Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   69 / 69

204K to 206.1K   out of 206.1K words

faɗa muryar tana rawa,she was afraid at this point idan wani abu ya samu Amreesh bazata taɓa yafe ma kanta ba,why did she choose to believe a stranger over her own? meyasa? why was she so foolish and naive..? '' Mahee..'' Amreesh ya sake kira weakly yana shafa fuskar Salmah kallon shi tayi her red eyes into his pale ones, yana shafa fuskarta yace'' Ranar nan da kika kaini Beach..and you confessed your love...'' jinjina kanta Salmah tayi alamun tana saurare tears streaking her face '' I wanted to confess to you...in a grand way... I wanted to tell you how much...how..much ...I lo..ve yo..u'' He begun to stutter, Salmah ta fashe da kuka mai cin rai,komai laifin tane,wani jinin ya fara bin bakin Amreesh...he had lost way too much blood,tashi zaune yayi once again suna kallon juna, matsowa Salmah tayi ta riƙe fuskar sa cikin hannun ta looking at him with so much love'' I love you Salmah... I love you beyond words...as long as I live...Bazan bari wani ya cutar dake ba, I'm sorry.... for how I treated you in the past few days...ban taɓa soyayya ba,bansan ya ake ba... definitely ban tashi cikin soyayya ba...i have always been secluded...only Seb... Sebastian.... I love you Salmah in this life time and the next '' Salmah didn't know what to feel or do at this point his calling her name for the first time and probably the last time...his confession of love.....kawai saita haɗe bakinsu kissing him passionately and warmly ... Amreesh yayi tilting ɗin kanshi kissing her back, Don ya tabbatar yaune ranar ƙarshe that they'd be together.... Kissing ɗin juna suke kamar zasu haɗe juna... police ne suka shigo wurin going all over suna dubawa inda mutane the place became chaotic

'' the fire's burning fast'' wani ya faɗa

'' call the fire brigades..''
haka maganganun suka cigaba da tashi , Salma da Amreesh were oblivious they were lost in the moment, rabuwa sukayi looking at each other,hannu Amreesh yasa cikin aljihu ya ciro wani diamond ring mai bala'in kyau ya riƙe hannun Salmah yasa mata kissing it after wards '' Keep it with you Mahee... wata rana...zan dawo..when ever you miss me....'' rufe bakin shi salmah tayi,'' don't say that plsss..'' ta faɗa cikin Muryar kuka '' i Couldn't love you enough... '' jawota yayi kawai ya rungume,suna zaune sai ga police sun iso wurin su mace da namiji '' Sir Emrys Woods..!" police ɗin exclaimed idon polisawan kamar zai zubo, miƙewa Amreesh yayi weakly da Salmah by his side, coldly ya kalli police ɗin guda biyu '' Go with them Mahee'' ya faɗa yana miƙa ta ga police ɗin mace, ƙara shige masa tayi tana girgiza kai tace '' Tare zamu '' sudai police ɗin sai kallon Amreesh da Salmah suke police ne ya fara Magana ta walkie talkie ɗin sa yana faɗin wutar ta kusan mamaye ko ina bayan ya sauke wayar yace '' Sir we need to leave as soon as possible,the fire is blazing furiously '' yayi maganar yar ƙaramar zufa na keto masa itama police ɗin mace har jikin ta ya fara rawa '' Go with them... don't be stubborn..'' turo baki Salmah tayi '' i Don't want to leave you....Dan Allah mutafi tare...'' ta faɗa tana kuka sosai riƙe hannunta yayi ya baiwa police ɗin with a hard voice yace '' Go...and make sure she gets to safety...idan har wani abu ya same ta...'' da sauri police ɗin yayi ma Junior ɗinsa alamar su tafi Salmah ta fashe da kuka tana riƙe hannun Amreesh her face so puffy daga kukan da tayi abayar jikin ta tayi ƙajin ƙajin, blood ɗin Amreesh stained it gashin ta kamar sheƙar tsuntsaye she looked so dirty,haka police macen tayi leading ɗinta daga inda suke itada Amreesh,suna fitowa fili taga ko ina naci bal Bal da wuta wurin ya kusa ƙonewa, zuciyar ta begun beating wildly ta juyo baya idon ta ya shige cikin na Amreesh that stood tall duk da raunin da yaji, Murmushi me kyau ya sakar mata slowly yace '' I'll be back someday...'' Salmah ta wani zabura zata dawo police ɗin ta riƙe ta gam '' let's go ma'am '' Salmah tana kuka tace '' dan Allah minti guda kawai inaso in faɗa masa wani abu..'' ganin police ɗin na mata turjiya yasa Salmah ƙwace hannun ta taa rugo da gudu, Amreesh ya lumshe idon sa with anxiety..yana matuƙar tsoron kada wurin nan yayi exploding while she's still here da gudu tazo ta shige jikin shi tana kuka sosai Amreesh yayi wrapping ɗin hannunsa around her shima yana ji kamar ya koma gida kawai... kamar yasa remote yayi erasing this very moment

🎶 I don't wanna say goodbye yet...no it's not over 🎶

🎶Our journey together has just begun...you can't leave me.eee🎶

🎶There are still unwritten chapters we need to fill in...🎶

🎶I love to be wrapped in the warmth of your hold.. I love to wake up into your arms every day 🎶

🎶I wish to love you every day every night and as long as Iive....🎶

o
🎶if you leave me...how would I carry on... without you?🎶

🎶I still want...to be with you every breath I take...🎶

🎶you teach me how to love..not how to live without you 🎶


🎶 I'd rather stay with you through every thick and thin 🎶

🎶Can't live without you.. Memories keep hunting 🎶

🎶in the warmth of your arms I wished to stay forever 🎶

🎶Let's make our love completely..is it impossible?🎶

🎶Are we too far late or can we change a chapter 🎶

🎶fighting from now till the end..you and me against the world...🎶

Cikin muryar kuka Salmah tace '' Amreeshhhh... how can ....I live like this? meyasa bazaka Zo mutafi baaaa.....'' she ended each sentence tana jan kalmar ƙarshe cikin kuka, numfashi ya sauke mai zafi
'' Zan zo mana...kawai ki tafi i will be right behind you...'' ya faɗa da sauri ganin hayaƙi ya fara tashi ga katako da suka fara faɗowa due to the fire '' kayi alƙawari?" Salmah ta tambaya '' nayi alƙawari '' he replied not wanting to drag further jinjina kanta tayi sannan ta sake kallon fuskar shi for the last time pecking him on his cheeks tace '' I will wait for you... I love you so much...'' Sannan ta sake top toeing kissing him on the lips one last time daga haka ta juya ta tafi Amreesh yabi bayan ta da kallo tanayi tana juyowa and she found him still standing there

tana zuwa police ɗin ta riƙe hannunta suka fita daga wurin Amreesh yayi ƙasa da idon shi feeling so miserable, zuciyar sa kamar zata tsage...it was hurting beyond words ya cije leɓenshi wincing in pain ya sauke ajiyar zuciya maƙogaron shi na kai kawo his Adams apple looking bigger..kukan zuci Amreesh keyi





'' Well hello EMRYS...'' Iris ya faɗa yana fitowa daga wani lungu fuskar sa haɗe, gefen rigarsa ya jiƙe da jini, slowly and calmly Amreesh ya juyo hakan ya ƙara tunzura Iris ya tsani yaga Amreesh looking so calm, ganin kallon da Amreesh ke binsa dashi with an expressionless face '' well I guess it's just you and me then...'' yana faɗar haka He lunged forward to attack Amreesh with a fist..riƙe hannun Amreesh yayi ya murɗe kafin ya buga Iris ƙasa ya bishi ya dinga naushi... Kamar Amreesh baiji ciwo ba cuz bugun Iris yake kamar An yimasa wahayi shiko Iris ya zura hannun shi inda ya soka ma Amreesh wuƙa,the two of them groaning like wounded lions,wurin kuwa sai ƙara tashi yake da wuta wani katako ne ya faɗo yana ci da wuta da sauri su biyun suka mulmula gefe lest it falls on them suka cigaba da faɗa,wani naushi Iris ya Kawo ma Amreesh a inda ya soke shi d wuƙa Amreesh ya kauce ya sa ƙafa ya kwashe Iris,faɗuwa yayi rigijib hannun sa ya faɗa saman katakon ɗazu,ihu ya kurma yana jaye hannunsa da sauri

wani katako daban Amreesh ya riƙa ya fara dukan shi dashi... the fight was Brutally fast...the two of them engaged in mortal Combat...da sauri suke attacking juna none was holding back basu ko damu da wutar dake tashi ba.
soon wurin was engulfed in flames,Babu hanyar fita babu hanyar shiga, Amreesh da Iris sunyi jina jina babu cikin su wanda baiji ciwo ba yet sun cigaba da faɗa amma Amreesh yafi jin ciwo... Iris na dariya yace '' You know I actually have fallen in love with your wife...I will surely survive this fight for her...don in aure ta bayan na kashe ka...'' wani wawan naushi Amreesh yayi masa abaki sai ga jini ya ƙara fitowa fiye da da, yana dariya like a maniac yace '' oh..it hurts..are you jealous?" nanma wani naushin ya karɓa...wuta ce ta fara zubowa daga sama the roofing falling off completely da sauri suka mulmula gefe Amreesh saman Iris,yana cigaba da punching ɗinsa kamar yasamu punching back...'' you know...the only thing holding me back..is the fact that you're my brother...I could kill you Iris...'' dariya Iris yayi furiously ya ture Amreesh daga jikin sa yan faɗin '' Brother my foot... you killed Our mother and triplet....Bazan taɓa yafe maka ba!" shima Amreesh a fusace yace '' I didn't kill them damn it!!!!" with a smirk Iris yace ''you can save that story for the fools'' kafin da wani irin ƙarfi ya shuri Amreesh a inda yaji ciwo...fresh blood ooze out.. Amreesh gasped for air idon shi suka fara Lumshewa,wani ƙaton katako ne me ƙusoshi ya faɗo from the roofing zuwa kan Amreesh that was about to lose conscious..... rufe idon shi Amreesh yayi fuskar Salmah flashing before his eyes...
********


Tunda suka fito take kuka tana ƙara kallon baya,snow ne yake zubowa from the sky...wurin daji ne sai dogayen itace,idan mutum ya kalli sama zai san it's just dawn.maybe 06:00am, daga gefe Ambulance da fire brigades da suka iso yanzu sai police mutane ne wurin da yawa birjik....ana kallo daga waje hayaƙi na tashi daga cikin warehouse ɗin,at this point Salmah was more than anxious is Amreesh really going to come? kodai wayo ya mata? abubuwa dayawa swirling in her mind that made her chest felt heavy...bata ga Amreesh ba,bataga alamar sa ba, Wurin akwai sanyi sosai especially Saboda snow flakes ɗin dake zubowa amma ita Salmah ko jin sanyin batayi.... Ahmad ne ya ƙaraso wurin looking so disturbed magana yake da fire brigades Salmah taji ance ''there are alot of petroleum drums inside...the place could explode anytime '' Zaro ido tayi jin since explosion at the same time duk wani sensory system naji kinta stopped working her heart was beating at an incredible speed '' ex..PLO..Sion?" ta faɗa with trembling lips.... Ƙara juyawa tayi tana kallon warehouse ɗin taga tana hango halshen wuta ai batasan sanda ta ƙwace hannunta daga hannun police woman ɗinnan ba ta sheƙa da gudu towards the ware house, mutane gasped sai ga Ahmad ya dafa mata baya tana gudu tana kiran Amreesh hawaye na ratata more snow flakes falling zuciyar ta na bugu da ƙarfi she was praying inside Allah kasa kada wani abu ya samu Amreesh,yanda take gudun ji take kamar bata sauri,Ahmad na zuciyar sa bugu take dum dum yana maimaita don't explode pls.... she wasn't about to lose another person in her life was she?...

Sauran mutanen wurin police da fire brigades bayan su cuz it won't look good idan su Ahmad suka runtuma ciki....har sunyi rabin hanya Salma a gaba Ahmad a baya she was hopeful when suddenly
BOOM!!!!💥 💥 💥 💥
THE PLACE EXPLODED

'' AMREESHHHH!!!!!NOOO!!!!?!!" Salmah ta faɗa kamar maƙoshinta zai faɗo tana kaiwa a guiwowin ta as she watched the flames eating up the Warehouse '' I promise...ki tafi kawai ina zuwa....'' ta tuna kalaman Amreesh na ƙarshe...luu tayi zata faɗi Ahmad daya iso wurin yayi saurin tarota ta faɗo jikin shi more snow flakes covering them.....

End of Book one.....

Amreesh ya mutu ko ko dai?
Iris.... Meya sa ya zama yanda yake?

wacece Hajiya Maleeka?

Samha da Dr Ahmad Are at war with one another zasu shirya?

me dark flames suke shirya ma Samha da Ra'esah?


ya rayuwar Salmah zata kasance without Amreesh,zata zama strong ko zata zama weak?

Iris yace ya kamu da son Salmah and he will survive the fight, yake nan? Do we have love triangle?

da gaske Iris mugun ne ko is it just circumstances?

find out in the book two of WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17 🍁 🍁







Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen Book one na WAYE SHI?(Behind the mask) book two paid book ne #1k, ga duk me buƙata sai ya biya kuɗin ta wannan account ɗin
9138091955
SALMA ALIYU Monie point

shaidar biya ta wannan number+234 9138091955


69 / 69