Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   64 / 69

189K to 192K   out of 206.1K words

cire kaya zuwa. . . .!!😳

Samha data gaji da zama a parlor ta juya Idonta dramatically ta kashe komai tana faɗin '' kullum sai a dinga barin mutum shika ɗai ba sallama!"
Kitchen ta tafi ta sha ruwa can ta hango ƙaton wata fari sal.. murmushi ne ya suɓuce mata tuna ranar da Ahmad yayi confessing soyayyar shi '' i love you so much Samha '' Samha ta lumshe idonta remembering the past ta wani ƙanƙame kanta tana murmushi kafin ta fara dariya fitowa tayi hannun ta Haryanzu zagaye da jikin ta '' i love you too!" Ta furta tareda Lumshe ido '' really?" Taji Muryar sa daga gefen ta da sauri ta buɗe idonta and he was there dawani charming smile a fuskar sa, Samha take kallon shi ba ƙiftawa kamar ta samu tv how did he get there? '' suprised?"

Ya faɗa in cool voice fuskar sa dab da Tata Matsawa baya tayi kamar zata faɗi bai yi ƙoƙarin taro ta ba like he would, bayan ta miƙe tsaye da kyau ya matso dab da ita yet again holding her waist yayi tilting kanshi tare da turo baki gaba in a pouty way
idon shi lumshe ganin hakan yasa Samha yin irin yanda yayi going in for a kiss...ji tayi ta kusa faɗuwa da sauri ta buɗe ido

Sai kuma ta rufe fuskar ta tana yar dariya ''shame on You Samha '' ta furta cike da shauƙi,ashe mafalki ne ,ta daɗe tsaye wurin kafin ta koma ciki daidai wayarta na tsuwa

Kwantawa tayi taja blanket rabin jikinta till she was comfortable sannan ta ɗauki wayar her heart hammering in her chest tayi picking

'' My lady!" Sassanyan Muryar sa came, ƙara ƙanƙame blanket ɗin Samha tayi,batasan Abinda ke damun ta ba but these days Muryar sa na haifar mata da wani irin feeling...she can't figure '' Uhm'' cije leɓensa na ƙasa Ahmad yayi his eyes shining in the dark

'' bakiyi Bacci ba?" Muryar sa ta ƙara shiga kunnen ta, Runtse idonta sosai tayi '' Uhm'' ta sake amsawa ɗan shafa kanshi Ahmad yayi tare da gyara zaman shi on the bed '' Thinking of me?" Samha ta buɗe idonta not knowing what to say '' Uhmmm?" Ta turo baki tace '' Ni bacci nake ji Saida safe!" Damn! Kwantawa Ahmad yayi yaja wani numfashi kafin yace slowly '' Good night my lady '' Samha batayi tsammanin hakan ba she thought zasu daɗe on the phone,while Ahmad would rather end the call to save him self!

'' Good night '' ta faɗa har zata katse kiran taji yace '' Dream of me... I love you!" Daga haka ya katse kiran, rungume wayar tayi a very radiant smile on her face “ I love too!”
Ajiye wayar tayi laying down properly...

Kwanakin da suka biyo baya cike suke da farin ciki, kullum da daddare sai Amreesh da Salmah sun fita kamar da,

Samha da Ahmad kullum da daddare sai sunyi waya their love blossomed very beautifully, their love for each other cannot be contained.. haka ma salmah da Amreesh,irin ƙaunar da suke nuna ma juna? It's hard to forget

Tsaye take a gaɓar teku tana kallon ruwa in sun yo gaba suyi baya,ga wani sanyi da iska masu daɗi, Daga gefe kaɗan mutane ne saboda Beach ne wurin,akwai masu sayar da abubuwa duk da dare ne,kamar ice cream,burger,suya da dai sauran street foods ɗinnan faɗin irin farin cikin da take cike bazai misaltu ba,ga taurarin da suka ƙawata sama da wata,hayaniyar mutanen dake wurin mafiyawanci couples made the place even more lively she loves every moment she spent with Amreesh, luckily koda yaushe sai ta ɗauki hoto for the sake of memory.....

Juyowa tayi taɗan kalli Amreesh dake tsaye wurin ice cream vendor tun tuni ya tafi amma har yanzu bai dawo ba
Saboda yaran da suka dabaibaye wurin,idan an kusa miƙo masa sai kaga yaro ya rugo ya karɓe at this point ji Amreesh yake kamar ya saye wurin duka

Saura yaro guda gaban shi har yana murna,sai ga wasu yara su biyar sun iso wurin ice cream vendor ya kalli Amreesh helplessly ganin yanda Amreesh ke hararar yaran '' they're just kids...dan Allah kayi haƙuri...'' bayan tafiyar wa'yannan yaran Amreesh ya faɗi flavor ɗin da yake so finally ana miƙo mashi wani yaro yazo ya cafe zai tsere Amreesh ya damƙi fisgo rigar yaron daya kasance Bature, ice cream vendor dai ya tsaya yana kallon ikon rabbi

Rage tsawo Amreesh yayi ya dawo daidai yaron suna kallon juna cikin ido '' Naka ne?" Amreesh ya tambaya with a cold voice,shima yaron blankly yake kallon Amreesh kafin yace '' Kai naka ne?" Amreesh was stunned ganin haka yasa yaron ɗaga gira guda as if challenging him sakin yaron Amreesh yayi ya miƙa hannu zai karɓi ICE cream ɗin gani yayi yaron ya saki ice cream ɗin ya faɗi ƙasa

And there was another long line, Amreesh gritted his teeth yaron slowly yace '' when I took the ice cream you should have let it go sai ka karɓi wani lokacin ba mutane,amma yanzu kaga kayi biyu babu baka samu ice cream ba... kuma mutane sun sake cika wurin do You know why?" Amreesh yayi shiru Yana sauraren yaron his words were making sense yaron ya cigaba da faɗin '' saboda mutane often think they're in control...so they waste time!" Daga haka yaron ya kama gaban shi, Amreesh ya daɗe duƙe a wurin,abinda yaron ya faɗa....was he perhaps thinking he had time with anonymous? Da ace yayi maganin komai from the beginning...would things have been different?

Miƙewa yayi jiki saɓule just in time message ya shigo

“ _Tik_ _tok_ ⏰ _Tik_ _tok_ _Tik_ _tok_ ⏰, _time_ _is_ _slipping_ _Emrys,few more days!_ ”
“ _Anonymous_ ”

Amreesh ya tsare wayar da ido longer than he should, it's slipping out of his grip,komai yazo masa a bazata,da a dane,da ba shida wani fargaba ko shayi,but at this point...ɗago kanshi yayi ya kalli Salmah dake masa waving looking so happy yayi ƙasa da idon shi,someone precious was involved.. someone he would fight the whole world to keep,Nan da nan wani quote da maman su ke yawan faɗa musu ya shiga yawo akan shi '' When there's love... why fear? So ya zama shine mafi girman ƙarfin mu ba rauni ba!" Maimaita kalaman yayi and his eyes instantly lit up komawa wurin vendor yayi ya yima yaran cin layi ya karɓi ice cream ɗin yabar wurin

Ya kawo ma salmah and the two of them shared it, he was very happy ya tabbata now more than ever zai yaƙi anonymous with all he's got!

Finally sai wurin sha biyu suka koma gida bayan sun ɗauki hotuna da yawa!
*********.
Zaune yake acikin office ɗinsa wani uban ciwon kai na nuƙurƙusar shi,ya rasa yanda zaiyi kawai sai ya kife kansa a saman table ɗin
Dr Haleema ce ta shigo hannayenta ɗauke da files '' Dr ba lafiya ne inata magana ba amsa?" Tayi maganar cike da ƙwarƙwasa ɗago idon shi da sukayi jaa Ahmad yayi ya kalleta and her heart skipped '' headache!'' ya faɗa shortly kafin ya mayar da kansa,wani irin daɗi Haleema taji Finally her wish is about to come true batareda ɓata lokaci ba ta zura hannu cikin farar coat ɗinta ta Ciro pills farare guda biyu '' paracetamol '' ta faɗa tare da riƙe hannun shi ta saka masa ciki,His hand was so soft kamar karta saki, Ahmad ya ɗago kanshi jin ta taɓa shi he didn't like it, basarwa tayi ta ɗauki gorar ruwa dake saman table ɗin ta cire murfin ta bashi,ba musu ya karɓa cuz he didn't want to talk much

Ganin yasha maganin Haleema taji kamar an biya mata kujerar Makka,damn! Farin ciki kamar ta zuba ruwa ƙasa tasha

'' Bara in Barka ka huta!" Daga haka ta fita tana Tsalle tsallen daɗi directly office ɗin ƙawarta Ameenah ta tafi ta bata labarin komai...Dr Ameenah wasn't happy Amma sai ta danne.

Ahmad ji yayi yana jin bacci sai ya miƙe ya ɗauki key ɗin motar shi ya fita daga asibitin gidan shi ya tafi directly...

Wurin ƙarfe tara ya tashi daga Bacci daya kwashe shi, toilet ya shiga yayi wanka yayi sallolin da ake binshi,bayan ya gama ya tuna yana buƙatar wasu files kuma suna gidan Amreesh miƙewa yayi ya sake ɗaukar motar shi ya fita



09:00pm

'' Bye!" Samha ta faɗa lokacin da taga motar su Amreesh tayi reverse,bye bye Salmah tayi mata daga ciki kafin motar ta fita daga gidan duka... komawa ciki tayi zuwa ɗakin ta

Motar su Amreesh na fita da minti goma ta Ahmad ta danno kai,ji yayi zuciyar sa na skipping haka kawai parking yayi ya fito walking slowly ga wani yanayi daya dabaibaye shi, kamar kasala kasala,kamar zazzaɓi oho shidai bai sani ba, ga wani uban zafi da yake ji daga ciki har waje ɗan dakatawa yayi trying to figure out what was wrong?

Cigaba da tafiya yayi after a while yana kawowa tsakiyar parlorn da baida haske sosai ya tsaya Tare Da dafe marar shi jin sharp pain a wurin,idon shi ya ƙara wani irin girma saboda abinda ya gani...he had an erection! Abin ya bashi mamaki sosai tunda shidai bai sha wani abu ba kuma bai ga komai ba ' Ya Allah ' ya furta walking slowly a dafe ya samu ya isa ɗakin shi

Toilet ya faɗa ya sakar ma kanshi ruwan sanyi amma maimakon yaji sassauci sai abinda yayi gaba ji yayi kamar jikin sa was on fire! He only wanted one thing...da sauri lumsassun idon sa suka buɗe sunyi wani irin azababben ja...
*****

Kwance Samha take tana tufka da warwara kafin ta miƙe firgit wardrobe ɗinta ta nufa ta duba kafin ta gano sky blue ɗin agogon da ta taɓa siya lokacin da Ahmad ya kaita tayi siyayyar zuwa makaranta dama don shi ta sai agogon kawai murmushi tayi tana rungume agogon '' bara in je in ajiye a ɗakin sa i will confess my love on new year!" Samha ta faɗa cike da farin ciki tana yar ƙaramar dariya

Saye take da riga fara t shirt iya rabin cinya sai pant red color,rigar taɗan kamata daga hips Dan tana Da hips Masha Allah brown hair ɗinta a sake... Her rosy scent rising in the air tayi kyau sosai

Fita tayi agogon riƙe a hannun ta ɗakin Ahmad ta shiga kamar kullum ɗakin ba haske sosai amma ko ina tsab tsab, ga ƙamshin sa daya cika ɗakin rufe ƙofar tayi ta isa gaban madubi ta ajiye agogon da kyakkyawan murmushin daya kasa barin fuskar ta, turarukan dake wurin ta kalla kamar ta ƙara sai kuma dai tabar shi ji tayi an buɗe ƙofar toilet da wani uban sauri ta juyo suka haɗa ido, ƙugunshi ɗaure da towel his sleepy eyes sun wani ƙara lumshe wa da ƙanƙancewa fiye da kullum wani matsiyacin kallo yake Binta dashi daga sama har ƙasa

Samha taji zuciyar tana bugu fiye da ƙa'ida,she didn't know he was around!

Ahmad kuwa ya dinga jin wani magnetic pull towards her,duk yanda yaso yayi controlling kanshi ya kasa '' My lady?" Ya furta da wani irin intoxicated voice yana Matsawa inda take idon shi na Lumshewa suna buɗe wa at the same time

Ganin yanayin shi yasa Samha ta fara matsa wa baya ido waje.... Yanda taga yanayin shi ta mugun tsorata hanyar ƙofa ta kalla and she moved towards it jiki na ɓari,saurin cafkota Ahmad yayi ta hanyar riƙe tsintsiyar hannun ta ya jawo ta da ƙarfi trying to hug her,kuka Samha ta fashe dashi ganin riƙon da yayi mata bana wasa bane and no matter how much she tried she couldn't escape

Ahmad kuwa abinda yake ji ƙara ninkuwa yake har ma ƙila idan bai yi ba he'd die

Ƙoƙarin rungume ta yake ta turje tana kuka '' Pls Samha '' ya roƙa yana sakin Gwauron numfashi girgiza kai Samha take hawaye na wanke mata fuska fasalta tashin hankalin da take ciki at this moment ɓata lokaci ne

'' Dan Allah kayi haƙur...'' samu yayi ya haɗe bakin su yana sauke ajiyar zuciya ya manne jikinsu ya mugun fita hayyacin shi, Samha ta shiga kiciniyar ƙwace kanta thrashing and kicking but it was of no use

Saida ta samu ta shure shi a gefen ciki da ƙafarta sakin ta yayi ya ɗan ja baya ya watsa mata rinannun idanun shi, jikin shi na wani tsuma,da wannan damar Samha ta taka gadon ta tsallaka towards the other side zata tsere har ta kusa fita ya damƙo gashin ta ta baya ya jawo ta da ƙarfi ta dawo jikin shi ya rungume ta ta baya pressing her hard against himself
Samha tayi ƙasa da bakinta ta gantsara masa cizo which had had no effect,baya yayi ya faɗa saman gadon da ita kafin yayi flipping ta dawo ƙarƙashi tana kuka tana cigaba da ƙoƙarin ceton kanta

'' Not today My lady...''


Ahmadu?? Wetin be dis?😳
Samha you don enter one chance!😬

Comment and share pls

WAYE SHI?(Behind the mask) Book 2 paid book ne ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin 9138091955
SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number+234 9138091955























WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17🍁🍁

https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt

Chapter Seventy nine:Broken hearts....


***Pah***

Zaune yake bakin gado abin duniya yabi ya ishe shi idon shi sunyi ja amma ba hawaye sai dai kukan zuci hannu ya miƙa ya ɗauki wani frame dake bed side drawer hoton wata mata ce da take tsananin kama da Amreesh komai nasu ɗaya except ita mace ce shi na miji gashin ta blonde a hoton
'' So sorry....so sorry hazel,I failed...na kasa kula da ya'yan mu,na faɗi a matsayina na uba!" Yayi maganar idon shi na kawo ruwa she was his wife maman Amreesh...ta daɗe da mutuwa yet he couldn't move on,ya kasa mantawa da ita!

Turo ƙofar tayi da ƙarfi ta shigo tana tafiya majestically da wani makirin murmushi a fuskar ta '' well well, The Loyal husband still hasn't n't moved on from his first wife?" Zama tayi kusa dashi har yanzu murmushin a fuskar ta ta miƙa hannu zata karɓi hoton da sauri Pah ya janye hannunshi holding tightly on the picture, murmushin dake fuskar ta ya ɓace ta wani haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba

'' kasan na tsani wannan abun da kake ko? Why can't you see me? Niba mace bace? Meya sa baza ka ganni ba!" Tayi maganar seriously da ciwo a Muryar ta

'' because you're not Hazel!" Ya mayar mata fuskar shi a tsuke idon shi void of emotions

Miƙewa Hajiya Maleeka tayi tareda shaƙe Pah ta karɓi hoton ta wurgar ya tararratse bayan ya daki bango '' You dared to say that to my face Yousuf?" Ta furta eyes blazing with fire tana ƙara pressure akan riƙon data yima wuyan Pah '' naga kwanakin nan har wani affection kake nunawa shegen yaron nan ko? Toh wallahi wallahi sai na saka kayi na damar abinda kayi! Amreesh ko? Kasa aranka kai da shi haihata haihata!" Ta ƙarashe maganar tareda dungunar da kan Pah ya daki headboard,Pah nata jan numfashi da sauri sauri don ba ƙaramar shaƙa yaji ba

Slowly ya miƙe jiki ba ƙwari ya isa inda hoton shi,ɗauka yayi ganin frame ɗin na glass ne kawai ya samu matsala

Hajiya maleeka tayi tsaye hannun ta riƙe da ƙugunta tana kallon Pah zuciya cike da baƙin ciki '' You may rid the memories of Hazel from the surface Zainab,but har abada Hazel tana cikin zuciya ta she lives there! As for Muhammad...'' ya dakata yana kallon ta ganin ta cika tayi fam murmushi yayi me kyau wanda ya bayyana kyaun shi ya kauda kai ya mayar akan hoton yana shafawa '' Ubangijin shi na tare da shi!" Fita Hajiya Maleeka tayi fuuuu zuciyar ta cike da ƙunci,all she had worked for na tsawon shekaru bazai tafi ga banza ba wallahi!
********

'' Dan Allah ka bari Ahmad.. don't do this to me pls!" Samha ta roƙi Ahmad desperately ganin yanda ta koma ƙarƙashin shi,he was heavy,stronger and muscular ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane, Samha ta gane cewa wasu lokutan koya ka kai ga iya kare kanka there are certain situations that you will always be at the receiving end kamar dai yanzu, hawaye suka cigaba da wanke fuskar ta it didn't happen when she was in china...it can't happen here!
'' I can't... I need you!" Yayi maganar yana sakin yar ƙara, Samha ta tsorata beyond words romancing ɗinta ya fara kukanta ya ƙara ƙarfi,haɗe bakin su yayi swallowing her cries his hands ravaging her body wani ƙunci ya cika zuciyar Samha,at this point ji take kamar Ahmad wasn't any better than Cheng xiao infact ji take kamar xio yafi Ahmad cuz shi atleast ya nuna maitar sa a fili....'' You can't do this...'' ta faɗa in between the kiss, zuciyar Samha ta kusa bugawa jin hannun Ahmad a ƙirjinta kafin slowly yayi ƙasa da hannun shi ya zare pant ɗin jikinta

She felt lifeless and abused for the unpteenth time Amma wannan yafi ciwo cuz Wanda ke mata hakan is the same person dake waƙen yana sonta,da gaskiyar Adrian da yace ta fara sanin waye shi first before she agrees to be with him...and her silly heart had fallen head over heels for him! Duk da babu wani sauran hope na tsira daya rage ma Samha ganin dai da gaske Ahmad illata ta zaiyi yasa ta fara kokuwa tana haɗawa da addu'oi

Shiko Ahmad bai masan inda kanshi yake ba ya fita hayyacin shi ya zama kamar wani bugagge zuciyar shi sai gudu take da ƙarfi, he had always had strong sexual drive kuma sai ga pills ɗinda Haleema ta ƙara mashi truly hakan zai iya yi masa illa

Acikin zuciyar shi kuwa sai haƙuri yake ba Samha shima ba da gangan yake ba,ƙara mayar da himma yayi zai shige ta Samha tayi wani ihu then hitting his throat with her elbow

Jini ne ya fito daga bakin Ahmad kafin ya faɗi gefe sumamme, Samha bata jira komai ba jiki na rawa ta tsere daga ɗakin,ɗakinta ta faɗa tasa key ta zare key ɗin tsabar ruɗewa ta sake

64 / 69