Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 69

3K to 6K   out of 206.1K words

Sannan after kamar 5 minutes ya fito daga motar. Me gadi Ya ƙaraso yana ta kwasar gaisuwa,"Barka da zuwa ne gida"Mallam salahu me gadi Ya faɗa. Batare da ya kalleshi ba ya amsa da "uhm" kawai yay gaba abin shi. Hakan be damu Mallam salahu ba dan ya riga da ya saba. Tura ƙofar apartment ɗin nasa yay yashiga bakin sa ɗauke da Sallama ciki ciki duk da ba kowa. Hannun sa ya kai a switch ɗin ya kunna tuni haske ya gauraye palorn and Masha Allah what a beautiful sight. Daga inda switch ɗin yake akwai wani shoe rack that was golden color, se kuma furnitures ɗin da suka kasance sky blue and White, a white marvel floor SE kuma set of sofas masu shen kyau suna sky blue daga tsakiyar palorn. Da square shaped center table da aka ƙawata da bowl of fruits SE A Plasma TV da ta mamaye bango ɗaya,daga saman ceiling kuma wasu irin chandeliers be masu azaɓaɓɓen kyau suma silver coloured daga right hand side ɗin palorn a little further was the dining table neatly arranged. Daga bangon da aka maƙala tvn kuma kitchen ne. On the left hand side ɗin kuma was a spiral staircase ne me ɗauke da sashe biyu left and right corners and in between wani parlor be anan ma ne ɗauke da purple furnitures and another TV SE dispenser daga farkon shiga parlon. .ahankali ya ɗan sunkuya ya cire takalmin da kafin ya idasa ƙarasowa ya janye staircase ɗin. Right hand aide ɗin yabi wanda yasa da shi da wata brown wooded for with a passcode. Wasu Yan nombobi ya danna se ga shi ƙofar ta buɗe. Shiga yay da ga ciki,duk da ba kowa ɗakin se ƙamshin pepper mint air freshener yake. Kujera guda ɗaya ce kawai daga gefe,nesa kaɗan daga gadon.

Se kuma taga da aka ƙawata da grey and White curtains.Amma the curtains were drawn kasancewar dare yayi. Daga left hand corner of the room kuma toilet ne,and a mirror da kuma drawer. Kayan jikin da ya fara cirewa se da ya rage singlet da boxer Sannan ya juya ya shiga toilet ɗin. Ya tara ruwa a bath tub ɗin Sannan ya zuba kayan ƙamshi da tura dukan wanka Sannan ya idasa cire kayan sa ya shiga ciki. Ya ɗau lokaci me ɗan tsawo kafin ya fito saye da blue bath rub, hannun sa riƙe da towel yana tsane gashin da da ya sauko har saman kafaɗar sa. Ma sha Allah, he looked so sexy. Ƙarasawa yay gaban mirror ya ajiye towel ɗin dake hannun sa ya fara shafa tsadaddun body lotions ɗin da(Ni dai ganin ze tuɓe yasa nai gaba abinda) few minutes later ya gama shiryawa in a soft green pajamas da suka yi kishi kyau sosai like a piece of art. Turaruka ya feshe jikin shi dasu. Duk wannan abinda yake fuskar shi bata changer ba ita was still stoic and void of emotions. Koda yagama parlor ya koma ya shiga kitchen ya haɗa ma kanshi coffee nan ya jira ya gama kafin ya fita daga kitchen ya dawo parlor ya kashe komai Sannan ya haye sama. Nan na ya kashe komai kafin ya koma ɗakin sa,he sat by the bed side ya karanto addu'ar Bacci Sannan ya kashe wutar ya ja blue duvet ɗinsa zuwa ƙirji and that was it...











.
WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17

Chapter three: the marriage
***************Salmah**********

09:00

AURA PRIVATE HOSPITAL

Tun lokacin da aka fara aikin take ta safa da marwa, she feels so restless and it has been 2hrs and yet the red light is not yet turned off. Zuciyar ta bugawa take da ƙarfi ga wani irin tsoron da ya mamaye zuciyar ta making her weak to the knees!

She feels so restless and daga lokaci zuwa lokaci take kallon empty hall way ɗin,there wasn't a single soul ita kaɗaice!

"Mahmah" Dr Ahmad ya kira , juyawa tayi se kuma ta kalli hannun shi dake riƙe da ledoji. Ƙarasowa yayi glancing at the theater room sannan ya dawo da dubanshi bisa kyakkyawar fuskar ta da tayi jage- jage da hawaye idanun ta sunyi luhu luhu she looked so pitiful. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin "insha Allah she will be fine" "I know" ta faɗa with a trembling voice and a restless heart "Amma me yasa haryan... haryan zu..."ta kasa ƙarasa maganar saboda kukan da yake cinta! So she turned away,Bata so take dinga nuna raunin ta Ako da yaushe. Amma she can't help it Samha is her weakness

She can't picture life without her vibrant little sister the one that makes her want to make it!

"She will be fine ki ta addu'a kawai, ga abinci kici pls.because it won't be nice if your sister recovers and you fall sick"!

"Bazan it's cin abinci ba Dr " ta faɗa tana goge hawayen ta"har sai Samha ta fito,we always do things together I can't do without her "

"Na fahimta, amma..."kafin Dr ya faɗa what he intended to say, the red light was turned off and the green light on. Sosai Salmah ta ji zuciyar ta ya fara bugawa daƙarfi

Idanu suka zuba suga Wanda ze fito,soon the door to the surgery room opened and the doctor stepped out fuskar sa ɗauke da murmushi ...ganin hakan yasa itama Salmah sakin murmushi it da Dr Ahmad suka ƙarasa wurin likitan.Dr Ahmad ma yaɗan ji relieve a zuciyar sa duk da be haɗa komai da suba

"Congratulations, surgery successful" likitan ya faɗa

Me Salmah zatay? Faɗuwa tayi tana sujud shukr ranta cike da farin ciki hawaye nata kwarara but this time na farin ciki ne bana damuwa ba.

Likita da Dr Ahmad idanu kawai suka zuba mata se da tagama ta miƙe dai daidai ana fito da Samha daga surgery room ɗin.

She looked pale and her lips dried.

"Samha" ta faɗa in a whisper tana kallon ƙanwar Tata da suke tsananin kama.

Shima Dr Ahmad yay ma Samha kallon tsanaki "Ma sha Allah" ya furta duk da Samha na cikin ciwo it didn't hide her beauty.

Juyawa tai wurin likitan tana faɗin "zan iya zama tare da ita?"

"She has been moved to the I C U , she needs rest and ba'a buƙatar kowa ya kasance da ita at the moment,Amma zaki iya zuwa gobe" likitan ya faɗa yana mata alama da ta biyo shi officer ɗin shi.

Bata ji daɗin ƙin bari ta kasance daƙanwar ta da akai ba amma ba komai ,abu ne muhimmanci shine the surgery is successful. Kuma gobe zatayi sammakon zuwa.

Biye suke da likitan ,ita da Dr Ahmad.likitan yaɗan shiga for a while kafin su shigo ya nuna musu wuri su zauna "baku da wani babban? Do you not have any other person in your family?" Likitan ya tambaya fixing his eyes on her

Girgiza kanta tayi Sannan tace"I'm her only family. Duk wani abu da zaka faɗa ka faɗamin" jin jina kanshi doctor yay sannan ya mata bayanin nasarar da aka samu a surgery ɗin da kuma abinda take buƙatar kiyaye wa.

Godiya tayma likitan sosai sannan Dr Ahmad shima yayi ma likitan Godiya tare da tambayar idan tana buƙatar wani maganin da za'a siya

Babu dan haka suka fita daga office ɗin likitan zuwa parking lot har yanzu Dr Ahmad riƙe yake da ledojin daya shigo da su ɗazun.

Cema ta yay ta jirashi ya shiga parking lot ɗin ya fito da motar shi Sannan ya tsaya dai dai ita. Buɗe empty side ɗin taya tashiga.

Bayan ta zauna tayi fastening sit belt ɗinta they drove off. Tafiya suke ina silence tun lokacin da tayi mashi kwatancen anguwar su ba wanda ya sake cewa komai cikin su,har sai da suka kawo dai dai ƙofar gidan su sannan ya juyo ta kalleshi " thank you for everything you have done for us Allah ya biya ka ya cikama burin ka ya biya ka da mafificin alkhair...."adduo'i take ta kwararo mishi.ya ji daɗin adduo'in ta sosai hakan yasa ya amsa da Ameen da kyakkyawan murmushi shimfiɗe a fuskar shi. Agogo ya kalla yaga it was 11:30pm hakan yasa ya miƙo mata ledojin daya ke ta ya so da su tun tuni bayan ta karɓa ya ɗoura da faɗin" Allah ya ba mara lafiya, lafiya...and I'm bringing the contract tomorrow Dan kiyi signing and the marriage will take place tomorrow" jin abinda yace yasa zuciyar ta bugawa da ƙarfi amma se ta dake ta jinjina kanta kawai

She will take life as it comes to her as long as Samha zata samu rayuwa ne kyau.

Buɗe ƙofar tayi tafita hannun ta riƙe da ledojin ta maida ƙofar ta rufe tanay Mishi bye bye. Binta yay da ido harta buɗe ƙofar gidan da ta kasance brown ta tura ta shiga ta rufe. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tada motar shi ya tafi. Ko da tashiga ba ta tsaya ko ina ba single room ɗin su ta nufa ta buɗe kofar ta shiga ta ajiye ledojin hannun ta. Hijabi ta tacire hakan yasa tulin gashin ta ya sauko izuwa hips ɗin ta. Fitowa tayi da zane a hannun ta sannan ta ɗibi ruwa a bucket ta nufi toilet few minutes later ta fito zanen ta ɗaure a ƙirji kayan da ta cire cikin bokitin, sumar kanta kuma a hannun ta, tana faman matar wa ajiye bokitin tayi ta wuce ɗaki ba nepa hakan yasa ta lalubo torch light ɗin su ta kunna hasken wasn't that bright but it was enough.

Kaya ta canja cikin sauri zuwa pink colored pajamas bayan tasa pad ɗinta.every where was neat hakan yasa ta zauna gefen gado tare da jawo ledojin da Dr ya bata ta buɗe take away ne ciki na farko shinkafa na biyun kuma chicken pepper soup

Shinkafar ta cinye duka, kasancewar tana bala'in jin yunwa kuma rabon ta da abinci tun jiya. Pepper soup ɗin Kuma ta adana she will warm it and take it to Samha tomorrow. Bayan ta gama all this ta kalkamta komai before she hit the pillow she was too tired to think about anything hakan yasa tana azakanta saman pillow ko 5 minutes ba a yiba Bacci yay gaba da ita.

Shima Dr Ahmad on his part gida ya wuce straight. Bayan ya yi parking,ya wuce ciki. Apartment ɗin shi shima ya haɗu ba ƙarya sama ya hau yay wanka ya canja kaya be Mayi tunanin abinci ba kawai ya hau gado, addu'ar Baccin na da ƙyar ya karanta kafin ya gama Bacci yay a won gaba da shi.

****THE NEXT DAY***"**

Kiran sallar farko Salmah ta tashi ,Bayan ta gama karanta adhkar ɗin safiya tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar material ja da ya fito da hourglass figure ɗin ta(coca cola shape) ta ɗan fesa tura re me sanyi ƙamshi sannan ta taje gashin ta daya kasance baƙi wulik ta ɗaure sannan ta ɗaura ɗan kwali. Ta bala'in yin kyau. Tana gama wa ta je ta ɗauko pepper soup ɗin da ta Shema Samha tayi warming Bata San ba a cin abinci me nauyi na few days after surgery. Duk wannan abinda take taga nawar tagama tagan ta a asibiti tare da Samha.

Tagama komai at exactly 07:30am ta shiga cikin ɗakin nasu da ba wani tarkace ne dashi ba can just a mattress set wardrobe shikenan. Hijabi fari tasa wanda yakai mata har ƙasa sannan tasa siɗaɗɗun takalmin jiya ta fito kitchen ta tafi ta ɗauko kula ta zube ɗumamen sannan ta wanke tukunyar kafin ta fito ta koma ɗaki ta ɗauko ma kulli tare da buɗa wardrobe ɗin su ta ɗauki wata ƙaramar purse ta ɗauki 2k ta ɗauki kular tasa a leda ta rufe ɗakin sannan tafita daga gidan gaba ɗaya.ko da tafita, ta ɓata lokaci kafin tasamu abin hawa dan haka se wurin tara ta isa.Ana sauke ta tabiya me napep ta wuce ciki bata tsaya ko ina ba se ward ɗin Samha. Ko da ta isa bata ganta ba har hankalin ta ya nemi tashi zata fita k Nan ta ta hangeta standing by the window

Ƙarasa shiga tai with a trembling voice tace "Samha" Samha that had been standing there for a while still wearing the hospital gown her gashinta dishelved,ta juyo with a beautiful smile on her face masha Allah suna tsananin kama Da sauri Salmah ta ƙarasa wurin and engulfed her in a very tight hug tana kukan farin ciki"I missed you so much Sam" ta ƙarashe maganar tana raba jikin su looking at her face,she looks so lean. Murmushin Samha ya ƙara faɗaɗa sannan da zazzaƙar Muryar ta tace" I missed you too anty Mahmah cry baby" ta ƙarashe maganar tana jan hanci Salmah da ke kuka shaɓe shaɓe! Tana jin kamar ta mayar da Samha a cikin ta. Kallon ta take ba ƙyafta wa her little sister looks so lean and pale kamar Bata da jini a jiki.

"Anty Mahmah stop looking at me, don't make me feel bad,nasan yanzu nay muni ko?"Samha ta faɗa tana ɗage gira."kin ƙara kyau Samha"Salmah whispered

"Okay" kawai Samha tace zata sake magana aka buɗe ƙofar it was the doctor bayan shi wata nurse ce biye da shi ya idasa ƙarasowa ciki fuskar shi ɗauke da murmushi

Salmah da Samha suka gaida su while Salmah led Samha to the bed likitan ya amsa gaisuwar su yana kallon Samha yana mata tambayoyi if anything is hurting ta ce babu abinda ke mata ciwo

He did he's check up kafin ya fita shi da nurse ɗin. Yana fita the two sisters looked at each other sannan suka sakar ma juna murmushi riƙe hannun Samha Salmah tayi tare da faɗin " I missed you a lot Samha, I could never imagine life without you, k ɗin rayuwa ta ce Please don't leave me" ta ƙarashe maganar tana kallon Samha with so much emotions swelling in her heart

Murmushi me kyau Samha tayi sannan tace" i also love You so much cry baby Mahmah, nima bazan taɓa iya ƙiyasto rayuwa babu ke ba" rungume juna sukayi suna farin ciki their love for each other increasing.

Suna Nan a haka sega shi an buɗe ƙofar it was doctor Ahmad saye yake cikin ƙananan kaya baƙaƙe ya matuƙar yin kyau murmushi ya saki tare da yin sallama,amsawa Salmah tayi tana maida mai martani murmushi sa Samha kan ta ɗauke fuskar ta gefe guda. Gaida shi Salmah tayi amsa wa yayi yana kaiwa zaune on the other side of the bed inda Samha ta maida fuskar ta yet again she looked away ɗan murmushi Dr Ahmad yaci "ya jiki ƙanwar mu"? Dr Ahmad Said juyowa tayi da sauri tana Mishi kallon up and down "wace ce ƙanwarku?" Ta tambaya fuming with anger. She didn't like the way he looks akan me ze da irin wannan kayan? Ita pa duk wani na miji da ke sa matsatstsun kaya gani ɗan iska take mashi"Samha" Salmah called out gently

She knows her sister if she doesn't like a person she wouldn't pretend to rolling ɗin idanun ta tayi tana ɗan turo baki

Murmushin da ke fuskar Dr Ahmad ya ƙara faɗaɗa. Soon wata nurse ta shigo hannun ta ɗauke da abinci tunda PRIVATE HOSPITAL NE it's their responsibility to provide the patient irin abincin da ya kamata su ci.

Gaida Dr Ahmad nurse ɗin tayi sannan Salmah da kanta ta karɓi abincin which was liquid ta fara feeding ɗin Samha da kanta.

Ita kuma nurse ɗin ya juya ta fita

Dr Ahmad shi kuma ya ɗauko wayar shi ya fara danne danne. Glancing at Samha every now and then

Idan sun haɗa ido se ta Banka mai harara,shi kuma se dai yayi murmushi.

"Sam this is Dr Ahmad je was the one who paid for your surgery you should thank him"Salmah tayi mata bayani 'did I ask him to pay ya faɗa a zuciyar ta tana ƙara turɓune fuska kamar baza tace komai ba se kuma ta ce" mun gode" batare da ta kalleshi ba.yi yay kamar be jita ba yaci gaba da danna wayar shi "that's no way to thank someone Sam " Salmah ta faɗa pausing to look at Sam "when someone is good to you, you should thank them. Ki tuna Wanda be gode ma mutane, ne gode Allah ba" Salmah ta tunasar da ita. Dr Ahmad miƙewa yayi yana amsa phone call a wayar,at the same time Yana tuna Salmah alama da ta biyo shi

Bayan yafita duban ta ta maida ga Samha WHO wasu looking in another direction without saying a thing she left.

Bayan ya fita Samha tabi ƙofar da kallo 'ko shi saurayin tane? Yanzu k Nan Mahmah will not love her alone? She has to share the love between them?' wannan tunanin yasa Samha jin ranta yanay mata badaɗi. Zame wa tayi ta kwanta.

Salmah kam koda tafita directly parking lot ta tafi tafi ta iske Dr Ahmad still making call wuri ta samu ta tsaya kusa da motar shi tana jira ya gama.

Few minutes ya gama ya zo inda take da murmushi yace" yanzu se a dena kuka ko" murmushi tayi wanda yasa dimples ɗin ta from both sides lotsawa. "I'm sorry for the way Sam spoke to you" ta faɗa after a while

Kauda kansa yay gefe an even bigger smile spreading on his face shi ba abinda ya gani tattare da yarin yar imba wauta ba,in ba haka ba daga ganin Mutun se harara?" It's okay " ya faɗa yana buɗe gaban motar ita kuma Salmah seta ji ba daɗi "do You have any family members?"ya tambaya "a'a" ta amsa a sanyaya. "Today is the wedding day waze zama waliyyin ki? "Kai "ta amsa kai tsaye jinjina kansa yay sannan ya

Ɗago with some documents on his hand " look through it and sign idan akwai abinda be miki ba se a canja" ya ƙarasa maganar yana miƙa mata pen

Amsa tay and flipped through the pages before signing. Ta miƙa mishi ɗan waro idanun sa Masu kyau "You didn't read and you just signed"? Ya tambaya utterly surprised,jin jina kanta tayi kawai"what if you are at a disadvantage?" Ya tambaya in a serious tone .yar karamar dariya tayi sannan tace "u helped me without knowing me Kuma sannan ka yarda dani kabiya kuɗin aikin before I signed the contract you bother about the fact that zan iya saɓama alƙawari

2 / 69