Author : Nimcyluv Category : Complete Novels
yanzu shikenan idan ba'a yi Sa'a ba haka ita ma Samha zata ƙare kamar sauran yan matan? Andrew dake zaune daga gefen su ya ɗan langwaɓar da kansa gefe with a smirk, idan har Mathew zai iya winning ɗin yarinyar cikin sauƙi har haka ke nan shi....
Mutane kam sun yi tsuru tsuru da ido wasu already sun fara tausayin Samha wasu kuma na ganin the drama she staged was just to get attention.
Mathew ya fara circling ɗin hannunsa a shoulder ɗin Samha yana gangarawa zuwa tsakiyar bayan ta,har yanzu murmushin nan kwance yake a fuskar sa. Ita ko samha tsabar mamaki ta kasa motsi, Ra'esah da fateemah ji suke kamar suyi kuka they wanted to help Amma babu yadda suka iya. Atunanin su Samha ta kasa komai ne saboda tsoro.
Emmanuel da chibuke suka haɗa ido kafin su wani sakar ma juna murmushin gefen baki, Emmanuel cikin harshen turanci yace '' Shegiyar yarinyar tazo hannu, daga taɓa ta har ta haw network '' chibuke yace ''i trust Mat to handle any girl''suka kwashe da dariya.
Ranƙwafowa Mathew yayi yace '' you're such a sexy girl, come to my room let me take care of....'' wani irin wawan ihu Mathew ya kurma kamar wata mace yana ja da baya sakamakon guiwar hannun ta da Samha tayi amfani da shi ta buge masa baki da iya karfin ta,jini ya fara zubowa
Once again the cafeteria was noisy,the Christian were busy shouting Jesus Jesus!!
Musulmai na faman faɗin innalillahi suna taɓa hannu
'' wannan yarinyar kanta na hayaƙi''
''Kai amma yarinyar nan bata da hankali ''
''who exactly is this girl ''
'' it seems like the girl has a death wish''
Waɗannan sune maganganun mutane. Su Ra'esah ko sun ma kasa motsi, their body froze who exactly is Samha? Wannan confidence daga ina. Wani irin fitsari Ra'esah da fateemah suka ji ya matse su lokacin da suka ga gabaki ɗaya members of dark flames sun zo table ɗin su.
Yanzu kam cafeteria everybody was holding their breath, mutane suna jiran suga abinda zai faru da Samha,
Ƙarasowa suka yi dukan su, su ukun suna Faman huci kamar wasu zakuna, wurin Mathew suka isa suna yi masa sannu, ɗaya daga hauren sa har ya fito, sai zage zage yake,shi wallahi ba zai ƙyale samha ba, suma sauran suna taya shi. Duk abunnan da ake Samha tana ji, amma bata damu ba. She really didn't give a damn.
A fusace Emmanuel yayo kan Samha ,dama shi yafi sauran zuciya fitsari ne ya fara zubo ma Ra'esah da fateemah, their body was shaking saboda tsabar tsoro,
Murya na rawa Fateemah tace '' Samha yana zuwa fa...'' laumar abincin gaban ta Samha ta kai baki kafin tace, '' Barsa ya ƙara so ya karɓi rabon sa''
Miƙewa Samha tayi tana fuskantar Emmanuel da yake naɗe hannayen rigar sa kaman zai yi faɗa da ƙato, his face looked so frighteningly ugly mutane har sun fara hasaso Samha a clinic, tuni masu cin abinci suka da kata da cin abincin su, suka koma kallon free live movie
Ɗaga hannun sa Emmanuel yayi zai wanke Samha dake tsaye hannu naɗe a ƙirji da mari when suddenly '' What's going on here?"
Duka juyawa akayi towards the direction of the voice,it was principal, bayan sa wani dogon baƙin ba samude, fuskar sa ba annuri ko kaɗan,shi baƙi kayan sa baƙaƙe from head to toe, it was Mr kanya the discipline master,ana matuƙar tsoron sa. Da ba dan yana wurin ba da babu abinda zai sa a nutsu wurin yayi shiru, ga tsawo ga ƙiba, ga mugun ta,ana matuƙar tsoron mr kanya a makarantar nan and he's impartial,idan ya kalli mutum sai mutum ya kasa numfashi,kuma You can never get used to his punishments.
Sauke hannun sa Emmanuel yayi a gefen sa, yana hararar Samha da ta ɗage gira guda as if asking 'meya hana ka?'
Emmanuel was pissed off, suma sauran mutane ba haka suka so ba.
Ganin anyi shiru,no body was willing to talk yasa principal ya ƙara so cikin cafeteria ɗin mr kanya biye da shi. Just now an anonymous student yaje ya faɗa masa abinda ke faruwa shine ya baro office dinsa yayo wurin tare da mr kanya, tsaya wa suka yi a tsakiyar cafeteria ɗin principal ya fara kallon students ɗin yana karantar su, kowa tsoro ya bayyana a fuskar sa, his gaze lingered on Dark flames Andrew da chibuke sun ɓoye Mathew a bayan su, cuz it will be a shame ace Wai mace ce tayi masa wannan lahanin, Mathew ko bakin sa ya wani irin sunkucewa kamar an kwaɓa flower. Zuciyar sa tafar fasa take sosai. Maida idon sa principal yayi akan Samha, instantly ya gane abinda ke faruwa, ya kuma yi mamakin ganin Samha da wando tunda su dai a iya sanin su females were to wear skirt. Dama shi Mr kanya tun lokacin da suka shigo ya kafe Samha da ido, ganin yanda yarinyar ta tsaya hannu naɗe a ƙirji ta wani tsuke fuska, jin kamar ana kallon ta yasa Samha ɗago idanun ta suka shige cikin na mr kanya da suke kanana kuma baƙaƙe farin ciki kam yayi ja har ya gaji, mr kanya ya ɗauka za taji tsoro tayi ƙasa da idon ta or at least ta gyara tsayuwar ta amma to his surprise sai itama ta kafe sa da ido, ƙan ƙance idon sa yayi itama Samha tayi yanda yayi tana turo baki a ranta tana faɗin 'ƙila ma maye ne yake wani kallo na haka, salan in ban rama ba ya lashe Ni, to aniyar moɗa tabi randa, kurwata kur ehe' ta ƙarashe tunanin tana murguɗa baki da fari da ido, mr kanya was astounded, no student had ever looked at him the longest as she did, ga yarinyar ba alamun tsoro tattare da ita,
Har principal yayi magana ya gama Samha da kanya were engaged in eye contact,shi Mr kanya ko ƙiftawa bai yi,ita ko samha idan ta gaji ta ƙifta sannan ta cigaba.
'' the school will not tolerate indiscipline of any kind from u students, Dan haka kowa ya kiyaye kansa idan ba haka ba zaku fuskanci horo mai tsanani daga hukumar makaranta. '' ya ƙarashe maganar yana kallon dark flames, kowa ya sadda kai banda Samha da bata San abinda ake yiba.
''Ms Aliyu'' principal ya kira,da sauri Samha ta matso kusa ya kalle ta daga sama har ƙasa kafin yace '' i assume you've read the rules and regulations of the school?'' jinjina kanta Samha tayi yacigaba da faɗin '' You have broken the rule of uniform, Amma za'a maki lamuni being a new student,daga gobe ki fara sa uniform ɗin ki kamar yanda makaranta ta tana da '' ya ƙarashe maganar yana kallon ta intently mutane sai jinjina kansu suke alamar gamsuwa da abinda principal ya faɗa, sadda kanta Samha tayi sannan tace '' I'm sorry I can't sir'' waro idanu students sukayi suna exchanging glances, Ra'esah da fateemah at this point sun fara jima Samha tsoro, saboda mr kanya dake tsaye wurin what if she gets punished?
Kafin principal yace wani abu mr kanya dake tsaye wurin, cikin Muryar sa me amo yace'' why can't you?" Ɗagowa tayi tace '' saboda bansa ba bi kwararo kwararo ina yawo da guntun kaya ba, this is a school not a place to seduce I believe zuwa da ƙaramin skirt that barely covers when their is the opposite gender in their early adulthood don't u think it's concerning? Idan daya na iya controlling ɗin kansa, wani zai iya?'' tayi tambayar directly tana kallon cikin idon mr kanya
At this point students, ƙarfin halin Samha ya dena basu mamaki,yanda take yaɓo maganganu as if she has a powerful back up? Shima principal yayi mamakin jawabin Samha babu wanda ya taɓa ƙalubalantar dokar makarantar sa,kuma da gaskiyar yarinyar idan ya auna,
Jinjina kansa yayi,zai sake magana aka yi ringing ɗin bell, dismissing ɗin kowa yayi to their classes sannan ya fita.
Mutane su ma suka fara tafiya to their various classes duk wanda zaka ji suna magana to akan abinda ya faru ne. Fateemah da Ra'esah na cikin yan kaɗan ɗin da suka rage basu tafi ba, gabaki ɗaya dark flames suka juyo suna kallon Samha wani irin kallo Mai ma'anoni
Chibuke daga inda yake yace '' it's not over yet MS fiesty,you don't know what you're in for, you have turned the slow burning *DARK* *FLAMES* into a blazing inferno and it will consume, you mark my words'' Andrew ya ƙara da faɗin '' it has just begun, wait for our retribution '' ya gama maganar yana kallon ta cike da tsana '' Emmanuel yace '' it's not over '' jikin Ra'esah da fateemah yayi sanyi sosai,sun tsorata matuƙa. Not just them mutanen dake jin tausayin Samha sun jimata tsoro, Samha cikin halin ko in kula ta matso kusa da chibuke, ya fita tsawo hakan yasa ta zama ƙarama gaban sa amma bata damu ba tace '' When I My self I'm a *FIRE* why should I fear a flame? What ever you think you have,I have got the best of it..'' matsawa tayi daga baya tana kallon su duka sannan tace '' it's not over, and I'm glad, if it was I would have been the saddest, *Samha*is not *afraid*'' ta ƙarashe maganar tare da jan hannun Ra'esah suka fita.
Iska Andrew ya kai ma naushi,'' dole muka wo karshen yarinyar nan a makarantar nan,her nerve is too much ''
Mathew da bakin sa ke masa wani irin zugi yace,'' idan ban wulaƙanta yarinyar nan a makarantar nan ba, hankali na bazai kwanta ba!!" Ya ƙarashe maganar cike da ƙaraji
Yan uwansa suka fara kwantar masa da hankali before they led him to the clinic
************Amreesh*
*A* *ZAKEE * CONSTRUCTION COMPANY
wani irin ƙaton gini ne gari guda, bayan sa akwai wasu gine gine guda huɗu gefe da gefen sa, hakan yasa it stands in the middle daga gaba,
Ma'aikatan cikin kowane daga gine gine sai kai kawo suke, yau BOSS zai dawo, kowa ya kama aiki dan ba ƙaramin aikin sa bane, yana shigowa ya kalli mutum sai dai kaji yace '' you're fired" so they are afraid for their jobs Dan ana biyan su sannan ga allowance.....
Turo kofar akayi, Amreesh gaba Secretary Ayman biye da shi riƙe da tarkacen sa, fuskar sa a mutukar ɗaure ba wasa tattare da shi, da sauri ma'aikatan suka tashi suka fara miƙa gaisuwa, directly elevator da zai kaisa top most floor ya shige dama kuma it was designed just for him.
thumb print ɗinsa yasa and the door to his office widened revealing a luxurious office komai na ciki Black and White cottons,sofas, couches....
Shiga yayi yacire suit ɗin sa ya rataye a bayan seat ɗinsa, despite it being clean sai da ya ɗauko handkerchief ya goge sannan ya zauna, few minutes later Secretary ya biyo sa da kayan sa, buɗe laptop ɗin gaban sa yayi ya fara danne danne kafin ya tsaya ya ɗago kansa, with a deep serious voice yace '' what's the schedule for today?" Secretary Ayman ya nutsu sannan ya fara karanto masa duk abubuwan dake pending ya kuma kamata yayi attending '' and lastly,diner with old man zakee'' haɗe rai Amreesh yayi kafin yace '' cancel out the dinner '' Ayman zai yi magana kallon da Amreesh yayi masa, yasa yayi gum da bakin sa. He bowed respectfully kafin ya fita. A ƙasa kuwa, ma'aikata sai magana suke akan BOSS ɗin nasu especially the new females suna yaba kyansa wani mai suna ya'u ya taɓe baki yace '' yan wahala, mutumin da baida zuciya shi zaku wani zauna kuna magana akai, wanda idan ya bushi iska tsab zai sa a Kore ki duka, mtscheww ku cigaba Allah yasa ya ji yarunya'' ya ƙarashe maganar yana jan tsaki
Wani abokin sa na taya sa.
***********Salmah
Tun lokacin da Amreesh ya tafi take cikin wani irin yanayi, she missed him and Samha and the house looks emptier, sau dayawa takan ɗauko wayar ta da nufin kiran sa amma mai xata ce masa? Wannan yake sa ta ajiye wayar gefe. Haka ranar ta ƙare Salmah bata ci komai ba,she didn't know what to eat and she wasn't hungry kawai taga nawar Amreesh ya dawo.
Da ƙarfe huɗu ta kalkamta ko ina duk da ba datti, an idea popped up in her mind hakan yasa ta jawo wayarta ta zauna saman kujera ta tanƙwashe ƙafafun ta tashiga dm ɗin Amreesh da tayi saving da REESH
Tayi typing ɗin message kafin ta tura, from time to time take duba wa ko yayi reply amma bai yi ba. She distracted herself by watching all sorts of boring stuffs.
05:39pm
Amreesh ne yake aiki a laptop ɗinsa from time to time yake tsintar kansa da tunanin salmah and he wants to return home, wannan sabon abu ne a gare sa cuz he was a workaholic koda yaushe shine ƙarshen tashi....
Wayar sa ce ta yi haske,he wanted to ignore it but he found his self checking the phone it was against his principles,idan yana aiki ya duba waya.
“𝑀𝐴𝐻𝐸𝐸”
_𝐼'𝑚 𝑚𝑖𝑠𝑠𝑖𝑛𝑔 𝑦𝑜𝑢 𝑠𝑜 𝑚𝑢𝑐ℎ,𝑐𝑜𝑚𝑒 𝑠𝑜𝑜𝑛 𝑖 ℎ𝑎𝑣𝑒 𝑎 𝑠𝑢𝑟𝑝𝑟𝑖𝑠𝑒 𝑓𝑜𝑟 𝑦𝑜𝑢_💖☺️
Kallon message ɗin yake ba ƙiftawa agogon hannun sa ya duba yaga it was 6pm, suit ɗinsa ya ɗauka da wayarsa ya fita , yanzu ma fuskar sa ɗaure, ganin ya fito yasa Ayman bin bayansa suka shiga elevator tare, ma'aikatan suka fara gaida su kamar ɗazu, bayan ficewar su sai ƙusƙus kake ji.... Body guards suka gaida shi respectfully kafin su shiga motar su, suna biye dasu baya
Saida suka ɗauki hanya sannan drivern yayi ma Secretary Ayman alamar Ina zasu? He couldn't ask the boss directly , Secretary Ayman dake zaune gefen driver ya ɗan juya ya kalli Amreesh da ya jingina kansa ya lumshe idanun sa, amma ba Bacci yake ba, kafin Secretary yace wani abu '' Home'' Amreesh ya faɗa a taƙaice Secretary yayi mamaki he wanted to ask to b sure amma ba damar
Haka driver ya fara tuƙasu sai wurin Bakwai suka isa, there was traffic congestion
Koda suka Parker aka buɗe ƙofar saida ya ɗau mintuna kafin ya fita, wayar sa in his pocket. Maida ƙofar driver yayi ya rufe sannan ya shiga driver seat ɗin driving them away. Shida Secretary suna magana akan dalilin da yasa Amreesh dawowa gida da wuri haka its a strange thing. Dan wasu lokutan har office yake kwana idan ko zai dawo gida the earliest is 10:00pm
Yana shigowa Salmah ta rugo da gudu ta rungume sa tana dariyar murna,shima yayi murnar ganin ta sosai,at last he's house has now turned into a home. He hugged her back taking in her scent, Bayan sun rabu tayi murmushi her hands around his neck tace '' sannu da zuwa,miji na, na kai na''
Yanda tayi maganar zai tabbatar maka da tsantsar farin cikin da take ciki shima hakan ya nuna a fuskar sa da take a sake unlike sanda yana office.
Riƙo hannun sa tayi leading him upstairs tana faɗa masa surprise ɗin data shirya musu, though she didn't say exactly what, he was looking at her intently sanye take da jar riga ta material ɗinkin fitted hakan yasa shape ɗin ta ya bala'in nuna.... Suna isa ɗakin sa she begun undressing him tana yi tana faɗa masa how much she missed him, and how bored she was hankalinsa ga baki ɗaya ya tattara akan ta, sai da ya rage singlet da boxers sannan ta tura sa cikin bayin telling him to hurry ita ma zata je ta shirya.
Ko daya shiga, ta riga da ta haɗa ruwan wanka so kawai he stripped sannan ya fara wankan.....
Jallabiya fara ta ɗauko ta ajiye masa kafin ta fita ta koma ɗakin su da Samha wanka tayi ta ɗauro alwala tazo tayi Sallah, nan ta zauna har akayi isha'i
Bayan ta kammala ta koma ɗakin Amreesh ta ɗauko wasu blue colored pajamas guda biyu the same color tasa nata, ta ajiye ma Amreesh nasa,she brushed her hair using his brush ta shafa Mayu kansa da turaren sa. Tana nan tsaye ya turo ƙofar ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, murmushi tayi masa ta madubi ,ciki ya ƙaraso ya rungumota ta baya and they stared at each other ta madubi murya ƙasa yace '' I wonder the surprise....'' ya ƙarashe maganar yana shin shina wuyanta, runtse ido tayi hannun ta saman nasa holding it tightly,
'' we are getting late '' ta faɗa bayan taga ya fara wasu abubuwan can kuma, she really doesn't want to miss on this with a deep voice yace '' can't it wait?" Ta juyo suna fuskantar juna tace '' a'a, I don't want us to miss on this '' ta gama maganar tana gyara masa gashin sa that looked dishelved just now, kayan da ta ajiye masa ta miƙa masa, karɓa yayi idanun sa akan ta, ƙasa tayi da nata feeling shy. Bayan mintuna kaɗan sai gashi ya fito cikin pajamas ɗin, binsa da ido Salmah tayi, faɗin irin Kyan da yayi ma kayan is a waste of time da sauri tayi composing din kanta da murmushi ta ɗauki turaruka ta fara yi masa wanka da su,sai da yace ya isa. She brushed his hair tayi styling ɗin sa in a way that makes him ooze a dangerous aura for the on lookers and a safe one for her.
09:00
Amreesh ne da Salmah suke tafiya in a quiet road surrounded by trees ga iskan sanyi dake kaɗawa gently,the street lamps sun haska ko ina kamar rana, ga wata da taurari a sama, the sight was absolutely breathtaking. Tafiya suke Salmah sai farin ciki take, holding his arm, Amreesh tun da ya girma,he had always been busy hakan yasa bai da lokacin irin waɗannan abubu, he felt a rush of excitement.
Tapping ɗinsa tayi ya juyo bayan sun haɗa ido tace '' ka ga wancan tauraron?" Ta nuna masa wani tauraro dake haske ya mafi sauran haske,jin jina kansa Amreesh yayi tana murmushi tace '' similarly you're the star that lights up my world...''
WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter nineteen:The mysterious man
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?