tun suna da ran zai canja har sun haƙura,yanzu kaɗaicin yafi nada,and they only had each other. Komai tare suke wanda yaƙa ƙarama alaƙar su ƙarfi.

Shi kuma Aliyu yana ƙin zuwa gida ne saboda aduk sanda ya dawo gida memories ɗinsu na hunting ɗin sa, he was broken,he was in deep despair....

Xiao daya fahimci hakan sai yayi nufin sheƙe ayar sa, da farko ya fara zuwa ma Samha da lallami amma ganin yarinyar zata bashi wahala he resorted to violence. Kullum idan yazo sai ya daki Samha irin duka mai illatarwa sannan zai bar gidan cike da haushi da baƙin ciki, Samha bata ramawa bata kuma magana,duk abinda zai yi sai dai yayi amma bai taɓa cimma burin sa ba.
Idan ya ji mata ciwo sai dai ta shige bayi tayi treating ɗin kanta in a way Babu wanda zai yi noticing .

Duk wannan abin da yake faruwa Mahma da Aliyu basu sani ba,don ita Mama tana shirye shiryen Junior WAEC ne At thirteen,hakan yasa ko an tashi sai ta zauna makaranta for extra lesson,da taso ta ƙi amma Samha tasa ta zauna'' i can take care of my self '' Samha take yawan faɗa ma Mahma
Babu yanda ta iya sai dai ta dinga zama lesson ɗin through out her mind wandering to Samha.

Aliyu kuma he never cared Bai da lokaci it made them wondered shi bazai karɓi ƙaddara ba? Idan matar sa ce shi ai suma Uwar su ce,meyasa su suka iya karɓar ƙaddara Banda shi? Shi ba Musulmi bane? Me yasa yake denying ɗinsu fatherly love? Ba uwa ba uba,da wane zasu ji?

Tsaye Samha take bakin window tana kallon garin with a distanced look tunda ta dawo ake ta tsuga ruwa da sanyi amma ita ko sanyin bata ji,saye take da wata riga polo sai wando iya ka guiwa,ta yanke gashin ta kamar yanda ta ƙudurta hannayenta naɗe a ƙirjin ta tana ci-gaba da kallon yanda ruwan ke zubowa it made her wonder ko ya Mahmah zata coping?

Turo ƙofar yayi ya shigo,it was Cheng xiao fuskar shi ba annuri ko kaɗan daga gani muguntar yau sai tafi ta kullum. Dumm! Ƙirjin Samha ya buga,inda take ya iso ya sa hannu ya finciko ta yana faɗin '' yau daga ni saike kuma yau sai nayi abinda naga dama'' ƙwace hannun ta Samha tayi tana matsawa baya, kallon ta yake daga sama har ƙasa yana lashe baki,it made Samha want to puke 🤮!!

Gani tayi yayi ƙasa da wandon shi and kafin ta kauda kanta she has seen it, a grown man's private part,wani irin bugu zuciyar Samha ta fara irin na tsoro,tsoron da bata taɓa jin irin sa ba. Kauda kanta tayi tana faɗin ' hasbiyAllah' dariyar shaƙiyanci xiao yayi ya jawo gashin ta yana dunguna kanta a wurin wai tasa baki, Samha felt assaulted,her survival instincts kicked in,yana kokawar kai bakin ta sai tin wurin a matuƙar bazata yaji saukar wani irin kick daya sa shi yin tangal tangal kamar zai faɗi,dafe wurin yayi yana faɗin 'shiiiiit!!!' Saboda yanda zafin ya ratsa har cikin kwakwalwar shi, fuskar shi tayi ja,

Samha ta koma gefe ta tsaya zuciyar ta na cigaba da halbawa, tunkaro ta ya ƙarayi ya kwashe ta da wasu wawayen maruka guda biyu da yasa ta faɗi goshinta ya daki bed side table sai ga jini.

'' Ashhh '' Samha ta faɗa jin wani irin ciwo har cikin ƙasusuwanta, bata gama warke wa ba ya ƙara tunkaro ta yayi ball da ita ya sa ƙafar sa ya taka marar ta. For a heart beat she didn't move,jin wani sharp pain daya sa taji gaba ɗaya ta dena jin jikin ta,

Shi ko xiao sai huci yake,yau da gaske yake he has to fulfill his urge. Har ya yo kanta yaji anyi Horn abakin gate daburce wa yayi,yayi hanyar fita yana gyara wandon sa zuciyar sa na bugawa da ƙarfi,if he gets caught....

Samha ta daɗe kwance wurin ko ina na jikin ta na mata wani irin ciwo, after a while ta miƙe ta nufi toilet kamar yanda ta saba tayi treating ɗin ciwukan da taji, bayan ta gama ta kalli kanta ta mirror toilet ɗin,wai yau ita Samha taga na miji tsirara? And she was almost defiled! Baban ta bai sani ba no body knew,how? Dama haka maraici yake idan mutum bai da uwa? Cuz ta tabbata da Salamatu na raye No such thing will happen!
Idon ta ya kai saman pendant ɗinta and she couldn't help but whisper '' I missed you Mom '' ajiyar zuciya ta sauke ta fara takowa Ahankali har ta kusa fita daga toilet ɗin taji wani irin amai na taso mata,bayan ta tuna abinda ta gani,koma wa tayi da sauri tayi ta kwarara amai,bayan tagama ta kalli wurin ɗan waro ido tayi ganin jini jini

Wanke wurin tayi ta fita,gado ta nufa ta kwanta tanajin wani irin feverish, karkarwa jikin ta ya fara,jawo blanket tayi ta lulluɓe zuciyar ta na ƙuna,she felt miserable she felt abused,she felt sick and assaulted....

















WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17

Chapter fourty six:The void





Wurin ƙarfe biyar da rabi Samha ta buɗe idanun ta jin ana jan duvet ɗin da ta rufe jiki dashi, slowly ta ware foxy eyes ɗinta suka faɗa cikin na Mahma da fuskar ta ke ɗauke da damuwa,ɗan motsawa Samha tayi da niyar tashi zaune amma taji ta kasa, Ko ina na jikin ta wani irin azababben ciwo yake mata,'' Moon baki da lafiya ne?" Mahma ta tambaya idanun ta na cikowa da hawaye,kafin ta rushe da kuka, weakly Samha tace '' lafiya ta lau,kai na ke ciwo da ciki na'' Ruɗewa Mahma tayi ta janye blanket ɗin daga jikin Samha at the same time idanun ta na sauka akan ciwon da taji a goshi, Samha didn't conceal it well,'' innalillahi Samha mai yasame ki?" Mahma ta faɗa tana ƙara jin tausayin Samha she felt so bad for her. '' faɗuwa Nayi '' inji Samha Muryar ta na mata wani irin ɗaci tuna abinda ya faru, zuciyar ta kamar ana hura wuta,so take tayi kuka amma ta kasa she just doesn't know how to cry '' kin tabbata faɗuwa kikayi?" Inji Mahma suspiciously cuz it didn't seem like it, tsuke fuska Samha tayi tace'' I'm unwell Mahma ki dena sani ina magana and ki Dena kuka it sucks!!!'' Goge hawayen ta Mahma ta shiga yi duk da sun ƙi tsayawa tana kallon fuskar Samha that looked pale,daga ganin ta mutum yasan bata da lafiya '' kije ki canja kaya, You stink ''yar ƙaramar dariya Mahma tayi despite the seriousness of the situation tace '' wallahi ba wari nake ba,ƙamshin turare ma nake shinshina kiji '' Samha ta kauda kanta gefe, miƙewa Mahma tayi ta fita daga ɗakin,ɗakin Aliyu ta nufa ta tura ƙofar ta shiga babu kowa except ɗakin was neat,for the first time in three years wannan ne karon farko da ta shiga ɗakin bayan rasuwar Salamatu, hawaye na sulala daga idon ta tanufi wurin da ake ajiye kuɗi, ɗauka tayi ta fito daga ɗakin ta fita daga gidan gaba ɗaya.

Har yanzu ana ɗan yayyafi, tafiya take da sauri sauri kafin ta fara gudu, zuciyar ta a ƙuntace,Tayi nisa wata mota ta sharo da gudu ta fallatsa mata ruwan jar laka, tsayawa Mahma tayi tana kallon kanta daga sama har ƙasa '' Damn!!!'' ta faɗa ta ɗauki wani dutse ta jefe motar dashi the glass shattered

Motar tsayawa tayi kafin wani ɗan iskan guy ya fito daga ganin shi kaga tantagar yar ɗan duniya, kwashe Mahma yayi da marin daya sa taga stars,kafin yasa ƙafa ya kwashe ta ta faɗi cikin ruwan laka, hakan bai ishe sa ba yasa ƙafa ya taka bayan ta,ƙarar azaba ta saki kafin ta juyo ta riƙe ƙafar throwing him off balance, faɗuwa yayi tim! Aƙasa bakin shi ya bugu saman kwalta, sai jini

Tana huci ta miƙe tayi kanshi ta fara taka bayan shi just like he did to her '' how dare you as*hole?" Tayi maganar tana kicking ɗin gefen cikin sa, sai ihu yake mutane suka taru ana kallo amma babu wanda
yayi attempting shiga ya raba.


Samu yayi ya riƙe ƙafar ta ya murɗe hakan yasa tayi losing balance ta faɗi,hawa saman ta yayi ya fara kai mata naushi a ciki, ihun azaba ta saki tana dafe wurin kafin ta tsole mashi ido da yatsanta and she gained the upper hand

Haka itada shi suka shiga dambe sukayi ma juna jina jina there were bruises all over their bodies kafin wani gentle man yazo cikin taron nan ya raba su, ya riƙe Mahma a gefe guda ɗayan mutumin kuma ɗaya kallon juna suke ido cikin ido kafin mutumin yace '' zakiyi nadama,mark my words'' Yayi maganar yana fincike hannun shi daga riƙon da mutumin da ya rabasu yayi masa,tsuki tayi tace '' You Are very stupid '' daga haka ta cire hannun ta Itama ta sheƙa da gudu, tunawa da tayi Samha na gida ita kaɗai and she was sick. Tana gudu tana share hawaye, she missed their old life

Chemist ta iso ta siya ma Samha magani bayan tayima mai chemist bayani, without proper diagnosis ya zari magani ya ba ta yayi mata bayanin yanda za'a sha,karɓa tayi ta bar wurin tana gudu with everything inside her saura kaɗan mota ta kwashe ta but she wasn't seeing,abinda take so kawai ta ganta kusa da ƙanwar ta.

Lokacin da ta shigo ɗakin su it was 6:39 not minding kayan ta da sukayi datti ta isa wurin Samha '' Samha tashi ga magani na siyo maki'' slowly Samha ta buɗe idon ta da muryar rashin lafiya tace '' ina kika samu kuɗi?" Mahma ta zaunar da ita ta miƙe taje ta ɗauko ruwa ta kawo mata da maganin kamar yanda akayi mata bayani ta bata,karɓa Samha tayi tasha tana kallon Mahma da tayi datti '' meya same ki?" Kallon kanta Mahma tayi, ita har tama manta '' faɗuwa nayi'' daga haka bata ƙara cewa komai ba, Samha tasan ƙarya ne but she didn't probe further sai ma kwantawa da tayi ta ƙara rufe jikin ta. Mahma ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka,inda mutumin nan yayi mata duka na wani irin masifaffen zafi, tsaki taja kafin ta kammala wankan taja towel ta fito daga bayin,gaban madubi ta zauna tayi shafe shafe tasa kaya every now and then idanun ta na kaiwa wurin Samha. Fita tayi ta shiga kitchen abinci mara nauyi ta dafa musu ta zuba cikin plate ɗaya ta dawo ɗakin ta tada Samha suka ci,ɗan kaɗan Samha taci tace ta ƙoshi, zata kwanta Mahma ta hana ta.

Da daddare Mahma sai kai kawo take tana jira ko Aliyu zai dawo amma bai dawo ba hakan yasa ta haƙura ta koma ɗakin su ta hau saman gadon Samha pulling her close ta rufa musu blanket sukayi cuddling juna,jikin Samha was burning with fever,itama Mahma zazzaɓi take ji amma haka ta daure....

For three consecutive days su biyun basu da lafiya amma na Samha yafi tsanani, kowane dare sai tayi ciwon ciki, abun kamar an saita sha biyun dare dot yake farawa baya tsagaitawa sai ƙarfe uku na dare, Mahma was the one taking care of her. In this life they only had each other,sun zama complete marayu despite the fact that suna da uba,suna tsananin ƙauna da tausayin juna..... kullum sai Mahma tayi fatan ko Aliyu zai zo but he never did,a rana ta huɗu ne bayan Mahma tayi bacci wurin ƙarfe goma Aliyu ya shigo, Samha na tsaye bakin window lokacin da ya shigo, a thought popped up in her mind hakan yasa ta jira sai wurin sha ɗaya kafin ta fita daga ɗakin su zuwa na Aliyu, tafiya take tana haki dan haryanzu bata gama warkewa ba,she looked slim and pale

Batareda ta ƙwanƙwasa ba ta tura ƙofar ta shiga,Aliyu na zaune bakin gado yana kallon hoton Salamatu a wayar sa yaji an buɗe ƙofar, kallo guda yayi ma Samha dake jingine da ƙofar ya ɗauke kai... Though he wondered why she was there

Samha ta ɗau kusan minti biyu tsaye a wurin tana tara abinda zata faɗi,shidai Aliyu yana jira yaji mai zata faɗa,'' Meya sa baka son mu? Especially me!!!" SAMHA tayi maganar weakly kafin ta sulale wurin ta zauna cuz bazata iya tsayuwa ba, cike da mamaki Aliyu ya ɗago yana kallon ta jin Abin da ta faɗa. Bai ce komai ba cuz he didn't even have the answer, Murmushin takaici Samha tayi that was not so visible tacigaba da faɗin '' I'm not expecting anything from you kuma bazan taɓa tsammatar komai daga gare ka ba,but remember kana da yaya,kuma Allah zai tambaye ka game da amanar da ya baka, don't we matter? Wasn't she also our mom? Bamu karɓi ƙaddara ba,then why can't you?.'' Aliyu was more than surprised jin abinda Samha ke faɗa, he never expected to hear it from her,Bai taɓa tsammanin zata iya magana haka ba. Kallon ta yake duk da ba haske yana iya hango bruises ɗin dake goshin ta,he could see how pale she looked was she sick?

Miƙewa Samha tayi da ƙyar tana faɗin '' There will come a day,you will beg to love me,love us Amma a wannan ranar i will reject you I will reject your love Mr Lee '' tayi maganar faintly kafin ta fita Aliyu yayi zaune a wurin kamar an ɗasa shi he couldn't move and she just called him Mr Lee

A hallway ɗin ta haɗu da Mahma,tun lokacin da Samha ta fita Itama ta biyo ta so she heard all she had said, ƙarasowa tayi ta rungume Samha patting her shoulders kafin the two sisters retired to their room


Rayuwa ta cigaba da tafiya,the two sisters grew closer while Aliyu remained a picture in their lives har mantawa ma suke suna da uba, A makaranta ma suna tare amma duk sanda Samha zata kasance ita kaɗai she always gets bullied, idan Mahma ta sani kuwa sai sun hau jirgin bala'i da koma wanene sun faɗo na masifa, she loves Samha so much she can't see her getting hurt.....

A gida kuma Chen Xiao ya dawo more cruel and violent than ever,duk abinda zai ma Samha she never reacts sai dai idan yayi ƙoƙarin forcing kanshi on her, he always rough handles her kuma daga ƙarshe ya fita da takaici da baƙin ciki, a cikin kwanakin nan Samha tayi noticing duk sanda zatayi tari, she always coughs blood, sharewa take kawai ita bata ɗauka wani abu bane,

Aduk sanda they had encounter with Xiao sai ya jima ta ciwo...

She felt empty from within, she has seeing him countless times ba kaya just tsirara,at the age of ten she has been through so much,fiye da yanda ya kamata ta gani , idan bacin da Allah yasa tana da wancan rashin lafiyar schizophrenia,da ƙila ta samu taɓin hankali ko ta zama depressed....

duk da bai taɓa samun Sa'a akan ta ba amma... what about the mental, physical and emotional abuse? Ya dake ta,yasa taga abinda bai kamata yara of her age sugani ba, yasa ta shiga emotional turmour doesn't that count?

In all this Ina baban su? Well he was still stuck in the past, tun lokacin da maman su ta rasu she never had any peace of mind,basu san mene ne soyayyar uba ba musamman ita...


The abuse went on for six years, lokacin da Samha tayi shekara sha uku Mahmah sha shida,it all ended wata rana Chen Xiao decided ya gaji kawai zai yi mai gabaɗaya ya huta.amma... dama,ina zai samu dama?

The opportunity came lokacin da akayi selecting ɗin Mahmah cikin wani inter State competition,ita Bama taso ta tafi amma Samha insisted akan sai ya tafi '' Are You sure you can manage? Zan iya zama asa wani on my behalf " Samha dake shirya ma mahmah kaya cikin akwati ta rufe akwatin tazo ta zauna kusa da ita ta riƙo

40 / 69