Author : Nimcyluv Category : Complete Novels
kansa suka miƙe he was groaning in pain...
****
Samha ce tsaye a garden hannayen ta goye a ƙirjinta,saye take da doguwar riga red color sai hular net itama red color ƙafafunta saye da slippers..ta tsare ƙaton watan da ya fito da ido,it reminded her of her pendant iska me sanyin dake kaɗawa didn't bother her at all... She was thinking of something..or rather someone!
'' My lady '' taji muryar sa kamar a mafalki juyowa tayi and she found him standing by the entrance hannayen sa goye a ƙirjinsa,kasa ɗauke idon ta tayi she continued staring da gaske shine ko hallucination take?
Murmushi yayi before he came closer ya hura mata iska a fuska '' Missing me?" Kauda kanta samha tayi tareda matsawa baya, zagaye shi tayi zata bar wurin ya jawo ta hugging her tightly '' I missed you so much '' he said sincerely tareda lumshe idon sa '' don't you miss me?" Ya tambayi Samha bayan ya ɗago ta daga jikin shi '' No!" Simple and short daga haka ta tafiyar ta yabita da kallo utterly puzzled
***********
Tana fita kitchen ta wuce ta ɗau cup ta zuba ruwa gulfing it down several times '' careful...baki ha komai ba,I'm sure you'd wanna save your little butt for what's coming next!" Juyowa Salmah tayi taga mariya saye da kayan bacci a night gown dako cinyarta bata rufe ba, sauke cup ɗin tayi tana kallon ta '' what do you mean?" Salmah ta tambaya looking confused, Ƙarasowa ciki mariya tayi tana tafiya her curves perfectly defined cikin sleeping gown ɗinta, wurin da ake haɗa tea ta nufa tana kallon Salmah da tayi tsayi tana jiran maganar ta,ta wutsiyar ido yar ƙaramar dariya tayi tareda faɗin '' it's nothing...'' ta basar ta cigaba da abinda take Salmah da hankalin ta bai kwanta ba tasake tambayar me take nufi murmushi Mariya tayi ta juyo suna kallon juna with a smirk on her face tace '' bari in tambaye ki WAYE mijin ki? What do you know about him? Me yasa kowa a gidan nan treats him the way they do like he doesn't belong?" Mariya ta jero tambayoyin Salmah ta bita da kallo staring blankly Babu ɗaya daga cikin tambayar da mariya tayi mata da take da Amsa akai,kurɓar coffee ɗin hannunta mariya tayi with a glint tace '' you're so foolish! Baki san komai game da mutum ba yet You married him,Ina hankalin ki yake? Was it his money ko kyaun shine ya ruɗe ki?" Mariya ta tambaya tana ƙara matso Salmah that looked skeptical batasan Abinda zata faɗa ba,kanta a ƙasa ajiye coffee mug ɗin mariya tayi ta ɗago fuskar Salmah suna kallon juna tayi mata murmushi mai kyau tace '' You have no idea what you're in for ms, baki san WAYE SHI ba yet You agreed to be with him..kiyi ƙoƙari kibar gidan nan kafin wa'adin daya ɗibar maki kafin ya kashe ki ya cika!" Mariya ta faɗa Salmah ta ɗago idonta a zare baki na rawa tace '' k..kashe Ni kuma?" Mariya faked suprised '' Oh..Ashe bani Sani ba?" Jinjina kanta tayi tana taɓe baki tace '' lallai kina cikin duhu,let me enlighten you... Amreesh is an occult...yana cikin secret society masu yin kuɗi da jinin mutane,mind you ba kece matar sa ta farko ba the other wives duka yayi amfani dasu to get rich!" Mariya tayi ƙarya a smile of victory filtering her face da taga yanda Salmah ta tsorata tana shaking,da Muryar tausayi ta cigaba da faɗin '' kinga ina son kine yasa nake faɗa maki gaskiya,i don't want you to end up meeting the same fate as the other women!'' Salmah cike da tsoro da kokonto tace '' bu...but me zaisa yayi Hakan?" Mariya ta matsa baya tana kallon outside the window tace '' you think he loves you kuma bazai iya yin hakan ba? That's what he shows his past wives kamar yana son su! Ina taƙaice Mali,mutanen farko da ya fara amfani da su were his mom and brother, shine yasa Pah baya magana dashi, shine yasa kowa a gidan nan doesn't want him around! Idan har zai iyayin haka ga Uwar da ta haife sa who do you think you're?" Salmah at this point was more than convinced har dai data tuna abinda old man Zakee ya faɗa ranar da sukaje gaishe shi that Pah ya manta da abinda ya faru and move on...da kuma dungeon ɗin daya ce Yana kai mutane... Hawaye suka fara bin fuskar ta she felt conflicted... Tsoro ya bayyana a fuskar ta ganin haka yasa mariya tsaya wa bayan ta '' Run while you still can....'' she whispered kafin ta fita daga kitchen ɗin, Salmah ta zube a ƙasa tana kuka she doesn't know what to do ta gudu? Yes abinda zata yi kenan! Yanzu zata tafi su gudu ita da Samha they won't stay!
Miƙewa tayi da sauri ta nufi upstairs khaleel ta gani approaching rawar jikin ta ya ƙaru,nufota yake looking at her lustfully yana Ƙarasowa inda take yayi tsalle zai rungumeta ta kurma ihu tareda ture shi gefe ya daki railing ɗin ya faɗi ƙasa shima ya saki tashi ƙara,da gudu Salmah ta faɗa ɗakin Samha ta haye saman gado tana duƙunƙune Samha, furiously Samha ta tashi tana faɗin '' Innalillahi!" Tare da turo baki,she really hates duk sanda mutum zai wani duƙunƙune ta,gani tayi Salmah na rawar jiki hawaye nabin fuskar ta cike da damuwa tace '' what's wrong?" Salmah ta wani ƙanƙame ta cikin kuka tace '' Samha, we're leaving bazamu cigaba da zama nan ba! He's into blood money...'' Salmah ta faɗa a matuƙar rikice a kuma tsorace '' shi wa?" Samha ta tambaya tareda yin tagumi tana kallon Salmah '' Amreeshhh'' Salmah ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka Samha tabita da kallo '' some body brain washed you?" Girgiza kai Salmah tayi kafin ta faɗa ma Samha duk komai da mariya ta faɗa mata...WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁
https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt
Chapter seventy one: Save me!....
Over the next few days abubuwa tsakanin Salmah da Amreesh deteriorated ko kaɗan bata zuwa inda yake aduk sanda taga yazo wuri sai tabar wurin jiki na rawa tsoron shi duk ya cika ta ji take kamar the next second sai dai ta farka ta ganta barzahu, Amreesh da yayi noticing hakan ba ƙaramin Abu ya tokare masa maƙoshi ba kenan an samu wani munafikin ya hure mata kunne, kallo guda idan kayi ma Amreesh zaka san baida lafiya he looked much more pale than usual sannan yaɗan rame... Mariya da tayi noticing abinda ke faruwa tsakanin Amreesh da Salmah was more than happy,her motive? Undefined! Musamman ranar da Amreesh ya kira Salmah ta saki ihu harda suma kowa aka zo aka taru wondering what happened, Amreesh bai kalli kowa cikin su ba ya ɗauke ta ya wuce ɗaki da ita, when she opened her eyes and saw him close to her ta sake kurma ihu tana roƙon kada ya cutar da ita...He was hurt,he was pained kawai sai ya tashi ya bar ɗakin... Koda ya dawo bata nan, kwantawa yayi ya ja blanket ya rufe har fuskar shi saboda wani azababben ciwon da yake ji a duk gaɓɓan jikin shi! And it went on every night
Tsakanin Samha da Ahmad kuma ita ma wasan ɓuya take da shi batasan meyasa ba,ada batasan wane irin kallo take masa ba, amma yanzu kallon namiji take masa a fully grown up man Wanda take tsananin so da ƙauna...but there's something..itama kuma batasan mey shi ba but it just doesn't allow her to go close,ko ido bata iya haɗawa dashi and idan suna magana sai ta fara ina ina,she feels so shy around him ada duk bata jin wannan....
Dr Ahmad noticed how distant they have grown..a wani gefen yana jin badaɗi cuz he had looked for her for the past 5yrs and he'd just found her kuma zai so su zauna tare yet they are distant..on the other hand yana ganin hakan daidai cuz yanzu abubuwa aren't the same and she looked shy and uncomfortable around...this means her feelings for him have grown stronger...
****** Hajiya Maleeka***
Zaune take a gefen gado saye da wasu baƙaƙen kaya irin na tsafi ko ina dakin duhu ba haske kokaɗan ta riƙe wani sarƙa silver colored tana juya shi a hannun ta,ɗayan hannun kuma riƙe da wani abun surƙulle, murmushi tayi kafin tayi chanting wasu maganganu ta jefa abun yayi sama kafin ya zama kamar tv... Amreesh ne ya bayyana ya dafe kanshi trying so hard to remember abinda ya faru in the past 25yrs ya dafe kanshi dake sarawa kamar zai tsage sosai,a wannan abun da yakeyi There are only to possibilities ko dai ya tuna abinda ya farun ya shiga coma ko kuma yayi losing ɗin memories ɗinsa gaba ɗaya and he could die.because you can't force yourself to remember what you were made to forget.using hypnosis 😵💫.. Murmushin mugunta Hajiya Maleeka tayi ta Kuma taɓe baki tana wani karkatar da kai tace '' Try as hard as you could Emrys...matsawar Ina raye...You won't remember!" Daga haka ta sake chanting ɗin wani surƙullen Muryar ta ta canja da wata ƙatuwar murya ta kira '' EMRYS.....!!!!" Amreesh dake ɗakin shi ya ɗago idon shi yana kallon straight ahead ita kuma a wurin Hajiya Maleeka directly ita yake kallo,sarƙar hannun ta ta ɗago placing it above his eyes ta fara swinging ɗin sarƙar side by side,idanun Amreesh nabin sarƙar idon shi suka juye 😵💫, after a while ta fara '' kai ne silar abinda ya faru a wannan daren..daga yau You won't try to remember abinda ya faru kaji!" Gyaɗa kanshi Amreesh yayi don ba a hayyacin shi yake ba,'' Sleep!! '' ta sake bashi order,Jan blanket ɗin Amreesh yayi ya rufe kanshi ya kwanta,at this point yayi kama da mutum mutumi don controlling ɗinsa take kawai.....
The next day Salmah bata ga Amreesh a dining ba hankalin ta ya tashi cuz over the past few days taga yanda ya rame,he had lost the glow on his face ya zama more isolated and lonely more aloof and cold ɗakin shi ta shiga bata ganshi ba ta fito looking so sad, yaushe ne ma? Ba ita tace zata zauna dashi ba in any condition? Me yasa take gudun shi yanzu? Was her love fake? Cikin garden ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita,miƙo mata ruwa yayi daga bayan ta yana faɗin '' Crying isn't the solution...naga yanda kike gudun ZAKEE over the past few days ba daidai bane,ba lallai ya faɗa maki ba but i can see how much he loves you and you suddenly treating him like this isn't fair...kina wahalar dashi knowingly or unknowingly...'' Juyowa tayi tana kallon Dr Ahmad baki buɗe she didn't know what to say..ƙasa tayi da idon ta,ajiye ruwan yayi ya juya yana faɗin '' make it right..don't push him into further isolation..'' daga haka ya fita daga wurin..zama Salmah tayi tana juya maganar Ahmad acikin ranta...what should she do? Abinda aka faɗa mata fa? Should she just... fashewa tayi da kuka tana dafe goshin ta '' ya Allah '' ta furta desperately not knowing what to do,bata tashi daga wurin ba sai da ta yanke hukuncin abinda zatayi next!
01:00am
Saye take da kayan bacci a pink nightgown da hular saƙa,her cleavage exposed, miƙewa tayi tasa slippers ta fara tafiya slowly kamar ɓarauniya ta nufi hanya '' leaving without a good bye?" Samha ta faɗa suddenly juyowa Salma tayi their eyes met,ƙasa tayi da nata tace '' i have to...ban kyauta da abinda nayi ma Amreesh ba,I broke my promise...I said...'' da sauri Samha tazo ta rufe bakin Salmah '' i understand Mahma and I'm honestly proud of you da kika ajiye tsoron ki gefe kika fuskanci reality!" Hawaye suka zubo daga gefen ido Samha ta share tace '' Hey don't cry..I got you okay?" Jinjina kanta Salmah tayi kafin ta rungume Samha then she left a ɗar ɗar Samha closed the door behind...
Tura ƙofar ɗakin Amreesh tayi ta shiga zuciyar tana ɗarɗar..ganin ɗakin take kamar wurin yan mafiya already her imagination was going wild, hawaye na wanke fuskar ta,ta isa gaban gadon tana leƙa fuskar Amreesh,buɗe idon shi yayi suddenly, zuciyar ta tayi wani uban tsalle kamar zata fito ta baki tayi baya baya ta faɗi, fashewa tayi da kuka Ganin Amreesh ya tashi zaune, pausing Amreesh yayi yana kallon ta with his sick eyes yanda take Matsawa da baya jikin tana matuƙar rawa she looked frightened by him kamar shi dodo ne, Salmah kuwa addu'a kawai take cikin ranta tana matsawa baya ganin Amreesh ya miƙe coming close to her... Sunkuyo wa yayi daidai tsawon ta amma akwai space tsakanin su,ta wani takure heart beating at a wild phase... Bayan kusan minti biyar a haka Amreesh yace '' do you think I'm a monster?" His voice deeper and quieter fiye da kullum, Salmah ta ɗago idonta ta kalleshi,duk da duhun ɗakin suna iya ganin juna saboda hasken dake fitowa daga A'c she could see how pale he looked maganar ma daƙyar yayi ta, sauke idon ta tayi tana ƙara takurewa her lips moving but she couldn't find the words '' I'm not what they told you Mahee... I'm not a monster...you're hurting me by being scared of me..'' ya faɗa tare da stretching hannun sa ya taɓa ta,ta saki kuka me ƙarfi pressing ɗin lips ɗinsa yayi together yana cigaba da kallon ta his heart aching '' zan iya sauwaƙe maki..I can divorce you idan baki so ki cigaba da zama dani..'' Amreesh ya faɗa wani irin ɗaci na mamaye zuciyar sa har zuwa bakin sa...the words were so bitter in his mouth.. Salmah ta wani ɗago da sauri jin abinda ya faɗa miƙewa Amreesh yayi yana tafiya slowly his heart burning and itching... Har ya kwanta saman gadon yaja ya rufa da blanket
Salmah tayi shiru kalaman shi na maimaituwa a kunnen ta,if he divorces her...No! Bazata taɓa iya rayuwa ba Amreesh ba! She might be scared of him,but she's unwilling to leave him! Ko da take faɗawa Samha su bar gidan cikin fitar hayyaci ne kawai she can't do that!
Miƙewa tayi zuciya cike da tsananin fargaba ta hau gadon ta kwanta bayan Amreesh hugging his waist...jin hannun ta da kuma ɗumin jikinta a nasa yasa ya buɗe idon sa da suke a lumshe kafin slowly ya juyo suna kallon juna runtse idonta Salmah tayi jin ya juyo her body was shaking incessantly Amreesh ya lura da hakan so he kissed her forehead tareda ɗaura hannun shi a waist ɗin ta pulling her closer cikin Muryar rashin lafiya yace '' Bazan taɓa cutar dake ba Mahee...and as long as I live Bazan bari wani ya cutar dake ba!" Slowly ta fara buɗe idon ta kafin ta kalli fuskar shi their gaze met..she saw sincerity a fuskar shi, ya cigaba da faɗin'' You mean the whole world to me,you staying away from me shattered my heart into pieces Mahee...kada ki ƙarayin hakan...Ni ba mugun mutum bane!" Amreesh ya faɗa sounding so vulnerable so sincere,wasu round of tears suka fara bin fuskar ta cuz ta gane cewa she was wrong to have trusted abinda Mariya ta faɗa mata from the beginning batareda tayi bincike ba she was so foolish!" I'm so sorry Reesh!''she voiced out murya na rawa hannun ta gliding on his face tayi nadama, '' I'm happy you're back to me,never leave me again pls'' Amreesh pleaded, jinjina kanta tayi,ya share mata hawaye his hand feeling softer and warmer... Suna kallon juna eyes burning with flame of passion ƙasa tayi da kanta claiming his lips,a passionate kiss was shared between them...
*****
The next day Salmah da Amreesh suka yi zaunen su ciki, Samha ce ta kawo masu break fast tana yima Amreesh ya jiki tana hararar shi ta gefen ido...tsuke fuska Amreesh yayi tareda faɗin '' nadai ji sauƙi ehe.. ya san ranki?" Samha ta saki baki tana kallon shi,yanda yake magana kamar dama farin ciki take rashin lafiyar shi ƙwafa tayi kafin ta juya ta fita, Salmah dake zaune tana serving ɗin abincin da Samha ta kawo ta girgiza kanta, Matsowa Amreesh yayi ya rungume ta closing his eyes words can't describe how happy and relieved he felt to have her back....
Karo sukaci da Ahmad lokacin da ta buɗe ƙofar zata fita daga part ɗin,da sauri tayi saurin Matsawa baya ido waje suna kallon juna cikin ido,da sauri tayi ƙasa da idon ta her heart begun marathons her stomach fluttered with butter flies Ahmad ya kafeta da ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa wai yanzu wannan itace ta ceceshi five years ago kuma yake ta neman ta just to find her under his roof!
Juyawa Samha tayi da sauri ta wuce ɗakin ta without turning back ciki ya ƙarasa wurin su Amreesh when he was giving the permission to enter yashiga
Da rana tareda sauran family members ɗin suka ci abinci, mariya couldn't help but notice sabuwar soyayya da kulawar da Salmah ke ba Amreesh,ba ita kaɗai ba har da sauran mutanen wurin ma suka su da suka san idan tana cin abinci Amreesh comes barin wurin take at 380, maraƙisiyya har takai lomar abinci taji lomar ta laƙe taƙi wucewa saboda tsananin shock itako mariya ko motsi ta kasa wasn't her plan a success? What happened now?
Kallon kallo aka shigayi yet no one spoke, Azeezah ce ta hangi yanda Ahmad ke whispering Abu a kunnen Samha dake zaune kusa dashi and she was blushing har fuskar ta tayi ja,wani irin baƙin ciki taji ya soki zuciyar ta,ƙasa tayi da idon ta abincin ya fita daga ranta gaba ɗaya... Har aka ci aka cinye basu dena mamakin sudden change ɗin da aka samu tsakanin Salmah da Amreesh ba...
Da daddare bayan Salmah ta dawo da plates ɗin da Amreesh ya ci abinci dasu ta wanke zata fita Mariya ta sha gaban ta looking so furious '' me kike yi da Haryanzu baki bar gidan nan ba? Ke ma kina so ki mutune kamar sauran?" Girgiza kanta Salmah tayi