Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 69

72K to 75K   out of 206.1K words

kafin tayi ƙasa da idon ta,buɗe ƙofar tayi ta fito walking slowly ta nufi cikin gidan,sai kallon ko ina take everything has changed

Kafin ta ƙarasa ciki sai ga Salma ta fito hugging her excitedly,sai murna take, raba jikin su tayi tana kallon fuskar Samha dake ɗauke da fake smile tayi missing ɗin Salmah da gaske amma yanzu tana cikin damuwa ganin how coldly Dr Ahmad treated her. Yana ganin ke nan duk abinda ya faru laifin tane?

Salmah ta lura da yanayin Samha amma sai ta dauka Maybe ta gaji ne '' muje ki huta '' Salmah ta faɗa tare da riƙo hannun Samha suka shiga ciki, cire takalmin ta Samha tayi suka ƙarasa har ɗakin ta, koda suka shiga akwatin ta was there, fita Salmah tayi leaving her alone, ajiyar zuciya samha ta sauke sannan ta shiga bayi tayi wanka

After a while ta fito tana tsane gashin ta da yaƙara tsawo da cika, ɗan turo baki tayi tana ayyana zata rage gashin aranta, mai ta shafa tayi oiling ɗin gashin sannan ta buɗe wardrobe ta dauko wata rigar saƙa loose fitted ash color da wando palazo shima ash tasa, ta fesa turaren da ta ɗauko daga ɗakin dr Ahmad, murmushi tayi kafin ta ɗauko wani ɗan ƙaramin hijabi white tasa

Sallah ta fara yi kafin ta miƙe ta fito tana tafiya kamar wadda aka zarewa laka, karo suka ci da Dr Ahmad, ya ɗago ta daga jikin shi without looking at her kafin ya sauka ƙasa, tabi bayan shi da kallo wani abu na tsaya mata a wuya, har yayi wanka ya sauya kaya zuwa riga ja da jeans baƙi sai zuba ƙamshi yake. Ganin ya fita daga gidan gaba ɗaya Samha taji hawaye na shirin zubo mata, juyawa tayi da sauri ta koma ɗakin ta, ta tsaya bakin window ta ɗaga labule tana kallon Motar sa har ta fita daga gidan

Zama tayi bakin gado ta dafe kanta slowly tace '' ba laifi na bane, i didnt know'' hawaye na wanke mata fuska, zuciyar ta nayi mata wani irin nauyi

Tunawa da tayi Salmah zata'iya shigowa ta ganta yasa ta saurin share hawayen ta jawo akwatin ta tana ciro kayan tare da shirya su cikin wardrobe tana tsaka da shirya kayan wani abu ya faɗo, duƙa wa tayi ta ɗauka, agogon da ta siya ma Dr Ahmad ne,
Maida agogon tayi ta ajiye cikin kayan ta,ta ci-gaba da gyara wardrobe ɗin ta. Bayan ta gama ta koma ta kwanta ranta ƙuntace tana saƙe saƙe har bacci ya ɗauke ta.


09:00

Tun bayan da tayi Sallah take zaune wurin tana tunani, bayan taje ta dubo Samha taga tana Bacci ta dawo ɗakin ta ta kwanta bacci yayi gaba da ita, mafalkin da ta daɗe batayi ba shine tayi yau, kuma na yau ɗin yafi na koda yaushe munana, she felt so worried

Tana tsaka da tunani aka turo ƙofar tun kafin ya ƙaraso ciki ƙamshin turaren sa ya iso, ido suka haɗa bayan ya shigo ƙasa tayi da idon ta. Inda take yazo ya zauna yana kallon fuskar ta,ita ko sai wasa take da yatsun ta kafin tace '' Sannu da zuwa '' jin bai amsa ba yasa ta ɗago suka haɗa ido,ƙasa ta sake yi da kanta zuciyar ta na lugude,miƙewa yayi ya matsa gefe yana rage kayan jikin shi kafin ya shiga toilet

Ajiyar zuciya Salmah ta sauke ranta na mata wani iri. Bayan minti biyar ta miƙe ta nufi wardrobe ta ɗauko masa kaya ta aje kafin ta fita daga ɗakin



Ɗakin Samha ta nufa,samun ta tayi tana waya ƙarasowa tayi ciki ta zauna bayan Samha ta gama wayar tace '' ke dawa kike magana '' Samha na murmushi tace '' room mates ɗina, ashe Eysah na da waya amma bata taɓa nuna mana ba shine yau ta ɗauko ta kirani wai tayi missing ɗina'' murmushi Salmah tayi bayan taji abinda Samha ta faɗa, shiru yabiyo baya suna kallon juna Salmah tace '' Ni naga kin ƙara girma kin zama wata riɗeɗiya,how fa?" Dariya samha tayi tace '' Na ƙara girma ko na rame?" Salmah tace '' girma dai'' taɓe baki Samha tayi ta miƙe tana shafa cikin ta '' Acici '' Salmah ta faɗa kafin suka fito zuwa parlor


Amreesh was already there, ɗago kanshi yayi ya kalli Salmah for few seconds kafin ya maida kanshi ga Samha, ɗauke idon shi yayi ya maida ga abincin gaban shi

Salmah taji wani iri a zuciyar ta, Samha dai,ko a slippers ɗin ta, bayan sun zauna Samha tace '' ina yini'' '' Lafiya '' ya faɗa curtly yana cigaba da cin abincin shi, Salmah ta zauna kusa dashi tana kallon shi

He didn't even look at her, ita dai samha tuni ta zuba abinci ta fara ci, sosai abincin yayi mata daɗi.

Amreesh na gamawa ya miƙe ya nufi study room Salmah tabi bayan shi da kallo me kuma ya faru? Hawaye taji sun cika mata ido tayi ƙasa da kanta kafin taja cup ta zuba ruwa tasha badan tanajin ƙishirwa ba sai dan kada samha taga hawayen ta.

Samha ma dai ta tafi Tata duniyar tunani da sauri ta ƙarasa abincin ta, ta kwashe kwanukan zata wanke Salmah tace '' ki barshi zan wanke'' Samha bata saurare ta ba ta kwashe kwanukan tana faɗin '' tunda mijin ki ya bar wurin hankalin ki ya bishi, and I know you want to go to him tashi ki tafi kawai '' ta faɗi hakan tana idasa shige wa kitchen, Salmah ta daɗe zaune a wurin kafin ta miƙe walking slowly ta nufi ɗakin su,he wasn't there har zata tafi study room sai kuma ta fasa instead ta shiga toilet, bath tub tashiga bayan ta haɗa ruwan wanka ta sa duk turarukan wanka...

Haka kawai ta fara kuka ita ma batasan dalili ba,or maybe Amreesh treated her coldly? To Amma mai tayi da ta cancanci hakan? Bacci ne yayi gaba da ita a wurin

Bayan Samha ta gama wanke wanken ta fito ta kashe komai kafin ta nufi ɗakin ta, gado ta faɗa kafin ta jawo wayar ta tashi ga contact tayi scrolling har ta tsaya akan number Dr Ahmad ta daɗe tana kokonton ta kira shi ko a'a daga baya dai ta kira shi har yayi ringing ya katse bai ɗaga ba. Ƙara kira tayi nan ma bai ɗaga ba, ana ukun data kira sai taji switched off Nan tagane Ashe ƙin ɗauka yayi. Ajiye wayar tayi ta kwanta tare da jan duvet ɗin ta rufe har kanta. Tayi alƙawarin bazata sake kiran shi ba.

Ƙarfe ɗaya saura Amreesh ya shigo ɗakin,idon shi yakai kan gado bai ganta ba,ya ɗauka ko ta tafi ɗakin Samha,rufe ƙofar yayi ya nufi toilet,yana shiga ya hange ta a bath tub tana Bacci ɗan waro ido yayi,ƙarasawa yayi wurin ta ya tsoma hannun shi cikin ruwan har sunyi sanyi, cije leɓen shi yayi kafin ya miƙe tare da ɗaga ta ya ajiye ta ƙarƙashin shower ya kunna, yana bin ta da kallo tundaga fuskar ta zuwa ƙirjin ta idanun shi lingered on her chest,ba tare da yasa abinda yake ba ya kai hannunsa yana shafawa ɗayan hannun sa kuma riƙe da ƙugun ta, buɗe idanun ta tayi jin saukar ruwa, da farko ta ɗauka mafalki ne sai da taji ana taɓa ta idanun ta suka buɗe da kyau, ido suka haɗa da Amreesh da shima ya gama jiƙewa da ruwa,tsuke fuska tayi tare da ture shi, gallara masa harara tayi kafin ta ɗauki towel ta ɗaura ta fita daga bayin tana ƙunƙuni, Amreesh was stunned me yayi kuma? Kashe shower yayi ya cire kayan jikin shi, ya ɗaura purple towel ya fito daga bayen

Haryan zu Salmah ƙunƙuni take, matsowa inda take Amreesh yayi ya riƙo hannun ta,fisge hannun ta tayi a fusace tace '' ka dai na taɓa Ni! The body is mine...''
'' and you're mine '' Amreesh ya katse ta tare da fisgo ta ta faɗo jikinsa.













WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17


Chapter twenty seven:The sex scandal

𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17


𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑇𝑤𝑒𝑛𝑡𝑦 𝑠𝑒𝑣𝑒𝑛: 𝑇ℎ𝑒 𝑆𝑒𝑥 𝑆𝑐𝑎𝑛𝑑𝑎𝑙....



Romancing ɗin ta Amreesh ya farayi a haukace ba kamar kullum ba,Salmah sai kuka take tana ture shi,baya ce bai da feelings ba? Yanzu kuma meye haka? Amreesh ya tafi Wata duniya daban sai romancing ɗin ta yake ba ƙaƙƙauta wa, tuni ya raba ta da towel ɗin dake jikin ta ɗaukar ta yayi ya nufi gadon da ita, ita ko sai kuka take tana turjewa

Ajiye ta yayi kafin ta samu damar tserewa ya faɗa saman ta cikin kuka tace '' wai meye haka? Baka ce baka da feelings ba?" Kuma dalilin da yasa tun farko take sakin jiki da shi kenan, Amma yanzu?Cigaba da abinda yake Amreesh yayi duk ya fita hayyacin shi kafin cikin wata irin murya yace '' i don't feel any body's touch but yours,ke kaɗai" yayi maganar hannunsa tsakanin ƙafafun ta yana cigaba da caressing ɗin ƙirjinta, ruɗewa Salmah tayi ga wani irin tsoro da ya shige ta, ta fara rokon sa amma Amreesh bai ji ba bai gani ba, Salmah ta fara jan numfashi kamar mai asthma saboda a yanayin da suke,it reminded of something that has happened in the past

Ihu ta saki tana kai ma Amreesh cizo da ya kushi,yanda yake mata ɗin sai kwakwalwar ta, take Mata kamar wancan situation ɗin ne ke maimaita kansa

Duk abinda take Amreesh bai masan tanayi ba, tun kafin ya kai ga shigar ta kawai sai ta suma, shima har ya ɗauko hanya ciwon kan da yake ako da yaushe ya kawo masa hari,na yau yafi na koda yaushe tsanani, dafe kansa yayi ya faɗa gefen ta, ɗayan hannun sa kuma dafe a saitin ƙirjin sa, idanun shi da fuskar shi sunyi ja Sai jan numfashi yake before he passed out beside her ( Nidai marubuci ya na runtse ido na ja blanket na rufa musu tunda tsira ra suke)......


Washegari....sai wurin ƙarfe goma Salmah ta fara buɗe idon ta tana sake lumshe wa, lokaci guda komai ya dawo mata,dirowa tayi daga saman gadon tana faman zare ido tana duba jikin ta,ji da tayi lafiyar ta lau babu abinda ya same ta yasa ta sauke ajiyar zuciya towel ɗin ta daya jefar ta jawo ta ɗaura, sannan ta shige toilet wanka tayi ta fito closet ta nufa ta ɗauko wata doguwar riga baƙa tasa da pant shima baƙi

Ta fito kenan idanun ta suka sauka akan Amreesh dake faman zufa now and then yana firgita ga hannun shi dafe da ƙirjin shi

Da sauri Salmah tayo kanshi tana jijjiga shi tana kiran sunan shi, sai yanzu ma ta lura dashi, kiran shi take tana kuka tana shafa kanshi da fuskar shi,sauka tayi ta shiga toilet ta dawo da ruwa tazo tana shafa masa
Dogon numfashi yaja kafin ya buɗe idanun shi da suka rine kwayar cikin ta koma pale green kallon Salmah yayi da ta tsorata da yanayin shi

Dafe kanshi yayi kafin ya tashi zaune hannun ta ya riƙo ya aza saman kanshi weakly yace '' yimin addu'a '' jinjina kanta tayi Sannan ta karanto '' Bismillah (×3) A'udhubillah WA ƙudiratihi alama ajidu wa uhadiru (×7) Amreesh sai numfashi yake ja, duk yaji jikin shi ba ƙwari ga wani irin rashin lafiya da yake ji....bayan Salmah ta gama karanta masa addu'ar rungume kansa tayi tana kuka, me ya faru? Tunawa da su biyun sukayi basu yi Sallah ba yasa su tashi, da sauri Salmah tayi ƙasa da kanta tana juya mashi baya, Amreesh smirked duk da rashin ƙarfin da yake ji sai da ya matso kusa da ita cikin raɗa yace '' matsoraciya '' yayi maganar yana idasa ɗaura towel ɗin dake hannun shi, ya nufi toilet turo bakin ta salmah tayi kafin ta hau sallaya ta kabbar ta Sallah har ta gama Amreesh bai fito daga toilet ɗin ba,a ɗarare ta nufi toilet ɗin ta ƙwanƙwasa,ba'a amsa, hankalin ta ya tashi hakan yasa ta tura ƙofar ta shiga,tsaye ta ganshi gaban madubin toilet ɗin ya dafe kanshi har yayi wanka ya ɗaura sabon towel

Ƙarasowa tayi ta riƙo hannun shi sai sannan ya ɗago jajayen idanun shi ya zuba mata, wani irin tashi tsigar jikin ta yake yi ƙasa tayi da kanta kafin tace '' Sallah '' jinjina kanshi yayi ya biyo ta suka fito toilet. Daga ganin shi yayi kama da marar lafiya zaunar dashi Salmah tayi ta nufi wardrobe ɗin shi ta ɗauko mashi wata jallabiya brown ta taya shi sawa da ƙaramin wando.

A daddafe Amreesh yayi Sallahr yana gama wa da ƙyar yayi azkar kafin ya haye gado yaja blanket ya rufa, hankalin Salmah ya tashi and she didn't know what to do sai hawaye ke bin fuskar ta

Fita tayi daga ɗakin zuwa kitchen suka haɗu da Samha ganin yanayin Salmah Samha tace '' mai ya faru?" Salmah na sheshsheƙar kuka tace '' bashi da lafiya,idan fa shima ya barni kamar yanda...''

'' shhh, Insha Allah babu abinda zai faru, besides kowa ma na rashin lafiya ki kira Dr uhm?'' toh Salmah ta faɗa tare da ƙarasa wa cikin kitchen ɗin ta ɗau kayan tea ta koma upstairs . Samha ta bita da kallo kafin ta fita daga kitchen ɗin zuwa parlor.

Salmah ta koma ɗakin wuri ta samu ta kwanta kusa da Amreesh hannun ta a ƙirjin shi dai dai inda ya dafe ɗazu,'' what's wrong,meya ke damun ka REESH? Waya ke cutar da kai!?" Tayi maganar hawaye wasu na bin wasu,tana kallon fuskar Amreesh that looked pale his lips reddish


Wayar ta ta ɗauko ta kira Dr Ahmad bayan ya ɗaga ta faɗa Masa Amreesh bai da lafiya yace gashi nan zuwa '' waya faɗa maki banda lafiya?" Ta tsinkayi Muryar Amreesh yana faɗa, muryar shi kaɗai idan mutum yaji zai tabbatar baida lafiya
Fashewa da kuka Salmah tayi looking at him ya Bata tausayi

Ganin tana kuka yasa Amreesh jawota ta kwanta saman ƙirjin shi,yace '' why are you crying? Lafiya ta lau ki dena kuka..." Salmah ta cigaba da rera kukan ta tana ƙanƙameshi,ji take kamar....! Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya shiko yana shafa kanta alamun lallashi.

After a while aka ƙwanƙwasa ƙofa, miƙewa Salmah tayi taje ta buɗe ƙofar,it was Dr Ahmad murmushi yayi,ta gaida shi ya amsa sannan ya shigo ciki, gadon ya nufa ya samu Amreesh yana Bacci

Tsira mashi ido yayi for a while, Amreesh ɗin daya sani ada,koda yana tafiya ana sama shi drip ne ,he never skips office Amma yau gashi kwance, examining ɗin shi Dr Ahmad yayi kafin yayi Mishi allura tare da bata magungunan da ya dace yasha,so yake ya tambaye ta mai ya faru amma kawai sai ya barshi.

Dr Ahmad na fita daga ɗakin suka ci karo da Samha a stairs,haɗe rai tayi tare da bi ta gefen shi zata wuce jawo ta yayi ya dawo da ita gaban shi holding her hand tightly,yace '' baki iya gaisuwa bane?" Yayi maganar ba wasa a tattare dashi. Kafeshi da ido Samha tayi,ba cin da tafara ganin girman shi da tayi masa rashin mutun ci. Shima kallon ta yake with his sleepy eyes ta ƙwace hannunta tare da faɗin '' ina wuni '' bata jira amsar shi ba tayi gaba. Dr Ahmad yayi tsaye wurin kamar an ɗasa shi daga baya kuma ya girgiza kanshi yana tafiya tare da faɗin '' zaki shigo hannu ai ''


Zaune take bayan tagama Sallah tunani iri iri aranta gani tayi Amreesh ya miƙe ya nufi toilet few minutes later ya fito alamun alwala yayi, kabbarta sallah yayi a gefen ta ita ko tabisa da kallo, she felt pity for him.

Bayan ya gama sallah ya juyo shima yana kallon ta kamar yanda take kallon shi,gani kawai yayi hawaye sun fara sauka daga idon ta, share mata hawayen yake wasu na ƙara sauka, matsowa tayi ta rungume shi kansa a ƙirjinta tana kuka,it makes him wonder 🤔 ita bata gajiya da kuka ne?

'' MAHEE '' ya kira gently yana zaunar da ita saman cinyar sa,'' na'am'' ta amsa da sheshsheƙar kuka yace '' why the tears? Lafiya ta lau fa '' Ita dai Salmah bata ce komai ba amma tayi shiru,sun daɗe ahaka kafin ya miƙe picking her up ya nufi gado da ita, har bawa zuciyar ta ta fara da ƙarfi sai zaro ido take,ajiye ta yayi sannan ya kwanta gefen ta wrapping his arms around her bayan ya cire mata hijabin dake jikin ta, ɗan kallon fuskar shi tayi kafin tace '' in haɗa maka tea?" Girgiza kansa yayi looking into her eyes ƙasa tayi da nata after a while ta tashi zaune ta jawo kayan tean da ta shigo dasu ta haɗa ta miƙa masa,ƙin karɓa yayi ta ɓata fuska kamar zata yi kuka zama Amreesh yayi sannan ya karɓi cup ɗin daga hannun ta still looking at her face

Kaɗan ya sha tean sannan ya jawo ta ya sa ta shanye sauran ta turo baki a shagwaɓe tace '' ai wayau kayi min, sai ka ƙara shan wani'' lumshe idanun sa Amreesh yayi tare da waro su akan ta,sosai taji tsikar jikin ta na tashi especially da irin kallon da yake mata, hannun shi ya kai yana gyara mata sumar ta kafin yace '' i had enough Ina so in kwanta '' ya ƙarashe maganar tare da karɓar kofin ya ajiye gefe sannan ya jawo ta suka kwanta facing each other matso da fuskar sa yayi kusa da tata,riƙe numfashin ta tayi tare da ƙoƙarin matsa wa baya ya riƙe ta,idanun ta suka ciko da hawaye tace '' baka da lafiya pah'' murya can ƙasan maƙoshi yace '' Ni na faɗa maki hakan?" Turo baki tayi ba tareda tace komai ba, numfashi yayi, pulling her close ya rufe idanun sa ita ma ta rufe nata.....

Dr Ahmad na fita daga gidan Amreesh directly dungeon ɗin da yasa aka ajiye su dark flames ya nufa, yaran shi naganin BOSS ɗin su,suka fara miƙa gaisuwa kafin suka miƙe leading him to the room where dark flames were kept, duk sunyi ƙajin ƙajin sun lalace kamar basu ba,gashin su da suka yi dying red yayi baƙi saboda

25 / 69