Author : Nimcyluv Category : Complete Novels
su cikin fitar hayyaci har ya ƙwace Samha the two of them falling on the ground, ƙanƙame Samha Yayi yana sakin ajiyar zuciya,jikin sa na cigaba da rawa, Samha hugged him back tana shafa bayan shi to calm him down '' it's okay '' she whispered... Miƙewa sukayi ya riƙe hannun Samha suka cigaba da tafiya he was more alerted now than ever sun kusa fita wurin wasu vampires charged at him suka wuce da Ahmad ta wani wuri daban da Samha bata sani ba, hankalin ta ya tashi '' My lady!" Dr Ahmad ya kira kafin su ɓatar dashi daga inda Samha take,binsu da gudu Samha tayi tana kiran '' My prince..!!" Amma ƙofar was shut duk yanda samha tayi ƙoƙarin shiga wurin it was closed,kuka ta fashe dashi,it was her fault dama bata ce su shigo hunted house ba, wayyo Allah! Tashi tayi ta idasa fita daga hunted house ɗin, cikin wani daji ta ɓullo, Inda dogayen itace ga wani stream inda ruwa ke bi suna zuba down wards,sai an tsallaka za'a isa ɗayan side ɗin,daga kanta samha tayi taga har Rana ta faɗi,the place was quite ba'a jin komai sai kukan tsuntsaye, ga sanyin da ya fara saukowa don har yanzu December ne,ƙasan wurin ganyayyaki that have withered,kallon ko ina Samha take bata ga dr Ahmad ba, and she didn't see a way to go back to the park sake fashewa tayi da kuka looking side by side ko zata ganshi, yanzu shine kawai Abinda take muradin gani, tafiya ta cigaba da yi cikin dajin tana kiran sunan shi hawaye na ratata,batasan dacewa ma gyalen ta ya faɗi ba, gashin taya walwale,tayi nisa ciki dajin tana kiransa ganin babu amsa sai ma dare dake ƙarayi ga kukan tsuntsaye yasa Samha tsayuwa wuri guda ta cigaba da rera kuka tana sambatu '' it's all my fault...I shouldn't have...I shouldn't have brought him...to the hunted house... I'm sorry '' haka ta cigaba da maganganu in a broken voice ta rufe fuskar tada tafin hannun ta she desperately wants to see him,so take su koma gida she won't bring him to a place like this tayi alƙwari..'' I'm sorry '' ta faɗa in a whisper kafin ta faɗi on her knees tana rusar kuka cikin ganyayyaki kamar ranta zai fita '' My lady...!" Ɗago jajayen idon ta tayi ta kalli direction ɗin da Muryar ta fito ganin shi tayi tsaye a ɗayan side ɗin, he looked dishelved gashin kansa yayi datti haka ma kayan shi yet there's still a smile on his face, miƙewa Samha tayi itama tanayi masa murmushi,wasu sabbin hawaye suna sauka akan fuskar ta, gashin ta duk yayi datti,not minding ta tsallako da gudu,ware mata hannun shi yayi and she fell into his arms tana sake fashewa da kuka da gaske ta tsorata,ta ɗauka shike nan,they will never see again '' Kayi haƙuri..duk laifina ne ''tayi maganar burying her face in his chest,shafa gashin ta yake idon shi a lumshe zuciyar sa na wani gudu kamar zata bar ƙirjin sa, tuni ya koma Park ɗin ya ɗauka ya iske ta but he didn't find har tsawon lokaci hakan yasa ya dawo cikin daji ya fara Neman ta,his heart beating wildly all sorts of bad things running in his mind,he was almost driven crazy har dai da yake jin sautin kukanta yet baisan inda take ba...
'' it's okay... I'm here now'' yayi maganar with so much relief in his voice cirota yayi daga ƙirjinsa yana goge mata hawaye with a smile yace '' Ashe my lady ta damu dani to this extent? '' murmushi Samha tayi tears sliding down the corners of her eyes.. girgiza kanshi Ahmad yayi alamun ta dena kuka...kallon sama yayi yaga har duhu ya fara saukowa and there's cold, hannun ta ya riƙa suka nufi hanyar komawa dajin.... Bayan sun dawo ganin mood ɗinta Ahmad yayi insisting sai sun haw ferris wheel 🎡 Samha didn't argue suka haw and the ride was fun,idonta akan Ahmad ko ƙiftawa batayi naɗan lokacin da suka rabu she understood how much he meant to her and how much she loved him, sauka sukayi suka haw Loopty loop ➿, shima wannan ride ɗin was fun kuma Samha ta cigaba da kallon Ahmad kamar tasamu tv..bayan wannan suka hau wani me kamar elevator suka kaiwa top floor saiga fire works an rubuta '' I love You My Lady '' juyowa Samha tayi ta kalli Ahmad and he flashed her his expensive smile ƙasa tayi da kanta,tana jin wani irin yanayi tattareda ita... Biyan kuɗi komai sukayi sannan suka nufi parking lot,wani abu Ahmad ya manta a cikin Park ɗin yace Samha ta jira yana zuwa jinjina kanta tayi ta tsaya waje tana jiran shi batareda ta shiga motar Ba,sai ga wasu drunkard su biyu sun zo suna teasing ɗinta, Samha bata da ƙarfin yin faɗa yasa ta buɗe ƙofar motar zata shiga,ɗayan su yayi saurin maida ƙofar ya rufe yana shafa fuskar Samha '' yan mata jimana!" Ya faɗa, Samha felt disgusted ta kwashe sa da mari,baya baya yayi ya faɗi kafin ya miƙe,su biyun suka tarar mata,ɗayan ya tsaya ta bayan ta yana jan gashinta, ta gaba kuma sai kokuwa suke da ɗayan dake ƙoƙarin kai hannun sa jikin ta,she felt helpless hawaye suka fara wanke mata fuska,kafin ta fara kuka, faɗa take sosai dasu biyun don sun fita ƙarfi,' why is everyone hellbent on sexually harassing them?' abinda ta ayyana ke nan,su biyun ko sai dariya suke cike da maye tureta na gaban yayi ta faɗi ta buge goshi ɗayan ya dawo gefen shi su biyu suka Cigaba da yimata dariya,kafin simultaneously sukayi ƙasa da wandon su,abinda ya faru China ne ya dawo kan Samha ta fashe da wani matsanacin kuka,she felt helpless and couldn't do anything,supa ma farkon yayi zai dire kan Samha yaji an riƙe rigar sa ta baya....
WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 🍁 🍁 17
Chapter sixty three: Intoxicated....
Jawo shi baya da karfi Ahmad yayi zuciyar sana ƙuna he was more than hurt,more than furious ganin yanda su biyun suka tarar ma Samha...dukan su ya shiga yi su biyun kamar Allah ya aiko shi his eyes were blinded, Saida ya masu jina jina har suka kasa tashi, a fusace ya isa inda Samha dake kwance wurin tana shaking ji yayi zuciyar sa na raɗaɗi, iskan wurin bai isar shi...he felt asthmatic, durƙusawa yayi ya miƙar da ita, ihu Samha ta saki kafin ta fara roƙon su rabu da ita thinking it was him...yes she was Samha,she was strong Amma ai wasu lokutan even the strongest of the strongest suna gajiya right? SAMHA ta iya faɗa,she could fight and protect her self Amma ita ma ta gaji, she's tired...she had her own internal battles to fight..it exhausts her... Wani ƙunci ya lulluɓe zuciyarsa jin yanda take roƙo da magiya, cupping fuskar ta yayi ''My lady...'' ya kira yana bubbuga fuskar ta,buɗe idon ta samha tayi, looking around kafin idon ta yayi settling akan fuskar Ahmad... ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi baya daga jikin shi...idon shine ya faɗa akan goshin ta dake fitar da jini... Slowly tace '' I'm fine,Dan Allah mutafi gida '' Ahmad baice komai ba ya buɗe mata ƙofar ta shiga shima ya shiga driving them off... Samha ta jinginar da kanta a headrest ɗin seat, hawaye na tsiyaya daga idon ta zuciyar tana zafi ba kasafai take tuna abinda ya faru in the past ba,she always puts that at the back of her mind but some how...wasu lokutan there are always situations to remind her that tasan abinda bai kamata tasani ba,taga abinda bai kamata ta gani ba, she wasn't like other kids her age...
*******
Salmah ce ke kai kawo a parlorn tana leƙa window from time to time saye take da mini skirt na jeans sai riga green short hand gashin ta into a low ponytail, fuskar ta ɗauke da damuwa, wayar ta ta ɗauko daga ɗaki tayi dialing number Samha,har tayi ringing ta katse Samha bata ɗaga ba,zama Salmah tayi ta dafe kanta feeling so anxious, Amreesh ne ya fito parlorn saye da riga fara armless da guntun wando hannunsa riƙe da laptop zama yayi yana aiki a laptop ɗin ta wutsiyar ido ya hango yanda take kai kawo,ɗago kanshi yayi staring at her kafin ya kirata,zuwa tayi ta zauna kusa dashi looking so worried, sanin dalilin dayasa take up and down ya faɗa mata Samha na tareda Ahmad and they will be back soon,gyaɗa kanta tayi feeling a bit relieved, cigaba da aikin shi Amreesh yayi, five minutes later sai ga samha ta turo ƙofar ta shigo,zumɓur Salmah ta miƙe da gudu ta isa wurin Samha ta rungumeta feeling so happy, Amreesh ya kalli Samha that looked haggard ga idon ta dayayi ja,ga jirwayen hawaye wondering what happened to her... Raba jikin su Salmah tayi tana kallon Samha,ganin goshin ta da aka sama plaster and kayan ta da suka yi datti yasa idon Salmah cikowa da hawaye '' Meya faru Samha?" Tayi maganar tana taɓa goshin Samha coldly ta ture hannun ta daga goshin ta tana faɗin '' I'm fine..zan iya kula da kaina'' wani Banzan kallo tayi ma Amreesh lokacin da suka haɗa ido kafin ta wuce ɗakin ta, Salmah tayi tsaye wurin kamar an ɗasata,har zata bita Amreesh ya hanata '' let her rest,ta gaji..'' dawowa Salmah tayi ta zauna sum sum looking down casted what happened suddenly?
Har akayi isha'i,tun Salmah na jiran fitowar Samha har ta gaji ta miƙe ta shiga ɗakin, The lights were off, sai ɗan ƙaramin hasken dayake shigowa ta windown da Samha ke tsaye wurin...Kunna hasken ɗakin tayi,tana kallon direction ɗin Samha dake saye da red pajamas...'' Sam'' Salmah ta kira, Samha bata juyo ba,bata kuma amsa ba duk da taji,ƙara kiranta Salmah tayi amma Samha taƙi amsawa sai ma hanyar toilet data nufa,da sauri Salmah ta riƙe hannun ta, ƙwace hannun Samha tayi a fusace tace '' Menene Salmah eh? Nace menene?" Suman wucin gaɗi Salmah tayi for the fact that Samha ta kira sunan ta and...'' meya faru Samha?" Salmah ta faɗa eyes blurred with tears, murmushin takaici Samha tayi kafin tace '' nothing happened..I figured yanzu kinyi aure and bisa dukan alamu ina shiga rayuwar ku keda mijin ki so I'm giving you space..'' Samha ta ƙarashe maganar wani ɗaci na tasowa a maƙoshin ta, Kallon ta Salmah take ido waje she couldn't believe abinda Samha ke faɗa,sake riƙeta zatayi Samha ta matsa da sauri '' I'm sorry Samha '' Salmah ta faɗa in a whisper, '' it's okay..ki tafi kawai '' Samha ta faɗa coldly tana Kora Salmah daga ɗakin ta,har bakin ƙofa ta rakata slamming the door behind ta jingina da ƙofar hawaye na wanke mata fuska,for the fact that Salmah zata iya tafiya wuri na tsawon kwanaki batareda ta damu da ta sanar da Samha ba,kuma ba tareda ta damu da taji yanda take ba it really hurts her,she was beyond hurt,she wasn't a narcissist..but then she only had Salmah yanzu idan ta juya mata baya itama how will she survive? Kuma daga dukan alamu Amreesh yayi mata katutu a zuciya she doesn't see anyone but him...hakan yasa kukan Samha ƙara ƙarfi as she coiled on the floor...
Salmah daga waje kuwa sai buga ƙofar take tana kuka asking Samha to open up tana bata haƙuri amma taƙi, Amreesh dake zaune ya taso lifting her up ya wuce da ita ɗakin su, ya shiga lallashinta it was hard for him to convince her and he put her to sleep da ƙyar... Idon shi darkened, miƙewa yayi har Ya nufi ɗakin Samha zai ƙwanƙwasa sai kuma ya fasa ya koma ya zauna ya cigaba da aikin shi a laptop
For three consecutive days Samha tacigaba da share Salmah,itako Salmah sai Binta take tana roƙonta,ganin yanda samha ke wahalar da Salmah saura kaɗan Amreesh ya daki Samha amma Salmah ta hana shi,he disliked yanda samha keta Gara Salmah here and there... Murmushi Samha tayi tana kallon Salmah da ta riƙe Amreesh tace '' Lucky girl...'' daga haka ta fice daga wurin, Salmah ta sake fashewa da kuka... ajiyar zuciya Amreesh ya sauke ya rungumeta yana lallashin ta cikin kuka tace '' I'm such a bad sister ko? Na kasa kula da ƙanwata,i failed..'' girgiza kanshi Amreesh yayi '' you're not Mahee'' ɗaukar ta yayi suka shige ɗakin su,can yanata kaya.. trying all sorts of things to cheer her up...
****
Kitchen Samha ta tafi, idon ta cike da hawaye ranta na ƙuna wai ita Amreesh zai daka, to ai daya daketan kawai dan yaga tana zama gidan su ko? Nan gaba she will become independent, infact ' zan zama haka I'm kwashe duk kuɗin dake account ɗin shi,if he becomes poor sai mugani!' ta ayyana aranta tana kwashe wa da Dariya imagining Amreesh as beggar, juyowa Azeezah dake riƙe da wine tayi tana kallon Samha,'' ke kuma ke dawa?" Azeezah ta faɗa tana tsuke fuska, barin dariyar Samha tayi ta kalli wine ɗin dake hannun Azeezah har taji ya biyo mata arai, Matsawa kusa Samha tayi daga gefen Azeezah,cup ta ɗauka batareda ta amsa Azeezah ba, '' dan ubanki wa kike ma dariya?" Azeezah ta faɗa a ƙufule,ajiye wine ɗin tayi ta juyo suna kallon juna itada Samha,ɗage hannu Samha tayi kamar me surrender tace '' A'a Ni ba dake nake ba pls'' Azeezah na huci tace ''yadai fi..'' wayar Azeezah dake cikin aljihun wandon ta ta fara ringing fita tayi daga kitchen ɗin, Samha ta sanfe da wine tana dariya '' tsuntsu daga sama gasashshe '' Azeezah ta biyo bayan Samha tana zaginta asking her to return the wine Amma Samha taƙi.
Rooftop Samha ta hau,tana kallon taurarin da sukayi ma sama ado,ga wani daddaɗan iska mai sanyi da daɗi dake kaɗawa, rooftop ɗin was dim lit ba haske sosai amma hasken dake wurin ya isa mutum ya hango tituna,sauran gidaje da kuma manya manyan gine gine, the view was beautiful and satisfying... flipping Gashin ta Samha tayi moving forth, wurin glass ɗin da aka zagaye wurin dashi ta gaba ta isa tana leƙa ƙasa,wurin nada nisa sosai.'' nan idan mutum ya faɗo sai lahira '' ta faɗa tareda zama tana turo ƙafafunta gaba, gashinta abin iska, she should have been scared but she wasn't... Ajiyar zuciya ta sauke tareda buɗe kwalbar wine ɗin ta zuba a cup tasha wani irin sorrow engulfing her heart,she missed their old life, she missed her parents jitayi wine ɗin yayi mata daɗi don haka ta ƙara wani cup tana sipping slowly..
Ƙamshin turaren sane ya cika mata hanci,da farko ta ɗauka kawai hancin tane but the scent persistently stayed in her nose, juyowa tayi with slightly drowsy eyes tana kallon shi as he approaches,
Da farko bai san da ita a wurin ba saida murfin wine ɗin ya faɗi making noise ɗago kanshi yayi ya kalli direction ɗin zuciyar sa saura kaɗan ta fito ta bakin shi,idan mistakenly ta faɗi she could die.. ɗauke idon ta samha tayi ta ƙara zuba wine ɗin for the third time tana sipping tana kallon nesa, memories ɗinsu na dawowa cikin ƙwaƙwalwar ta daga day one har ƙarshe.. hawaye suka taru a idonta,'' My Lady...'' Ahmad ya kira gently juyowa Samha tayi looking at him with intoxicated eyes '' Ashe kaine..'' tayi maganar da muryar maye... Ahmad was stunned Ina tasamu alcoholic wine? Saukowa Samha tayi hannun ta riƙe da bottle ɗin wine ɗin clutching tightly onto it kamar za'a ƙwace mata,miƙa hannu Ahmad yayi zai karɓa ta ƙi bayar wa tana hararar shi, wasu kujeru da table ta hango tayi wurin da sauri tafiyar ta pretty normal Dan wine ɗin bai wani fara aiki ba, Binta Ahmad yayi asking her to bring the bottle taƙi,zama tayi ta ƙara zuba ma kanta acikin cup tana sipping,zama Dr Ahmad yayi ya bita da ido kawai.. fuskar ta doesn't look intoxicated... Amma idon ta? Sun wani ƙara sirancewa, shape ɗinsu ya ƙara fitowa and she looked sleepy, ajiye cup ɗin wine ɗin tayi tana kallon Ahmad dake kallon ta,yanzu suna cikin haske.....
WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁 🍁
Chapter sixty four: The best thing...
Lumshe idon ta tayi, emptying the bottle of wine cikin cup ɗin da sauri Ahmad ya ɗauke kafin ta rigasa,turo baki tayi tareda miƙa hannu '' Bani!" Ta faɗa tana zaro mai ido as if to scare him, girgiza kanshi yayi kafin ya miƙe ya isa railing ɗin ya saki cup ɗin ƙasa,da sauri Samha ta iso daidai cup ɗin na kaiwa ƙasa ya tararratse, sweeping ɗin Gashin ta tayi backwards ta juyo tana kallon Ahmad angrily,shima yana kallon ta da Muryar maye tace '' kai.. ma kayi tsalle..kaje ka dawo min da wine ɗina '' ta faɗa glaring hard at him, girgiza kanshi yayi ya matsoeya riƙe hannunta '' mutafi ciki!'' ƙwace hannun ta Samha tayi tana ja baya, Ahmad ya tsaya yana kallon ta pressing his lips together,bai so sauran mutanen gida su san abinda ke faruwa he'd rather take her inside yanzu kafin wani ya ganta,ƙara riƙo hannun ta yayi yana faɗin '' let's go inside my lady '' gantsara masa cizo Samha tayi da sauri ya sake ta yana yarfe hannu, komawa tayi ta jingina da railing ɗin gashin ta nabin Iska tace '' idan zaka tafi,ka tafi..i won't go back where I get nothing but pain...'' Ahmad yayi shiru yana sauraren ta,baro railings ɗintayi tana takowa with uneven steps tazo ta tsaya kusa dashi,idon ta cike da hawaye tana nuna saitin zuciyar ta tace '' it hurts alot..tunda na taso right from child hood,I have only ever received pain...you know...da farko i thought I could bear it..but I was wrong...na kasa jurewa!" Tayi maganar slowly tana share hawayen daya silalo mata, Dr Ahmad kuwa ya kafe ta da ido his expression unreadable,cusa hannun ta tayi cikin gashin ta turning her back to him ta cigaba da faɗin '' i tried so hard don inga ban buƙaci kowa ba,i pretended to be cold and heartless just to avoid getting hurt... Amma na gudu