Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 69

93K to 96K   out of 206.1K words

fara cire kaya gabanta,da sauri ta zo zata wuce ya jawo ta,turo baki tayi, ya lakace mata hanci yace '' ba sai ki tayani ba?" Yayi maganar his eyes glistening ya mutse fuska tayi tace '' I'm on my period '' sai da tayi maganar taji wani iri,sakin ta Aliyu yayi yana faɗin 'okay'
Yana sakin ta tayi sauri ta fita kamar zata faɗi tsananin sauri shafa gemun sa Aliyu yayi yana murmushin dashi kaɗai yasan ma'anar sa kafin ya shige bayen.

Salamatu ta isa kitchen da niyar dafa abinci taga har ya dafa taliya, murmushi tayi me kyau slowly ta furta '' romantic Leo'' zuba musu tayi ta ajiye saman dining waiting for him,few minutes later taji foot steps juyawa tayi their eyes met,daga shi sai shorts ba riga da sauri ta ɗauke kanta heart pounding, zaunawa yayi kusa da ita har jikin su na gugar na juya,ga ƙamshin turaren sa da ya cikama ta hanci, slowly in a whisper yace '' waiting for me Mrs Lee?" Ɗan matsawa tayi, feeling a little uncomfortable tace '' let's eat '' Aliyu bai yi ƙoƙarin taɓa ta ba, suka fara cin abincin cikin natsuwa,haɗiye taliyar kawai take badan ta nuna ba,it was half cooked can taji Aliyu na faɗin '' wannan taliya,waih! Garo garo sunan wani abinci'' kwashe wa da dariya Salamatu tayi har sai da ta faɗi ƙasa,Aliyu ya bita da ido,sai da tayi ta gama sannan ta miƙe suna haɗa ido tasake tuntsire wa da dariya ganin Aliyu zai tashi,ta kwasa da gudu ta shige ɗaki


Shima Aliyu yar dariya yayi kafin ya ɗauke plate ɗin ya wanke, ya gyara komai. Parlor ta dawo ya zauna yana kallon wani American film.

Sai wurin ƙarfe goma ya kashe komai ya shigo ɗakin. Tsayawa yayi bakin gadon yana ƙare mata kallo yanda tayi coiling kamar wata macijiya, gyara mata kwanciya ya fara yi ƙafar sa ta zame yayi kanta, his heart beat changed buɗe idanun ta tayi suka haɗa ido, kawai sai yafara unbuttoning ɗin rigar ta,riƙe hannunsa tayi tace '' I'm on my period '' yace in a low voice '' na maki wani abu ne?" Ƙasa tayi da idon ta heart racing can taji yace '' isn't romance allowed lokacin period?" Ita dai bata ce komai ba ganin kamar bata so yasa Aliyu ya sauka daga jikin ta ya gyara mata kwanciya like he intended shima ya kwanta yana faɗin '' let's sleep '' jikin ta yayi sanyi and he was right. She shouldn't stop him, hawar da rabin jikin ta tayi saman nasa tana turo baki a kuma shagwaɓe tace '' nifa ban hanaka ba'' ƙin amsata yayi,tace '' kaji'' nan ma bai yi magana,sai ji yayi hawaye na sauka a ƙirjin sa kafin sheshsheƙar kuka da farko ya ɗauka wasa ne but...

Buɗe idanun sa da suka yi ja yayi, looking at her crying face yace '' Na maki wani abu ne?" Ƙin tankasa tayi itama ya ɗan kalleta for a while kafin ya riƙo fuskar ta kissing her tears yace '' i don't want you to ever feel forced,I want your consent Rosy'' ya yi maganar sincerely ta turo baki tace '' ai bance ka tilasta min ba'' yace '' but u're unwilling '' kwantar da kanta tayi saman ƙirjin sa in a low voice tace '' kunya nake ji fah, and it's not right to look shameless '' jinjina kansa yayi ta cigaba da faɗin '' Ni ban taɓa yin wannan ba,how is it possible in saki jiki idan anayi?" Jin tace bata taɓa yi ba ba ƙaramin daɗi Aliyu yaji ba, she's a virgin and he'll be her first, yana shafa bayan ta yace '' baki taɓa me ba?" Ɗago kanta tayi daga ƙirjinsa tayi masa wani kallo sai kuma ta turo baki taƙi magana
'' uhm?" He probed cike da jin kunya tace '' Leo kafa sani '' yace '' ban sani ba Mrs Leo a faɗa min '' maƙe kafaɗa tayi yayi yar ƙaramar dariya holding her waist ya ɗago fuskar ta, they stared at each other with burning passion kafin tayi ƙasa da kanta kissing him slowly making sure he felt every bit of it, while hannunta played on his chest,tun anayi slowly har yazama intense.....

Washegari Aliyu ne sanye da suit brown color da suka mugun yi masa kyau,his curly hair yasha gyara, sai ƙamshi mai daɗi yake ta zubawa Salamatu daga gefen sa maƙalƙale dashi kamar zatay kuka, she didn't want him to go. Tun jiya ya samu email daga chan group of company zai yi resuming aikin he's documents have already been processed maybe a little interview.Murmushi Aliyu yayi bayan sun kawo bakin ƙofa yayi hugging ɗinta pecking her on the forehead yace '' i will be back soon '' yayi maganar yana raba jikin su badan taso ba ta sake sa,bye bye yayi mata *reluctantly*
Itama tayi masa bye.drivern da aka kawo ma Aliyu ne ya fito bowing respectfully yace '' good morning Sir, I'm your new driver Xun Lang '' yayi maganar bowing respectfully murmushi mai kyau Aliyu yayi jin sunan drivern sai ya jinjina kansa yace simply'' I'm Aliyu '' ya faɗin hakan yana zama cikin motar bayan driver shima ya zauna, jinjina kansa Lang yayi ya ja motar suka tafi,tun kafin ranar tayi nisa Aliyu ya ƙagu ya koma gida. 40minutes drive suka iso Chan group of company,Saida akayi inspecting ɗinsu daga bakin gate kafin aka bari suka isa ciki, Lang yayi parking yazo ya buɗe ma Aliyu ƙofar ya fito bowing respectfully yace '' see you later Sir '' jinjina kansa Aliyu yayi yana mamakin su basu gajiya da bowing every now and then?

Cike da natsuwa ya shiga ƙaton company yana yaba kyawun wurin da girma da tsarin sa. Confidently Aliyu ke tafiya fuskar sa ba murmushi amma a sake,gawani kwarjini da yake dashi, tunda ya shigo ma'aikatan wurin suka tsaya da abunda suke both male and female, kafin su fara ƙus ƙus asking who he was the females blushing intensely especially idan Aliyu ya kalle su.

'' oh my God who is he?"

'' is he some model?"

'' wow I have never seen a handsome guy like him ''

'' wait is he from America?"

'' hell I never knew black ppl are this handsome, I'm officially a fan''

Waɗannan sune maganganun da yan mata keyi and much more,su kuma mazan wasu na yabawa wasu na kushewa

Aliyu da ya isa reception sai magana yake da receptionist Amma ina ta kafe sa da ido kumatun ta sunyi ja,she was blushing for the last time Aliyu yace '' Excuse me miss '' firgit ta dawo a ɗan gigice sai bowing take tana faɗin sorry. Jinjina kansa Aliyu yayi kafin ya faɗa Mata abin da ya kawo shi. Wayar ta tayi dialing sai ga wata mata sanye da farar riga da skirt tazo magana receptionist tayi mata tana nuna mata Aliyu, jinjina kanta tayi turning to Aliyu tace follow me.




















Chapter thirty five:Chao miao





Wani office ta nufa yana biye da ita,ƙwanƙwasa wa tayi aka bata izni sannan ta tura kofar ta shiga Aliyu biye da ita, wani mutum ne da zai kai atleast 55 years of age zaune saman kujerar da laptop gaban sa, bowing respectfully tace '' Mr Ma, he is here '' ɗago kansa mutumin da aka kira mr ma yayi,kansa rabi soisaye ba gashi, fuskar sa a murtuke yana kallon Aliyu, alama yayi ma ma'aikaciyar da ta tafi, ƙara rusunawa tayi one last time sannan ta fita. Aliyu dake kalle kallen office ɗin da yayi masa kyau yaji Muryar Mr Ma na faɗin '' kalle kalle kazo yi ko aiki?'' yayi maganar with a hardened voice like he had a personal grudges against Aliyu. Aliyu felt a bit embarrassed yayi ƙasa da kanshi ya zo ya zauna a kujerar dake fuskantar ta mutumin, ya gaida shi cike da girma mawa, mutumin sai kallon Aliyu yake kamar so yake ya tsoratar da Aliyu, Aliyu na ya kafe mutumin da ido,the 2 of them looked for a moment kamar suna game ɗin eye contact babu cikin su wanda keda niyar cire idon sa. Mr Ma sai ƙara tsuke fuska yake yana ƙara ƙanƙantar da idanunsa,Aliyu kuma looked relaxed almost amused da abinda Wannan tsohon yake

After a while, Mr Ma ya sauke ajiyar zuciya ya kauda idanun sa ganin Aliyu bazai cire nasa ba yana ƙunƙuni da Chinese sai kuma ya juyo a fusace ya daki table ɗin '' be respectful young man '' yayi maganar yana nuna Aliyu yacigaba da faɗin '' A China idan babba na kallon ƙarami,u have to lower ur gaze young man!!!!" Aliyu was stunned,ya ga dai tunda ya shigo bai yi wani abun rashin ɗa'a ba ko? Amma ganin tsohon sai balbala masifa yake har fuskar sa tayi ja yasa Aliyu faɗin '' pardon zan kiyaye next time '' sai sannan tsohon ya dena balbalin bala'i. Tsohon ya sauke ajiyar zuciya ya fara yima Aliyu magana calmly kamar bashi bane yayi ta masifa just now. After a while yafara tambayar Aliyu questions kafin daga bisani ya ƙara kiran yarinyar da ta kawo shi ta tafi dashi. Wurin ma'aikatan nan na ɗazu suka koma, attention ɗin mutanen wurin yarinyar ta kira, '' Attention everyone '' kowa ya juyo suna kallon ta,more like suna kallon Aliyu dake kallon su kamar yana karantar su,tace '' Muna da sabon ma'aikaci tare da mu,hope you all will welcome him and guide over what he doesn't know " tayi maganar tana kallon overly excited faces of the female workers, tafi sukayi dukan su kafin ta matsa giving Aliyu a chance to introduce himself, ɗan matsowa Aliyu yayi fuskar sa sake yace with a deep voice '' Hi my coworkers,suna na Aliyu Sabo, ina fatan dukan mu zamuyi aiki cikin haɗin kai to take this company to a new heights thank you '' wurin ya kaure da tafi fiye da farko, matan suna ƙara macewa akan Aliyu. Wurin zaman sa yarinyar ta nuna masa before she left, receptionist daga inda take sai satar kallon Aliyu take da gaske ya tafi da imanin ta. Goge wurin zaman sa Aliyu yayi,yayi yar addu'a ya zauna sannan ya fara aiki da files ɗin da aka ajiye masa akan table ɗinsa, the girls were stealing glances at him suna giggling yanda yayi focusing akan aikin sa there's this oozing *Aura* of sexiness daya ƙara masa kyau da kwarjini.

Bayan an tashi break mutane mata da maza sai zuwa suke offering to take him to the cafeteria, wasu na introducing kansu especially mata,it was a long day for Aliyu.....

Tun lokacin da Aliyu ya tafi taji duk gidan ya ishe ta yayi mata faɗi, ƙasa ta sauko saye da wata riga marar nauyi milk color, TV ta kunna ta fara canja channels kafin ta kamo wani channel da ake taekwondo Nan da nan taji tana so ta koya zama tayi da kyau ta bada hankali tana haddace each and every move.

The day went by slowly,
Da karfe 08:00 Salamatu na zaune tarasa abin da ke mata daɗi,ta kira Aliyu tun tuni yace yana zuwa but he's still not back, har ta kusa ta fara kuka sai gashi ya turo ƙofa ya shigo,ido suka haɗa ta ɗauke nata shiko sai kallon ta yake kafin ya ƙaraso ciki bayan ya cire takalmin sa daidai ita ya ranƙwafa yace '' Rosy'' miƙe wa tayi ta nufi stairs idanun ta cike da hawaye saurin riƙo ta yayi sai ƙoƙarin ƙwace kanta take,ganin ta kasa kawai sai ta fashe da kuka, tsare fuskar ta Aliyu yayi da ido kafin slowly ya rungume ta '' I'm so sorry '' ya faɗa after a while sai kuma ya raba jikin su looking at her face yana share mata hawaye yace '' kiyi haƙuri,next time i will be back early uhm'' ita dai har lokacin kuka take,and honestly haushin sa take ji. Ɗaukar ta yayi suka tafi ɗakin tare, ya ajiye ta at the edge of the bed ya fara cire kayan sa, ƙasa tayi da kanta, tana turo baki. Bayan ya cire kayan sa duka yazo inda take ya ɗaga ta ya fara cire mata nata itama,riƙe hannunsa tayi tana hararar sa, shi kuma ya marairaice mata fuska '' I missed you so much '' ya faɗa yana turo baki kamar ƙaramin Yaro,ta jaye jikin ta daga nasa tana faɗin "Oh really?" *Sarcastically*
Rungume ta ta baya Aliyu yayi yana faɗin '' Yes, tunda na tafi ke kaɗai make tunani, when i was given a file to work on nayi nisa cikin tunanin ki, lokacin da na kalli laptop ɗin dana ke aiki akai, kinsa mai nagani?" Yayi tambayar yana ci gaba da raba ta da kayan ta cike da dabara,girgiza kanta Salamatu tayi ,ya juyi da ita suna facing juna yace '' for the past hour and half sunan ki nake ta rubutawa!" Ƙyalƙyace wa da dariya Salamatu tayi ganin yanda ya wani ya mutse fuska, shima murmushi yayi though it was foolish,abinda yayi kenan da gaske dena dariya Salamatu tayi tace '' da gaske?" Jinjina kansa yayi pitifully sannan yace '' shine yasa na daɗe'' ajiyar zuciya salamatu ta sauke feeling a bit better,koda ya kalli kanta she found that she was just wearing her br*h, shit!!! Yaushe yayi mata wayau har haka, kallon Aliyu take da ke murmushi innocently kafin tayi wani yunƙuri har ya saɓe ta sai toilet.....

Da ƙarfe 9:00 suka fito cikin pajamas kala ɗaya dining suka nufa salamatu ta zuba musu wani abincin Chinese da ta koya because she was bored,kallon Abincin Aliyu yake ba ƙyafta wa, abun kamar ƙazanta, the look on his face amused her.

Ya ɗago kansa yace '' what's is this?'' yayi maganar yana yatsine fuska Salamatu ta zauna kusa dashi ta ɗauki cokali ta ɗebi abincin takai bakin sa tana faɗin ''Châw miàn'' waro ido Aliyu yayi ganin abinda take bashi, riƙe hannunta yayi yace'' we are Nigerians not Chinese,bazan iya cin wannan ƙazan...'' galala Salamatu tayi da ido jin abin da Aliyu ke faɗa, he was depreciating her effort kusan awa biyu masu kyau ta kwashe tana dafa wannan just for him and now this...? Saukar hawayen ta a hannunsa ya sa ya ɗago ya kalle ta, tears were spilling kamar broken dam, cikin Muryar kuka tace '' awa biyu nayi a kitchen just for you '' tana gama faɗar hakan ta tashi zata tafi,saurin riko ta yayi ya zaunar kusa dashi yana goge mata hawaye yace '' zauna zanci'' murmushi tayi ta fara ɗibar Abincin yana mai wa bakin sa, loma gudan farko yayi wuƙi wuƙi da ido, ji yake abincin da yaci na ƙoƙarin dawo wa, ruwa ya jawo yasha, yana Faman zufa, Salamatu wasn't listening sai ɗura masa take shi ko sai zufa yake yana ƙarawa sai da ya cinye tas. Tayi murmushi tace '' yayi daɗi?" Jinjina kansa Aliyu yayi with a fake smile, the food was spicy kuma yayi gishiri chaii! Shikam yaga ta kanshi.

Kwashe komai tayi ta wanke ta dawo parlor inda yake sukayi cuddling ɗin juna suna kallon wani Chinese series Nan take faɗamasa ita Bama taci abincin ba she couldn't it looked some how in her eyes,xaro ido Aliyu yayi yace '' shine kika sa naci har da kuka?" Dariya tayi tace '' i made it for you''.Yace '' then I should be rewarded right?" Batasan mai yake nufi ba sai jitayi subtly ya fara romancing ɗin ta, tun tana gane series ɗin harta zo bata ganewa sai da ya ririta ta sannan ya wuce da ita ɗaki.


Kwanaki sun cigaba da tafiya Aliyu ya zama sanannen ma'aikaci a wurin aikin su,yan mata sai bin shi suke shidai he made it clear yana da mata but they weren't ready to leave him, akwai wata mai suna xue yao, ita ko ina yake she always made excuses to be with him, sai taita taɓa shi duk da ya nuna bai son haka.

Tsakanin sa da Salamatu kuma wani irin so da ƙauna mai tsayawa arai suke ma juna however,har yanzu tsakanin su romance ne kawai it makes her wonder ko baida lafiya ne? Bawai ta ƙagu bane,a'a kawai dai tasan in every functioning marriage there has to be intimacy duk da suna yi but it wasn't to the core right?.

Ta damu da wannan sosai and she had no one to talk to, a ɗayan ɓangaren kuma ta maida hankali tana koyon martial arts har ta ɗan Iya basics sannan tana koyon Chinese cuisines har ta ƙware ma, kuma tana yin abincin yan Nigeria. Aside from that ita da Aliyu basu manta da asalin su ba,from time to time he takes her out kuma da shigar su ta yan Nigeria suke fita siya kallon su.

Cikin wata shida Aliyu ya gina masu sabon gida wanda nasu ne na kansu, ya zuba komai da zasu buƙata amma ita salamatu bata sani ba,
Birthday ɗin salamatu Aliyu yayi inviting ɗin coworkers ɗinsa suka zo ayi celebrating ɗin birthday ɗin,duk da ita Salamatu bata sani ba, ranar yini tayi tana baƙin ciki because it was her birthday yet Aliyu bai tuna ba! She hates him!! Tana nan zaune daga ita sai wando bum short dakuma wata farar riga shara shata,gashin ta yayi wani iri, idanun ta sunyi ja, zuciyar tana tafarfasa idan Aliyu ya dawo zai gane dan ko abinci bata ma dafa ba.
Da ƙarfe 07:30 tana zaune bayan tayi wanka tasa wata doguwar rigar Atamfa ta gama sallah, kicin kicin tayi da fuska tana daddanna wayar ta transferring the aggression to the phone kira ya shigo wayar ta,it was an unknown number kamar zata share sai kuma dai ta ɗauka, '' Hello Is this Mrs Aliyu?" Ɗayan ɓangaren ya faɗa duk da dai Salamatu batasan ko waye ba,sai da hankalin ta yaɗan tashi jin abinda ake faɗa, tace'' eh, nice any problem?" Daga ɗayan ɓangaren yace '' pls come to Qingwangfu road, street no5 house no 40, your husband...'' wani irin dum zuciyar Salamatu tayi kafin mutumin ya idasa maganar sa ta katse sa da faɗin

32 / 69